Free chapter · Read without an account

Chapter 25

by Amanarcool · SAUTIN KARSHE

SAUTIN ƘARSHE

BY AMANARCOOL

YOTA/021

Under Yota's Amazing Pens 

Book 1 

Page 25


Bayan sallar isha Jamila na zaune tana cin abinci, sai ga yaro ya yi sallama ya ce "An ce wai Jamila ta zo in ji Aliyu" kafin Jamila ta yi magana Ammu ta yi wuff ta ce "Je ka ce gata nan zuwa" yaron na fita ta mayar da dubanta gare ta ta ce "Jamila tashi ki shirya ki je ki ga waye yake nemanki, wata ƙila ma addu'ar da na daɗe ina yi ce Allah ya karɓa, da ma na gaji da ganinki da nake yi a gabana, shekaru goma sha tara ai ya ci a ce na aurar da ke." Shiru ta yi ba ta ce komai ba sai bin Ammu da ido da take yi, tana mamakin wannan surutun da take yi sai ka ce mai wata ƙatuwar budurwar da ta fi shekaru talatin, gefe ɗaya kuma tana nazarin wane Aliyu ne ya zo nemanta? A iya saninta bayan Yayan Ma'u babu wani mai wannan sunan da take kulawa balle har ya zo nemanta. "To ko dai shi ne ya zo?" Ta tambayi kanta a zuciyarta, da sauri ta girgiza kai, saboda ta san Aliyu ba zai taɓa zuwa gurinta ba, mutumin da ko gaishe shi ta yi baya kallonta, amsawar ma da ƙyar yake yinta. "Wai Jamila ba aikowa kiranki a ka yi ba ne? Wannan wane irin iskancin ne za ki shanya ɗan mutane a waje? Ko so kike ya yi tafiyarsa ne? Maza ki tashi ki tafi ba na son shashanci, ina murna zan ɗauke ki daga gabana shi ne za ki tsaya kina shirme." Cewar Ammu tana binta da kallo, tashi ta yi tana tunzura baki ta ce "Wai ke Ammu dududu nawa nake? Da za ki dame kanki da zancen ba ki aurar da ni ba har yanzu." Takalmin da taga Ammun ta ɗakko ne za ta jefe ta da shi ya sa da sauri ta yi waje.

Yana tsaye a bakin ƙofar gidan ya juyar da fuskarsa can gefe. Da sallama ta isa gurin. Ya juyo da fuskarsa yana amsa sallamar, kasancewar akwai hasken solar dake kusa da wurin ya sa ta gane sa, da sauri ta ce "Laaa Yaya Aliyu da ma kai ne? Ai ban yi tunanin kai ba ne, bari in ɗakko maka shimfiɗa" ta yi maganar tana juyawa da sauri za ta shiga ciki. Ji ta yi ya ce "A'a ba sai kin ɗakko ba." Tsayawa ta yi ta fasa shiga gidan, cikin farin ciki ta ce "Barka da dare Yaya, da fatan kana lafiya? Ya Innarmu da Ma'u duk suna lafiya?" Jin ta ambaci Ma'u sai da ya runtse idanunsa, a hankali ya buɗe su ya dubi ta, ya ce "Alhamdulillah"

Fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Ma sha Allah." Shiru ya yi yana nazarin ta ina zai fara yi mata zancen da ya kawo shi, sai can ya nisa ya ce "Jamila da ma ina so zan tambaye ki ne, kuma ina fatan za ki faɗa mini gaskiya, ka da ki yi mini ƙarya, idan na gano ƙarya kika yi mini zan yi miki abin da ba ki taɓa tunani ba." 

Jamila ta ce "In sha Allah Yaya zan gaya maka gaskiya matuƙar na san abin da za ka tambaye ni ɗin." Ya ce "To ma sha Allah, da ma a kan ƙawarki Asma'u ne, shin ko akwai wani wanda kika san tana kula shi? Ma'ana wanda ya nuna yana sonta?" Shiru ta yi tana tunanin, daga bisa ni ta girgiza kai ta ce "Gaskiya babu wani wanda na san Ma'u tana kulawa, kwata-kwata ba ta kula samari, ko da kuwa sun tare ta a hanya da maganar suna sonta share su take yi, wani lokaci ma har faɗa nake yi mata a kan ta daina wulaƙanta hakan ba daidai ba ne, saboda duk wanda ya nuna maka yana sonka ko da wasa me ba ka da masoyi kamarsa." Ta kai ƙarshen maganar tana satar kallonsa.

Tsare ta Aliyu ya yi da ido, sai ya ji kamar maganarta ta ƙarshe da shi take, murmushi ya yi ya ce "Shikenan ki ji nagode." Babu musu ta juya za ta shiga ciki, ya ce "Jamila"

Ta juyo ta ce "Na'am Yaya"

"Saƙonki ya je inda kike so ya je, nagode da tunatarwa." Daga haka ya bar ƙofar gidan. Murmushi ta yi, cikin farinciki ta shige gida.

.....

Sudais na kwance saman makeken gadonsa, bacci yake so ya yi ko ta halin ƙaƙa amma abu ya gagara. Agogon wayarsa ya duba yaga ƙarfe ɗai da minti arba'in na dare. Lumshe idanunsa ya yi yana tuna sati ɗaya kafin rasuwar Abbansa, wata magana da suka yi da shi, duk da kasancewarsa yaro mai ƙarancin shekaru a lokacin, amma yana da wayo da kuma fahimtar abubuwa da yawa. A lokacin yana da shekaru goma, Faruk yana da Shidda, sai Zahra da take da shekaru biyu da ƴan watanni. Suna zaune a madaidaicin falon gidan, Sudais na kusa da shi, Abba ya dafa kansa ya ce "A duk lokacin da zan buɗe idanuna in kalle ku, sai na yi hamdala ga Allah da ya azurta ni da ku, na kan ji farin ciki mara misaltuwa a zuciyata. Haƙiƙa babu abin da zan yi wa Allah da ya wuce in ƙara gode masa, ƴaƴa rahama ne, ƴaƴa abin so ne ga kowa. Musamman idan Allah ya ba ka nagari, masu jin ƙan iyaye. Sudais ina fatan kai da sauran ƴan uwanka Allah ya albarkaci rayuwarku, ko bayan raina ina fatan ku zama abin alfahari a gurin mahaifiyarku da ma sauran al'ummar musulmi. Ubangiji Allah ya raya mini ku, ya nuna mini ƴaƴanku. Zan yi farin ciki da ranar da zanga jininka Sudais dana sauran ƴan uwanka a duniya. Sai dai kashhh, wannan rayuwar ba lallai ba ne na iya ganin wannan ranar." 

Mammy ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Haba Abban Sudais, bai kamata kana yi mana irin waɗannan surutun ba, sai ka karyar mana da zuciya, especially ma Sudais, yanzu zai fara saka damuwa a ransa." Abba ya yi murmushi ya ce "To A'ishatuna na daina kin ji ƴar Aljanna."

Ita ma tana murmushi ta ce "Yawwa ko kai fa ɗan Aljannar mijina." Abba ya sake dafa kan Sudais ya ce "Allah ya nuna mini jininka ko da na farko ne a duniya, kuma ina fatan yaron idan namiji ne ya biyo ni, domin kuwa na fika kyau nesa ba kusa ba." Ya yi maganar yana jan hancinsa, sai a lokacin ya yi murmushi ya ce "Amin Abba." 

Abba ya ce "Mammyn Sudais ɗakko mini tsarabar nan ta da abokina ya zo mini da ita daga ƙauye." Mammy ta ce "A'a ni Mammyn Faruk ce da Zahra" ya yi dariya yana faɗin "Ba na son wannan kissar ta ku ta mata, kun fi kowa so amma sai ku nuna cewar ba na ku ba ne." Dariya ta yi ta ɗakko kayan ta kawo masa. Ya buɗe ledar yana kallon yaransa ya ce "To ku zo mu ci, tsarabar ƙauye ce da Abbanku Ƙasimu ya zo mini da ita daya je can ƙauyensu ganin gida." 

Sudais ya ce "Abba ai ba mu san shi ba, har yau ba ka taɓa nuna mana shi ba, labarinsa kawai muke ji a gurinka." 

Abba ya yi murmushi ya ce "Kar ka damu, in sha Allah cikin satin nan zan zo da shi har cikin gidan, ai dole ma ku san shi, saboda akwai kusanci sosai a tsakanina da shi. Na yarda da shi sosai, shi ya sa nake faɗa masa wasu sirrikana." Jinjina kai Sudais ya yi, ya ce "Abba to kana da hotonsa ka nuna mana." Ya ce "Eh ina da shi, yana ɗakina bari idan na tashi zan ba ka." Haka dai suka ci gaba da hira cikin farin ciki. 

Sudais ya sauke ajiyar zuciya, idanunsa suka yi masa jajur, "Allah Sarki Abbana, ashe ba ka da rabon ganin girmanmu ma bale yaran da zamu haifa, ni gashi jinin nawa na farko tun yana cikin mahaifiyarsa na rasa shi daga shi har ita" ya yi maganar yana runtse idanunsa da ƙarfi, "In sha Allah sai na binciko duk abin da ya yi sanadiyar mutuwarki Ilham, ke ce mace ta farko dana fara yi...." Sai kuma ya yi shiru ya kasa ci gaba da maganar.

.....

Aliyu na tafiya babu zato ya ji an shakume shi da ƙarfi, tsayawa ya yi yana kallon waye zai yi masa irin wannan riƙon, wani mutum ya gani yana haki, jikinsa har rawa yake yi. Ya fito da wani memori ya bawa Aliyu tare da wata takarda a ciki, ya ce "Don Allah ga amanar wannan abin zan ba ka, akwai wani video ne a ciki. Sauran bayanan da komai yana cikin dakartar nan, ka riƙe mini amana, ban yarda ka ka duba komai a yanzu ba. Amma duk lokacin da ka ji zuciyarka ta uzzura maka da son sanin me ye na amince maka da ka duba, idan Allah ya ƙaddari zan rayu in sha Allah zan neme ka na karɓi abina, idan kuma ban rayu ba ka yi ƙoƙarin cika mini burina da yake cikin takardar nan, ka yi sauri ka bar gurin nan kar su ga ka tsaya da ni kai ma su yi yinƙurin hallaka ka." Daga haka ya mutumin ya bar gurin a guje. Aliyu ya waiwaya bai ga kowa ba, da sauri shi ma ya bar gurin, kasancewar gurin babu yawan jama'a. Unguwar can take wajen gari, shi ma ya zo gurin wani abokinsa.

Da ƙyar mutumin ya ƙarasa bakin wani ƙaramin titi da ababin gawa ba su cika binsa ba. Ya zo zai tsallaka titin kenan sai ga wata baƙar mota ta zo aguje ta ture shi, faɗuwa ya yi a gurin take kansa ya fashe ya fara fitar da jini. Fitowa ya yi daga cikin motar ya ɗauke wayarsa, sannan ya koma cikin motar, babu imani ya dinga up and down saman ruwan cikinsa da motar sai da hanjinsa suka fito sannan ya bar gurin a guje.

....

Da safe Ma'u ta farka da wani irin tashin zuciya, hannunta ta sa ta toshe bakinta, da sauri ta miƙe daga saman tabarmar da take kwance, ta nufi banɗaki. Da ƙyar ta isa ta durƙusa ta fara kwarara amai har sai da ta ji cikinta ya ƙulle guri ɗaya. Inna da ke cikin ɗaki tana ji sautin aman da take yi, runtse idanunta ta yi tana ambaton sunan Allah, jin Ma'un na shan azaba ya sa ta fito da sauri, a durƙushe ta same ta a banɗakin ko ɗago da kanta ta kasa yi.

"Ma'u" ta kira sunanta cikin tausayawa tare da miƙa mata hannu alamar ta zo.

Kasa tashi ta yi, sai hawaye dake bin fuskarta. Cikin damuwa Inna ta ce "Ki tashi mu shiga ciki kar wani ya zo ya tarar dake a haka." Da ƙyar ta taimaka mata ta miƙe tsaye, suna shiga ɗaki Ma'u ta zauna saman gadon ta duƙar da kanta ƙasa, cikin kuka ta ce 

"Inna"

Inna ta ce "Na'am."

"Inna ni dai mutuwa zan yi"

Inna ta zuba mata ido, sannan ta ce "Me ya sa kika ce haka?"

"Soboda wannan halin da nake ciki, ba zan iya ba Inna, gara na mutu da wannan baƙar wahalar da nake sha. Inna ban san ya a ka yi abin ya zo jikina ba"

"Ki daina tunanin mutuwa Ma'u. Ki bar komai a gurin Allah, i dan ke ba ki san yadda aka yi cikin nan ya samu ba, Allah ya san da komai, kuma shi zai kawo miki ɗauki, wannan duk zafin laulayi ne, in sha Allah cikin na yi ƙwari za ki daina." Kawai
Ma'u ta fashe mata da kuka. "Amma Inna wa zai yarda da ni? Kowa yanzu kallon mazinaciya zai dinga yi mini".

Inna ta kasa magana, domin ita ma tambayar da take yi wa kanta kenan, ba ta san ya jama'a za su ɗauki lamarin nan ba. Sallama suka ji ana yi, ko da Inna ta fito sai taga yara ne matasa suka shigo da buhu biyu na shinkafa ɗan gote, da catin ɗin taliya, jarka mai, da kwalin magi. Sai bandir ɗin kuɗi dubu ɗari a saman kayan. 

Inna ta ce "Yara waɗannan kayan daga ina kuma?" ɗaya daga cikin su ya ce "Wani bawan Allah ne ya ce a kawo nan gidan sadaka ce." Daga haka suka juya suka fita.

Sakin baki ta yi tana bin bayansu da kallo.



Mun kusa kammala book 1, book 2 na kuɗi ne, ga mai buƙatar ci gaba da bibiyar wannan littafin zai iya tura 1k ɗinsa, 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya.


Amanarcool 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol