Free chapter · Read without an account
FREE PAGE-1/2
Wata tsohuwa ce zaune akan kujera 'yar tsugunno tana tankad'e garin masara, a cikin wata 'katuwar 'kwarya. "Oh! Ni Indo, ko ina Ameenatu ta tsaya ne? A ce tun almuru mutum ya fita har yanzu shiru." Shiru ta yi kamar wacce ake fad'awa amsa, wani gutun tsaki ta ja ta ce, "Ni ma na cika mantuwa halin Ameenatu sai dai wanda ba da shi Ibro da Hansai suka haifeta ba, yarinya sai ka ce rainon kaka." Tankad'enta ta ci gaba hankali kwance, ba tare da damuwar komai ba har ta gama, ta mi'ke ta shiga madafa. Kamar wacce aka jefo ta shigo a guje ta bi ta kan 'kwaryan ta yi d'aki, baki bud'e tsohuwar ke kallon garin da ke zube a 'kasa, sannan ta bi sahun 'kafafunta da kallo, tana shirin magana ta ji sallama daga zaure, tana tsaye a inda take ta bada umarnin a shigo, ta hau 'ko'karin tattara garinta da ke 'kasa.
Ganin mutanen da suka shigo yasa ta d'agowa tare da mai da fuskarta alamun ba wasa, mutune biyar ne sai 'kananan yara 'yan ganin 'kwaf, Tumba mai awara da 'yarta, sai Halliru Mai Kaji, sai wata yarinya da namiji, jikin yarinyar sai zuba yake da manja, sama-sama suka gaisa, d'ayan namijin ne ya ce,
"Mun zo ne domin Ameenatu."
"Uhm ina sauraronku." "Uwar yarinyar ta aiketa ta kai man ja gidan Sahura doguwa, ta had'u da Ameenatu a hanya, ba laifin zaune tsaye ko kwance ta juye mata shi a jiki bayan ta d'ura mata shi a baki."
Kallon yarinyar ta yi wacce a jiki da tsayi ta linka Ameenatu, nuna ta yi daga sama zuwa 'kasa ta ce, "Ke kina shirgegeyiya haka kamar buhun siminti ta ya jikata zata yi miki wannan aika-aikar? Kin kwaso wasu 'kafufuwanki kamar fatanya da wannan jemamman tsohon naki kun zo sharrin dai da kuka saba yi ko? Toh ahir d'inku kurwar jikata ko harararta maye bazai yi ba ballantana ci, kai kuma Halliru fad'i naka." "Zuwa ta yi kamar mutuniyar kirki tana taya Ni aiki da fira, ashe ta sa 'kawayenta su d'ebarmin 'kwayaye, sai da ja'irar yarinyar ta tafi na ga 'barnar da ta yimin." Halliru Mai Kaji ya kai 'karshen zancen yana haki kamar ya zai sha'ko wuyar Tsohuwar, kallon Tumba da ke cika tana batsewa ta yi ta ce, " ke ma fad'i kar ta kasheki." "Ni ai sai na ga fitinanniyar jikar taki ta fito tukunnan." Ta fad'a tana kallon yarinyarta, wacce goshinta ya kumbura ya yi lemon tsami, ba ta iya bud'e idonta saboda yashin da aka watsawa idon, ga bakinta na jini, fuskar kanta ta canza kammani, kakka'be hannnuwa Tsohuwar ta yi ta ce, "Ameenatu dai bata nan, sai ki fad'i abin da ke ranki ko ki had'eye abarki." Dukansu kallon shatin 'kafafuwan da ke zane a 'kasa da gari suka yi, ba sa tantamar Ameenatu tana ciki tana jinsu. Baki bud'e suka maida dubansu ga Tsohuwar, wacce ta 'kara tamke fuskarta.
"Uhm ke fa nake jira, ina da abin yi fa, in ke baki da aikin yi to Ni ina da shi." Ta fad'a tana kallon Tumba, sannan ta waiwaya ga Halliru ta nunasa da yatsa ta ce, " Ban ta'ba ganin mutumin banza ba irinka, tsabar rashin mutuncin ka kalli tsabar idanuna ka kira jikata da ja'ira, to babu ja'ira a zuri'ata sai dai ka gani a kanka, da kake maganar sun daukar maka 'kwai, dad'ina da bad'i saurin zuwa, zakkar da baka fitarwa ita suka fitar, ka godewa Allah da ba kazar suka d'auka ba, da kuka kwaso jiki kuka zo so kuke na biyaku, ko kuma na kama marainiyar Allah na jiba kamar jaka, to ba da Indo ba, na daina zubin adashin da babu d'auka ballantana riba, da a ce iya gaskiya kuka fad'a da na biya, amma sai kuka yi rashin sa'a harda sharri a maganarku, dan haka ko gaban Hashimu Mai Gari zaku je ba Baballe Mai Unguwa ba ku je, ku ce Ni Indo Saleh 'kawar wasan 'kasar uwarsa Lantana Sabi'u nace ba zan ba ku ko sisi ba, ku wuce ko fitarmin a gida gayyar tsiya tun kafin nayi muku rashin mutunci, kun ci sa'a yau bana jin rashin mutunci da surutu da kun ga tsiye da ta uwayenku ja'irai."
"Wallahi Inna ki ji tsoron Allah, wannan ba gata kike yiwa Ameenatu ba, a ce yarinya ta yi laifi ba za ki hukuntata ba sai dai ki goyi bayanta, wannan ba gata bane."
"Na daketa saboda gani tsinanniya ko? Na ce na daketa saboda gani tsinanniya ko?"
Gaba d'aya zaro idano waje suka yi ciki mamaki, bud'e baki Halliru ya yi da nufin kare kansu ya ce,
"Inna ba haka muke nufi ba fa, tunatarwa ne dai muke miki."
Wani kuka Tsohuwar ta saki,sai kace wacce aka ce wani nata ya mutu, cikin kukan ta ce,
"Bayan kun kirani da tsinanniya sannan kuma kuka ce min ma'karyaciya, ko iyayenku ba su isa su kira Ni da wad'annan sunayen ba ballantana ku 'kananan 'kwari, bari na nuna muku cewa ku din kananan kwari ne."
Ta'baryar da ke aje a gefen turmi ta d'auko, sanin halin Inna ya sa kafin ta jiyo sai dai ta ga takalma.
"Ai da kun tsaya kun ga 'karshen rashin mutunci marasa mutunci kawai, ke kuma ja'irar sai ki fito ai."
Lekowa tayi a hankali sai da ta tabbatar sun tafi kan ta fito tana kyalkyala dariya.
Taɓe baki Kaka tayi kan ta ce, "Kin ganki nan da wuya kamar mariƙin lema da ma na bari sun jajjaga mun ke ai na huta."
"Yoo su jajjagan mana wa aka ma asara? Kece za ki yi kuka wallahi bani ba,na ga ranar ma ban da lafiya kuka kike ehee sai in mutu ma kowa ya huta tunda kin gaji da ganina kuma ma."
Zaro ido kaka tai kan ta tallafo kan Ameenatou , "Kin ga rufamun asiri bar maganar mutuwar nan, yanzu je kiyi wanka kin ga rabonki da wanka tun shekaran jiya."
"Aradun Allah ba zan ba sai kace wata 'Yar ruwa,ni kifi ma na ke sha'awar ci bara in kira Furera da Lantana muje gun tumbiɗa mai kifi."
Daura hannu akai Kaka tayi.
"Oh ni Indo Allah Na Gode ma da ka bani Ameenatou yanzu duk abun da ki kai yau bai isheki ba sai kin karo wani?"
Ameenatou ta fara tafiya tana tsalle-tsallenta , "ki aje mun ruwan wankan inna dawo zan yi,bara muje gun Alhaji tumbiɗa mu dawo aheee kifi dadi wallahi zan rago miki kar ki damu Babar Maman Ameenatou Indo."
Har ta fita ta dawo aguje.
Sai da Kaka ta firgita.
"Ke lafiya? Me yafaru kuma?"
Buta ta dauka tana nishi, "Wallahi kashi nake ji, kashi zanyi wayyo kashina kar ka fito."
Tsaki Kaka ta yi, "yo ni na zata ma karshen duniyarce tazo ai irin wannan gudu." Ta ci gaba da shararta tana yan wake-wakensu na da.
Ameenatou kuwa kamar an shuka dawa a bandaki tunda ta shiga kusan minti talatin ba ta fito ba.
"Ke Ameenatou na ce ko Barci kika soma a bayinne?"
"Eheeem, eheeem kaka yasin kwan nake kasayarwa."
Sai da Ta kusa Awa daya a bandaki kan ta fito tana nishi.
"Tab wallahi naci kwannan da yawa ni kaina warin yadameni,gidansu Furera mu ka je muka dafe kwayayenmu mu ka cinye su tas." Ta karasa maganar tana kyalkyala dariya.
Kaka ta ce, "kyaji da shi dai."
Ameenatou sai da tazo gaban kaka sannan ta sake mata tusa mai bala'in wari ta fice aguje tana dariya, "Kaka kema ga rabon ki."
Rike hanci ka ke tayi tana masifa, "zaki dawo gidannan ki sameni wallahi sai na rama, har ni za afadawa tusa? Mu da muke adashenta ina jiran ki ba kaffara sai na rama tusar nan zaki sha mamaki."
Ameenatou na fita.......
A ci gaba ko a tsaya?
In ga ruwan sharhi jama'a🤸♀️
22/10/2021
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_
_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:22 PM] ***: ***
°°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_
_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_
_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_
_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_
_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_