Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Amanarcool · SAUTIN KARSHE

A falo ya tarar da Uncle zaune tare da Mammy, sai Faruk da Zahra dake zaune a kusa da shi sun saka shi a tsakiya. Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Sudais, Uncle ma murmushin yake yi, "Oyoyo my Uncle, kai ne ka zo ba'a kira ni ba? Yanzu da Allah bai kawo ni ba shikenan sai ka tafi ba tare da na ganka ba" ya yi maganar yana yi wa Zahra alamar ta ɗaga daga nan. Tashi ta yi ta koma kusa da Mammy ta zauna, Uncle ya yi dariya yana faɗin "Ni na isa na zo gidan har na wuce ba tare da naga shalelena ba? Yanzu nan na shigo, kuma ina da niyar zan kira ka" zama Sudais ya yi ya ce "Yawwa Uncle ɗina, yau na yi busy ne da yawa ban samu kiranka ba. Ya gida? Ya al'amurra?".

Uncle ya ce "Alhamdulillah, ya naka al'amurran ina fatan dai babu wata matsala ko?". 

"Alhamdulillah Uncle, yau dai mun kai ƙarshe da mutanen da na yi maka zancen su, za su gudanar da harkar gine-ginen gidaje ne a ƙarƙashin haɗin gwiwar kamfaninmu". 

"Ah to ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora, amma ka saka ido sosai, ka kula da kyau domin ganin an gudanar da aikin cikin tsari". "To shikenan Uncle in sha Allah zan kula". 

"Sannu mai Uncle, saboda ka ga Uncle mu gabaɗaya ka manta da mu? Tukuna ma a kan me za ka kori ƴata a guri kai ka zauna? Ina ce dai ko ita Uncle ɗinta ne". Mammy ta yi maganar tana kallon Sudais, murmushi Sudais ya yi ya ce "Mammy wani lokaci kina da son jan zance". 

"Kai kuma ba ka son a ja zancen ko?". 

"Uncle ina Aunty Ilham? Tana lafiya?". Zahra ta tambaya tana kallonsa.

Uncle ya ce "Tana gida, lafiyarta ƙalau. Yanzu ma a kan maganarta ne na zo". 

"To Allah Uncle Allah ya sa zancen saka ranar aurenta ne za a yi da Ya Sudais?" Ta faɗa tana murmushi. A fakaice Sudais ya wurgawa Zahra wani irin kallon da sai da hantar cikinta ta kaɗa, irin kallon nan na idan na kama sai kin gane ba ki da wayo. Uncle ya ce "Eh a kan zancen aurenta ne, sai da ba da Sudais ba, Sudais ai Yayanta ne". Shiru Zahra ta yi ba ta sake magana ba, Mammy ta ce "Ai ko yana Yayanta akwai aure tsakaninsu, sai dai in Allah bai ƙaddara shi ne mijinta ba". 

"Eh haka ne, yanzu dai mu bar wannan maganar" cewar Uncle saboda ya fuskanci Sudais baya son zancen, shi kuma duk abin da Sudais baya so to ba zai yi masa dole a kansa ba, ya ɗora da faɗin "Kun san akwai masu zuwa gurin Ilham, to duk a cikinsu hankalina yafi kwanciya da Saddik ɗan gidan Alhaji Bashir aminina, last week mun yi magana da Bashir to abubuwa ne suka sha kaina, ina ta so in zo mu tattauna da ku ban samu time ba sai yanzu". 

"Uncle Aunty Zahran ta amince da Saddik ɗin?" Zahra ta tambaya fuskarta ba yabo ba fallasa. "Ke, idan na sake jin bakinki a gurin nan sai na yi mugun saɓa miki, manya na magana kina saka musu baki". Sudais ya yi maganar fuskarsa a ɗaure. 

Dafa kafaɗarsa Uncle ya yi, ya ce "A yi mata haƙuri dai mutumena" sannan ya mayar da kallonsa ga Zahra ya ce "Eh ta amince, kafin na zo muku da zancen sai da na tabbatar da ta amince. Yanzu kawai amincewarku nake nema, idan kun bayar da goyon baya a kan wannan maganar sai a bashi damar zuwa wajenta. Duk da bana son a ɗauki dogon lokaci ba a yi auren ba". 

Faruk ya yi gyaran murya ya dubi Sudais ya ce "Am zan iya yin magana?". 

Daga Mammy har Uncle dariya suka yi, Sudais kuwa ya kawar da fuska yana murmushin gefen baki, Mammy ta ce "Yi maganarka ai kai namiji ne ba mace ba, balle a hana ka yin magana". Faruk ya ce "Uncle da farko da ka zo da zancen nan na ji wani iri a raina, amma da na ji wanda za ta aura sai na ji hankalina ya kwanta, saboda na san Saddik mutumen kirki ne, gashi da haƙuri, kuma yana da girmama na gaba da shi. Ni dai a nawa ɓangaren babu damuwa, Ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairinsa". Uncle ya ce "Ma sha Allah, kai fa Sudais me ye ra'ayinka?". Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Yaron yana da nutsuwa, Allah ya nuna mana lokaci musha biki" daga haka ya yi shiru. "Ke fa Aunty A'sha?" Uncle ya yi maganar cikin sigar tsokana, Mammy ta ce "Nima na amince, Allah ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi" cikin jin daɗin amincewar da suka yi Uncle ya ce "Amin ya hayyu ya ƙayyum, kema Zahra ya kamata ki fito da mijin nan sai a haɗa auren ku a yi tare, tun da kin kammala karatunki". Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai ƙasa, nan suka ci gaba da hira, sai dai Sudais shiru ya yi yana saurarensu. Uncle ya daɗe a gidan kafin ya yi musu sallama ya tafi.

*****

Durƙushe take a gabansa ta riƙe ƙafarsa ɗaya tana kuka mai taɓa zuciya. Duk da cewar ba ta da wani kuzura a jikinta, amma hakan bai hana ta riƙe ƙafarsa ba da dukkanin ƙarfinta. Cikin muryarta da ta dusashe saboda tsabar kuka, ta ce "Ina haɗa ka da Allah da Manzonsa, ka yi haƙuri ka da ku cutar da yaron nan, ka ji tsoron Allah, ka tuna bayan wannan rayuwar akwai wata da zamu yi a gaba, ka tuna da tsayuwar da zamu yi a gaban mahaliccin mu. Yanzu me ye ribarka idan ka salwantar da rayuwar wannan yaron? Ka na da amsar da za ka bawa Ubangiji ranar gobe ƙiyama a kan cutar da yaron da bai da haƙƙin kowa a kansa? Don Allah ka yi haƙuri ka da ka cutar da shi, ni na yarda na karɓi ƙaddarar da ta zo mini da hannu bibbiyu, kuma na san Allahna yana tare da ni, yana sane da duk halin da nake ciki, kuma in sha Allah zai kawo mini ɗauki, amma wannan yaron ba zan iya jure ganin an cutar da shi ba". Ta kai ƙarshen maganar tana wani irin gunjin kukan mai sosa rai.

"Oga wai me ya sa za ka tsaya kana sauraren wannan yarinyar ne?". Cewar wani gabjejen mutum da yake tsaye a cikin ɗakin. Alhaji ya ɗaga masa hannu yana murmushin mugunta ya ce "Rabu da ita Zaki, na san abin da take buƙata, kuma yanzu za ta samu, karɓi yaron nan, fita da shi ka miƙawa Cinedu shi, zan zo daga baya". 

Ba tare da Zaki ya sake magana ba ya karɓi yaron ya fita da shi. Tana ganin an fita da yaron ta kurma wani uban ihu, jikinta na wata irin karkarwa take faɗin "Don Allah kar ku yi masa komai ku dawo da shi, ni ku kashe ni na yarda, amma shi kar ku taɓa shi". Wata uwar dariya Alhaji Sango ya ɓarka, babu ɗigon imani a zuciyarsa ya ja ta zuwa saman gado, nan ya farmata da tumurmusa, iya ƙarfinsa yake sauke mata ba tare da ya yi la'akari da cewar ita yarinya ce ba. Tun tana ihun neman agaji har ta gaji ta koma fitar da numfashi da ƙyar, ya daɗe yana gana mata azaba kafin ya bar ta, sauka ya yi daga saman gadon ya saka kayansa ya fita ya bar ta nan kwance tana fitar da numfashi da ƙyar. 

****

"Halima kina da sauran maganin ciwon kan nan da aka baki asibiti ki bani kaina ne yake yi mini ciwo?". 

Halima ta ce "Ma'un Inna yau kuma ko Aunty ba zan samu ba? Aka kira sunana haka gatsau?". 

Ma'u ta ce "Don Allah ba na son dogon turanci na ce miki kaina ke ciwo, idan akwai shi ki bani kawai". Halima ta ce ''Akwai sauran ɗaya bari na ɗakko miki" ɗaki ta shiga ta ɗauko maganin ta ba ta, Ma'u ta karɓa ta ce "Aunty Halima don Allah ɗebo mini ruwa?" "Uhum" kawai Halima ta ce ta je ta ɗebo mata ruwan ta kawo, ɓalla maganin ta yi ta saka a bakinta ta kora da ruwa, tana nan zaune kusan minti talatin da shan maganin ta ji ciwon kan ya tsananta, dafe kanta ta yi, tana girgiza jiki, ganin hakan ya sa Halima da sauri ta ce "Subhanallah! Ma'u ba dai ciwon kan ba ne?". Ai tana rufe bakinta Ma'u ta fara kwarara amai baƙi ƙirin mai shegen ƙarni, tun tana iya yunƙuri har sai da ta kasa yunƙurawa, gabaɗaya sai da ta amayar da duk abin da yake cikinta sannan ta samu sawaba, tana gama yin aman ta miƙe da ƙyar ta tashi tsaye, sai dai tana tashi ta kurma wani uban ihu ta zube a gurin. Aliyu da yake soron gidan jin ihun Ma'u ya sa da sauri ya ƙaraso cikin gidan. Halima ya gani duƙe tana girgiza ta. "Me ya sa meta?" Ya tambaya yana kallonta, "Kanta ne yake ciwo, shi ne na ba ta sauran maganin da nake da shi, to tana shan maganin ba da jimawa ba ta fara amai, tana gamawa kuma ta faɗi". 

"Ita ta yi wannan aman?". Halima ta gyaɗa masa kai alamar eh. Ya ce "Ɗebo mini ruwa a kofi". Tashi ta yi ta ɗebo masa ruwan, karɓa ya yi, ya kafe kofin a bakinsa yana addu'a yana tofawa a ciki, bayan ya gama ne, ya ɗago da kan Ma'u ya buɗa bakinta ya kwalala mata ruwan a ciki, sauran kuma ya shafe mata fuskarta da su, tari ta fara yi, jikinta ya ɗauki karkarwa, Aliyu ya ce "Ya isa haka tashi". 

A hankali Ma'u ta buɗe idonta ta sauke su a kan fuskarsa, "Ina yake yi miki ciwo yanzu?". Ya tambaya yana kallonta.

Muryarta ba ta fita sosai ta ce "Babu". "To tashi wuce ciki ki kwanta ki huta" tashi ta yi cikinta ba ƙwari ta shiga ɗaki, kwanciya ta yi tana tunanin to me ya faru ne? Ita dai ta san ta karɓi magani a gurin Aunty Halima ta sha, daga nan ba ta sake sanin me yake faruwa ba. Aliyu bayan Ma'u ta shiga ɗaki bin aman ya yi da kallo, sannan ya ce "Halima ki gyara gurin nan. Ni zan koma asibiti, ina tunanin gobe za a bamu sallama". 

Halima ta ce "Ma sha Allah, to Allah ya kai mana rai" ya amsa da "Amin" tare da barin gidan.

*****

Yana zaune saman kujera ya baje, sanyi AC na ratsa shi, turo ƙofar falon a ka yi tare da yin sallama aka shigo, ɗaga kansa ya yi yana kallon wanda ya shigo ɗin. Zama ya yi yana faɗin "Sannu da hutawa Alhaji". 

"Yawwa Cinedu, ina fatan dai zuwa yanzu komai ya kammala? An daɗe da aika yaron nan inda aka saba aika sauran yaran?". 

Fuska ba annuri Cinedu ya ce "Alhaji akwai matsala fa. Yaron nan fa ya ba da matsala. Duk lokacin da muka yi ƙoƙarin nuna jininsa sai a nuna mana akwai matsala jininsa yana da mugun dafin da idan aka yi amfani da shi zai iya ruguza komai". Zaro ido Alhaji Sango ya yi, ya ce "Kan bala'i, wannan wane irin yaro ne haka? Me ye a cikin jininsa da har ya bamu matsala?". Cinedu ya ce "To muma dai abin ya ɗaure mana da kai, tun lokacin da muke yi wannan harkar bamu taɓa samun matsala irin wannan ba sai yanzu". 

Ajiyar zuciya Sango ya sauke ya ce "Kuna ji, kar a taɓa yaron, ku dawo da shi gurin yarinyar nan, shekara da shekaru muna yin wannan aikin ba tare da mun samu matsala ba, don haka ko a yanzu ba zamu same ta ba, a rabu da shi a nemo wani yaron, ni zan san yadda zan yi da shi, ina son ku ba Zaki shi ya mayar da shi gurin yarinyar nan yanzu". 

Cinedu ya ce "To shikenan an gama Alhaji, faɗa taka cikawa tamu, na barka lafiya" . Daga haka ya yi masa sallama ya fita. 

Yana fita Sango ya ce "Ka ji mini ja'irin yaro, to zan yi maganinku daga kai har ita ɗin, bari dai in gama moreta".


Amanarcool
***




Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol