Free chapter · Read without an account

41

by Rufaida Umar · ALWASHI 2

ALWASHI 

   66

Ta kauda kai daga kallonta da yake, gaba ɗaya fuskarta ta koma kalar tausayi tana wasa da yatsun hannunta tace. 

"Don Allah ina son shiga gidan Zakiyya gobe."

Ya yi shiru kawai yana duban yadda gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Shi sai yanzu ma yake tunanin duka-dukanta wai nawa ma take? Ƴar ficikar yarinya da ita kawai don Allah ya mata ƙirar halitta na gaɓɓai ya sa take ganin daidai take da shi. 

"Na yi tunanin ban kai namijin da za'a nemi iznina ba kafin a fita."

Ita dai ta yi shiru, a zuciyarta kuwa har tsaki ta ja tana ikrarin ai wannan ma larura ne da kuma gudun kar ta je mota ta yi sama sama da ita. 

"Allah ya kaimu. Idan kin shirya ki jira ni"

Amsar da ya ba ta kenan kafin ya sa kai ya fice. Ta bi bayansa da harara kamar koyaushe. 

"Yen yen yen! Mtsw" Ta furta a fili. 

"Me kika ce?" Ba zato ta tsinkayi muryarsa, a firgice ta juyo. Ganinsa ta yi tsaye a bakin ƙofar, to me ya dawo da shi? Ta shafi ƙeyarta. 

"No ba magana na yi ba."

Ɗan murmushi ya yi da tun ɓata ransa da ta yi bai ƙara yi don wani abu nata ba. Yanzun ma abu ya tuna ya dawo, ya kuma ji da kunnensa abin da ta faɗi har da tsakin da ta ja. 

"Ok, taimakan da phone number din Mama."

Ya furta yana miƙo wayarsa, cikin rashin 
fahimta ta ce.

"Wace Mamar?" 

"Har Mama nawa muke da su? Ok, ta Maiduguri. Mamarmu."

Ta ɗan yi tsai tana kallonsa, har a lokacin yana daga ƙofar ita kuma tana tsakiyar falonta. Me zai yi da lambar Mama? 

'Ƙila ya ga dacewar ace ya kira sun gaisa ne. Kawai ki ba shi, hakan ma zai sa Mama ta daina zargin da wata a ƙasa a aurensa da ki ka yi.'

Wata zuciyar ta mata wannan tuni, 

"Uhum?" Ya furta yana ƙara miƙa wayar da ɗan gira don ya kula kamar ta faɗa wata duniyar. Idanunta a kansa, ya sani ba shi take kallo ba, amma kallo ne da yake jin yana mishi shawagi a sassan jiki. 

"Ki daina kallona haka mana."

Ya yi furucin yana dauke kai daga dubanta, ta ɗan haɗe rai, ita bai san ma ta lula tunani ba ne? Wayarta dake saman kujera ta ranƙwafa za ta ɗauka, idanunsa suka yi kyakkyawan gani, ya yi azamar ƙara kauda kansa, gaba ɗaya ya yi dana sanin dawowarsa, dama ya tafiyarsa idan ya so ko Haseenah ya yiwa magana ta aiko masa. 

"Zan maka sending ta text."

Amsar da ta ba sa kenan, bai ce uffan ba ya juya ya fice. Ba ya buƙatar doguwar magana. Yau shi kansa ba wani gane kan nasa yake yi ba. Don haka koda ya wuce sashen Kausar, ɗakinsa kurum ya nufa.  

Ya ji shigowar saƙon, lambar ce kawai aka rubuta. Ya buɗe ya yi saving ɗinta.

***
Washegari bayan ya isa ofis ya ba ɗaya daga cikin direbobin  ofis  ɗinsu muƙulli don ya ɗauko Laila ya kai ta gidan Zakiyya. 

Ta yi kusan awa biyu da shiryawa tana zaman jira, ranta duk ya ɓaci saboda tana son su ɗan yi maganganu da Zakiyya kafin zuwan matashiyar budurwar. 

Koda direban ya iso, ranta duk a jagule haka ta fita. Wata brown atamfarta England ta saka, ta yafa milk din mayafin da ya hau da jaka da takalminta. 

Da kwatancen da Zakiyya ta ba su ne suka isa har gidan nata. Direban na ajiye ta ya juya ya tafi bayan ta ba sa lokacin da zai zo ɗaukarta kamar yanda ya nemi sani. 

Zakiyya ta tarbe ta suka shiga ciki, madaidaicin gida ne mai kyau. Gidan ya burge Laila ƙwarai. Bayan sun zauna ganin irin kallon da Zakiyya ke bin ta da shi ya sa ta harare ta. 

"To uwar iya, mene ne ki ke bi na da kallon ƙurilla? Na san magana ce a bakinki."

Zakiyya ta fashe da dariya.

"Au ashe kin gane, ke kuwa ko auren love ki ka yi ai sai haka. Irin wannan ƙyalli da murjewa da fatarki ta yi? Kawai dai kin ɗan rame na gani, shi ma da hankalinki kwance ba lallai a gani ba."

Tsaki Laila ta ja. 

"Ke kika ga haka. Ƙarfe nawa za ta zo ne?" 

Zakiyya ta hangame baki. 

"Daga zuwanki kya tambayi ƙarfe nawa mata za ta zo? To sai wuraren uku ma na ce ta shigo."

Laila ta jinjina kai. 

"Hakan ma ya yi. Kinsan Allah Zakiyya? Na ƙagu na gama mission ɗina na tattara na fita a rayuwarsu. Ba za ki gane ya ake ji zama a cikin maƙiya ba, duk yanda zan kwatanta maki ba za ki gane ba. Ke wani abin fa ma da za ki ga na ɗan yi na kyautatawar, kawai idan na ɗan ji wa'azi ne haka a media dangane da mutuwa, gaba ɗaya sai jikina ya yi la'asar na ga damar yi masa wani gyaran ko na girka abinci. Duka- duka dai bai fi sau biyar ma ya ci abincina ba."

Murmushi Zakiyya ta ɗan yi cike da tausaya mata. 

"Wallahi Laila ni fa sai da na ji inama ba ki aure shi ba. Kawai na rasa meyasa wani bin nake tunanin dama ace yafemasa kika yi kawai ba ki shigo rayuwarsa ba."

"Haidar fa? So kike na zuba idanu tarihin yaro ya lalace? Ai ina! Gwara yaron ya girma ya san cewa an ɗaukarwa Uwarsa fansa."

"Kina tunanin shi ma Haidar zai tashi da tsanar Areef kamar mu?" 

Ɗaure fuska Laila ta yi. 

"Dole ne ma, ki faɗa min akwai wani masoyin Sameera da zai ji irin zaluncin da Sada's Family suka yi mata bai ji raɗaɗin zuciya ba? To babu shi! Haidar kuma jinin Sameera ne, shi ma kuma na sani zai girma da tsanarsu."

Murmushi dai har yanzu Zakiyya ta ke, a ranta ta sani wannan hasashe ne kawai na Laila, kuma mafarki ne da kawai take fatan tabbatuwarsa, amma ba su isa su ja da duk yanda Allah zai juya lamarin ba. Can ƙasan ranta, tana fatan Allah ya sa Laila ta yafewa Areef, ta na rantsuwa da Allah, da ace Sameera ce, tuni komai ya wuce a wurinta. Sameera ta fi Laila raunin zuciya da ma sauƙin kai, zafin kan Laila da nata sun fi zuwa ɗaya. Halinta da ya zo ɗaya da Lailar ne ya sa ba sa jituwa a bayan. 

"Tunanin me kike kuma? Ko ruwa fa ba ki ban ba balle wani abin motsa baki."

Laila ta katse ta, dariya ta yi lokaci guda tana miƙewa. 

"Allah ya baki hakuri babbar yaya. Amma dai gidan ba baƙonki ba ne tunda gidana ne. Zo ki zaɓi me kike so, samosa ko springroll ko meatpie na soyamaki yanzu yanzu?"

Laila itama miƙewar ta yi tana mitar ai wannan ma salon rowa ne a tsaya tambayarta me za ta ci. Suka shige kicin ɗin tare.

Laila na zaune saman kujera yayin da Zakiyya ke suyar haka suka yi ta tattauna tsarin aikin da Budurwar mai suna Suhailat za ta gudanar musu. Har Laila ta sanar da ita shirin da Hajja ta ce tana jiran Zakari kan a soma gudanarwa. 

"Zakarin nan fa ƙwallon shege ne shi ma, na fadamaki shi ma ya so neman Sameera da banzan hira, ni shi na sani ma da shan sigari don bana mantawa haɗuwarmu da shi abin da yake zuƙa kenan."

Fadin Zakiyya. Laila ta jinjina kai tana tauna samosa wanda ya ji nama a ciki. 

"Na san da haka, ban damu da ko kalar iskancinsa ba, tunda har na sami contact din sabon shiga a  bariki irin Suhailat, ki tabbatar na shirya ko da wane ɗan iskan ne zan yi gogayya da shi muddin zan ga ƙarshen mutanen nan."

Haka suka dawo falon bayan sun gama har Laila suka yi sallar azahar. Ƙarfe huɗu saura kuwa sai ga kiran Suhailat ta shigo layin da Zakiyya ta mata kwatance. Haka Zakiyya ta leƙa, bayan Suhailat ta hango ta kamar yanda ta ce mata za ta gan ta a baƙin gate da farin hijabi, ta ƙaraso suka shiga ciki. 

Laila ta dube ta da murmushi a saman fuskarta. Suhailat ta ɗage niƙaf ɗin da ta rufe fuskarta da shi tana murmushin.

"Mun ƙara haɗuwa. Ina wuni."

Da murmushi Laila ta amsa, haɗuwarsu ta farko tun tana Kano, ta hanyar wani abokin karatun Na'eem da Na'eem ɗin ya ba sa aikin nemo musu ƴar bariki da idanunta ya goge wacce ba ta shahara a media ba, ba a san fuskarta ba, a can suka shirya suka haɗu da Laila. Wannan duka ya faru ne tun a lokacin da Laila ta sakawa ranta sai ta tarwatsa rayuwar Areef, bayan haɗuwarta da Hajja Zayha. Ko Hajja Zayha ba ta da masaniyar wannan shirin nata. 

"Lafiya lau Suhailat. Ya gajiyar hanya?"

Suhailat ta cire hijabi tana dariya, Laila da Zakiyya suka dubi juna ganin wani shegen ɗinkin atamfa da ke jikinta. Hannun vest aka yi wa atamfar, gabanta an yi wani kwalliyar pattern da stones, gown ne da ya matse ta kusan rabin dukiyar fulaninta duk a waje  A kafadarta da saman ƙirjinta har da wani zane aka yi mata na baƙin lalle ne ma ko tattoo, oho. 

"Ai gajiya kam ta jima da ɓacewa ɓat Hajjaju. Yau sati na cif a garin nan."

Da mamaki Laila ta ce. 

"Sati ɗaya? Dama kin san wasu ne?"

Ita ma da mamakin ta dubi Laila bayan ta ɗauki meatpie ba tare da ko jira a mata tayi ba ta gutsira.

"Hajjaju ai ko ƙasar ta kama na bari zan bari, ni fa international nake abina. Kar ki wani damu, sabgar kaina ce ta kawo ni amma yanzu na sallami tsohon najadun."

Zakiyya dai shiru ta yi tana ƙare mata kallo, za ta iya ɗara su a shekaru, farin bleaching ne da ita don har wani ja take yi. Tana da hudar hanci, a kunnenta kuwa huji hudu ne, uku daga ƙasa sai ɗaya a can sama. Ba wata kyakkyawa ba, amma tana da mazaunai da cikar ƙirji.

"Ok, muje zuwa aikin da nake so ki gudanar mana."

Waya ta ɗauka ta danna ta buɗo hoton Areef tun wanda Zakari ya aikomata ta dire a gaban teburin dake gabansu. Suhailat ta zubawa hoton ido kafin ta ɗauki wayar ta fiddo idanu.

"Kuma bahaushe ne shi wannan din Hajjaju?"

Laila ta haɗe rai. 

"Yes, so nake ki yi duk yanda za ki yi ki samu dama a kansa, ko ma ta wace hanya za ki bi, ni dai abu ɗaya nake buƙata. Ya kasance da ke, ko bai kasance da ke ba, wannan ba damuwata ba ce. Hotunanku tare nake so, idan na ce hotuna, kin san irin waɗanda nake nufi ko?"

Suhailat da har lokacin idanunta ke kan hoton Areef tana jin wani kwaɗayin kaɗaita da shi ɗin ta gyaɗa kai sannan ta dube ta tana ƴar dariya. 

"Ni ko na sani Hajjaju, ko turmi da taɓaryar kike son ganinmu za ki gani."

"A'a ke, ba fa nufinmu ku kusanci juna ba. So..."

"Zakiyya, idan hakan ma ta kasance mene ne wai? Please ki bar ta ta yi aikinta yanda ya kamata."

Laila ta katse Zakiyya da faɗin haka, Zakiyya ta saki baki tana kallon Laila, tana da hankali kuwa? Wane irin tunani ne haka? Laila na hangen gaba kuwa? 

Ta kasa magana har Suhailat  ta amince cewar Laila ta sha kuruminta, kafin ma cikar sati ukun da ta ba ta, komai zai afku. 

Murmushi Laila ta yi, a take ta ƙara tura mata manyan kuɗaɗe har dubu ɗari biyar, ta dubi Suhailat da ta yi ƴar ƙara farin cikin wannan kuɗaɗe ta ce. 

"Ina maki albishir cewa muddin kika gudanar da abin da nace, kika turon hotunan komai, toh ki shirya don sai na girgiza asusunki fiye da haka."

Cike da farin ciki Suhailat ta dube ta. 

"Na yi maki alƙawari ni kuma sai na cika. Zan tabbatar maki da cewa ni ƙarshe ce. Kawai ki ban lambar wayarsa da address din kamfaninsu, inda zamu haɗu da komai, ki bar shi aikina ne. Hotuna kike buƙata? Ki saka a rai kin samu kin gama."

Suka yiwa juna murmushi, Laila wani irin farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta.  Zakiyya ba ta ƙara magana ba har Suhailat ta zura hijabinta da niƙaf, ta lodi snacks dinnan a leda bisa umarnin Laila, ta haɗamata da lemu, ta yi musu sallama ta fice bayan Lailar ta aikamata lambobin Areef ɗin da ma address din yanda ta buƙata. 

Laila ta miƙe fuskarta a mugun sake ta ce. 

"Madam bari na yi sallah, na gaji da kallon ƙurillar nan da kike min."

Zakiyya ta girgiza kai.

"Laila kar mu kai ga nisa fa, kar muje mu yi abin da zai haifar da dana sani."

Laila wacce ta soma tafiya da nufin shiga banɗakin dake falon ta tsaya gami da juyowa.

"Please kin ga, kar ki ɓatan rai domin wallahi raina yau fari ƙal yake. Mene ne sabo a wurinsa toh? Akwai kalar abin da bai aikatawa? Malama kar ki ishe ni."

Daga nan ta ƙarasa shigewa banɗakin ta bar Zakiyya da jin wani iri a zuciya amma kuma tana hasko ƙamshin gaskiyar Lailar, babu abin tausayi a jikin Areef, ai shi ma ɗan iskan ne. Da wannan ta watsar da jimamin nata. 

Koda suka yi sallah girki suka yi suka ci abinsu, suka ƙara tasa hira har  biyar ta wuce. Can suka ji hon a waje. 

"Da alama direbanki ya zo. Bari na leƙa."

Zakiyya ta furta gami da miƙewa ta saka zumɓulelan hijabinta ta fita, gidan ta buɗe, ganin motar ya sa ta dawowa ta sanar mata. Tare suka jera bayan Zakiyya ta dunƙulo leda dauke da kayan snacks din da suka ƙanƙare. 

Buɗe murfin motar gaba da aka yi ne ya sa su ganin wanda ke ciki, suka dubi juna. Laila ta ƙara juyowa ta dube shi, ba ta yi tsammanin shi ne zai zo ɗaukarta ba. To ya aka yi ma ya san gidan? 

Zakiyya ta shanye mamakinta ta gaishe shi fuska a sake. Ya amsa da murmushi yana tambayar maigidan nata. Ta sanar da shi ba ya gari. Ya dubi Laila har lokacin fuskarsa a sake. 

"Muje ko?" 

Laila ta kauda kai tana shan mur, a dole ta buɗe gidan gaba ta shiga Zakiyya na miƙa mata ledar suka yi sallama. Shi ma sallamar ya yi wa Zakiyya sannan ya shige ya ja. Zakiyya ta bi su da kallo fuskarta dauke murmushi, gefe guda da tausayin wannan rayuwa da mutum kamar Areef ya jefa kansa ciki. Haka ta juya ta koma gidanta ta rufe. 

***
A motar babu wanda ya ce uffan ban da wayar da Areef ke amsawa ta bluetooth da ke kunnensa. A jikin sitayarin kuwa wayar ce saƙale jikin phone holder. Da wani baturen ne suke magana kan wasu kayayyakin da suka ƙara yo order ba su kammala siyayyar ba. Laila dai hanya kawai take kallo, ganin ba hanyar gida suka yi ba ta dube shi. Aka yi katari ya juyo don duba gefenta ko mota ta taho saboda kwanar zai shiga. Idanunta ya faɗa cikin nata, ya kauda kai. Yau gaba ɗaya ya kasa gane kansa a kan Laila. Tunaninta hana shi sakat ya yi a ofis, ganinta da jin tsiwarta kawai ya ji yana so, wannan ne ya sa shi neman direban ya masa kwatance ya zo da kansa, ta waya suka dinga magana har ya ƙarasa gidan. 

Laila da ta maida kallonta gefe itama ta ce. 

"Where are you taking me?"

Murmushi ya yi hankalinsa na kan titin yana wani irin tafiya kamar baya so. Muryar kaɗai wani daɗi ya ji ta mishi. 

"Siyar da ke zan yi."

Ta ɗaure fuska ba ta ƙara magana ba har suka iso tafkeken gidan da hasken motar ya haska mata baƙin  number plate din dake jikin bangon gidan wanda aka yi rubutu da golden "No 12, Bakori's Residence." Nan ta gane wato gidan Innarsu suka zo. 

Daidai sadda maigadin ya buɗe suka shiga, koda ya yi parking ba ta motsa ba don har ga Allah ita abin bai burge ta ba. 
A dole kawai ta shiga. 

Sai dai koda ya je sallah ya dawo, ya yi mamakin yanda ya samu tana ta hira da dariya da Inna. Ya ji dadi, haka suka yi sallama Inna na ta yabon Laila har tana cewa wai Areef ya yi dace. Laila ba ta san ma sadda ta yi ƴar dariya irin na 'tsohuwa ba ki san ni ba'. Shi kuwa ya bi ta da kallo don ya gane sarai dariyar ta rainin hankali ce. 

A hanya ma kurame suka zama, shi ba ya so ya yi mata magana ranta ya sosu, ita kuma dama ba ta da abin ce masa. Ita ke da girki sai dai ba ta da damuwar me zai ci, ta ga ma ya yiwa kansa dabara ya cika ciki da dambun shinkafa a gidan Innar. Ita kuwa ruwa kawai ta sha. 

***
  MAIDUGURI


©Rufaida Umar

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol