Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Amanarcool · SAUTIN KARSHE




Farin cikin da Faruk yake ciki ya kasa ɓoyuwa a fuskarsa, cikin hanzari ya tashi ya shiga gida. Sudais kuwa duƙar da kansa ya yi ƙasa yana jin wani abu ya tokare masa ƙirji, wannan auren da aka ɗaura masa ya sa shi tuna wani abu da ko a mafarki bai yi zaton ganinsa ba ko kuma faruwarsa, ji ya yi Hanif ya zungure shi, ɗago da kansa ya yi yana kallonsa, kafin ya yi magana jama'a suka fara zuwa suna yi masa barka da fatan Allah ya sanya alkhairi. Hanif ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Ni ba na son wannan munafurcin, malam ka saki jiki ka nuna farin cikinka tunda da ma abin da kake nema ne ya samu" ya ƙarasa maganar yana murmushi. Banza ya yi da shi ya ci gaba da gaisawa da jama'a. Dady ma sai taya shi murna ake yi. Alhaji Bashir tsabar kunyar da ya ji ana gama ɗaura auren babu wanda ya san tafiyarsa. 
Cikin tsananin farin ciki Faruk ya shiga gidan, Mammy na zaune a falo tare da jama'arta, yana zuwa ya zagaya ta bayanta ya duƙar da kansa daidai kunnenta ya ce "Mammy an ɗaura an ɗaura." Mammy ta yi murmushi tana faɗin ma sha Allah, finally dai Ilham ta zama mrs Sadikk, Allahumma bareek, Ubangiji Allah ya ba su zaman lafiya da zuri'ar ɗayyiba." 

"Mammy ba fa da Saddik aka ɗaura auren ba." Cewar Faruk yana kallonta, jin abin da ya faɗa ne ya sa jama'ar gurin juyo suka kalle shi. "To idan ba da Saddik aka ɗaura auren ba da wa aka ɗaura?" Mammy ta tambaya, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Da Yaya Sudais, Mammy Allah dai ya nufa Yaya ne mijin Ilham." Da wani irin mamaki Mammy take binsa da kallo, ƙanwarta da take zaune a kusa da ita ta ce "Sudais kuma? Kamar yaya? Ka yi mana bayani yadda za mu fahimta." Faruk ya ce "Kamar yadda kuka ji na daɗa Aunty, Allah bai nufa da Saddik za a ɗaura auren ba, shi ya sa sai da aka zo gurin ɗaurin auren sai aka fasa yi da shi aka ɗaura da Yaya." Yana gama faɗar hakan ya bar falon. Wani uban ihu Zahra ta yi, a guje ta juya ta koma ciki. Kamar wadda aka jefo ta shiga ɗakin, Ilham ta ce "Subhanallah Zahra lafiya kuwa?". 

"Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah, Allah kai ne abin godiya, congratulations Aunty Ilham an ɗaura, an ɗaura aurenki da Yaya Sudais ba Saddik ba." Zabura Ilham ta yi da ƙarfi ta riƙe Zahra tana faɗin "Ban son irin haka Zahra, wace irin magana ce kike yi? Ke da kike rarrashina da ba ni haƙuri shi ne za ki dawo kina zolayata?" Ta kai ƙarshen maganar muryarta na rawa, Zahra ta dube ta da kyau ta ce "Har abada ba zan taɓa zolayarki ba ko in faɗin abin da na san zai saka ki yin kuka ƴar uwa, wallahi Allah da Yaya Sudais aka ɗaura miki aure ba da Saddik ba." Ilham na jin sai ta saki Zahra daga riƙon da ta yi mata, ta koma bakin gado ta zauna ta yi shiru tana tunanin saƙon da aka turo mata jiya da daddare, lokaci ɗaya ta fashe da kukan farin ciki, da sauri Zahra ta zauna a kusa da ita ta dafa ta tana faɗin "Haba Aunty me ye haka kuma? Ke da ya kamata ki yi godiya ga Allah da ya cika miki burinki ya karɓi addu'ar da muka daɗe muna yi. Ai ba kuka ya kamata ki yi ba, yau ranar farin ciki ce a gare mu baki ɗaya."

Ilham ta goge hawayeta, wani irin murmushi mai cike da nuna tsantsar farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce "Zarha wani daɗin idan ya yi yawa ba ka sanin lokacin da kuka farin ciki yake zuwar maka, haƙiƙa yau ta kasance rana mai ɗunbin tarihi a gare ni, ranar da na daɗe ina fatan zuwanta, ranar da har na fitar da rai da ganinta sai gashi Allah ya nuna mini ita, kai Alhamdulillah Allah nagode ma da ka amsa addu'ata. Yau nazama mrs Sudais." ta kai ƙarshen maganar tana faɗuwa kwance saman gadon. Ummie ta ce "Sannu Ilham, da farko ina taya ki murnar samun muradin ranki, Allah ya sanya alkhairi, wato tsabar jin daɗi ba zama ki tsaya tambayar dalilin daya sa aka fasa aurenki da waccan ba?" 

Ilham ta ce "Ban damu da sanin da lilin da ya sa a ka fasa aurena da Saddik ba, ina da tabbacin koma me ye Allah ne ya ji tausayin boyarsa ya ba ni Yaya Sudais a lokacin da na fitar da rai da samunsa." Nan suka fara tsokanarta, Ilham ko a jikinta, sai gashi ta saki jiki kamar ba ita ba.

Da ƙyar Sudais ya samu ya zillewa jama'a ya bar gurin, motar Hanif ya shiga ya zauna yana kunshe idonsa, ya kasa tantance a wane hali yake ciki. Hanif ya ce "Duk wannan abin da kake yi na me ye? Ni fa iyayi ne ba na so." 

"Hanif ja motar nan mu tafi bacci nake ji" Sudais ya yi maganar ba tare da ya kalle shi ba, shi ma bai sake bi ta kansa ba ya tada motar suka bar gurin.

Lokacin da Momy ta samu labarin wanda a ka ɗaura auren da shi masifa ta dinga yi kamar za ta tashi sama. Nan ta fara kiran wayar Dady sai dai bai ɗaga ba, wayar Ilham ta kira, tana ɗauka ta balbale ta da masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Ilham na jinta ta yi mata shiru, sai da ta gaji don kanta ta kashe wayar.

Murmushi Ilham ta yi, ta shiga gidan message ta turawa Sudais saƙo sannan ta ajiye wayarta. Shiru ta yi tana tunanin saƙon da a ka turo mata jiya da daddare, "Assalamu alaikum ƴata, sunana Hajiya Amina mahaifiyar Saddik, Ilham na turo miki saƙon nan ne saboda ina son in ji gaskiya daga gare ki ba tare da kowa ya sani ba. Ina so ki san cewar farin cikin ɗana yana da matuƙar muhimmanci a gare ni, sannan kema ina son farin cikinki, don haka daga ke har shi ba na son a tilasta wa ɗayan ku auren wanda zuciyarsa ba ya so. Na ji wasu maganganu na cewar auren dole ne a ke son yi miki da Saddik, shi ne bari in tambaye ki domin in tabbatar da gaskiyar da nake son ji daga gare ki. Ina roƙonki da ki faɗa mini gaskiya ba tare da jin tsoro ko kuma jin kunyata ba, idan har kin san ba ki son Saddik ki gaya mini. Ba zan ji haushinki ba, kuma ba zan sanar da kowa cewar na yi magana da ke ba. Idan har da gaske ba kya son wannan auren, zan tsaya tsayin daka wajen tabbatar da cewar ba a yi auren ba. Duk da cewar gobe ne ɗaurin auren kuwa, domin ni a tsarina babu auren dole a ciki. Ki kwantar da hankalinki ki yi mini bayani, duk abin da za ki faɗa zai tsaya tsakanina da ke ne." Ilham ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gama tunanin saƙon da mahaifiyar Saddik ta turo mata.

...…

"Amina"

"Na'am"

"Me ye dalilin da ya sa kika a fasa auren nan? Kuma ba ki tashi cewa a fasa ba sai ranar ɗaurin auren? A ranar ma sai da kika bari an je gurin ɗaurin auren? Wannan wane irin abu ne haka? Amina kin san kunyar da kika sa na ji kuwa? Kin san amintakar dake tsakanina da Nasir kuwa? Ni na ma rasa me ya sa na biye miki har na aikata abin da bai kamata na aikata ba, wallahi sai yanzu nake danasanin biye miki da na yi."

Amina ta ce "Alhaji sai dai fa ka yi haƙuri, domin a yanzu dai ta faru ta ƙare, ka san kwata-kwata auren dole baya cikin tsarina. Duk wanda nake da iko da shi ba zan bari a yi masa auren dole ba, to balle kuma har in bari a yi shi a gidana. Yarinyar nan ba ta son Saddik Yayanta take so, mahaifiyarta ce ke son tilasta mata auren Saddik saboda Yayan na ta ya ƙi saurarenta, ni kuma da na samu labari shi ne na tambayi yarinyar cikin hikima kuma ta tabbatar mini da haka, to a kan me zan bari a aurawa ɗana ɗaya tilo da nake da shi yarinyar da ba ta son shi? Salon ta zo ta jefa mini shi a cikin wani hali? A'a ba da ni za a yi wannan ba."

Alhaji Bashir na ji abin da matarsa ta faɗa sai jikinsa ya yi sanyi, domin shi ma baya goyon bayan auren dole, kuma ya san tunda har ta faɗi haka to da gaske ne, saboda duk masifarta sai ta tabbatar da abu kafin take yanke hukunci a kansa. Ya ce "Shikenan Allah hakan shi ne mafi alkhairi." ta amsa da "Amin" tana faɗin "Ai shi ne ma alkhairin."
....

Ba ƙaramar dambarwa a ka yi tsakanin Dady da Momy ba kafin ta amince da zancen auren nan, domin kuwa ƙiri-ƙiri ta ce "Sai Sudais ya sakar mata ƴarta tunda ba sonta yake yi ba, munufurci ne aka ƙulla shi ya sa a ka warware aurenta da Saddik a ka aura masa ita." Sai da Dady ya nuna mata cewar namiji sannan ta saduda, sai dai ta ce "Kar a dawo da Ilham gidan nan, a bar ta can ta zauna a ɗakinta." Dady ya ce "Ai ko ba ki faɗa ba da ma ba za ta dawo gidan nan ba, ta tafi kenan sai dai ta zo mana ziyara." Yana faɗar haka ya fice ya ba ta guri ta shiga surfa masifa. 

Sudais na kwance a wani gidansa da yake can wajen gari inda yake zuwa ya huta idan baya son hayaniya. Hanif na gefensa sai tsiya yake yi masa tare da cewar "Shi ma yau zai shiga daga ciki" shi kuma ya yi masa banza domin bashi da lokacin da zai biye masa, hankalinsa yana wani gurin, ɗakko wayarsa ya yi zai duba wani abu sai kawai ya ci karo da saƙon da Ilham ta turo masa. 
"Ban san yadda zan bayyana maka farin cikin da ke cikin zuciyata ba, tun farko burina da addu'ata kai ne, kuma duk da yadda abubuwa suka kasance, Allah cikin ikonsa ya ƙaddari kai ne dai mijina. Wannan ya sa na ƙara yarda da cewa abin da Allah ya rubuta wa bawa ba ya wuce shi. Alhamdulillah, na yi matuƙar farin ciki da kasancewarka mijina. Ina roƙon Allah ya sa albarka a cikin aurenmu.Ya sa soyayya, da fahimtar juna a tsakaninmu, Allah ya sa mu kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali na har abada, ya haɗa zukatanmu a guri ɗaya. Ya kuma sa mu kasance tare har ƙarshen rayuwarmu.
Ina sonka mijina, kuma ina gode wa Allah da ya sa ka zama rabona. Allah ya ba mu zaman lafiya da zuri'ar ɗayyiba. Ka huta lafiya my lovely husband." 

"Hmmm" shi ne kawai abin da ya faɗa ya ajiye wayar ba tare da ya yi abin da ya so yi da wayar ba. 

Sosai Mammy take mamakin me ya sa a ka fasa auren da Saddik a ka ɗaura da Sudais, lokacin da Faruk ya dawo gida har ɗaki ta je ta same shi tana tambayarsa amma ya ce mata shi ma bai san dalili ba, ta kira wayar Dady nan ya sanar da ita bai san dalili ba shi ma, amma zai zauna da Bashir ya ji me ya faru. Duk da a yanzu koma me ye ai aikin gama ya gama tunda har an mayar da auren ga Sudais. Dady ya gaya wa Mammy cewar a bar Ilham nan ba sai ta koma wancan gidan ba, Mammy ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ai uwa uwa ce, dole ne ta je ta yi bankwana da mahaifiyarta kuma ta riƙe ta gafara." Ba zai iya musu da ita ba ya sa shi ce mata "To" bayan sallar azahar Mammy ta sa a ka mayar da Ilham can gurin Momy.

Momy ba ta bi ta kan Ilham ba ta ci gaba da sabgogenta, sai da yamma ta yi lokacin da Dady ya ce "Ta shirya a kai ta ɗakin mijinta. Ya sanar da su nan gidansu Mammy za a kai ta ɓangaren Sudais, kafin ya gama gyaran gidansa." Sai a lokacin Momy ta kira ta ɗakinta, Ilham na zaune bakin gado ta sunkuyar da kanta. Momy ta ƙare mata kallo sannan ta ce "Ina taya ki murna na samun abin da kike so, sai dai ba baki nake yi miki ba, Ilham ina jiye miki abin da zai je ya dawo, tun farko na nuna miki ban amince da aurenki da wannan yaron ba. Ba don ba na son farin cikinki ba, sai don abin da idona yake gani, na so ki aure Saddik domin ina da tabbacin a can ne za ki samu dukkan farin cikin da kike buƙata, amma saboda munafurci a ka yi kitimurmurar da sai da a ka fasa aurenki da shi da a ka mayar ga wanda kuke so ke da mahaifinki. Duk da haka ba zan fasa yi miki nasiha ba, ki sani aure ba wasa ba ne. Gidan miji ba gidan uba ba ne. Ba kowace magana ake gaya wa miji ba, ba kuma kowa ne hawaye ne za a share miki ba, ina so ki yi haƙuri, ki riƙe mutuncinki, ki kiyaye addininki, ka da soyayya ta rufe miki ido har ki manta da darajarki ta ƴa mace, idan kin ga ana tauye miki haƙƙinki, ko ana muzanta miki, ka da ki ce za ki yi shiru saboda gudun ki ɓata ran wani, ki fito ki yi magana, Allah ya ba ku zaman lafiya."

Cikin kuka Ilham ta ce "Momy don Allah ki yi haƙuri ba ni da masaniya a kan fasa auren.." ba ta ƙarasa Momy ta ce "Tashi ki wuce ana jiranki, ba na son jin komai daga gare ki, koma me ye ki je kawai." "Momy don Allah kar ki yi mini baki." 

"Ilham tashi ki tafi, Allah ya sa albarka a cikin rayuwar aurenki." Tashi ta yi tana kuka, Dady da kan shi ya saka ta a mota ya bar gidan da ita.


Amanarcool
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol