Free chapter · Read without an account
Tangled Fate
🔥TURƁAYA🔥
Story
and
written
By
Zainab Bint Abdulrahman
(Zeeyluv💞)
***
*From the most precious Association*
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
YOTA KO DA KUƊINKA SAI DA RABONKA💃🏻💃🏻💃🏻
Yota Id/027
Page...............8
Kallon kallo su ke yi tsakanin shi da Afeef gaba ɗaya ya ma rasa ta ina zai fara yi wa Afeef ɗin bayani ya fahimce saboda ga dukkan alamu ya ji abubuwan da ya faɗa tun daga farko. Cikin hawayen da ya gama wanke mishi fuska Afeef ɗin ya fice a gidan. Wajen mashin ɗin sa ya nufa ya fige mashin ɗin a sittin.
Cikin fargaba Asad ya bishi ya na ƙwalla mishi kira amma sam ko bi ta kansa Afeef din bai yi ba saboda yanda zuciyarsa ke tafarfasa wai Asad ɗin ne da bakin sa ya ke faɗin zai yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninsu.
Kalmar ta daɗe ta na yi mishi amsa kuwwa a kunne hakan yasa ya ke wani sharara gudu a tsakiyar titi Asad na bin shi da mota a baya ya na danna mishi horn haɗe da faɗin "Afeef stop the bike" amma duk a banza ko bi ta kansa bai yi balle ya sa ran zai tsaya ɗin. Cikin wani irin ƙuzari ya take giyar motar sa Afeef bai ankara ba sai ji ya yi an sha gaban shi da wani irin ƙarfi wanda ƙris ya rage ya kife da mashin ɗin...........
**************************
Zaune ta ke ɗare-ɗare a kan sofa riƙe da pizza a hannu gefen ta kuma exotic juice ne a kan sofar. Gaba ɗaya hankalinta na kan cricket game ɗin da ake yi a Tv. Wani tsalle tayi ta na faɗin "Catch it" yayin da ball ɗin ya tafi sama.
Daidai nan Aunt Laylah ta fito ta same ya tana ta tsallen murna ta na waƙen-waƙen ta. Ganin Aunt Laylah ya sa ta ce "Look Aunt, kalla ki ga ina son guy ɗin nan, i just love endlessly."
Aunt Laylah ta ce "Hayat wannan ɗan wasan fa ya yi aure tuntuni ki ma daina wannan haukar na ki mutumin ma da bai san da zamanki ba a doron duniya ba."
Hayat ta ce "Aunt ni kam ya san da ni tun da ya san ya na da masoya a duniya to kuwa ya san da zamana. Yanzu dai zauna ki gani yanzu zai jefa mana six runs."
Aunt Laylah ta ce "Ba zai ci ba" Da murmushi Hayat ta juyo ta ce "To mu yi bet Aunt idan ya ci za ki ba ni EGP 500, idan kuma bai ci ba ni zan ba ki." Da confidence Aunt Laylah ta ce "Agree."
Haka sun ka lalace a wajen yanda su ke motsa jikinsu kai ka ce su ke buga cricket ɗin. Aunt Laylah ne ta shiga yi wa Hayat dariya ta na faɗin "Oya bani kuɗina ai dama na faɗa miki ba zai ci ba."
Rufe bakinta ke da wuya dai gashi ya jefa six runs ɗin. Tsalle wajen Hayat da murna ba'a magana sai dariyar mugunta ta ke yi wa Aunt ɗin ta ce "Aunt my money." Ta yi maganar ta na miƙa wa Aunt ɗin hannu.
Rai a ɓace Aunt ta ciro kuɗin a wallet ɗinta ta miƙa mata. Hannu ta saka za ta amsa Uncle da tun shigowar shi ya na bayansu ya na kallon duk abin da ke faruwa ya yi sauri riƙe hannun Hayat ya na faɗin "No no no no"
Ɗaga ido Hayat ɗin ta yi su ka haɗa ido da shi ya girgiza mata kai alamar a'a. Narai-narai ta yi da idonta kamar za ta fashe da kuka cikin eye signal itama ta yi mishi inkiya da "Why Uncle" Uncle ya dubi Aunt ya ce "Yarinya ƙarama ta yi miki wasa da hankali bs tare da kin sani ba.
To wannan tsohon wasa ne kuma ta san me zai faru shiyasa ta yi miki haka." Zare ido Aunt ta yi cikin mamaki sai ynz ma ta lura da gashin da ke fuskar ɗan wasan saboda yanzu ya daina ajiye gashi a fuskar sa.
Juyowa ta yi ta kalle Hayat ɗin da ta ke ta mata dariya. Kanne mata ido ɗaya ta ce "Actually Aunt wannan shine favorite cricket match ɗina shiyasa a duk lokacin da na ke cikin damuwa kawai sai na kunna wannan match saboda gemun nan na shi na tafiya da ruhi na."
Uncle ya ce "Abin da ya kamata ki lura shi ne Hayat ce kaɗai za ta kunna tsohon match sannan ta zauna ta na kallon shi cikin armashi kamar yanzu ake yi match ɗin saboda shashanci irin na ta."
Tun da su ka fara maganar su ma gaba ɗaya ta rasa abin cewa. Can dai ta kauda maganar da faɗin "Yau Amjad ka yi magana da Hayat ɗin?"
Uncle cikin ɗan mamaki ya ce "Magana kuma! Wace maganar?" Aunt ta ce "Hakan ya na nufin cewa ba ka faɗa mata komai ba kenan game da maganar mu?"
Cikin inda inda ya ce "Amm oh! Actually Hayat dama mun yanke shawarar komawa Paris ne gobe, kuma a cewar Aunt ɗin ki, ta ce ba zai yiwu ki zauna ke kaɗai a Cairo ba."
Tun da ya fara maganar ta ke cin pizzar ta kamar ba da ita ya ke maganar ba. Aunt Laylah ta tare numfashin sa da faɗin "Fito ka yi mata bayani kai tsaye babu wani corner corner, kawai mun yake shawarar zamu tafi gobe kuma tare da ke zamu tafi that's all."
Hayat ta yi tsalle ta dire ta ce "Wallahi Aunt na gama magana ta, idan kin ga na bi ku mun koma Paris tare to na samu abin da ya kawo ni cairo ne."
Aunt Laylah ta miƙe cikin faɗa ta na faɗin "Wai ke Hayat meye ya sa ba za'a yi miki magana ɗaya ki ji ba shin ni na ke iko da ko kuwa ke kike da iko da ni?."
Gani abin na su ya na neman ya zama hayaniya yasa Uncle faɗin "To duk ku yi shiru ya isa haka, zan nemo mafitar abin yi." Wani kallo Aunt ta watsa mishi sannan ta juya ta kalla Hayat ɗin itama ta yi ƙwafa ta nufa ɗakinta zuciyar babu daɗi, ta rasa ya za ta yi da wannan shegen kafiyar na Hayat ɗin.
Itama Hayat ɗakinta ta nufa fuskar nan a kumbure. Dafa kai Uncle ya yi ya na tunanin mafitan da zai amfani da shi wajen magance wannan matsalar tsakanin Aunt da Hayat.
Ya san Aunt ta na kan gaskiya da ta ce Hayat ba za ta zauna ita kaɗai a nan ba, sannan kuma ta gefe guda ba ya son ya kuntatwa Hayat ɗin ta hanyar tilasta mata yin abin da ranta ba ya so, saboda sosai ya ke matuƙar so da tausayinta duba da yanayin ƙaddarar da ya yi wa rayuwarta giɓi.
Shi ya saka shima bai wani goya bayan auren da Aunt ta so yi mata ba kafin bayyanar asalinta ba. Saboda ya san duk daren daɗewa dole wata rana sai miji ko danginsa sun goronta mata a kan haka musamman ma da ba wani soyayya aka yi ba kafin auren.
Sai gashi dukkan alamu sun nuna cewa ba mutanen kirki bane ma ashe su ke nema cusa Hayat ɗin cikinsu, gwara da Allah yasa ma hakan ya faru tun kafin a je ko ina.
Haka ya dinga safa da marwa a parlour ya na saƙawa ya na warwarewa. Can ya ɗan dakata daga safa da marwan haɗe da faɗin
"Yes! Alhamdulillah i have found a solution to the matter!" Cikin sauri ya ɗauko wayarsa ya fara laluɓen wata number. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗauka. Cikin girmamawa ya fara gaisuwa cikin ladabi daga nan kuma ya juye harshen shi zuwa larabci.
"Shukran, shukran." Kawai ya ke ta faɗi wanda ya nuna ga dukkan alamu ya samu abin da ya ke buƙata ne. Daga haka su ka yi sallama ya ajiye wayar ya na faɗin "Alhamdulillah Ya Allah." Fuskar nan a washe kamar wanda aka yi wa busharar wani abu.........
*******************************
Asad ne ya fito a motar da sauri ya ƙarasa inda Afeef ya ke saura ƙris mashin ya danne shi. Cikin zafin nama Asad ya ɗaga mashin ɗin ya na faɗin
"Afeef ba ka da hankali ne kake wannan irin gudun da mashin a kan titi, what if something bad had happened to you ya kake son na yi da rayuwata?"
Cikin ɗaga murya Afeef ya ce "So what! You could have let it happen. Meye bambancin hakan? Ka ce mu ba ahalinka bane ka yanke duk wata alaƙa damu. So let it be just go away."
Cikin wani irin rauni da ya ke dashi a kan ƙanin na shi wanda Allah ya jarabe shi da tsananin sonsa duk da sanadiyar shigowar uwarsa rayuwar mahaifinsu ne ya jawo musu duk wani halin taƙaicin da su ka tsinci kan su a ciki.
Amma kasantuwarta na mahaifiyar Afeef ya sa ya goge duk wannan laifin a idonsa ya ɗaura shi kan ubansa saboda albarkacin haihuwar mishi Afeef da ta yi wanda ya ke jin sonshi tamƙar ya maida shi ciki ya ɓoye saboda ko misƙala zarritin ba ya son abin da zai zo ya taɓa mishi Afeef ɗin har ya yi sanadiyar cutra da shu.
Ya ce "Afeef kasan ma duk saboda me na ce haka ne? Afeef ba ka da alaƙa da wannan mutumin, mutumin da na ƙi jini, da ni kake da alaƙa Afeef ba da shi ba."
Afeef ya ce "Amma ai cewa ka yi ba ka buƙatar ajiye duk wata dangantaka da ko wanne daga cikinmu."
Cikin sanyin murya kamar zai yi kuka wanda ba'a shi da wannan halin ba ya matso kusa da Afeef ya ce "Afeef kai wani ɓangare ne a jikina, babu yanda za'a yi na yanke alaƙa da kai. Idan na ce su ba ina nufin da kai a ciki ba.
Afeef bana taɓa kawo wa raina kana zaune a cikinsu, kai daban na ke ganinka daga cikinsu. Ɗaga kai Afeef ya yi idonsa sharƙaf da hawaye kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya nema waje ya zauna.
Ganin haka ya sa Asad ɗin ɗan yin murmushi ganin abin da Afeef ɗin ya yi ya nuna mishi alama da ya fara saukowa kenan daga dokin zuciyar da ya hau. Shima waje samu ya na kusa da shi haɗe kafe shi da ido. Kauda kanshi Afeef ɗin ya yi zuwa ɗayan side ɗin ya juya mishi ƙeya.
Murmushi mara sauti Asad ya ce "Ka tuna lokacin da aka fara kawo ka gida lokacin ba ka iya tafiya ba ma sosai? I use to extend my hand to you. Amma sai ka riƙe min ƙafa kana ƙoƙarin tafiya and...." Afeef ya ɗauka da faɗin "And then i used to fall down, and then i would start crying from pain" Asad ya ƙarasa da faɗin and then i will have to make Basbousa(abincin Egypt ne da yara su ke so sosai) for you."
"Kuma idan na ci basbousa ɗin still na ƙara fashewa da kuka." Cewar Afeef ya na tuna ƙurciyar shi kamar yanzu komai ke faruwa haka ya ke kallon abin. Asad ya ce "Ai kai rigimarka tun kana yaro ba irin na jinsin mutane bane."
Dariya Afeef ya yi ya ce "Akhy ka tuna lokacin da na ke jin tsoron tsawa idan ana ruwan sama da daddare sai na gudu na zo cikin blanket ɗin na ɓuya"
Asad ya ce "Gari na wayewa dole na shanya katifar a rana kuma ba." Murmushi Afeef ya yi ya ce "Akhy you did so much for me back then." Ya yi maganar ya na share hawayen idonsa tare da matsowa kusa da Asad ɗin saɓanin da da ya saka distance mai nisa a tsakaninsu.
Shafa kanshi Asad ya yi cikin kulawa ya ce "What are elder brothers for?" Afeef ya ce "We are brothers Akhy right? So why can't we meet openly? Why can't we celebrate our birthdays together? Why can't we have lunch and alot of things together? Why is it so complicated? Why brother???"
Ya yi maganar ya na miƙewa tsaye haɗe da jin shi ya gaji da ɓoye wannan alaƙa ta su, ya gaji haka ya na buƙatar nuna wa duniya ɗan uwanshi wanda a ko ina zai buga ƙirji da shi ya kira shi jinin sa. Shima Asad ɗin miƙewa ya yi tare da rasa abin da zai faɗa wa ƙanin na shi kawai sai zuba masa ido ya yi.
Afeef ya ci gaba da faɗin "Akhy ka na saka komai ya tafi daidai me zai saka wannan ma ba za ka saka shi shima ya tafi daidai ba don Allah." Ya ƙarasa maganar hawaye na gangarowa a idonsa tare da rungume Asad ɗin ya na faɗin "Please make it right Akhy plsssss." Shi dai Asad shafa kan shi kawai ya ke yi alamar lallashi ya na jin tausayin ƙanin na sa har cikin ransa amma ba ya ji zai iya yi wa Afeef ɗin abin da ya ke so indai a kan mutumin da duk duniya ba shi da maƙiyi sama da shi ne.
Da ƙyar ya iya fisgo kalmar "Stop crying now, idan ƴanmata su ka ganka za su ɗauka baby ne kai bayan ƙoshesshen namiji ne nan mai jini a jika." Da sauri Afeef ya shiga share hawayensa jin an ambaci mata ya ce "Kuma hakane fa Akhy kar a raina ni saboda haka daga yanzu babu hawaye, babu hawaye." Ya ƙarasa maganar tare da hargitsa sumar kanshi.
Tallabe mishi ƙeya Asad ya yi duk suka saka dariya gaba ɗaya. Asad ya tallabo fuskar Afeef ɗin ya yi a tafin hannunsa ya ce "Afeef na roƙeka da girman Allah karka sake maimaita kwatankwacin abin da ka aikata yau ka ji?" Girgiza kai Afeef ya yi alamar to............
*********
SHAREEQ KHAN MANSION
Zaune su ke su ukunsu kamar yanda su ka saba duk inda ka ga ɗaya to tabbas sauran ma su na kusa saboda mawuyacin abu ne su yi nisa da juna. Nudrat ta ce "Kun ga irin kallon da Irfan ya ke ta bin Hamra da shi kuwa? Oh my god, what a perfect match." Duk su ka sanya dariya ban da Hamra da ta yi murmushi kawai.
Humairah ce koma kusa da Hamrar ta na faɗin "Faɗa min gaskiya, lokacin da ya miki wannan kallon ba ki ji daɗi ba? Ba ki ji daɗin irin kallon da ya dinga bin ki da shi a wajen ba huh?" Haka su ka tasa Hamra a gaba da tsokana iri-iri ita dai ba ta tanka su ba sai dai na murmushi ta yi murmushi wani lokacin kuma ta kai wa ɗaya daga cikin su duka idan su ka faɗi wani abin.
Ƙarshe ma tashi ta yi ta bar musu wajen gaba ɗaya, itama Nudrat ta bi bayan jim kaɗan bayan ta tafi ta cewa Humairah "Bari na je na dubo Hamrah kin santa da shegen arahar hawaye kamar an buɗe famfo, kar ya zama na ta na can ta na sana'arta ne ba mu sani ba." Humairah ta ce "Eh hakane maza je ki dubo ta sai ku taho tare ya kamata mu fara tsare-tsaren abin da ya kamata tun kafin lokaci ya fara ƙurewa. Ni bari na jira ku a nan."
Shigowar shi gidan kenan babu daɗewa, rigar jikinsa kawai ya cire ya bar singlet ya nufa balcony. Hango Humairah ya yi ita kaɗai a wajen hakan ya sa waiwaiga karaf idonsa ya sauka a kan followers ɗin da ake sakawa a glass na decoration ɗin gida.
Wajen glass ɗin ya nufa a hankali ya zaro flowers ɗin sai ya na nufa gurin ta ya na gyara gashin kansa. Ta bayanta ya nufo ya yi gyarar murya haɗe da miƙa mata flowers ɗin. Da sauri Humairah ta juyo ganinsa tsaye a wajen ya sa ta ce "Au dama kai ne?" Ya ce "Da wa kike tunanin ki na da shi a gidan da zai kawo miki flowers bayan ni mai sonki." Ya yi maganar yana ɗage mata gira.
Karɓar flowern ta yi daga hannunsa ta na murmushi haɗe da faɗin "Ina ka tafi bayan tafiyar su Irfan?" Cikin salon yaudara ya ce "ouh! Na je siyo wa Humairah my darling flowers mana." Da tsananin murna ta ce "Oh really saboda ni ka je ka siyo flowers ɗin nan? But why?f" Ta yi maganar ta na kai flowers ɗin hancinta ta na shinshinawa.
Hannun ya saka a cikin gashinsa ya na ɗan hargitsa su haɗe da faɗin "Saboda so da ƙauna mana."
Humairah ta ce "Oh wow! Anywhere ga dukkan alamu ka siyo su ne cikin soyayya, so abin da ya kamata na yi shi ne na gode maka saboda haka thank you."
Afeef "Oh no Humairah a cikin sharuɗar soyayyata babu sorry sannan babu Thank you" Hamra da tun daga nesa da su ke tahowa ta hangen Afeef a wajen hakan ya saka ta taɓo Nudrat ta na yi mata signal. Daidai lokacin da Hamra da Nudrat su ka ƙaraso wajen, Nudrat ce ta fara ƙananan tari.
Ganin su a wajen ya saka nan da nan kuma ya fara kame-kame tare da faɗin "Nudrat me ya sa ba ki sha wa tarin nan magani ba?"
Dariya su ka saka ganin yanda ya ke ta kame kame ya ma ƙi bari su haɗa ido. Ganin haka ya sa ya ce "Fine" ya na juyawa da niyyar barin wajen garab ya gwara goshinsa da bango. "Auch!" Nan ma su ka sake kwashewa da dariya ba tare da ya bi ta kansu ba ya dafe goshinsa ya na barin wajen.
Kallonsu su ka dawo da shi kan flower ɗin da ke hannun Humairah. Tattaɓawa su ka shiga yi fuskarsu ƙunshe da dariya haɗe da faɗin "Humairah wannan flower ɗin fa daga ina?"
Yashe baki ta yi cikin farin ciki ta ce "Afeef ne ya siyo mini musamman da ya fita." Nudrat da faɗin "Ohhhhhh!" Kasaƙai ta yi ta na kallonsu ganin kamar sun maida shasha. Ganin haka ya sa Nudra riƙo hannunta tare da jiyo da ita ta yi pointing wajen show glass ɗin da ake saka flowers sannan ta ce mata "Daga can."
Zare ido Humairah ta yi ganin babu flower ɗin da ke cikin wani flower pot da ke wajen, a ranta ta na sake jaddada rainin hankali irin na Afeef da har ya saka ta kasa gane flowers ɗin gidansu ne...............
Tsaye ya ke a garden ɗin da ke cikin gidan gaba ɗaya babu wani walwala a tare da shi bare ya samu nutsuwar zuciya. Ya rasa ta ina zai fara gyara kuskure da ɓarnar da ya yi shekaru ashirin da su ka wuce. A kullum da wannan ciwon ya ke kwana ya ke tashi.
Rabon shi da samu nutsuwa da farin cikin zuciya kamar sauran mutane da su ke rayuwa a doron ƙasa tsawon shekaru ashirin kenan tun bayan faruwar abin da ya saka shi a matsayin mummunar ƙaddara mai tarwatsa farin cikin zuciya har ma da na gangan jiki.
Jaddah ce ta ƙaraso wajen ganin yanayin fuskar ɗan na ta da ya bayyana damuwar da ya ke ciki ƙarara. "Lateef wannan ba fusaka uban da aka sanyawa ƴarshi rana bane."
Murmushin da yafi kuka ciwo ya yi sannan ya ce "Wannan shine fuskar mahaifin da ya ke so da mararin haɗu da ɗansa da ya fara kasancewa gudan jini a wajensa duk ya kasa duk da kuwa yanda ya ke da burin yin hakan"......................
#AutarYotaPen
#EcothTeamOfYota
#FamilyDrama
#EmotionalStory
#BrokenRelationships
#SiblingBond
#HiddenTruths
#HeartTouchingStory
Want the next chapter?
Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.