Free chapter · Read without an account

CHAPTER [14

by Hindatu Auwal · ZAREN KADDARA

Dayike dama anan suke ganin likita duk lokacinda ciwo yakama ɗayansu,bayan sunsayi kati sakamakon mantawa dasukayi danata acan gida.

Tasamu daman ganin likita bayan gwaje-gwaje da test test da aka dingamata.

Doctor yagane matsalanta seyemata allurai don tasamu hutu,sunanan a'inda yabarsu shiyasa yanafitowa suduka suka miƙe idanunsu nabayyanarda saƙon dayake a allon zukatansu.

Ganin haka yasanyashi yinmusu bayani nantake"heart attack tasamu,da 'alama tanacikin damuwa sosai,alhamdulillah numfashinta yadawo dai-dai.

sedai banada tabbaci akan zata tashi lafiya ƙalau because sometimes idan irin haka yafaru to idan mutum yatashi sekaga yasamu parilise wasu kuma sesu faɗa coma na tsayin lokaci,wasu kuma depression yakamasu dasauran su.

Ayanzudai tana coma wanda muke saran farkawanta nanda wasu ƴan awanni,sekuita mata addu'a akan Allah yafarkadda ita lafiya"

Alokacinda yakai aya alokacinne Ummy da yaya Najib suka iso wurin,dama Mahmud yaturama Yaya Najib rashin lafiyan Ummah Khadijan da asibitin dasuke ayanzu.

Sedai be gayamai dalilin ciwon nataba,shiyasa yanzu suna isowa yaya Najib yaga Doctor Mufeed agabansu yaƙara tambayan ba'asi,briefly yaƙaramai bayani yawuce abinshi.

Adokan aikinsu yasan yakamata yatambayesu dalilin shiganta wannan halin sedai duk cikinsu begame natsuwan daze iya yin hakanba.

Kiraye kirayen sallahn magrib yasanya mazan miƙewa daga zaunen dasuke.

Adam kuwa dama yana tsayene idanunshi kaphe akan Ummah Khadija da fuskanta ye fayau,harrama tayi lokaci guda.

Ahanyan dawowansune yaya Najib yakasa haƙuri sedaya tambaya Mahmud dalilin shiganta wannan halin.

Jiyayi cikinshi yaƙulle,nan take ƴan hanjinshi suka bada sautin ƙulu luw,hatta yaya Najib sedayaji sautin,amma betankamaiba sakamakon zaƙuwa dayayi yaji dalilin dayasanya ƴar uwanshi shiga wannan halin.

Gabaɗaya tsahon rayuwanshi betaɓa sanin yawu nada kauriba seyau dayakeso yahaɗiyeshi yakasa,ilahirin jikinshi rawa yakeyi kaman yanda zuciyanshi yake rawa,yabuɗe baki yakai sau goma amma yakasa furta ko kalma ɗaya.

Ganin haka yasa yaya Najib ƙin motsawa balle yatankamai,abuɗaya yasani shine baze jirgaba anan wurin harse yaji inda aka kwana aragaya.

Idan ubangiji yasoka da alheri seya turomaka ɗauki tahanyar dabakai zatoba,kaman yanda wayan yaya Najib yaɗaururi asa'ilinda ruhin Mahmud yakeneman arcewa yabar gangan jikinshi.

Tundaga ringing tone ɗin yasan mahaifiyansu ce,cikeda ladabi yaɗauka tamkar yana gabanta,dawannan daman Mahmud ye amfani yashige ciki dasauri yabarshi anan yana amsa waya.

A'inda ɗazu yatsaya anan yaganshi,idanunshi nakafe akanta ze'iya rantsewa akan ko ƙifta idanunshi bayayi.

Jiyayi zuciyanshi yamatse aƙirjinshi,tinanin halinda Adam ɗin zeshiga kaɗai asanda mahaifiyannashi tarasu nasa numfashinshi barazanan barin gangan jikinshi.

Sallaman yaya Najib acikin ɗakin yasanyashi jan numfashi me ƙarfi,bugun zuciyanshi naƙaruwa.

"Wai meye yasameta haka"?

Hatta iskan wurin sedaya yatsaya cak yadaina circulation saboda girman tambayan,idanunshi dasuka rine da fargaba da tashin hankali yasauke akan Adam.

Sedai komotsi begayayiba balle yanuna yaji abinda yaya Najib ɗin yace.

"Dakupha nakeyi,meyasameta tayanke jiki tafaɗi"

Yaya Najib yatamabaya aƙufule alaman haƙurinshi yakusa ƙarewa,aƙagare yake yaji abinda yasameta tunda yarigada yaji stage ɗinda take ciki ayanzu.

Shikaɗai yasan halinda zuciyanshi yakeciki,hatta numfashi daƙyar yake iya shaƙa,aduniyanshi behaɗa soyayyan ƴan uwanshi dakomaiba arayuwanshi.

balle khadija da halayyanta da ɗabi'unta ke samar matada matsuguni acikin zuciyan duk wanda yamu amalanceta.

Dadukkan wani haƙuri dayemai saura adaidai wannan lokacin yabuɗe bakinshi da cewa

"meyasa....

Sallaman Doctor Mufeed da abokan aikinshi yasanyashi maida bakinshi yarufe.

cikeda ƙwarewa yafara checking ɗinta bayan ƴan wasu daƙiƙu yaɗago kai idanunshi yatsayar akan Mahmud da tambayan.

"Kaine mijinta koh?"

Be iya amsamaiba sekanshi daya ɗagamai alaman"Eeey"

Yacigabada cewa,

"Tun yaushene tashiga halinda take ayanzu"

Zufane yaketomai daƙyar ya iya buɗe bakinshi yaɗaga harshenshi daƙyar sautin muryanshi yafito.

"Muma bamusaniba saboda anshiga ɗakin datakene kawai akaganta ahaka."

"Kafin tashiga wannan halin wani maganane kukayi da ita naƙarshe."

Kaman yanda Doctor Mufeed yarufe bakinshi,haka kowani part dayake kulawada jii na Mahmud yaɗauke,zaren tinaninshi yatsinke hakan yasa yarasa ko kalma ɗaya acikin ƙwaƙwal wanshi balle yafurta taga Doctor Mufeed da Yaya Najib dayaketa tambayanshi tun ɗazu.

Besan ƙafafuwanshi sunyi sanyiba sedayaji suna neman sugaza ɗaukanshi,ye aziman daphe garu yana yalwata idanunshi tawani ɓangaren.balle ye kuskuren ganin kalan kallon dasuke jifanshi dashi.

kaman saukan aradu haka yaji sa'ilinda Doctor Mufeed yamaida akalan tambayanshi zuwaga Adam.

Tambayan besanyashi ko motsawaba balle yanuna musu yaji,ido yazubamai tsoro na lulluɓe duniyanshi amemakon tashin hankali da fargaba.

betaɓa sanin soyayyan Adam nada matsuguni megirma acikin zuciyanshiba se ayanzu da masarrafan tinaninshi ya aikomaida saƙon

"'Anya Adam besamu matsalaba"?.shi shaidane akan kalan sonda yakema mahaifiyanshi,yanasonta fiyeda rayuwa da kanta,yana..."

Sautin muryan Adam dawani irin yanayi dayafi ƙarfin ko wace kalma dayasani tun farkon rayuwanshi har izuwa yanzu data ratsa masarrafan jinshi,tadakatarda duk wani hatsaniya dake cikin kanshi zuwa ƙwaƙwal wanshi.

"Kafin tashiga wannan halin sedatafara suma akayayyafamata ruwa tafarka sakamakon mijinta dayakawomata ƴaƴanshi nagabada fatiha"

Kaman ansamusu pause haka sukai tsam da ransu ko motsi sungazayisedai ataciki maganan Adam suke war warewa sunamusu fashin baƙi.

gyaran muryanda Doctor Mufeed yayine da maganan databiyo baya yasanyasu maida hankalinsu gareshi,

"Shin kasan exact time ɗinda tashiga wannan halin"

"A'a"

ya'amshi ataƙaice.

Dactor Mufeed yaɗauki file ɗinta dake gefen gadonta under drower yakama rubutu,sedaya kammala sannan yasa hannu yadanna ƙirjinta dai dai saitin zuciyanta daƙarfin gaske,amma bata motsaba sedaye haka sau uku amma ba'abinda yacanja.

Bakinshi yakai saitin kunninta yafara kiran sunanta amma batako motsaba,se numfashinta dayake hawa da sauka ahankali.

Kallonsu yayi basa buƙatan yabuɗe bakinshi yasanardasu mummunan labarin da fuskanshi tarigada tabayyana.

Baki yabuɗe daniyyan yinmusu bayani amma seyarasa ta'inda zefara,don haka seyamaida bakinshi yarufe,yafau takaddaya kama rubutamusu abinda ake buƙata.

"Ga wannan pls urgent asiyoshi a pharmacy,idan kundawo sekunimi doctor fu'ad shine da dutyn dare"

Adam ya'amshi takaddan batareda yafurta ko kalma ɗaya ba.

Ummy ce kawai ta iya amsashida"tom"

Amma daga Mahmud har Yaya Najib tambaya iri ɗayane azukatansu shine wani condition take ciki ayanzu sedai abinda suka gani zane a allon fuskan doctor yakashe duk wani ƙuwarin guiwa dasuke dashi.

Ganin Adam naƙoƙarin fita yasa Yaya Najib cemai yatsaya suje tare.

Shikuma Mahmud cikeda kunyan abinda ya'aikata yema Ummy sallama yakoma gida.

*** Da sallama yashiga cikin palon muryan Mubeen da Mubeena kawai yaji sun amsamai sallaman.

Dukda muryoyinsu sun dakushe saboda kukan dasukasha.

Idanunshine suka shiga cikin na Mardy tai saurin ɗaukesu,baya buƙatan seta buɗe baki ta tambaya yakaranci haka 'a fuskanta.

Soyakeyi yabuɗe baki yabata labari sedai bakinshi yaƙi bashi haɗin kai,abuɗaya yakeji ayanzu shine saƙonda ƴar ƙaraman muryan dake cikin kanshi tana sanardashi kada yafurta kalman dayake faman taunawa akan harshenshi,

domin ƙarya ne,ba haka maganan takeba,bakuma ze iya gayamata gaskiyan halinda Ummahn ta takecikba,meye amfanin ƙaryan dazeyi mata ayanzu?na wannan lokacinne kawai zatai farinciki sedai dazaran gobe tayi taje taga halinda take ciki to amaƙaryaci zata ɗaukeshi,dama awannan matsayin yake agunta.

Acikin ƙwayannin idanunta yaga yanda yakaryamata zuciya,yasan baze maida komai kamar daba amma zeyi iya ƙoƙarinshi wurin ganin yanuna musu suduka yasauya.

Badon yasoba sedai bayida yanda zeyi yashige cikin bedroom ɗinsu yahaɗomusu kayan dazasu buƙata acan asibitin.

Haryasakai zefice daga ɗakin yajuyo yakalli ƙusurwan dayasan yatafi yabar Asma'u agun yakalla amma seyaga wayam.

Nantake ƙirjinshi yahau luguden bugu,baki yabuɗe daniyyan tambayan Mardy dake zaune amma kallon dataimai yasanya sautin muryanshi ƙin fitowa.

Idanunta tasauke ƙasa,can yaji sautin muryanta,bayan sanyin dayayi naban mamaki akwai wani yanayi mewuyan fassaruwa atattare dashi,

"Tanacikin ɗakina,sukuma jariran Inna tajeyinmusu wanka"

Yana kallon yanda hawaye suka zubomata taɗaukesu dabayan hannunta kamun tamiƙe dasauri tashige cikin bedroom ɗinda suke kwana.

Alokaci guda idanunshi suka ciko taph da ƙwalla,jikinshi nayin sanyi irinna nadama.

Daƙyar ya iya ɗaga ƙafafu wanshi yabar ɗakin.

@@@

Koda yakoma ayanda yabarta ahaka yasameta,yema Ummy seda safe yadawo gida,bejima dashigowaba yaji Adam yashigo sannan yamaida ƙofan yarufe.

Gajiyanda yayi da kwanciya batareda yasamu bacciba yasanyashi miƙewa yaɗauro alwallah yakama sallah.

Kaman yanda Mahmud yakwana beruntsaba haka Adam,Asma'u da Mardy suka kwana.

Da zaran sunrufe idanunsu hotunan mutanen da sukai sanadin zuwansu duniyane yake cikamusu idanu dayanayi me ciwo.

Masu karatu kuya haƙuri semun haɗu a chapter 15.

Dafatandai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment sannan kui sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima.......

*ZAREN KADDARA*

حبلاالقدر*

® By Hindatu Auwal

HIKAYA WEITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOKS:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

_______________________________________

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol