Free chapter · Read without an account

CHAPTER[8

by Hindatu Auwal · ZAREN KADDARA

*KANO* *Hamrah*

Aytsoro rahamane agameda yanayinda maganganunta suka jefata aciki,ba iya zuciyanta da ƙwa ƙwalwan tane suka gane zata iya aikata fiyeda abinda tafurtaba.

mafitanta ɗayane shine tainisa da ita,maganin kar ayi tokar afara,maso abinka kuma yafika dubara,ba aborida sanyin jiki,da zaphi zaphi akedukan ƙarfe.kafin taje gida tasan abinyi itakuma tarigada tayimata nisa.

kaman wacce akaraɗama faskare agadan baya haka tamiƙe bashiri,wadrope ɗinta takalla setarasama mezata ɗauka,kuɗi taɗauka tamaida wadrope ɗin tarufe.

hijjab tasanya datakalmi kawai tafito da alama tsananin ɗimuwan da ƙwaƙwalwanta tashiga taman tarda ita Asma'u tana makaranta.

seda tasanya kafa daniyyan ficewa afalon sannan komai yadawomata tiryan tiryan kaman anahaska matashi amajigi.

se alokacin tafashe da kuka mesauti,kuka takeyi meciwo,kukannata yasamu daman yin tsayine sakamakon kewa da soyayyan mijinta dasuka tasomata dasauri tamiƙe,sotakeyi taji muryanshi,sotakeyi yararrasheta kaman yanda yasaba tun yarintanta.

wayanta taɗauka harta fara ringing takashe saboda tinawa datayi yanzu yanahanya indai bawani ikon Allahba toshiyake driving.

rubutu tafaramai da zuciyanta"bansan lokacinda nafara sonka arayuwanaba kaman yanda bansan lokacinda nadiro duniyaba,inada tabbacin soyayyanka dawwa mammiyace acikin zuciyata tamkar yanda nakeda tabbacin zanmutu.

kaine komai nawa don Allah duk abinda zanzama kada kagujemun,ka kasance mai'uzuri agareni kaman kodayaushe.

every day I want to see your eyes,hold your hand and kiss your lips. I love you more each day. I love you more than word can ever say. I love you so much mijin Hamrah"

shiganshi Abuja kenan sakonta yashigo wayanshi,ye murmushi dukda wasu kalaman nata sunɗarsamai ba lafiyaba da ace batuƙi yakeyi ba toba abinda zehanashi kiranta yaji lafiyanta se akai rashin sa'a tuƙiyake.

ya ajiye wayan yana ƙudurcema ranshi daye packing zedallamata kira,

tana ajiye wayan talumshe idanunta da harsun kumbure saboda kuka.

yanda kasan ankunna majigi haka ƙwaƙwal wanta tafara haskomata asalinsu tiryan tiryan batareda ansami wani gardamaba.

Amguwan fulani babban anguwace dake cikin zaria local government,kafin tasami yalwa da cikan daza'a kiratada Fulani local government.

azamanin dayawuce anguwace datakafu tun iyaye dakakanni.suɗin bananne tushensuba tushensu na Maiduguri a Maidugurinma sujinin Fulanine.

Ƴan ta'addan dasuka damesune awannan lokacin yasanyasu gudun hijiran dole,basuyada zango ako inaba se ajihar Kaduna cikin karamar hukuman ZARIA.

Gidan sheik Isma'il naɗaya dagacikin manyan gidajenda kanashiga katambaya za'akaika.

Umar nadaya dagacikin ƴaƴa 18da Allah ya azurta Mlm Isma'il dashi.shikaɗai mahaifiyanshi tahaifa Allah yemata rasuwa,kasance wanshi bafullatani behanashi yin karatun zamaniba domin sedayayi degree kafin ya auri Sumayya ɗiyar wan mahaifiyanshi.

ƴaƴa uku Allah ya'azurtasu dashi,Isma'il shine babba,seyema kanshi takwara wato Omar se auta Asma'u.

sun raini ƴaƴansu cikin so da kauna ahaka har suka kai munzalin aure,anan kusada gidansu suduka suka zauna harda Asma'u.

Rayuwa sukeyi cikin farinciki,inda Isma'il da matanshi Umaimah sukeda ƴaƴa biyar,Umar kuma nada ƴaƴa biyu rakh.

Asma'u cekawai Allah bekawo mata haihuwanba shiyasa akabata Umar.idan kana niman pure love soyayyanda babu gauraye tokasami soyayyanda ketsakanin Aunty Asma'u da Omar.

shekarunshi 10ciph aduniya Allah yabama Asma'u cikinda tafiddaran samu itada mijinta Hisham.zokaga farinciki wajen wannan ahalin.

hankali kwance takerainon cikinta,duk inda Umar yadawo daga makaranta toyana maƙaleda Auntynshi.rananda cikinta yafara motsi kasa sukuni tayi don Omar taroyara yayi yanacewa suzosuji babyn Aunty namotsi.

aranan wata jumma ace kuma ta tashi da matsanancin naƙuda.batareda bata lokaciba suka ɗauketa suka kaita asibiti.

duk yanda likitoci sukakaiga ƙoƙarin ganin tahaihu dakanta hakan besamuba dole seda akaimata theater.kokallon abinda tahaifa batasamu damanyiba Allah yaɗauki rayuwanta.

wannan rasuwa tamatuƙar girgiza kuwwa.akaima yarinya huɗuba da Hamrah kaman yanda suka zaɓi sunan tunkafin rasuwanta.

tunda aka haifi Hamrah shikenan Omar yasami abinyi,yarasa dukwani sukuni bayada kwanciyan hankalinda yawuce yaga ƙanwartashi ahannunshi.

kobarka mutane sukazo daƙyar zebada itah aganta,bakuma zejirga daga wurinba harse anbashi itah sannan zeshafamuku lafiya.

ganin haka yasa Daddy(Isma'il)haƙura yabarma matan ƙaninnashi rainon Hamrah,don shima yaso abama matanshi.

kaitsaye zamu iya cewa Omar akabama Hamrah ba mahaifiyan shiba,saboda fiyeda rabin kulada itah shiyakeyi,Mamy kemata wanka shikuma yemata shafa,sannan yasanyamata kaya,plate ɗin abincinsu ɗayane.

idan zetafi makaranta kuwa to dakuka suke rabuwa,shiyasa lokacin shiga makarantanta beyiba akasanyata,to!anan dinma ba'atsiraba sabod batazama a'a jinsu se malaminsu nacikin karatu zatashigo ajin bakuma wanda zatakalla kaitsaye seat ɗinda yakezama take tunkara itama tazauna,rigiman duniya kuma bazata rabudashiba.

daƙyar da siɗin goshi akasamu tai ƙawaye,saboda tun asali Omar shine abokinta,abokin nishaɗinta,shima bayada wasu abokai bayanna makaranta.

ahaka rayuwa tadinga juyamusu harsuka girma suduka.

yanada29 yrs yakammala masters ɗinshi itakuma tanada 19takammala Diploma,besha wahalaba yasamu aiki 'a companyn Alh.Zanna asannane yaji bayada muradin aikin dukda murnanda ƴan uwa da abokan arziki suketayashi.

dama yakuke tinanin zeji daɗin samun aikin bayan shale lenshi bataso,ganin halinda suka shiga yasa iyayennasu tuntuɓansu akan sunason junada aure?

dama ko ba atambayesuba ansan amsan,akatsaida biki 2wks,aurenda yakasance mafari kuma tushen shaƙuwansu.

daƙyar tasamu taiya ƙwato kanta daga kogin tinaninda tafaɗa.tayunƙura daƙyar tamiƙe akan diga diganta,sefaman kiraye kirayen sallah akeyi tashige bayi taɗauro alwallah tazo tagabatarda sallah tananan azaune har la'asar tayi tamiƙe tagabatardashi.

5:00pm Asma'u tai sallama cikin zazzaƙan muryanta,kallo ɗaya zakaima kyakkyawan fuskanta kagane agajiye take,jin yanda Hamrah ta amsata asanyaye,ga fuskanta daya kumbure,idanunta sunyi jajir suma harsun tasa.

dasauri tacire takalminta taƙaraso inda takezaune akan sallahya,ledojin hannunta ta ajiye taname saka idanunta acikin nata.

"meke damunki_lafiya naganki ahaka?_bakyada lafiya?!!!"

tajeromata tambayoyin cikeda kulawa,daƙyar taƙaƙaro murmushinda ko laɓɓanta basugama rufewaba,

"lafiyata ƙalau,kitashi kije kiwanka inzakici abinci kizo kidafako indomie ne"

har cikin ranta takejin akwai wani abu badai daiba sedai bata taɓamata gardamaba bakuma zatafara ayanzuba.

tamiƙe jiki baƙwari tarigada tayi sallah acan makaranta,hakama taci abincin walima sekawai tahaɗama kanta ruwan wanka tayi.

nan danan tashirya cikin doguwar riga ta atamfa ɗinkin doguwar riga simplece babu wani tarkacen kwalliya.mai kawai tamurza se tiraren sugar baby datafeshe jikinta dashi.

mamakine yakamata ganin har yanzu Nury nanan a'inda tabarta ɗazu,ga taguminda tayi hannu biyu,taƙarasa wurin taname dafata.

tai firgigit kaman wacce ta tashi daga bacci,ƙwallan datake tallabewa da kwayannin idanuntane suka zubomata.

Asma'u tabuɗe baki daniyyan magana Hamrah takatseta cikin salona bada umarni,

"kije kihaɗo kayanki muje Zaria"

ga abin farinciki amma Asma'u tagaza yinshi sema zuciyanta data shiga bugawa phat-phat batace komaiba tamiƙe har takai ƙofan ɗaki sekuma tajuyo tanacewa,

"Rasuwa akayine"

don'ita yanayinta dakuma ambaton Zaria datayi yasanyata tinanin sedai in rasuwa akayi saboda bazata manta rananda tadawo suke hirada Daddy tawaya tace

"zatazo tagansu"secemata yayi"tayi haƙuri mahaifiyanta tahaihu bayan tagama wanka sesuzo tare"

kai Hamrah taɗagamata alaman"eey"

sakamakon abinda yafaru yayi muninda bekamata tagaya mataba,saboda ƙananun shekarunta,bugu daƙarima kunyan faɗa takeyi.

ɗakin tashiga tahada kaya a trolley guda don batajin ka kanninnata zasu barsu sudawo dawannan tsohon cikinna Nury.imma bata haihu kafin agama karɓan gaisuwanba,kayanda taimusu tsaraba taɗiba15set in case.

inda tabarta anan tasameta idanunta ƙur'akanta.

"Nury nafito"

miƙewa tayi tanufi bakin ƙofan batareda ta'amsataba,

"Nury kayankipha?!"

ta tambaya asanda taga tanakokarin rufe kofan palon.

"akwai acan"

ta amsata muryanta acunkushe,batasake cewa komaiba sebinta da ido datayi,basusha wahalan samun abin hawaba kaman yanda basusha wahalan samun motan dazata kaisu Zariaba.

kaman yanda kowace tasha take seda akaɗauki bayanin kuwwa,sannu ahankali suka fara tafiya tambayoyi phal zuciyan Asma'u dasuke muntsilanta sedai batason furtasu dubada halinda takeciki.

9:00pm motansu tatsaya a pz wurin shiru yake sejephi-jephi kakeganin abinhawa,suna zaune driver yafita neman bakanike at least 30mnt sannan yadawo taredashi,wata matace taƙaraso wurin da ɗiyarta,daga gani bafullatanace itama gaciki tsoho suna kallon matan tacikin hasken solarnda kegefen titin.

haka sunajin sautin kukanta da sautin muryanta datake roƙon drivern akan yataima kamata yaɗauketa zuwa cikin zaria.mijintane yasaketa kuma yakoreta acikin darennan.

ganin ita tafita bukata kuma tafita nisa shiyasanyata buɗe motan tafito Asma'un ma fitowantayi bisa umarnin Nury tamatsa wurin drivern tanacewa,

"bawan Allah dama zansauka ananne tunda naga akwai wata wacce tafini buƙata.ni ayanzu zan iya samun adaidatan daze ƙarasadani,itakuma ayanzu nawa zanbaka kakaita inda zataje"

"kawo ₦200"

a'aljihun riganta taciromai tabashi,matanda ketafaman rizƙan kuka ta tsagaita tanamata godiya.sosai taji daɗin addu'an saboda tanacikin yanayinda takematuƙar buƙatan addu'an.

drivern dakanshi yasaman mata napep ɗin da zekaita tudun wada yace anan zetsaya.

Asma'u taso taji sunan anguwan nasu sedai takasa tambaya sakamakon kanta dayasaramata acikin kanta take lissafin rabonta dagarin shekaru 6kenan,tadai tina kusada zaria local government amma bazata iya tina sunan nasu local government ɗinba.

10:00pm suka tsaya atudun wada,sauke ƙafafunta datayi aƙasa yedai daida amsawanda bayanta yayi,taishiru tana ƙoƙarin danne ciwonda yatasomata kowace adai data tazo setawuce kaman haɗin baki.

marantane yaƙulle taduƙa agun tanasalati ganin haka yasanya hankalin Asma'u tashi tafara ƙoƙarin tsaida motoci amma hakan yaƙi samuwa.

*ZARIA*

*Mardy*

"Mardy mekike tinani haka"

Adam yafaɗa yana taɓota.don semagana sukemata amma takauda kanta tanakallon waje,wasu irin hawayene masu zaphi suka zubomata asanda tajuyo.

tana bude baki daniyyan magana taji wani irin gunjin kuka yatahomata,tai amfani da hannun damanta tatoshe bakinta sabbin hawaye narige rigen saukomata dagacikin jijiyoyin idanunta da ɗayan hannun tanunamai abinda tagani,ye saurin kallon wurin

"'a'uzubillahi minashshaiɗanin rajim"

yafaɗi cikin tsananin tashin hankali,sedai sautin befito daƙarfiba iya kanshi maƙoshinshi,shiyasa su Mubeen da Mai napep ɗin basujiba.

nantake jikinshi yaɗauki ɗuminda bayada alaƙa da zazzaɓi,saboda wannan dagacikin zuciya yake fitowa yanarabama kowani sashi najikinshi.

bashiri yalumshe idanunshi yana ƙaranto duk addu'an dayazo yazobakinshi.soyakeyi yamanta sedai yakasa dayanada dama dayakoma mintinan dasuka wuce yagoge abinda suka gani.

betaɓajin yanasha awan makantaba se ayanzu dayakeson daina ganin photon mahaifinshi,bakinshi cikinna matanda bamaharra manshiba bega ta tafuskanba iya tashi yagani.

Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan,semun haɗu a chapter 9.

Dafatandai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,don Allah kui mana comment sannan kui sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima.........

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

® By Hindatu Auwal

HIKAYA WRITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

______________________________________

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol