Free chapter · Read without an account

G_D - 20

by Khadeeja Candy · GUMBAR DUTSE

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her +234 ***

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 2️⃣0️⃣

Sai da suka ci suka koshi a waje, sannan Baba Ramatu ta kwashe kayan ta kwankwasa aka bude ta mikawa matashiyar data kawo musu abincin.

"Ga shi tace a baki ki hau abun hawa, ita kuma yarinyar ta shigo"

Kudi ne za su kai 15k aka bawa Baba Ramatu a matsayin kudin abun hawa, ta karba da hannu biyu tana far'a baki har kunne, kyauta da alheri na daga cikin halin Adda Sa'adatu, sam bata da rowa bata rike hannu, ko ta sanka ko bata sanka ba zata iya maka alheri, abun ta baya hadata da kowa, kuma komai ka ga ga kinta zaka shedi cewar tana da yawan kyau, ko ba kadan ba tana yi da yawa, domin tana shi kuma mahaifinta yana da shi, haka ma mijinta da dan'uwanta, bata rasa ba ta ko'ina.

"Ki shiga ciki, kin ji dai duk abun da na kara jan kunnenki a kai ko Batula, dan Allah karki ba mu kunya"

Batula ta daga ido ta kalli Baba Ramatu tana jin kamar ace ta tafi da ita karta a nan da bata san kowa ba, idonta ya cika da hawaye har yana sauko mata.

"Mu mun tafi sai anjima, Allah ya bada hakurin zama"

Ta tsaya a gurin tana ta kallon Baba Talatu da kuma wanda ta yi jagoran kawota gidan tana hawaye, wata zuciyar na bata shawarar ta bi bayansu kar ta zauna a gidan, yayinda ɗayar kuma take tuna mata da gargadin Umma Hindu. Ta share hawayen da suka bata mata fuska ta shigo cikin falon ta zauna a inda ta zauna dazun can raɓen kujera tana ta sharar kwalla. Gaba daya mantawa aka yi da ita a gurin, tana ta jira shiru ba a ce ta taso ta yi wani aikin ba tana rabe a gurin har bachi ya dauke ta.

Sai da ta yi bachinta ta more, daf da zata farka ta ji an shureta da kafa.

"Ke tashi isashiya ai ba bachi kika zo ba, yara sun dawo tashi a nuna miki aikinki a gidan"

Ta zabura ta tashi da sauri.

"Ya sunanki ma?"

Batula ta fara mata na kurame.

"Ki bude baki ki yi magana mana, ni ba zan gane komai a haka ba"

Ta bude bakin ta fito halshenta waje tana nuna Adda Sa'adatu, tare da makoshinta.

"Me ya samu bakin? Miye haka? Ni fa bana son shashanci"

Batula ta yi mata alama da babu.

"Babu me?"

Adda da tsaya tunani, can kuma sai ta canka.

"Baki iya magana"

Batula ta daga kai da sauri jikinta har rawa yake saboda tsoro.

"Kur... Kurma ce ke ko Yaya?"

Ta daga kai, kana ta nuna mata kunnenta alamar tana ji amman bata iya magana.

"Kuma aka kawo min ke? Amfanin me zaki min to? Amman Ramatu ta kai zahilar kauye, yaushe zaka dauko yaro mai nakasa ka kawo a birni ga aiki? Taya ma za'ayi communicating? Shiyasa duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara, da kauye dan kauye ne be taba canjawa yanzu miye amfanin haka?"

"Gaskiya, bata yi tunani ba"

"Ina fa Jalila? Wane irin abu ne wannan? Bari zan duba number ta na ce ta zo ta dauke ta"

Ta fada cike da bacin rai. Wanda aka kira da Jalila ta kalli Batula ta ce.

"Zo na nuna miki dakin yaran"

Batula ta bi bayanta cike da ladabi, zuciya na fal fal fal ita kam dai sam bata natsu da gidan ba, balle kuma mutanen cikinsa. Wani bangare suka nufa Batula na biye har suka isa gaban wasu dakuna ta tura dakin farko ta shiga, Batula ta tsaya bakin kofa har sai da yarinyar ta ce.

"Ki shigo mana kin san ai ba zuwa zan yi na dauko ki ba ko?"

Batula ta shiga jikinta na rawa irin masu tsoro da bakunta. Jalila ta nuna mata dakin.

"Kullum zaki na goge dakin ki share, falo da kitchen akwai mai gyarawa, ke baki aikin kula da yaran ne kawai, idan suka bata dakin ki gyara, idan suna son za su yi wasa su fito musu da kayan wasansu, haka ma idan suka ji yunwa ki zuba musu abinci, idan suka dawo makarantar boko ki cire musu uniform ki wanke ki goge, ki saka musu na islamiya, shi ma idan suka dawo ki saka musu wasu tufafi, suna da uniform set bakwai, so a sati zaki iya wanki sau daya ko biyu, Adda dai bata son taga kayan dauda a dakin yaranta, idan suka cire kaya ki kai gurin wanki akwai mai wankewa, ke uniforms kawai zaki na wanke musu, sai kuma kula da su kar su yi wata barnar ko su bata wani abu ko su kai kansu ga halaka, kullum da asuba za ki tashe su su yi sallah kuma ki shirya musu zuwa makaranta"

Batula ta ji komai, amman bata haddace duka ba, kuma yadda aka zana mata aikin kamar ba zata iya ita kadai ba. Gashi ta ga gado har uku da alama yaran uku ne.

"Kinji ai"

Batula ta daga kai tana kokarin tariyo abubuwan da aka fada mata. Jalila ta bi ko'ina daki daki ta nunawa Batula, har a inda zata aje kayan abincinsu idan sun gama ci, da kuma inda zata dauko ko ta zuba musu, gurin da za ta aje kayan wankin yaran da kayan wasansu duk aka nuna mata. Sannan suka fita daga bangaren gaba daya, BQ Jalila ta kaita ta nuna mata wani daki a cikin dakunan da suke gurin.

"Nan ne dakinki, a nan zaki rika kwana, akwai bandaki a ciki da komai, a nan za ki aje kayanki"

Wani Sabon kunci ya sake mamaya Batula, abu ne mai wahala ta iya rayuwa ita kadai a guri balle kuma nan da bata san kowa ba, kuma daki mai girma kamar wannan. Damuwa ta bayyana a fuskarta amman bata isa ta ce aa ba. Tun a ranar Batula ta fara aikinta tana yi ana mata fada wai kamar ba a fada mata ga yadda zata yi ba.

  Cikin takura da damuwa ta karasa aikin, da dare yayi dayar mai aikin ta kawo mata abincin a wani madaidaicin cooler, ita bata ci a falon ba, domin Adda Sa'adatu ta fada bata bukatar kowa ya ci mata abinci a falo, duk wanda zai ci abinci ya tafi waje. Ta ci abinci da be wuce loma biyar ba, gaba daya kewa da bakunta ya hana cikinta dibar girkin da ya ji nama da kayan hadi mai dadi..

.Tunanin inda zata kwana ya saka ta zare hannunta daga abincin, ya wanke hannu da pure water da aka bata, ta dauki abincin ta tura kofar falon ta shiga da zimmar maida ragowar a kitchen.

"Aa Ba a kai mata ragowar abinci a kitchen idan ba na yaranta ba, sai dai ki aje ragowar a BQ gobe idan za ayi wanke wanke sai ki dauko a wanke, daga yau wannan ce kular abincinki"

Batula ta daga kai, ta zauna a gurin jiki a sanyaye tana kallon tv da hankalinta ma ba gurin yake ba. Yaran suka zo suna tambayar Batula sunanta ita dai ido ta sakar musu, sai Jalila ce ta fada musu cewar bata magana.

"Anty Jalila kurma ce kenan?"

"Eh"

Duk suka zuba mata ido, mai wayon cikinsu ta fara cewa Jalila ta koya mata kurmanci zata yi magana da ita. Batula ta kwanta a gurin rumgume da kolarta domin bata son tafiya BQ ko kadan, bata san ya aka yi ba bachi ya dauke ta sai jin ta yi ana tashinta.

"Ke ba a min bachi a falo, yanzu idan na yi bakin kunya sai a tararda ke kina ta sharbar bachi? Jalila bata fada miki idan kika gama abun da zaki yi ba, BQ zaki rika zuwa? Ko da rana a can ake zama, ina da masu aiki har biyu ke ce ta uku ba sa zama min a falo, tashi ki tafi inda aka nuna miki ki kwanta"

.

Ta tashi rai a jagule kamar wanda bata son tafiya haka ta fita falon, Adda Sa'adatu ta maida kofar ta rufe, Batula ta dade tana kallon BQ din, kamar ba zata ba, hawaye ta yi har ido ya raina fata, ga tsoron gidan ta tsoron kwana ita kadai ta isa dakunan tana yi tana waige kamar ance wani na biye da ita.

  Waje ta samu matan zaune kan tabarma suna ta sauraren littafi a karamar waya, dayar ta dago ta kalleta. Sai Batula ta rabe gefe tana fargabar kar su ma ace kyamar mutane suke.

"Zo nan ki zauna"

Dayar ta fada tana mata alama da ta zo, domin ba su yi zaton ma tana ji ba, a ji kamar an dauke mata wani nauyi kai, ta nufi shimfidar ta sauri ta zauna, sannan ta ake kular abincinta ta hade hannayenta ta musu gaisuwa.

"Allah ka rabamu da talauci, yarinya kurma a dauko ta a kawo aiki, ko tufafi bata zo da su ba"

"Hmmm ke dai Allah ya kyauta, ai indai baka da shi ka shiga uku..."

Suka yi ta tattauna lamuran rayuwa na yau da kullum, Batula na jinsu wani abun har da ita soke jefowa ita dai bata bar musu alamar tana jin abun da suke fada ba. Da dare ya raba dayar cikinsu ta fahimci Batula na tsoron kwana ita kadai a dakin, sai tace ta shigo nata dakin su kwana a tare, ita ta bawa Batula mayafin da zata lulluba ta yi mata shimfida a masa suka ka kwana a daya har safe.

  Da assusuba suka farka dukansu har Batular da bata gama sanin kan gidan ba, bayan sun yi sallah, wanda Batula ta kwana a ɗakinta ta yi mata na kurame.

"Ke ki tafi tun yanzu ki buga kofa ki shiga ki tashi yaran su yi sallah"

Batula ta daga mata kai tana jin tsoro saboda garin be gama wayewa ba, har yanzu da sauran duhu, abun ka da marar galihu haka ta fita dakin ko'ina kallo take kyau kamin ta jefa kafarta domin ganin take kamar wani abu zata taka, duk kuwa da kasancewar akwai haske ko'ina saboda manyan guluf masu matukar haske da aka saka a kowane lungu da sako na gidan. Ta isa bakin kofar ta buga, ta matsa baya ta tsaya, shiru ba a bude ba, ta sake bugawa tana juyawa ta kalli ko'ina wai kar wani abu ya same ta, ta kusan rabi awa tana buga kofar ba a bude ba tsoro duk ya cika ta, ga kuma rashin jindadi da ya gama bayyana a fuskarta.

Guri ta samu ta zauna tana ta kallon harabar, an karka duniya abun da yake dukiya, wasu abubuwa ma bata taba ganinsu ba sai a gidan nan, ga motocin alfarma da shuke shuke ta ko'ina, wani bangaren na gidan an kawata shi da gilashi, an yi rufin da tsawo kamar gidan sama bayan kuma gidan ba gidan sama ba ne. Bayan ta gama bawa idanuwanta abinci ta mike tsaye ta sake buga kofar, wannan karon tana bugawa aka bude mata, Jalila ce tana sanye da kayan bachi wando da riga.

"Shigo"

Batula ta hade hannu biyu ta mata gaisuwa sannan ta shiga cikin falon.

"Ai na nuna miki dakin yaran jiya, shiga ki tashe su su wanke baki su yi sallah, sai ki musu wanka zan zo na nuna miki tufafin da za a saka musu"

Ta nufi hanyar dakin cike da taka tsantsan irin na mai gudun laifi, a kofar dakin ma sai da ta kwankwasa sannan ta tura ta shiga, ta wahala kamin ta samu su tashi daga bachin ta rikasu daya bayan daya suka shiga bandakin sai kuma ta rasa me zata fara musu, domin bata taba amfani da brush ba a rayuwarta, bata ma san yadda za a hada toothpaste ba, da gawayi take wanke baki ko asuwa ba, bandakin ma abun kallo ya zama a gurinta, saboda na su bandakin na kasa ne, wannan kuma ko'ina tiles ne ga haske da wasu karafuna da bata gane kansu ba, ga madubi da kujera har biyu, kallon yadda bandakin yake ya mantar da ida dalilin ta na shigowarsa, Batula ba yarinya ce mai tabe tabe ba balle ta ce bari ta taba wannan da wacan ta ga ko miye a ciki, itadai idonta sun wadatar da ita.

Mamaki be gama cikata ba, sai da babban yarinyar ta nufi abun da take ganin kamar na zama ta ga ta bude shi ta zauna a ciki ta yi fitsari, dayar kuma ta bude madubin ta dauko brush dinsu ta toothpaste, ta tara hannunta a jikin abun da Batula bata san miye ba domin basa da fanfo ta dai ganshi kamar wani karfe mai lankwasa, ga mamakinta sai ya fitar da ruwa, ta kara bude ido ko a mafarki bata taba ganin hanyar ruwa ba bayan gulbi korama ko rafin da suke zuwa dibansa.

Yar kallo ta zama yaran su suka yi komai da kansu, suka gama suka fito, da yake kallon be isheta ba, sai ta sake bin ko'ina tana tantance abubuwa da haddace aikin kowane abu.

Bayan ta fito ta rakube gefe daya tana kallon gadajensu, kusan a rayuwata ba zata ce ta taba bachi akan gado mai katifa da kyau irin wannan ba, Umma Hindu bata barin su hau gadonta na karfe, gashi kuma tarbiya bata barinta hawa gadajen mutane idan ta tafi, a inda suke kwana kuma sai dai sun shinfida tabarma ko buhu su kwanta, da dai gadon kara ne, wannan kam ta sha hawansa ba adadi.

Tsakanin jiya zuwa da ta zo gidan zuwa yau, ta fahimci rayuwa a ba daya ba ce, kuma duniya tana da fadi mutanen cikinta kuma daban dabam ne, ta ga masarrafin ruwa da bata taba ganin irinsa ba, ta ga abun wanke baki ba irin nata ba, ta ga Tv da ba ta yi tunanin akwai irinsa ba, ga kujerun alfarma da ba a barin talaka ya hau kansu, ga Kitchen da gurin cin abinci da aka yi ma gata, a kauyensu mai mota daya girmama shi ake, a nan kuma ga motocin kusan guda biyar a gida daya, ga girman gidan da bata gama tantancewa ba, ta kai hannunta ta taba tiles din gurin da take zaune, abu ne mai matukar sulbi da sanyi ga fari kamar ba a taka shi, wai kuma duk a haka mace biyu da yaya uku ne suke rayuwa a gidan sai masu aiki macen biyun ma bata san matsayin dayar ba, wata kila Hajiyar ce kadai matar gidan.

Taba kofar dakin da aka yi ne ya katse tunaninta, ta tashi da sauri, Jalila ce anan din ma ta sake shigowa, ta leka bandakin ta fito.

"Zo na nuna miki wani abu"

Batula ta bita tsantsin tiles na janta, Jalila ta taba wani gurin tana nunawa Batula.

"Kullum da safe idan kin shigo ki rika taba wannan, ruwan ciki zai yi zafi, nan kuma zaki taba wannan da wannan, dayan na gefen zafi dayan na sanyi, za ki yi mixing ki musu wanka"

Ta karasa gurin flushing shi ma ta nuna mata idan suka yi kashi ta taba wani gurin ruwa su fito su wuce da kashin, karamin kuma ta wanke masa. Batula ta daga mata kai ba dan ta fahimci wasu abubuwan ba. Ta bude shower ta kashe, a nan wani mamakin ya kashe Batula, wato ruwa har ta sama suke zubowa kuma ba ruwan sama ba, ba sai mutum yayi wahalar zubawa ba zubo masa kawai za su yi yayi wanka. Jalila ta dauko mata uniform din yaran sannan ta fice

Bayan da yaran suka gama sallah ta kama hannun karamin ta shiga da shi ciki bandakin, ta daga shi ta saka a tub ta duba inda soap yake ta dauko sannan ta bude ruwan da shower suka sauko, ruwan na sauka jikin yaron yaro ya fasa ihu ya matsa gefe da karfi tana kara, ta murda ta kashe ruwan zafin da sauri jikinta na rawa bata yi zaton ruwan zafi ta kunna ba, yayayunsa na jin ihun yaron suka leko.

"Laaaa ta zuba masa ruwan zafi"

Batula ta girgiza kai da sauri tana nuna abun da ta taba ruwan ya zubo. Dayar kuma ta fita da gudu gurin kiran mahaifiyarsu, Batula ta karasa inda yaron yake tana duba jikinsa idonta har ta fada tsabar tsoro da rawar jiki, domin ba da niya ta yi ba. Tamkar an katse hanjin cikinta haka ta ji lokacin da Adda Sa'adatu ta shigo bathroom din tana sanye da hijab.

"Kona shi kika yi? Babana Daddy me ya same ka?"

Batula ta nuna shower da kuma gurin da ta taba. Adda Sa'adatu ta riko yaronta tana duba jikinsa.

"Mahaukaciyar banza jahila"

Ta kaiwa Batula duka a kokarin Batula na matsawa baya kar ta kai mata dukan ta zame ta fadi kanta ya bugu tub din.

"Ban da hauka yaushe zaki sakewa yaro ruwan zafi? Ko kuma so kika yi ki kashe shi?"

Ta dago dafe da goshi tana hawaye ta girgiza kai, ba nufarta kenan ba. Adda Sa'adatu ta bude shower turirin zafin ruwa ya buge.

"Amman wannan yarinyar so kika yi kashe min ɗa ko? Bayan kurmanci ina jin har da hauka yana damunki, ki fice daga bandakin nan ko na ci ubanki"

Batula ta nufi hanyar fita da gudu, a nan ma ta sake zamewa ta fadi kanta ya bugu tiles din guiwarta ma ta amsa, ta sake tashi tana jin azazaben zafi ta fice daga tafiya tana jin guiwar karfa kamar zata cire. Ta dawo falon ta zauna tana ta hawaye ta dafe goshinta da ya kumburo, gaba daya ta firgice bata san hukuncin da za a mata ba. Adda na fitowa ta sake jifarta da wani zagin.

"Uban me zaki zauna ki min a falo? Ki kona min ɗa kuma ki zauna falon uwarsa saboda baki da hankali?"

Batula ta mike tsaye da sauri ta nufi kofar fita, yadda zata murda ta bude kofar ma ya zame mata aiki, sai da Jalila ta bude mata shi ma dan zata fita, Batula ta fice da sauri ta tsaya harabar gidan tana ta kuka. Tana kallo aka aka saka yaron mota tare da Adda Sa'adatu da direban gidan suka fice da shi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol