Free chapter · Read without an account

FREE PAGE-6

by Aisha Sani Abdullahi · AMEEENATOU 'YAR KAKA

_*INA MATUKAR BUKATAR ADDU'O'I DA GA BAKU NAN KU MA SU ALBARKA MASOYA🥰🙏KOMIN KANKATA KO GAJARTA KUMIN DAN ALLAH*_

_*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_

_"Ina ji ajikina cewa duk randa na daina sonka to numfashi na ne yazo karshe,ka sani ka kara sani in har zanyi numfashi to sonka na cikin raina ko ince rayuwata ma gabadaya, indai ana so bayan rai, tabbas zan ci gaba da sonka har bayan raina,tare da yi mana fatan kasancewar mu atare,shin ka san mahimmacin murmishinka gareni kuwa? tamkar yiwa makaho addu'ar budewar ido ne, misalta irin Farinciki da yanayin da zai shiga,to wannan kwatane a Farincikin da nake shiga aduk sanda na ga kana murmushi,bance ni kadai za ka so ba,amman ina da tabbacin zanyi kokarin cike duk wani gurbi da ke zuciyarka ta hanyar da ba za ka taba so ko tunanin kulla alaka da wata 'ya mace ba,Ina Sonka tamkar Raina! Ko ba yanzu ba kuma ba yau ba koda kuwa bana duniya ina fatan ka so ni kwatankwacin son da nake ma hakan zai matukar kara faranta mun rai Habeebiy Da'eeman ba iya suna bane ina fatan hakan akullum in sha Allah."_ _*Fisabillah🥰duk wanda yaji dadin kalaman ya kara mun àddua*_

A firgice ta jiyo tsabar firgita saura kad'an ta fad'o, duk da yanayin tsoro da ta shiga hakan bai ta yi laushi ba.

"Kai dai Malam Dattin nan ka fiye jaraba da rashin ha'kuri, daga kawai ka ga mutum saman bishiya sai ka fara zage-zage, kamata ya yi ka samo tsafga ka ce keee uban me kike yimin a saman bishiyata, Ni kuma sai in ce bishiya ba ta uban wani ba ce tashen Allah ce sai dai mutum ya zama sanadi, na zo d'ibar zakka ce da ka gagara fitarwa, in kana iyawa sauko da Ni ka zane, sai ka kamo ni ka sauko ka fara duka, amma ka wani zo kana ta hayayaga ba."

Kamar yadda ta kawo shawara haka Malam Datti ya yi, domin kusa da shi ya samu tsafgar, yana shaud'a mata d'aya a duwawunta ,ban da ihu da tsalle, ba abun da take, sai da ya yi mata shida masu shiga jiki a na bakwan ne yana shaud'a mata ta shige cikin malun-malun dinsa, cakulkulu ta fara yi masa mai kama da yakushi, da ya kai bulalar da niyyar duka sai ta zille, kuka take wujiga-wujiga har da majina, hakan bai ya sa ta nutsu ba ta daina, ganin tana neman haukatar da shi ne yasa ya fara 'ko'karin cirota, sai da 'kyar ya cirota yana haki, ganin ta ku'buta da 'kyar yasa ta bawa wandonta iska, har ta yi nisa ta dawo ta kwashe magwonron da ke 'kasa ta kara gaba fitttttt.

Haka ta kama hanya tana tafe tana kuka harda majina tana kuma shan mangworonta kamar dole.

Lokacin da ta iso bokon an fara tarar 'yan makara, firifect d'in da suke tsarewar tsabar dariya ko tsaida ita ba su yi ba, ita d'in ma bata yi niyyar tsayawa ba, amma ta 'kuduri aniyar duk wad'anda suka yi mata dariya tun daga hanya har makaranta sai ta d'au mataki a kansu.

Tun daga nesa ta hango Malamin da ke cikin ajinsu, Malamin *wata mie is niem* ne a ciki.

Tana zuwa ta shige aguje kamar zaburarriya.

Tsawa ya mata yana, "You ba? You ba? U ar just coming now? Eheen I will deel with you in and out."

Kallon shi tai tana daura hannu aka , "Onkul Aradu I Noyin Going to bishiyar Dirimi, going to Bishiyar Mangoron Baba Datti kadai,kuma shi ma Kaka ta ce dan uwanmune Kakan kakanshi abokin makocin Kakanmune wallahi Onkul."

Uncle Ibrahim bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba.

Can kuma ya make, kan ya ci gaba da cewa, "Oya Go Out, i said Go Out." Ya karasa maganar yana nuna mata hanyat fita da hannu.

Gatsinan Mangoron ta tai kan ta ce, "Sholly Onkul I noyin Karawa wallahi Na ce ma mangoro ne ba dirimi ba,kuma in zaka sha ma ga shi sai inje gida in karbo ma gishiri gun Kakata."

Ba yadda ya iya haka ya bar Ameenatou a ajin nan ta zauna dan inya biye mata ba za suyi karatu ba sai dai cikinsa ya kulle dan dariya da takaici.

Zama tai agefe su Furare na kallonta sai ta galla masu harara

"Onkul wallahi i no lyk botin yara,ni ka ce masu stopi kallo mie, ehee in baka haka ba na kama yara wallahi botin (bitin) din su zan kuma sai na haifosu ehee dan ina da cikinsu." Ta nuna su Lanata da hannu.

Kallon su ya yi ya ce, "Ku daina kallon mana sarauniyar turanci in ba so kuke ta kashemu da turancinnan ba." Wani dadi Ameenatou taji adole ance mata ta iya turanci kara washe bakinnan tai tana damkar mangoro.

"Oyaa Class Wanene zai fadamun me za ace in Mutum bai da lafiya da turanci? Kun ga yanzu dai mu ka gama kuma duk wanda ya fada dai,dai zan mi shi kyauta." Cewar uncle .

Ban da zaro ido ba abun da suke suna kallon juna domin duk basu san me zasu ce ba.

Tuni Ameenatou ta daga hannu.

Uncle ya ce, "Oya Meena."

Ta tashi ta ce, "Onkul wallahi inna fada me kadai zaka ba wa kyautan ko?"

Ya ce, "Eh Go On."

Ta washa baki

"Ita Noyin Lafiya Wal."

Kallonta kawai ya tsaya yi.

"Onkul ba ka ce su tafa mun ba fa kuma na fada ai."

Dariya ya yi kan ya ce za su tafa miki amman Hausa da turanci kika hada ai.....

Kan ya yi magana aka biga bell din fita break.

Tuni suka fice suka bar sa tsaye mussamman Ameenatou da tayi wani irin tsalle.

Tsayawa ya yi kawai yana tunani duk da rigimar yarinyar shi kam birgeshi take sosai.

Ameenatou zama tai ta cigaba da shan danyen Mangoron ta kamar dole.

Furera da Lantana suka zo.

"Ameenatou dan Allah kiyi hakuri ba za mu kara guduwa miki ba."

Harara ta dalla masu kan ta ce, "e da kuka tafi kuka bari ya tsalamun duka a Duwaisatu na ba."

Furera ta ce, "Dan Allah kiyi hakuri Googo Ameenatou."

Ameenatou ta yi tsaki kan ta ce, "Banzaye jikokin masu sai da daddawa sai kuzo ku zauna ai."

Jiki na rawa suka zauna kamar iyayensu sun basu umarni.

Lantana ta ce, "Ni kam wancenn Onkul din na mun kyau yasin dama ya aureni ya kai Ni birni."

Ameenatou ta tabe baki, "tab wallahi bai kai onkul Al-ameen dinmu kyau ba Kaka ta ce fari ne sol kamar bature,ke tsaya ko son shi kike? Aradu in kina son shi mu tura mai sakon soyayya yadda na ga ni Film dinnan."

Lanatana ta rufe fuska "ni ysn ina son shi tom."

Ameenatou ta ce, "Fures dauko mana takarda da biro Aradu mun zama an binni ,zanna fada ku rubuta me za asa."

Furera ta dauko ta karda da biro.

Ameenatou ta gyara zama.

Yawwa rubuta" Salamu alaikom,dilla ma bani in rubuta ai nima na iya burutun ehee."

Nan ta fara.

_"Onkul aradu tonda nigganka nafaddarijiyar sonkkaninakefa danAllah ka sonnnikarka kacebakasona,inkakisonimituwa, zanyi,dagamasoyiyarka *lantus* kowar,fures,da,goghoameenatou,inajira,kajojjmuyi,aure,mutaibbinni._

Akayi zannen wata markadaddiyar HEART mai kama da ayaba agefe.

"Yesh wallahi ni yar binni ce yara na iya kalaman soyayya fa yanzu fures ki tashi muje mu kai,ke kuma Lantus ki tsaya amaryar onkul Ibrahim."

Suna zuwa Ameenatou ta ce....

_*BANA GANIN SHARHI FA😟KO A TSAYA NE?*_

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:25 PM] ***: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

****

_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol