Free chapter · Read without an account

Hs 37

by Sayyid (Boy) · HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

_Page 37_

"Wai me ya kai ki gidansu ne?." Amrah ta tambyaeta. "Ke ban da lafiya fa, rashin lafiya har da kwana asibiti." Bhatool ta faɗa ma ta. "Shegiya ko dai ciki ne?." Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. "Ke dallah lokacin ko sati biyu ban yi ba." 

"Hakane kuma." Amrah ta faɗa. "Dalla zubamun abincin." Amrah ta sake faɗa. "Ta shi ki zuba." 

"A'a zubamun." Ta shi Bhatool ta yi ta shiga kitchen ɗin, 'yan mintuna kaɗan ta fito da abincin ta nufi kan dinning. "A'a kawo mun nan malama." Amrah ta tare ta, dawowa Bhatool ta yi ta ajiye kan centre table. "Ke wallahi jarabarki ta yi yawa wallahi, ya makaranta." 

"Alhamdulillah, mun kusa fara exam fa Bhatool." 

"To yanzu ni Amrah ina ruwana da exam." Bhatool ta faɗa. "Ni kam Bhatool da zaki bi shawarta ki yi exam ɗinki, wanan Neil ɗin fa kina zaune baki fara ba har ma gama waccan, yanzu da ciki zaki ce a jira ki haihu, daga haihuwa zaki ce sai kin yaye shi, a ƙalla shekara uku lokacin kam mun gama YSU." 

"Hakane kam, nima ina wanan tunanin amma kuma naga Senate bai son YSU." 

"Bai son ta kuma Bhatool?, sai dai idan ke ce kika nuna mai bakyaso har shima ya ce baya so, anam fa ya ganki kuma da kin masa magana ta fahimta wallahi zai barki, ai yana sonki ke ma kin sani, ko da a farko ya cize dakin nuna mai ke fa kina so wallahi shi ke nan zai barki." 

"Zan gwada ma sa magana kam, tun da fa yanzu muna yin wanan jarrabawar aji uku zamu shiga, kuma kin ga shi a frist semester duk siwess ne abun da zai zo da sauƙi." 

"Shine dai 'yar gari." Amrah ta faɗa ta na kai abincin bakinta. "Ke ni fa kin san me?." 

"Sai kin faɗa." 

"Bikinsu Juju za a yi fa?." 

"Ƴa'yan yayar Abbanku?." 

"Su fa shegu, Kuma kin san wani iskanci Bhatool?." 

"A'a sai kin faɗa." 

"Wai babu anko." 

"Dalla ai sun hutar da ku ma." 

"Ke Bhatool ba zaki gane ba, yanzu ai salan aga ƙure adakar mutum ne, ga shi duk kayan bikinki nagama status da su." 

"Au sai yanzu fa nagane, kai wayanan shegu ne Amrah." 

"Lamba ɗaya ma Bhatool, nifa ina ga wallahi sai dai na zo nan na ari kayanki."  Dariya Bhatool ta yi sanam ta ce. "Wallahi ki zo ki amsa, har da gwala gwala mai." 

"Shegiya ba zan amshi gwala-gwala bai, sun san ba nawa ba ne, ku koma su sa abini hanya a ƙwace asareni." Dariya Bhatool ta yi sanan su ka ci gaba da hirar su. 

Sai bayan magariba Amrah ta fara shirin tafiya, Bhatool ce ta ce. "Yau dai sai na raka ki har bakin titi, ko na samu naga anguwan?."

"Wai baki taɓa fita ba?." Amrah ta tambayeta. "Sau ɗaya na ta ɓa fita, shima da daddare ne." 

"Gaskiyya ne agaisheki." 

"Yanzu yaushe zaki zo ki amshi kayan?." 

"Sai satin bikin." 

"Allah ya kaimu." Daga haka suka fice. Fitowar Bhatool bakin gate idanunta suka saukan akan Ahmad wanda ya bugeta, fuskarta cike da murmushi ta ce. "Ina yini?."

"Lafiya ƙalau Bhatool, nan e gidanku kenan?." 

"Eyh Wallahi anan muke." 

"Ya jikin naki?." 

"Jiki da sauƙi wallahi." 

"To Allah ya ƙara sauƙi."

"Amin Na gode." Daga haka suka huce suka barshi, sai da suka yi nisa ne Amrah ta ce. "Ke wanan fine boy ɗin fa?." Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. "Ke ni naga kishi wajen Senate akan wanan gayen." 

"Anan unguwar yake kenan?." Amrah ta tambaya. "Eyh nan yake, kwanaki ne fa na zo fita ya bugeni, shine muka je asibiti anan naga kishin senate." 

"Ah ba dole ya yi kishi ba." 

"Ke Amrah zan juya, ki gaida gida." 

"Toh shi ke nan Bhatool Na gode." 

"Aha." Bhatool ta faɗa tare da juyawa, har lokacin  Ahamd ɗin na tsaye da alama wani yake jira wajen ita dai bata ce da shi komai ba ta shige gida. 

Wanka ta yi ta ɗau shiri cikin doguwar rigar ta ta wani material da ta yi matuƙar yi ma ta kyau, tasan dai Senate zai ƙara awa guda kafin ya dawo, amma ta gwammaci ta yi shirintata jira shi. Tana cikin shirin ne ta je Senate na ƙwala ma ta kira. "Bhatool! Bhatool!! Bhatool!!!." A firgeci ta miƙe tana faɗin. "Lafiya?." 

"Ban sani ba, me wanan yake yi a ƙofar gidan nan?." 

"Waye?." Ta faɗa. "Bana son raini hankali, wancan Ahamd ɗin."

"To ni yanzu ya za ayi nasan me ya ke yi dan Allah." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Kinsan na tsani rainin hankali fa, ki faɗamun me ya ke yi ko na ci mutunci ki." 

"Wallahi Senate bansaniba, ni fa ban ma san yana wajen ba." 

"Aouh, bakisan yana wajen ba." Ya faɗa yana ɗakko wayarsa. "Wannan bake ce ba?." Ya faɗa yana nuna mata wayar, karɓa ta yi tana kallon hoton tabbas ita ce da shi, amma bata san lokacin da aka ɗauki hoton ba da kuma dalilin da yasa aka ɗauki hoton ba. "Bake ba ce?." 

"Ni ce." Ta faɗa zuciyarta cike da tunani da ruɗani. "Me ya fitar dake?." Cikin inda inda ta fara magana. "Am...rah ce." 

"Amrah ce me, Amrah ce a hoton?." 

"A'a, ita ce ta zo shine na rakata." 

"Haka ake fita babu umarni miji, Bhatool karki raina mun hankali." Kuka ta fashe da shi ta kasa cewa komai. "Wallahi Bhatool ki kiyayeni, ku fita sabgar wancan ɗan iskan na faɗa miki, ke bakisan muhimmancin aure ba ne ko me?, sai yanzu na gama ganewa baki da wani cikakken hankali a tare da take, to wallahi zan sai ta miki zama na gaya miki." Kukanta ta ƙarawa ƙarfe, zuciyarta na mata wani irim zugi wanan abun da me ya yi kama, ita dai ita ce amma ba ta san menene amfani wannan hoton ba, sharri ne ake so ayi mata ko me. 

Ƙarar takunsa ta ji ya shige cikin ɗaki, ta ɗago da kai ta kalli kan dinning abincin da ta dafa. "Wanan wace irin rayuwar aure ce ni Bhatool?." Ta yi wa kanta wanan tambayar. "Komai sai cakuɗemun yake, babu farin ciki kwata-kwata." Haka tai ta faman tunane-tunane har dare ya fara yi sosai Senate bai fito ba. Ta shi ta yi ta nufi ɗaki ta ɗaura alwala ta yi sallah, sanan ta ɗaga hannu sama ya fara addu'a. "Ya ubangijin sammai da ƙassai, na kawo kuka na a gareka, ka shiga cikin al'amarin gidan Aurena, ka duba ni ka kawo mun sauƙi da mafita, Ya Allah idan da alheri a zaman aurena da Senate ka tabbatar, idan babu ka kawo karshen zaman ta hanyar da yafi sauƙi, ya Allah wannan abun da ya faru yanzu, kasan komai ban da masaniya, Ya Allah Ka kawo mun sauƙi." Haka tai ta addu'a ta ce wannan ta ce wannan. 

Bayan ta idar ne ta koma gefen gado ta zauna tare da rafka tagumi kamar wata marainiya marar ga ta. Can kuma shawarwarin Yaya Karima suka faɗo ma ta mussaman na bada haƙuri, ba shiri ta miƙe ta fito zuwa ɓangarensa, ta yi mamakin ganinshi kan dinning yana cin abinci, sai dai ta ji daɗi ko bakomai ba ta yi asarar lokacinta ba. 

Daga nan ta koma ɗaki ta zauna, zaman jiranshi ko zai shigo amma bai shigo ba har ta yi bacci.

Washe gari Bhatool ta yi ƙoƙarin ta shi da huri ta haɗa ma sa breakfast, sai dai ba ta kai ga kammalawa ba ta ji ficewarsa daga gidan, kuka ne kawai ya rage Bhatool ba ta yi ba amma ta je wuya iya wuya, ta fara gajiya da Senate da abinda ya ke ma ta, idan ba ya son ta ne kawai ya hakura su rabu. 

(Ayi mun afuwa dan Allah, wannan week ɗin ba za ku sami Post sosai ba, amma in sha Allahu by next week komai zai dawo ready Na gode." 

Legendspen
***


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol