Free chapter · Read without an account

Collision Beyond Chance

by Zainab Bint Abdulrahman · TURƁAYA

🔥TURƁAYA🔥


Story


           and 


               Written


                    By


Zainab Bint Abdulrahman 


               (Zeeyluv💞) 


              *** 


*From the most precious Association*


YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION 

(YOTA)


YOTA ID/027



🛎️PAID ADVERT🛎️



✨🤍 ZEEVANA LUXE 🤍✨

Where Modesty Meets Luxury


👑 Ki bayyana kyawunki cikin nutsuwa da ƙima.


A Zeevana Luxe, muna kawo miki ingantattun kayayyaki masu inganci, salo, da daraja, domin kowace mace ta haskaka cikin kamala.


🛍️ Muna samar da:

🌸 Luxury Abayas

🧕 Elegant Hijabs

👗 Classy Gowns

🪡 Quality Fabrics & Materials

👜 Premium Bags

👖 Stylish Palazzos

🍫 Candies & Confectioneries

🥐 Fresh Pastries & Snacks

💊 Quality Supplements

✨ Da sauran kayayyaki masu inganci.


✔️ Inganci da za ki amince da shi.

✔️ Farashi mai sauƙi.

✔️Service mai nagarta.

✔️ Isar da kaya cikin sauri.


💎 Zeevana Luxe ba wajen sayen kaya kawai ba ne... wuri ne da ƙyalli, ƙima da inganci suke haɗuwa domin ki.


📩 Ku tuntuɓe mu ta wannan lambar: *** ko kuma ***…. Domin ki kasance cikin matan da ke zaɓar aji maimakon yawa.


ZEEVANA LUXE

Luxury Beyond Fashion.



Page...............12



Ido waje gaba ɗayansu su ke yi wa juna kallon kallo, ko wanne ya na tunanin karon da su dinga yi a haɗuwar su na baya da su ka haɗu a gurare daban daban. A tare su ka miƙe tare da haɗa baki wajen faɗin, "You!!!" su na nuna juna da hannu. 


Kame kame ta shiga yi haɗe da faɗin, Hayat:

"Actually Farhat ta ce mini ɗakin da ke hannun dama ne."


Fuska tamke Asad ya ce,"Ba ma ki iya bambance tsakanin dama da hagu. Yanzu har dama da hagu ma ba kya iya tantancewa. Saboda tsabar kanki a doɗe ya ke sai tsiwa da fitsara kawai ki ka iya."


Cikin sigar masifa ta ce, "Oh my goodness! What's wrong with you? Me ya sa kullum kake neman faɗa da ni ne?"


Da mamaki Asad ya zare ido ya na kallon a ranshi ya ce, lallai ma yarinyar ta raina min wayo amma zan koya mata hankali. A fili kuwa sai ce wa ya yi, "Au ni ne ma kullum na ke neman faɗa da ke kenan saboda kin raina ni? Ai wannan gadona ne."


A kaikai ce ta kalle shi ta ce, "Oh really? Ita fa ta ce mini ɗakin da ke hannun dama ne."


"Then me ya sa kika shiga na hannun hagu?" Ya yi maganar a ƙufule.


"Abin da yake hannun hagunka, a gare ni dama ne. Kuma abin da yake hannun damanka, a gare ni hagu ne. Shi ya sa na ɗauka wannan ne ɗakin da take nufi. And by the way, ni na fara shigowa wannan ɗakin kafin kai. Saboda haka wannan ɗakina ne. A Paris ma haka ake yi."


"Malama wannan Cairo ne, ba Paris ba."


Hararar shi ta yi haɗe da faɗin, "Ai na ga alama duk mutanen Cairo sun rasa hankalinsu kamar yadda kai ma ka rasa naka."


Cikin wani irin hargitsatsen tsawa ya ce kamar zai kai mata duka ya ce, "Keeeeeeee."


A firgice ta ja da baya ta na runtse ido da ƙarfi tsabar firgita haɗe da toshen kunne.


Daidai nan Ummie da Farhat su ka ƙaraso ɗakin a sittin sakamakon hayaniyar da su ka ji ya ke tashi. Ganin yadda Hayat ta cure jikinta waje ɗaya ta na hawaye yasa Ummie ƙarasawa wajen da sauri ta na jawo zuwa jikinta faɗin, "Dear what's wrong? Are you okay?" Don ita a tunaninta ko wani abin Asad ya yi mata. Sai a sannan ta na samu sukuni jin ta a jikin Ummir sannu a hankalin ƙwarin gwiwar tsiwarta ya soma dawowa. 


Buɗe ido ta yi wanda ya yi gaje gaje da hawaye idon nan fal tsiwa ta ɗago daga jikin Ummie ta zuba masa idonta a kai ta ce, "Whenever you see me you always shouted at me like this." Ummie da Farhat su ka kalla juna da mamakin jin furucinta. Nan Ummie ta yi wa Farhat inkiya da ido a kan ta zo ta kai Hayat ɗaki. 


Farhat ta ƙaraso wajen da Hayat ɗin ke tsaye a gefen Ummie ta ce, "Sorry mu je na kai ki ɗakin baƙin." Hayat ta share hawayenta tare da fakar idon Ummie ta ɓalla mishi harara. Zaro ido ya yi kafin ya yi yunƙurin yin wani abu tuni ta yi gaba abinta ta bar shi muzurai. 


Bayan fitar su Ummie ta dube shi ta ce, "Asad me Hayat ke nufi da "Whenever you see me ɗinnan?"Kun san juna ne dama???" Sake tamke fuska ya yi a kumbure ya ce, "Ummie rabu da wannan fitsararriyar yarinyar da ba ta da ɗa'a. Ta taɓa shan mini gaban mota ina tuƙi amma saboda rashin kunya ta kalla tsabar idona ta ce min wai laifina ne don ta raina ni.


Da na san wannan yarinyar ce za ta zo gidan wallahi tun farko da na hana. Bacin ma kin riga kin yi wa iyayenta alƙawarin za ki riƙe ta da cikin daren nan za ta bar gidan nan spoilt brat kawai." Tun da ya fara masifar Ummie ke kallonsa ta na ƙunshe dariyar da ke cin ta, ganin wai Asad ne da dogon jawabi haka mutumin bai ƙaunar surutu mai tsayi gashi ya samu daidai da shi wanda idan ba'a yi wasa ya fara dogon surutu kenan daga yau don yadda ta lura da Hayat babu tsoro a lamarinta.


Ummie cikin sigar tausayi ta ce, "Haba Asad, ka bi a hankali mana ba ka ganin yarinyar ce, Allah sarki the innocent poor thing."


A ƙufule kamar wanda ta watsa wa ruwan zafi jin kalmar da ta kira Hayat ɗin da shi ya ce, "Ummie please, ki bar kiranta da wannan sunan saboda ba ki san halinta bane, na tabbata kema da kin san halinta da ba za ki yarda ta ƙara kwana a gidan nan ba. Ba ta da tarbiyya ko kaɗan sannan ba ta iya shigar mutunci ba." 


Dafa kafaɗarshi ta yi ta ce, "Asad, calm down. Baƙuwa ce ita a cikin ƴan ƙanƙanin lokaci za ta yi tafiyarta, ba wai ta zo zama damu ba kenan na har abada ba. Saboda haka ka yi haƙuri."


"Shikenan tun da kin ce haka. Amma ki faɗa mata kar ta ƙara shiga harkata, ta tsaya a iya matsayinta na baƙuwa."


Ummie ta ce, "Okay." Ta juya za ta fita ya sake cewa, "Kuma ki faɗa mata ta koya ladabi." Nan ma Ummie ta ce "Okay." 


"And of all things, get her belongings out of my room now." Cikin tsare gida ganin abin na shi ya na neman ya wuce gona da iri Ummie ta ce, "Asaddd!" Jin yadda Ummie ta ambace sunan shi ya sa ya fahimci ya fara kai ta bango hakan ya sa yayi shiru ba tare da ya sake cewa komai ba. Ummie ta juya ta bar ɗakin...


Bin ɗakin ya yi da kallo gaba ɗaya iskar ɗakin canza launi ba yadda ya saba jin ƙamshin ɗakinsa ba. Can ya hango veil ɗinta a ƙasa kusa da sofa. Duban shi ya kai zuwa kan sofar sai ya ga trolley ɗinta a buɗe hargitse da kaya rabi ya na cikin trolley ɗin rabi kuma ya na kan sofa. Tsaki ya ja cikin daren nan ya shiga kimtsa ɗakinsa don ji yq ke yi idan bai gyaran ba, ba zai iya bacci ba. Zai wuce ya hau gado kawai ya ci karo da tin ɗin juice da ta sha ta ajiye sauran ba ta ƙarasa ba. Nan take kuwa sauran juice ɗin ya zube mishi a kan carpet ɗin da ke gefen bedside ɗinsa. Ji ya yi kamar ya yi ihu don takaici.............



********

Farhat ce ta shigo ɗakin Ummie bayan ta kai Hayat ɗakinta sannan ta koma ta kwaso mata kayanta ta kai mata. "Ummie na kwashe duka kayan Hayat daga ɗakin Ya Asad yanzu babu sauran komai kuma." Cewar Farhat ɗin ta na zama kusa da Ummie.


Ummie ta ce, "Na yi na yi na shawo kan Asad yadda za su shirya da Hayat amma abin ya gagara saboda ga dukkan alamu haɗuwarsu ta farko bai fara da kyau ba."


Farhat ta ce, "To Ummie kamata ma yayi ki godewa Allah da bai ga Hayat a cikin shigar jeans ɗinta ba. Kuma kin sa kallon da ya ke yi wa masu irin wannan shigar."


Shiru Ummie ta yi ta na jin Farhat. Can ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Farhat kafin zuwan Hayat na tuna ki na tambayata ko ita ce yarinyar da aka fasa aurenta kwanaki ko?" Farhat ta ce, "Yes, yes."


Wani ajiyar zuciyar Ummie ta sauke ts ce, "Eh ita ce wanda ranar ɗaurin auren imam ya tambayeta ta amince da wannan auren ta ce a'a ba ta amince ba sannan bayan haka ta tashi ta gudu ranar aurenta." Da mamaki Farhat ta zaro ido ta na ɗaura hannu a baki. Ummie ta ce, "Amma kin san meye? Abu mafi muhimmanci shi ne kar Asad ya ji wannan abin da na faɗa miki ko da wasa okay?" Farhat ta jijjiga kai. Sannan Ummie ta ƙarasa da faɗin, "Saboda kin san halinsa sarai kin san me zai biyo baya idan ya ji labari. Sannan bayan haka ma ai na kwanaki kaɗan nan ina fatan komai ya daidaita zuwa lokacin."


Farhat ta ce, "Ummie ina da shawara. Zan faɗa wa Hayat idan Ya Asad na gida ta daina saka ƙananan kaya koh?" Ummie ta ce, "No no. Babu yadda za'a yi mu yi haka Farhat baƙuwa ce fa, kuma babu yadda za'a yi mu saka baƙuwa yin abin da mu ke so. And anyway, lokaci ya yi da Asad zai fahimci cewa akwai mutane masu mabambantan ra'ayoyi da halaye. Kasancewar mutum ya bambanta da kai ta yadda yake tunani ko mu'amala ba yana nufin mutumin banza bane shi. Duk yadda ra'ayin mutum yake, wajibi ne mu girmama shi, Okay?"


Farhat ta kaɗa kai ta na murmushi daga haka ta haye gadon Ummie za ta kwanta. Ummie ta ce, "Meye haka? C'mon tashi ki tafi ɗakinki ba za ki zi ki takura min a nan ba." Farhat ta ce, "Wallahi ni kam Ummie na ga guri sai dai ki yi haƙuri yau don ƙwiyar komawa ɗakina nake yi. Good night." Ta na gama faɗi ta ja blanket ta rufe har kanta. Ta na ji Ummie na mitar za ra takura mata amma ta yi lafur har bacci ya yi awon gaba da ita........



**********


Kwance ya ke idonshi a kan ceiling ya na karanta wasiƙar jakin da ya saba wanda zuwa yanzu ya zame masu jiki. A zuciyarsa ya ke ayyana cewa, "Yanzu tsawon kwana biyu kenan cur har yanzu Leen ba ta kira ni ba. Gashi a karo na biyu babu adadi na sake kara mata zuciya." Ya yi maganar ya na jawo wayarsa da ke gefensa.


"Wai har yanzu ba ka yi bacci ba Lateef? Me kake yi da waya a hannu? Tun safe na lura gaba ɗaya hankalinka na kan waya motsi kaɗan sai ka duba waya ban san meye alaƙantakada waya yau ba." 


Abie ya ce, "Emm dama akwai kiran da na ke expecting ne mai muhimmanci, shiyasa yanzu ma na ƙara dubawa amma har yanzu shiru ne babu wani bayani."


"Yanzu waye zai kiraka a cikin wannan tsohon daren? Me ya sa kake jira kawai ka kwanta ka yi baccinka kiran zai zo ko na da safe ne." Cewar Ammie cikin sigar kwantar da hankali. 


Bai san lokacin da zancen zucin da ya ke ya fito fili ba. Ya ce, "Kiran nan ba zai taɓa shigowa ba."


Ammie ta ce, "Mene?" Abie ya yi saurin waskewa haɗe da faɗin, "A'a karki damu ki koma ki kwanta."



*******


Washe Gari


Gaba ɗaya ahalin Shareeq Khan sun taro a main parlour ɗin gidan ana ta duba kayan auren Hamra da aka kawo daga gidansu Irfan bayan iyayen sun tafi. Akwati guda su ka kawo na Shabka mai cike da kayan zinariya. Sun kawo furanni, da wasu kyaututtuka na musamman. Haka su ka dinga ɗaga kayan ɗaya bayan ɗaya su na sam barka. 


Nudrat ce ta ci karo da mayukan bleaching lokacin da ta ke fiddo da kayan cosmetics. Ta ce, "Ai wannan skin lightning cream ne." Da mamaki sauran mutanen parlourn su ka ɗago su na bin hannunta da ido. Gaba ɗaya jikin yayi sanyi kafin ka ce me, har Hamra ta fara hawaye. Ganin haka ya sa Humairah faɗin, "Hey Nudrat wa ya ce miki duka wannan na Hamra ne? Yanzu haka saboda mu aka sako shi kin san ana saka wa ƙannen amarya na su gift ɗin a cikin Shabka." Ta yi maganar cikin son ta kauda tunanin su da abin da su ke tunani musamman yadda ta ga Hamra ta shiga damuwa lokaci ɗaya. 


Shiru suka yi su duka gaba ɗaya jikinsu a sanyaye su ka ci gaba da duba kayan cikin wani irin yanayi saɓanin da, da su ke yinsa cikin farin ciki da annushuwa. Wani takarda ne ya faɗo daga cikin kayan cosmetic ɗin da Nudrat ke riƙe da su a hannu. Takardar ta ɗauka ta duba sai ta ga an rubuta, "To Hamra." Nudrat ta ce, "No Humairah ba na mu bane sunanta aka rubuta a jiki." 


Tuni hawaye wanke wa Hamrar fuska baƙin ciki ya maye gurbin farin cikin da ta ke ciki. A fusace Afeef ya tashi ya na haɗa kayan tare da faɗin, "Mayar musu da kayansu za'a yi, ba ma so su riƙe tsiyarsu ba matsiyata bane mu." Ammie ta ƙaraso wajen ta na faɗin, "Afeef, Afeef, ka rabu da su, ka ƙyale su." Ko saurarenta ma bai yi ba ya ci gaba da haɗa kayan. Sai da ta zo ta fisge kayan a hannunsa cikin tsawa ta ce, "Wai ba magana na ke yi maka bane Afeef? Me ya sa kake ta wannan fushin ne ko don kai ba'a sako maka komai ba?" Cikin huci ya ce, "Wani irin magana ne wannan Ammie? Ba ki ga irin cin fuskar da su ka yi wa Hamra bane ta hanyar aiko mata da skin lightning cream ba. Don me zamu tsaya ana yi mana irin wannan tozarcin da cin fuska?"


Jaddah ta ce, "Ka yi gaskiya Afeef amma.." Ya tare numfashinta da faɗin, "Amma me Jaddah? Idan har za su iya aiko da waɗannan abubuwan har ma su iya indicating sunanta a kai, ai wannan babban zagi ne da cin fuska a garemu." 


Mom ta miƙe ta na faɗin, "Haba Afeef, abin da kake tunani bane. Idan ma hakan ne to meye a ciki? Ni ban ga wata a nan ba. Saboda ba ka san wahalar da ake sha bane kafin a samu irin waɗannan mutane. Ni kaɗai na san wahalar da na sha. Sannan maganar gaskiya Hamra ta na da kyau sai dai matsalar baƙar fatarta da ya bambamta da mutanen yakinmu na nan. Amma su ka haƙura su ka amshe ta a hakan, to meye don sun aiko mata da mayukan da zai ƙara mata haske?" 


"Mom kin san meye abin takaicin? Product ɗin dw su ka kawo mata kaɗai abin cin fuska ne ba iya mayukan ba. Saboda ina tabbatar miki idan kika shiga ƙananun kasuwannin garin nan babu inda ba za ki ganshi ba an kasa, wasu su kasa akan tebur, wasu a ƙasa, wasu a kai suna tallar shi wasu kuma a wheelbarrow za ki ga su na tura wa.

Sannan ko da gwalagwalai za su kawo mana da lu'ulu'u ba za su taɓa ƙarar mu da komai ba, ahalinmu za su kasance masu ƙarfi fiye da su. Su ya kamata su godewa Allah saboda yar'uwamu Hamra mai matuƙar ƙima da daraja za mu ba su wadda ba za a iya auna muhimmancinta da kuɗi ba. Su ne ya dace su kasance masu godiya, ba mu ba."


Cikin ɓacin rai Mom ta dube Ammie ta ce, "Arwa gidan mace ya kamata su kasance masu takatsantsa a koda yaushe. Ya kamat ki yi wa ɗanki wannan bayanin. An yi wa Hamra baiko da yaro ɗan gidan mutunci, saboda haka idan wani abu ya faru da ya yi sanadiyar lalacewar auren Hamra ta dalilin baƙar zuciya irin na Afeef to babu ruwa." 

A zuciye ya fice ya bar musu wajen ba tare da ya sake cewa komai ba. 



**********


ASAD KHAN EMPIRE


Koda ya tashi da safe, still jin ɗakin ya ke yi kamar ba na sa ba musamman ma gadon da ya kwanta a kai don da ƙyar ya samu ya iya bacci a kai shima saboda bai san lokacin da baccinsa ya sace sa bane saboda kwanciyar Hayat ta yi gadon. Don haka ya tashi da ƙudurin canza gadon gaba ɗaya yau idan ya fita ya saka a zo a sa mishi wani gadon a fita da wancan. 


Wanka ya yi, sannan ya fito ya shirya cikin shigar suite ɗinsa na zuwa office mai launin coffee brown. Zama ya yi gefen bed ya na saka takalmi mistakenly ya zauna a kan raguwar pizza ɗin da Hayat ta ajiye jiya da daddare. 


Da fara'arta ta fito parlourn sanye da wando iya gwiwa sai riga mara nauyi da ya sauko saman cinyarta. Nan ta samu su Ummie har sun gama shirya komai na breakfast ita da Farhat ta ce, "Good morning." Ta ƙarasa ta na ba wa Ummie side hug cikin fara'a. Ummie ta shafa kanta tare da faɗin, "Morning dear how was ur night?" Ta amsa da, "Cool Ummie." Sannan ta ƙarasa inda Farhat ke zaune ita ma ta ba ta side hug su ka gaisa cikin fara'a. Kujerar da yafi ko wani kujera shiga mata rai a wajen ta jawo ta zauna daga Ummie har Farhat su ka zare ido su na ƙoƙarin yi mata magana daidai nan Asad ya fito daga ɗakinsa..........




A hanzarta a fara payment kar a yi babu ku🙌🏻 ɗari #500 ne kacal👌🏻

Saura pages uku free pages su ƙare ɓ

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol