Free chapter · Read without an account

G_D - 26

by Khadeeja Candy · GUMBAR DUTSE

*◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦*

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

*Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢*

*Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her +234 ****

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 2️⃣6️⃣

BATULA POV.

Sai da ta yi kamar ta dawo tace a rubuta mata abun da zata siya, sai kuma ta hakura ta kama hanya a haka, babu abun da take ji a yanzu kamar tsoro, gari ne da bata san kowa ba, unguwar da aka kawo ta ma bata san sunanta ba balle nan da Jawad ya dauko ta, ko bata ta yi bata san yadda za ta kwatanta inda za a kaita ba, ba baki balle ta yi bayani, gashi tun da ta fito bayan manyan gidanje da motocin dake wucewa a hanya bata ga alamar wani shago ba.

Haka dai ta mike hanya tana tafe tana waige waige, tafiya ce da ta dauke ta minti talatin da uku, dawowarta haka ne saboda nisan tafiyar da take, unguwar babu mutane balle ta tambaya ina ake siyar da kati, wata zuciyar na raya mata ta koma tace bata gane gurin ba, sai dai zaton ko ta koma za a sake aikowata ko ayi mata fada ya hana ta komawar haka ta cigaba da tafiyar, ta kai karshen hanyar da Hajja Yelwa ta fada mata ta karya kwana ta sake kwarya kwana bata ga shago ba, ta sake mika kafa kenan zata shiga wata kwanar, a cikin daidaikun mutanen da suke tafiya, ta hango wani yana tafiya a hankali, ita tana tunkarar hanyar ne shi kuma yana dawowa. sai da ya kusa isowa inda take sannan ta fara ganin fuskarsa da kyau.

Tsayawa ta yi cak tana kallon mutumen dake sanye da black t-shirt da aka bude maballanta rabin kirjinsa a waje hakan ya bawa kyawawan six-pack dinsa damar bayyana kansu a faffadan kirjin nasa, kansa daure da bakin rawani halshen rawanin ya sauko gefe, fari ne sol, kyakkyawa.

Ta sake dubansa da kyau tana tariyo kamanin mutumen can, ta dora fuskar wacan akan ta wannan da yake dosota sai ta ga babu banbanci, a kamanin da haiba, mazan taka da sura, kwarjini, kyau, cikar zati, tsayayyen tsari, nutsuwa da jarumtaka. Banbancin kawai na hulla da rawa ne, wacan hulla ce a kansa facing kan wannan kuma bakin rawani ne da ya kara masa annuri. Ta tuna abun da yayi mata wacan karon take ta yi baya baya tsoro na kara bayyana a fuskarta, bata gama shawarar abun da zata yi ba, jikinta ya juya kafafuwanta suka ranta a na kare ta fara yankan haryar da iyakar karfinta da nufin komawa gida.

hankalinta be kara tashi ba sai da ta ga yana dugu da ita daidai, kuzari da karfi ba daya ba, kan kace me ya sha gabanta ya juyo yana gudun ta baya baya.

"Toh bari mu gwada gudun tun da shi kike so"

Ya fada fuskarsa mai haske a sake, yana kallonta da idanunsa masu jan hankali, sai ta zube kasa jikinta na rawa numfashinta ma kamar zai fice. Shi ma ya tsaya sai ya sakar mata murmushi mai sanyaya zuciya, kima da martaba shi suka kara bayyana tun kafin ya yi magana.

"Ina zaki je? Me kika zo yi nan?"

Ta kasa amsawa idonta na kanshi Kallonsa kaɗai ya isa ya tabbatar mata da cewa kyawu da kwarjini sun yi masa kyakkyawa masauki a muhalli na musamman.

"Kin iya magana da wannan yaren?"

Da yaren kurmanci yayi mata tambayar ta hanyar amfani da hannunsa, ta sakar masa ido mamaki ya mamayeta.

"Ko baki iya ba?"

Ya sake tambaya da irin maganar kurame, sai ta amsa masa da sauri.

"Na iya"

Ya sakar mata murmushin da ya ratsa idonta ya zauna a zuciyarta, ta sauke idonta kasa kwarjinsa ya cikata ga kuma tsoron da yayi mata kawanya. Bata hankaro ba ta ji hannunsa a fuskarta ya dago ta ta kalleshi.

"Ina zaki je?"

Ya furta, ta dan matsa baya ta amsa masa da taren kurmanci.

"An aike ni na siyo kati ne"

"Waya aike ki?"

"Hajiya"

"Wace Hajiya"

A hankali yake mata magana kamar mai magana da karamin yaro, yakan furta mata ne ita kuma ta amsa masa da kurmanci.

"Gidan da aka kawo ni?"

"Waya kawo ki?"

"Daga kauyen aka kawo ni nan aiki"

Ya mike tsaye da kyau yana kallon unguwar.

"Nan ai bata zaki yi, ba a siyar da kati a unguwar nan, baki ga yanayinta ba? Sai kin je wata unguwa ko zaki samu, duk wanda ya aiko ki nan ya so ki bata ne kawai"

Sai a lokacin da tuna da kudin da suke hannunta, ta fara dube dube.

"Me kike nema?"

"Kudi"

"Ya fadi ko?"

Ta daga kai.

"Amman zaki iya gane gidan daga nan?"

Ta daga kai, ya matsa ya mata baya madadin ta yi haba sai ta juya.

"Ina zuwa?"

Ta juyo.

"Kudi zan dubo ko zan gani"

"Nooo zo muje zan baki wasu, ba zaki ga wacan ba"

"Aa ba zan iya binka ba"

Yayi murmushi.

"Ba abun da zan miki zaki tsaya bakin gate ne na dauko kudin na baki, kin san sunan mai gidan da kika sauka gidansa?"

"Aa amman zan gane gidan"

"Tohm muje"

Ya jera da ita suna tafiya, taku daya biyu sai ta kalleshi sai ta ga fuskarta da murmushi, tana jin tsoro ganin take kamar zai sake taba mata wuyane, shi kam be kalleta ba tun da suka kamo hanya, yana yin murmushin ne saboda ya sani a duk lokacin da ta kalleshi. Cikin unguwar suka dawo gida uku kamin akai na su Jawad mutumen ya tsaya.

"Kin ga gida nan, bari na dauko miki kudin"

Batula ya tsaya ta daga kai tana kallon gidan mai farin fenti da bakin gate, hannunsa ya saka aljihu ya ciro remove ya matsa gate din ya fara rabewa biyu.

"Ko zaki shigo?"

"Aa, ni ka bar kudin zan fada musu ya fadi"

Ta juya.

"Za su miki duka kuwa"

Maganarsa ya saka ta juyo cikin yanayin damuwa.

"Kai ka taba min wuya"

Yayi murmushi ya daga mata kai.

"Ni ne, zo mana na dauko kudin na baki"

Wannan karon ta samu kanta da kasa masa musu, ba dan ranta ya so ba ta bishi kamar zata yi kuka. Gida ne babba mai girma komai na harabar black na white ne, an yi tsarin gidan kamar na turawa komai sab irin na masu tsari da gayu. Gidan sama ne da aka kawata ko'ina da fulawoyi masu zagaye har kan windows.

Da alama mai gidan gwanin son furanni ne, ya isa gabna wata makekiyar kofa ya saka code ta bude, sai ya juyo ya miko mata hannunsa.

Ta marairaice fuska kamar zata masa kuka ta girgiza kai alamar ba zata shiga ba, mutunen ma yana bata tsoro ballen gidan da bata san abun da zai mata ba.

"Ba zan cutar da ke ba, kawai ina son mu sabu ne, tun a lokacin da na fara ganinki hankalina ya kwanta da ke, da kika gan ni can na tafi yawo ne, akan dokina duk inda zan je doki nake hawa saboda na saba, ina da motoci"

Ya nuna mata saitin inda motocinsa suke ta juya kalli gurin, an yi musu kebantaccen guri gurin ma an kawata shi da furrani.

"Sai dole nake hawan mota, na fi son hawan doki"

Ya nuna bangaren dokin, ya juyar da idonta can ta kalli kosashen bakin dokin dake cikin ni'ima.

"Kin ga yanzu ai mun zama makota, duk lokacin da kike bukatar abokin hira, ko aka bata miki rai, sai ki zo gurina, ban taba tunanin Allah zai sake hadamu ba, amman yanzu kin ga mun hadu"

Ta girgiza masa mai ta juya da sauri daman tun farko bata san dalilin ta na biyo shi ba. Ya saka yatsunsa biyu a bakinsa can kasa halshensa yayi fito, dai ga wani katon bakin kare mai katon baki ya fito da gudu, sanye da sarka a wuya yana haushi, kafa mi na ci ban baki haka Batula ta dawo da gudu ta tsaya kusa da shi da hannu yayi ma karen alama da ya tsaya sai kuma ya tsaya. Sai da ya fara shiga ciki sannan ta shiga. Dan fili ne da aka yi ma kwalliya ga gurin aje talkami da saka wasu, ya cire nasa talkamin ya saka na gida sannan ya kalli kafarta.

"Ina talkaminki"

"Bana saka talkami haka nake yawo"

Ta amsa da kurmanci jikinta na ta rawa kana kallonta kasan tsoro take ji hawaye kamar za su fito mata. Matsawa yayi musa da ita sai ta masa baya ya kara matsawa be tsaya ba har ta kai jikin kofar falon tana kallonsa hankalinta a tashi, hannunsa ya kai ya kama rigar jikinta ya karanta rubutun dake jiki da kyau kasancewa logon kawai ake gani, rubutun yayi kanana sai an matsa an saka ido sosai. Ga rigar ta yi mata kyau sosai duk da kasancewar ta mata fadi kuma ta mata tsayi. Ta maida numfashi kamshin turarensa mai dadi ya ziyarci hancinta.

"Stairs zamu hau"

Ya nuna mata, domin komai na gidan yana sama ne, ba irin gidansu Jawad ba ne da dakunan suke sama falo a kasa.

"Aa ni ban taba hawa gidan sama ba, bana so tsoro nake ji, dan Allah ka bar ni na tafi gidan da aka kawo ni"

"Zan barki ai ba wani abun zan miki ba"

Ya kama hannunta, sai ta fisge.

"Aa bana so, ina ganin jiri bana son na hau tsoro nake ji, ko can gidan bana hawa sama"

Hawaye ya fara sauko mata.

"To ya kamata ki koya, gidajen unguwar nan ai gaba daya gidan sama ne, gidan da kika zo ma ai gidan sama ne"

Ya rika hannunta tana girgiza masa ga numfashi na fita karfi, amman be sake ta ganin babu sarki sai Allah yasa ta rike hannunsa da karfi tana jin baya kamar zata zauna.

"Taso ki hau"

Ya sake janyota, hawaye na sauko mata ta rike shi gam, ta fara taka stairs din.

"Rufe idonki"

Ta runtse idon da karfi, kowane step tana dakashi ne da bugun zuciyarta da fitar numfashi mai karfi, yana kallonta yana murmushi har suka haura.

"Toh ba gashi ba har mun haura"

Ta bude ido sai jiri ya dauke ta yi saurin runtse ido ta duka kasa tana kuka.

"Babu wani matsala fa"

Ya rikata daker suka sauko, ya sake haura da ita, da za su sake yin na biyar ya saka ta bude idon ya haura da ita idonta a bude suka sauko idonta a bude amman numfashinta na tsayawa domin har lokacin tsoro take ji, ya gwada haka da ita kusan sau goma sha biyar tun tana jin tsoro tana hawa haka har ta dan fara sakewa.

"Yanzu zaki iya hawa da kanki"

Ta girgiza kai.

"Zaki iya, ki rike wannan karfen kina tafiya, sai ki yi haka ki sauko"

Duk yadda ta nuna masa ba zata iya ba, be barta ba a dole sai da ta gwada hawan ita kadai tana rike karfen ta kai har sama sannan ta sauko, ta yi hakan sau hudu, ko wane yi sai ya taba mata ya karfafa mata guiwa, ana biyar be bari ta sauko ba ya haura ya isa bakin kofar falon ya fara wucewa.

Ta bi bayansa ta shiga da tsoro, ba fentin gidan ne kawai baki da fari ba, har kujerun falon bakake ne haka ma curtains din bakake ne, fentin falon kuma fari sol, kowane lumgu da sako na falon fulawoyi ne, shi ma dai cike yake da sanyi kamar na gidansu Jawad.

Rawanin kansa ne farkon abun da ya fara cirewa lokacin da suka shiga falon, gashin dake dunkule a kansa ya sauko har bayansa, gashin kansa har ya fi nata kyau da gyara, domin nata kitson kanta ma ya tsufa, abu ne sabo a gurin ta, namiji da gashi, bata taba gani ba ya juyo ya kalleta yana aika mata da murmushinsa mai sanyi.

"Ka ba ni kudin zan tafi"

"Zan dauko miki"

Ya nufi wata kofar, kamin ya shiga ya juyo ya kalleta.

"Zaki ci abinci?"

Ta girgiza kai.

"Ba zaki ci girkin maza ba? Amman kina saka rigar maza"

Ta yi shiru kawai tana kallonsa. Ya shiga be dade ba ya fito rike da plate dauke da soyayen dankali turawa.

"Abincina tun na safe ban samu na ci ba"

Ya zauna ya fara daukar dankalin yana ci, ganin hakan ya saka ta fahimci ba kudin zai bata ba ta juya da nufin ficewa.

"Kina son ki tambaye ni?"

Ta juyo ta daga masa kai.

"Minene?"

"Kai wanene?"

Yayi murmushi.

"Sai me kuma?"

"Miyasa ka matse min wuta ranar?"

"Saboda kin min kyau, ina son na san sunanki, ban san kin iya yaren kurame ba shiyasa"

"Ya aka yi ka iya yaren kurame bayan kuma kai kana magana?"

"Ni ai na iya abubuwa da yawa"

"Miye sunanka.?"

Yayi murmushi yana kallonta na wasu dakiku kamin ya amsa.

"Maza"

"Maza"

Ta maimaita da yaren kurmanci tana kallon idonsa, sai ya daga mata kai a hankali yana murmushinsa mai kyau.

"GUMBAR DUTSE..."

Kwarjininsa ya isa cikin idonta, da ko wane karo murmushinsa fadar mata da gaba yake, ta sauke kai kasa, can kuma ta dago tana kallon falon dake ta kamshin turaren yar fillo +234 ***, ga wani katon hoton wata mata lake a falon daga can sama, gefen hoton kuma hotunan yara ne. Shi ma juyawa yayi ya kalli hotunan, ya dauke kai ya juyo ya mike tsaye dauke da plate din ya isa inda take tsaye.

"Bude baki"

Kwarjininsa ya hanata musa a karo na biyu, kamar yadda ya sakata shigowa gidansa. Ta bude bakin a hankali ya saka mata zirin soyayyen Irish din.

"Rufe"

Ta rufe.

"Zauna"

Ta fara taunawa a hankali.

"Yanzu kin ga ni da ke mun zama kawaye, idan kina son zuwa nan da kowane lokaci zaki iya zuwa, kuma idan kin zo ki sake jikinki kamar kina gidanku"

Kallonsa ne kawai abun da take.

"Sauka ki jirani, bari na sha ruwa na zo na raka ki, sai mu fada musu bata kika yi ko?"

Ya lakaci hancinta da karamin yatsansa yana murmushi, ta bishi da ido har ya koma dakin da ya shiga dazun, sannan ta juya ta fita falon, tana rike karfen stairs din ta sauka kasa a hankali har tana mamakin kanta, ashe zata iya tsoron fadowa ko zamewa yana nan tare da ita, sai dai ta cilasta ma kanta koyar hawa da sauka ne saboda ta saba.

Sai da ta sauka kasa gaba daya sannan ta dawo ta gefen stairs din ta daga kanta kasa tana kallon kofar falo. Hango shi ta yi ya fito rike da gorar ruwa daga can shi ma ya tsaya yana aiko mata murmushi, kallonsa dai kawai take zuciyarta cike da tambayoyi da kuma fargaba. Bude ruwan yayi ya sha sannan ya sauko ya bude mata kofar falon ta fara fita, shi ma ya fita. Tana kallonsa ya jefar da gorar ya ciro wata roba a hannunsa ya tattara gashinsa ya daure guri daya, sai kuma hakan ya kara masa kyau, ya saka maida hannun aljihu ya ciro 1k ya mika mata. Ya cire dankalin daya lulluba da shi ya mika mata a hannun gyalen dake kafadarta ya maida mata shi saman kai, sai gashi ta fito yar birni abunta.

"Mu tafi"

Ta fara tafiya, ya bi bayanta suna nisa ta juyo.

"Kare nan zai iya cizo na"

"Sai na kira shi yake zuwa"

Bata yarda ba, tana tafiya tana waige hankalinta be kwanta ba sai da suka fice gidan ya sake amfani da remote dinsa ya matsa gate din ya rufe kansa, sannan suka kama hanya suna isa bakin gate din gidansu Jawad ta fada masa nan ne gidan.

"Tohm shiga, kin ga ba mu da nisa, da kin tashi gidana kawai zaki zo gida uku ne tsakaninmu"

Ta tura kofar dake bude ta shiga mutumen ma ya shiga, Mai gadin dake daga cikin gidan ya taso da saurinsa zai tare mutumen.

JAWAD POV.

Tsayawa yayi shi da Ariz suna kallon gate din da Batula ta shigo tare da wani namijin da ba su san waye ba, Izza ta hana Jawad karasawa ko daga murya ya tambaya sai hannunsa yayi amfani fa shi ya yi ma mai gadin alama da ya bar su su karaso, Batula na gaba Jawad na kallon kowane takuna na kafarta da babu talkami, mutumen na bayan hannayensa hade a abayansa har suka iso inda Jawad da Ariz din suke tsaye, kamshi turaren mutumen ya zagaya, na Jawad ya zagayo suka hade da juna suka gauraya, suka bada wani kalar kamshi mai wuyar fasasara.

Mutumen ya mikawa Ariz hannu suka gaisa sannan ya bawa Jawad, Jawad ya daga masa kai kawai fuska ba yabo ba fallasa daman shi be gaisawa da wanda be sani ba.

"Ta bata ne tace nan ne gidan da take, shiyasa na kawo ta"

"Yanzu nan ake ta nemanta, ka kyauta gaskiya mun gode Allah ya saka da alheri"

"Karka damu, yi wa kaine"

"Batula"

Ya kira batula da idonta yake kasa, ta dago ta dube shi, dan kar su fahimci abun da yake son fada sai yayi mata magana da kurmanci.

"Ni zan tafi sai anjima, idan kika tashi kawo min ziyara ina nan koda yaushe"

Ya aika mata da murmushi, sai a lokacin ta karbi kyautar murmushin da yake ta mata, ta ba shi nata kadan dake nuna alamar godiya. Uffan Jawad be ce ba har mutumen ya fice, Jawad ya juyo ya dawo bangaren Gwaggo Batula da Ariz suka biyo shi, sama ya haura, Ariz ya labarta ma Gwaggo abun da ya faru yana dorawa da.

"Ko gaisuwarsa fa be amsa ba, balle ya masa godiya"

"Wannan mai siffar yan daudu zan yi ma godiya?"

Jawad dake daukowa ya fada, Ariz ya saki baki.

"Wannan Mutumen zaka cewa haka? Ya fika mazantaka fa, kawai dan ya bar gashi? Ai ka zauna turai kaga yadda maza suke barin gashi kuma ba haramun ba ne"

"Ya dai fika kai, ni ban yarda akwai namijin da ya fini ba"

Ya fada cike da kufula, ya mikawa Batula littafi da biro. Tana karba ta san abun da yake nufi bata jira ya tambaye ta ba ta rubuta masa abun da ya faru, ta mika masa.

Ya karba ya karanta a take yanayin fuskarsa ya kara sauyawa zuwa bacin rai, daman be warke daga wanda Adda Sa'adatu ta saka masa ba, ya karbi pen din yayi rubutu akai ya mika mata.

"Waya baki kudin?"

"Ban san sunanta ba"

Ta rubuta masa.

"Muje can bangaren"

Ya furta sai ta mike tsaye ta wuce gabansa ta fita fallon ya rufa mata baya, aka bar Ariz da Gwaggo da ke ta fada wai saboda me za a aike ta yarinya bata san gari ba.

***

Shin wai waye mutumen nan ne?

Yaushe Batula zata samu hutu?

Wa Jawad zai aura?

Zinatu zata dawo ga tsohon masoyinta Jawad ko aa?

Me ya raba Zinatu da Jawad?

Turaki zai hadu da Batula?

Hajja Yelwa zata so matar da Adda ta samo masa?

Adda Zata so wata, bayan matar da ta samowa kanenta?

Jawad zai yarda ya auri Ayla da Hajja ke masa kamfen?

Batula zata samu walwala a gidan?

Ya rayuwarta zata kasance?

Bakinta zai bude?

Ina labarin kawayenta?

Da karkarar da ta baro?

Da mutanen da suka cutar da ita?

Hajja Yelwa zata hakura ta sakawa Jawad da Adda ido?

Zata bar Batula ta huta?

A gurin wa Batula zata samu hutu da kulawa?

Ta ina?

Turaki da Jawad za su samu fahimtar juna?

Miye labarin Turaki da iyalan gidansa?

Turaki zai yarda kanwarsa ta sake kula Jawad?

Wa Ariz zai aura?

Akwai tambayoyi da yawa da kuke bukatar amsoshinsu, duka kuma amsar tana dunkule a cikin littafin GUMBAR DUTSE book 2

_____________________

Laifin dadi karewa inji masu iya magana.

A nan na kawo karshen book 1 na Gumbar Dutse.

Khadeeja Candy✍️

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol