Free chapter · Read without an account
Chapter 21
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
Tunda suka dawo daga asibiti take bacci sai yanzu ta farka, ba laifi ta ji ƙarfin jikinta sosai sakamakon magunguna da ta sha. Ko da ta kalli agogon ɗakin taga ƙarfe biyu daidai. Tashi ta yi ta shiga toilet ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallah falo ta fito ta zauna, Momy ta kira a waya suka gaisa, sannan ta kira Daddy shi ma suka gaisa, nan ya sake yi mata nasiha, godiya ta yi masa sosai sannan suka yi sallama. Tana ajiye wayar ta ji ana knocking, jin ba a shigo ba kai tsaye ya sa ta yi tunanin Zahra ce, tashi ta yi ta je ta buɗe ƙofar, Sudais ta gani a tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa. Da sauri ta ja da baya tana faɗin "Sannu da zuwa Yaya." Ta yi maganar tana ƙoƙarin karɓar jakar hannunsa, bai amsa mata ba, kuma bai ba ta jakar ba, ya raɓa ta ya wuce, da falo ya so ya zauna amma ganin Ilham, da kuma shigar da take jikinta, ya sa ya wuce bedroom ɗinsa, domin idan ya zauna yana kallonta da wannan shigar za a iya samun matsala.
Bai daɗe da shiga ba sai ga Zahra ta zo ta kawo musu abinci, Ilham ta yi murmushi ta ce "Thank you so much Zahra, da ma yanzu nake shirin zuwa wajen Mammy in ci abinci, saboda wata irin yunwa nake ji." Dariya Zahra ta yi ta ce "To na hutar dake ba sai kin je ba."
"Ai kuwa dai kin kyauta, in sha Allah gobe zan fara girki da kaina, yau ma na so in fara to sai ya zamana ba na jin daɗi." Ta yi maganar tana murmushi.
"Allah ya sauwwaƙe Anty, ki ce gobe zamu fara shiga kitchen? Don kin san tare zamu yi girkin nan, tunda ke tun farko kina faɗin ba kya son ƴar aiki." Daga haka Zahra ta juya tana faɗin "Bari in gudu kar Yaya ya ce na cika masa mata da surutuna."
Danning ta kai abincin, ta zuba na ta ta ci, bayan ta gama ci ne, ta yi shiru tana tunanin ko ta je ta yi masa magana ya zo ya ci abinci? "To idan kuma na je ya rufe ni da masifa fa? Tunda ya gargaɗe da in daina shigar masa ɗaki." Ta yi maganar a hankali, "Ai mijinki ne, kuma ya zama wajibi ki dinga kula da shi, ko da ba zai kula ki ba, je ki ce masa ga abincinsa nan." Wata zuciyar ta ce nusar da ita hakan. Tashi ta yi ta je ƙofar bedroom ɗinsa ta tsaya, knocking ta yi amma shiru bai amsa ba, ta sake yin wani, nan ma shiru, sai a karo na uku ya ce "Lafiya dai?"
Ta ce "Da ma abinci ne na ce ko za ka ci a kawo maka? Ko kuma a bar shi a dinning ka zo nan ka ci." Har ta fitar da ran zai yi magana sai kuma ta ji ya ce "Bar shi can, zan zo in ci, amma ki bar falon nan ki koma ciki."
Cikin sanyi jiki ta ce "To shikenan." Daga haka ta juya ta shiga bedroom ɗinta, gabaɗaya sai ta ji ba ta ji daɗin abin da ya faɗa ba, kenan tsanar da yake yi mata har ta kai haka? "To amma me ya sa ya iya kusantata bayan baya son ganina?" Ta yi tambayar ba tare da tana da mai ba ta amsarta ba. Haka Ilham ta zauna a ɗaki cikin damuwa da tunani daban-daban a zuciyarta.
.....
Saddik ba ƙaramar damuwa ya shiga ba na fasa auren nan da aka yi ba, Allah ya sani yana son Ilham, sannan ya yi niyyar zama da ita a kowane hali, yana tabbacin ko da ba ta so shi a yanzu ba gaba za ta so shi. Amma sam Hajiyarsa ta kasa yarda, babu yadda bai yi da ita ba akan ta haƙura ta bari a yi auren amma fafur ta ƙi. Ta ce "Shi idan bai damu da rayuwarsa ba ita ta damu da ita, kuma tana son ganinsa a raye, ba ta shiryawa rasa shi a yanzu ba."
Lokacin da Alhaji Bashir ya yi wa Daddy bayanin abin da ya faru. Duk da Daddy ya ji zafin abin da aminin nasa ya yi masa amma sai ya nuna masa babu komai ya wuce, da ma can Allah ya nufa ba shi ne mijinta ba. Sosai Alhaji Bashir ya ji daɗin fahimtar da Daddy ya yi masa.
Daddy da ya je gida ya sanar da Momy abin da ya faru, amma bai sanar ita batun mahaifiyar Saddik ta yi magana da Ilham ba. Mamaki ne ya cika ta na inda Hajiya Amina ta samun wannan labarin. Sai dai daga baya ta tuna da ta yi maganar da Hajiya Zulai, tabbas ita kaɗai ta yi wannan maganar da ita, kenan ita ta je ta sanar da ita? A ranar ta kira Hajiya Zulai a waya ta gaggasa mata maganganu masu zafi, daga ƙarshe dai suka yi baran-baran.
.....
Zuhura tunda ta dawo daga asibiti abin duniya duk ya ishe, tausayin bayin Allahn nan take ji sosai a ranta. Gabaɗaya ji take yi komai baya yi mata daɗi, idan ta tuna abin da ta ji ta kuma gani a daren jiya sai ta ji hankalinta ya ƙara tashi. "To wai ko Abbi zan je in gaya masa abin da yake rauwa ne? To amma ai ba ni da wata hujjar da zan nuna masa." Ta yi maganar tana sauke ajiyar zuciya, "Shikenan daga yanzu na san abin da zan yi, zan sake saka ido a kansu" ta faɗa tare da kwanciya ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke bugu da sauri.
....
Sosai mutuwar Abida ta ratsa zukatan mutane, Inna ta yi kuka ba ɗan kaɗan ba, saboda babu wanda ya yi tsammanin ciwon nan zai dawo mata har ya yi ajalinta lokaci ɗaya, duba da yadda ta samu sauƙi sosai. Ma'u kuwa kamar mutum mutumi ta koma, sai dai tacyi shiru tana sauraren ƴan zaman makoki, ta rasa inda za ta saka kanta ta ji sanyi, gashi tana fama da rashin lafiya a jikinta, ita kaɗai ta san halin da take ciki, Aliyu ma sai dai ya yi shiru yana kallon waje. Haka dai aka ci gaba da zaman makoki a gidan zuciyar kowa babu daɗi.
.....
Kusan kwana goma da auren Ilham da Sudais, amma har yanzu baya zama guri ɗaya da ita, balle har su yi hira. Baya sakar mata fuska kullum cikin shan ƙamshi yake, sai dai duk da haka sau uku yana kai mata ziyarar dare. Ilham ba ta damu da rashin kulawar da yake nuna mata ba, kullum ƙoƙarin yin abin da za ta faranta masa take yi. Yau da safe kafin ya fita ya ce mata "Hanif zai zo yau." Yana fita ta shiga kitchen ta ɗora girki, ko da sha biyu ta yi ta kammala girkinta, ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar les mai kyau, ta duba cikin kayan lefenta da aka ba ta shekaran jiya ta ɗakko wata sarƙar gold da saka, sosai kyawunta ya sake fitowa. Sudais ba zo gidan ba sai wajen ƙarfe uku da rabi.
Sannu da zuwa ta yi musu, cikin girmamawa ta gaishe da Hanif. Ya amsa cikin sakin fuska ya ce "Amarya ba kya laifi ko da kin kashe ɗan masu gida, ina fatan na same ki lafiya." Ilham ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah." Sudais dai na zaune yana latsa wayarsa bai ce musu ƙala ba. Hanif ya dube shi ya ce "To Sarkin ƴan shariya ai sai ka daina danna wayar nan haka ko." Ba tare da Sudais ya kalli shi ba ya ce "To acici na san abin da kake yi wa." Dariya Hanif ya yi, ya miƙe tsaye ba tare da jin kunyar Ilham ba ya nufi danning, bin bayansa Sudais ya yi, Ilham ta zo ta yi serving ɗinsu. Sosai Hanif yake santin abincin, sai yaba ƙoƙarin Ilham yake yi da ta yi wannan girkin. Takaici ne ya ƙular da Sudais ya ce "Kai banza ne, wannan abin da kake yi za ka sa yarinyar nan ta raina ka fa, ko in ce ta raina mu duka."
Hanif ya yi dariya ya ce "Kai yanzu nan har kana gudun ta raina ka?" Wani banzan kallo ya yi masa ya ce "Kai ma kasan ba zan ɗauki raini ba, kuma ba zan ba ta damar da za ta raina ni ba."
Tuntsurewa ya yi da dariya, ya ce "Kana gudun raini ne za ka je kana rufe ƙofa da ita? A lokacin da kake yin abin da ranka yake so da ita ba ka yi tunanin za ta iya raina ka ba sai yanzu? Wata ƙila ma har ɓarin zance ka ke yi a lokacin ba tare da kasan ka yi ba." Haushi ya sa Sudais bai sake kula shi ba, Hanif ya shiga yi masa iskanci kala-kala, ko da suka gama cin abincin, Ilham ta gyara gurin, Hanif bai wani daɗe a gidan ba ya yi musu sallama ya tafi. Suna zaune a falon daga shi har ita babu wanda ya yi magana, kiran Zuhura ne ya shigo wayarsa. Har zai ɗauka sai ya tuna da waccan karon da ya ɗauka a gabanta haushi ta ji, tashi ya yi ya shiga bedroom ɗinsa ba tare da ya ɗaga wayar a nan ba.
...
Ana ta ci gaba da gudanar da gine-ginen gidaje, kasancewar an tanadi komai a ƙasa ya sa tuni aka ci ƙarfin ginin. Sudais na bibiyar duk abin da yake gudana, gefe ɗaya kuma yana ci gaba da bincikensa ta ƙarƙashin ƙasa. Su Alhaji Badaru sai shirye-shiryen yadda za su gudanar da al'amuransu suke yi, sun tsara cewar idan aka ƙayyade kuɗin gidajen tare da Sudais, daga baya za su sauya tsarin komai ba tare da ya sani ba, sannan duk wata ƙofa da zai sa ya san abin da yake faruwa za su toshe ta. A haka dai aka ci gaba da aiki.
...
Bayan sati biyu da rasuwar Abida Ma'u jikinta ya tsananta mata, sai dai ba ta bari Inna ta fahimci cewar ba ta da lafiya ba, ko da ta gane ta a sanyaye idan ta tambaye ta ko lafiya? Sai ta ce rashin Abida ne yake damunta. Duk da Inna ta fara lura da sauyin da Ma'un ta fara yi amma ba ta mayar da hankali wajen bin ƙwaƙwafin sanin me ya fara canzatan ba.
Tana kwance ita kaɗai a ɗaki tana tunanin babu wata tsera tsakanin rasuwar Halima da ta Abida, Halima watanta biyu da ƴan kwanaki da rasuwa, ita kuma Abida sati biyu da ƴan kwanaki, abin da ya faru da su yanzu kusan wata uku kenan. Runtse idanunta ta yi, tana ambaton sunan Allah, saboda tuna abin da ya farun da ta yi. Hawaye ne suka dinga zubo mata babu ƙaƙƙautawa. Sake runtse idanunta ta yi, ta tuna daga lokacin zuwa yanzu ba ta sake.... Ai ba ta gama tunani ba ta zabura da ƙarfi tana dafe ƙirjinta, a razane ta ce "Na shiga uku ni Ma'u, me yake shirin faruwa da ni?"
....
Zahra ce ke driving Ilham na zaune a gefenta dafe da kanta da yake yi mata ciwo, Zahra ta dube ta ta ce "Sannu Anty, wannan ciwon kan ya uzzura miki ko dai ƙaruwa muka samu ne?" Ta yi maganar tana Dariya.
Murmushi Ilham ta yi ta ce "Ni ba ni da komai, kawai ciwon kanne Allah ya kawo mini yanzu, da a lokacin da muka fito daga gida ne ya fara yi mini wannan ciwon, da babu inda za muje sai dai mu fasa fitar nan." Zahra ta ce "Haka ne, amma ya kyauta miki da ya bari sai da kika je kika ga Momy sannan ya zo miki, idan kuma Baby ne aka samo mana Allah ya inganta ya raba lafiya." Sake dafe kanta ta yi tana faɗin "Auren sati biyun ne har ciki zai bayyana a jikina yanzu?" Ta yi maganar tana runtse idanunta ta ce "Washhh Allahna, Zahra ko asibiti za mu je ne a duba ni kafin mu ƙarasa gida? Ciwon kan nan ya uzzura mini, ji nake kamar zai rabe mini gida biyu." Zahra ta ce "Eh to ina ga hakan ya kamata a yi, bari ga wata asibiti nan sai mu shiga a duba ki." Ta yi maganar tana juya kan motar suka nufi get ɗin asibitin, ko da suka je ba su wani daɗe a ciki ba, a ka duba Ilham tare da ba ta magunguna sannan suka fito. Duk da sun so su yi mata gwajin ciki amma taƙi bari. Da ƙyar Ilham taga an isa gida, ana zuwa ta ɓalla maganin ta sha, sannan ta kwanta.
Amanarcool
***