Free chapter · Read without an account
An Unforgettable Encounter
Page 2:
Da wani irin mamaki ya tsaya bin motar da kallo ba tare da ya yi yunƙurin yin wani abu ba saboda tsananin mamakin tsantsar rashin kunya irin na yarinyar.
Dogo ne baƙi amma irin baƙin nan ne da ake ma laƙani da black beauty, yadda kasan baƙin balarabe haka ya ke. Ya na da manyan idanu farare tas da su kamar ba sa ganin rana. Shape ɗin fuskarsa gwanin sha'awa wanda kai tsaye ba za ka ka kalar shape face ɗin ba wanda ya ke ɗauke da dogon hanci, gashin kanshi a kwance yake kamar na larabawa.
Shi kansa gaba ɗayansa da larabawa ya ke yanayi sa dai shi jikinsa a murɗe ya ke haɗe da faffadan ƙirji, fuskar nan a daure ba ko alamar dariya a tattare da shi, amma da ganinsa za ka ga alamar nutsuwa tattare da shi ba irin masu rawan kan nan bane......
Tsabae ɓacin rai ma, rasa abin yi ya yi. Saboda tun da ya ke babu macen da ta taɓa faɗa mishi magana irin wannan fitsararriyar yarinyar. Yana tsaye a wajen wani ya nufoshi yana faɗin "Ya na ganka haka ranka a ɓace? wa ya ɓa ta maka rai kuma yanzu?"
Ba tare da ya bashi amsa ba ya yi mishi nuni da wayarsa da ke yashe a ƙasa. Da mamaki ya durƙusa ya tattara wayar ya na ƙara tambayar shi garin ya hakan ta faru amma ƙala bai ce mishi ba sim card ɗinsa kawai ya amsa daga hannunsa wanda ga dukkan alamu sun nuna cewa abokinsa ne.
Zagayawa ya shiga mota ya zauna wajen zaman mai zaman banza abokin na sa kuma ya shiga mazaunin driver ya tada motar suka fi ce daga wajen. Sake je fo masa tambayar abokin ya yi ya ce, "Wai ya ina ta maka magana za ka mayar da ni ɗan iska ne?" Abokin ya faɗa a ɗan fusace. Amma har yanzu ci kanka bai ce mishi ba.
Hakan ya sa shi ma ya tattara shi ya watsar saboda ya san ba zai tanka ɗin bane. Mayar da hankalinsa ya yi kan tukin ya ci gaba da tuki hankali kwance, shi kuma uban gayyan ya lafe kan kujera idonshi a lumshe har lokacin ya na kara hasaso abin da ya faru face ɗinta ne kawai ke yi masa gizo a ido. Da ƙarfi ya furta,
"No i can't let's her go free i must teach her a lesson." Da sauri abokin ya taka burki ya juya ya na kallonsa da mamaki kamar kunnensa ne bai jiyo masa daidai ba, idan kuwa daidai ya jiyo masa to tabbas kuwa maganar mace abokinsa ya ke yi, tabbas dole ya ambace ranar yau da blessed day. Ta ka burkin ne ya yi sanadiyar buɗe idon hamshaƙin.
Harara ya watsawa abokin haɗe da faɗin, "Sadeeq halan zuƙe zuƙe ka fara kake neman hallaka ni a kan titi halan."
Idonsa a kan shi yaƙi ko ƙyaftawa ya ce, "Wait, tsaya guy kai da wa? Kamar fa maganar mace na ji ka na yi?"
Banzan da shi ya yi tamƙar ba shi ya gama magana yanzu ba. Nan ta ke Sadeeq ya fashe da dariya ya ce "Really i can smell something fishy, ka ce kogin love ka faɗa. No wonder shiyasa mana na ganka duk ka birkice, wayyo abun ka da sabon shiga."
Sai kuma ya ƙara kwashewa da dariyar ƙular da mutum ya na faɗin,
"Wow ina zan ga wannan beb din mai tarin sa'a a cikin mata, wanda ta samu damar tafiya da My G cikin ruwan sanyi haka. Gaskiya da na ganta dole na yi mata kyauta ta musamman. Finally my FADEEL is in love nan take FADEEL ya ɗago kai ya na watsa mishi wani irin bahagon harara haɗe da jan tsaki ya ce "You insane Sadeeq, ka na buƙatar ganin Psychiatrist. Idan za ka tada mota mu tafi to idan kuma ba za ka yi ba bani key ɗin motata mtsewww." Ya ƙarasa maganar ya na jan tsaki da shi kanshi bai san na meye bane........
********
Sai da ta ga sun yi nisa sannan ta sauke ajiyar zuciya tana gode wa Allah da ya sa ta tsallake hannun wannan mai ƙirar Samudawan in ji ta. Harararta Asmy ta yi ta ce, "Wallahi na so da ma ya fasa wannan bakin na ki da bai da linzami at all, sai shegen takalo faɗa amma babu ƙarfin kare kai mtseww***
Ai ni ina ji a jikina ma kin haɗu da daidai ke wallahi dan wannan da gani ba irin wanda ki saba tsokanowa bane ki sha ba ƙila daga kan wannan kin daina wannan shegen tsiwar banza matsoraciya kawai."
Ci kanki Fa'eezah ba ta ce mata sai ma idonta da ta maida kan titi ta na tuƙinta cikin nutsuwa amma kuma zuciyarta ba'a natse ya ke ba, saboda ita kanta a tsorace ta ke domin ba ta taɓa ganin mai gwarjininsa ba kawai mazewa ta yi don kar ya harbo logonta.
Ko me Asmy ta tuna kuma? Sai ta kwashe da dariya ta na faɗin, "Ni kam zan so ganin yadda za'a kwashe a next episode Allah ya sa ina wajen don ga dukkan alamu yanzu aka fara series ɗin." Ta ƙarasa maganar da dariyar mugunta ganin yadda Fa'eezar duk ta bi ta tsure amma shegen tsiwarta da ƙarfin hali ba zai bari ta nuna hakan a fili ba.
Sai a sannan Fa'eezah ta ɗago daradaran idanunta haɗe da watsa wa Asmy Harara ta ce, "Aniyarki ta bi ki ba abin da zai ƙara haɗani da wannan basamudan." dai-dai tana ƙarasowa ƙofar gidansu Asmy. Asmy ta ƙumshe dariya ta ce, "Malama sauke ni a nan ni gida zan shiga."
Ba tare da ta ce komai ba ta yi parking Asmy ta sauka tare da ɗaukar na ta ledar da su ka yi siyayya. Ta ce, "Alright Mrs. Basamude bye." ta faɗa ta na dariya. Tsaki Fa'eezah ta yi tare da figar motarta ta ƙarasa gate ɗin gidansu saboda ba su da tazara da su Asmy ɗin.
Horn ta yi mai gadi ya zo da sauri ya buɗe mata gate ya na mata sannu da zuwa ta amsa masa da ɗan murmushi a fuska kasancewarta mai mutunta ma'aikatan gidansu don duk da kuɗin mahaifinta bai sa ta zama mai girman kai da wulaƙanta na ƙasa da ita ba. Wannan dalili ya saka su ma ma'aikatan gidan su ke sonta haɗe da ganin girmanta duk da kasancewarta ƙarama, dan dududu ba za ta wuce 19yrs ba yanzu.
Tun kafin ta gama parking ta yi arba da motar da ke pake a gefenta da mamaki ta bi motar da kallo ta na mamaki baƙi su ka yi ne haka a gidan tun da ta san wannan ba motar gidansu Hajiya bane (Kakarta kenan Hajiya Maimuna).
Tun a entrance ɗin gidan ta fara cire kimono ɗin da ke jikinta ta riƙo shi a hannu ya rage daga ita sai camisole da ke cikin kayan mai hannun armless wanda ya ba wa sirrin jikinta damar bayyana gaba ɗaya. Wannan dama habbit ɗinta ne fara cire kaya daga entrance kafin ta karaso cikin main parlor. Tun daga nan ta fara ƙwalla kiran, “Mommyyyy where are you i'm bac...” Maganar ce tw maƙale mata a bakinta sakamakon tozali da ta yi da wani a hikimce a parlournsu ya kafeta da ido kamar tsohon maye.
Shi kuwa tun kafin ta ƙaraso main parlour ɗin ya ɗago da niyyar kai cup ɗin juice bakinsa idonsa ya sauka a kan ƙirjinta da camisole ɗin ya bayyanar da surarta gaba ɗaya. Kasa ɗauke kanshi ya yi daga gareta da ganin kallon da ya ke bin ta dashi kasan cewa eh wannan ɗan hannu ne a harkar mata.
Muryar Hajiya Shafah ( Mommy wato matar daddyn Fa'eezah kenan ) ya ankarar dashi daga suman wucin gadin da ya tafi. Saurin ɗauke kanshi ya yi ya na basarwa kamar bai san meke faruwa ba. Mommy ta ƙaraso ta rungumota ta ce, “Daughter har kin dawo? ina sama na ji muryarki, hope kin dawo lafiya?” Fa'eezah ta ƙara narkewa a jikinta ta na ƙara shagwaɓe fuska kafin tace, “ Lafiya qalau na dawo Mommyna, sai dai gajiyar tuƙi gashi Asmy taƙi yarda ta karɓa tuƙin daga hannuna.” Ta ƙarasa maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.
Mommy ta ce, “Ai dole ki gaji kin kwaso rana maza je ki yi freshing up ki ji daɗin jikinki sai ki zo ki yi lunch, yau favourite dishes ɗinki na sa aka yi miki musamman. Kin ga bayan na sai ki kwanta ki huta ko!” Ɗago kai ta yi da niyyar barin jikin mom ɗin caraf ta kamashi ya na kallonta saurin kauda kai gefe ya yi ya na basarwa kamar ba shi ba.
Har za ta wuce sai kuma ta dawo da baya haɗe da faɗin, “Wai Mommy ina mu ka samu tsohon meye ne?” Uhmmm kun sai dai mutuniyar ta ku akwai iya ɓallo ruwa.......
Da sauri Mommy ta ce, “Meye kuma daughter a nan gidan?” Da hannu ta yi mata nuni da wanda ta ke nufi ta na faɗin “Yo ba ga mayen nan ba tun da na shigo ya ke ta bi na da ido babu ko ƙyaftawa har sai da na ji kaina ya fara juyawa.”
Ware ido ya yi da mamaki ya na kallonta sai kuma ya basar ba tare da ya ce komai ba. Yaƙe Mommy ta yi tare da faɗin, “Au daughter wai Imran ki ke nufi?Sorry ba ki sanshi ba ko? Ɗan uwanki ne ai.” Cikin rashin fahimta Fa'eezah ta ce, “Ɗan uwana kuma?”
Mommy ta ce, “Eh amma karki damu yanzu dai ki samu ki je ki watsa ruwa tukunna then i will explain everything to you okay?” Daga kafaɗarta ta yi irin ko oho sannan ta nufa sama inda bedroom ɗinta ya ke.
Ta na shiga bedroom ɗin ta watsa kayan da ke hannunta kan sofa ta ƙarasa cire kayan jikinta sannan ta ɗaura towel a kirji ta shige toilet tayi wanka ta fito. Ta na fitowa ko cream ba ta nema ba saboda zafin da ake yi. Wando 3quarter ta saka mara nauyi da wata riga shara-shara tun da ta san ba mai shigo mata ɗaki kai tsaye.
Saman lafiyayyar bed ɗinta ta faɗa ta yi kwanciyarta dama ta na fashin sallah ba yi za ta yi ba. Nan da nan kuwa bacci ya yi awon gaba da ita......
********
Tun da su ka dawo gida maganar ta ne ya ke ta mishi kai kawo a zuciya wai ƙaramar yarinyar da ba ta wuce sa’ar ƙanwarsa ta samu damar faɗa masa magana yau har ta na da guts ɗin ce masa makaho and he doesn't do anything. Tsaki ya yi a karo na babu adadi tun daga dawowarsa.
Ƙoƙarin ture maganar a ransa ya yi sannan ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai boxer ya faɗa toilet ya na sakar wa kanshi ruwa. Kusan 20mins ya na ƙarƙashin shower kafin ya kamalla ya ɗauro alwala ya fito saboda asr ya gabato. Ya na fitowa farar jallabiya kawai ya zura a jiki tare da fesa turare. Sosai jallabiyar ya ƙara fito da black skin ɗinsa mai shekƙi sai ya fito tamƙar wani black arab. Fitowa ya yi daga part dinsa ya nufi Masjid.......
WANENE FADEEL?
Comments and share.
💋Zeeyluv.......✍🏻