Free chapter · Read without an account
CHAPTER [23
mardy datun zuwansu take kuka ahankali tabuɗe baki daƙyar,
"karku karɓi kuɗinshi inajin wani ba'ali megirma nadanneni da nauyin laifinane inda'ace na sitirta jikina 'a matsayina na ƴa mace,nayima sitirata ɗinkin daya dace dahaka befaruba,
bansaniba kohakan zezama excuse agareku amma bandani,laifine dabazan taɓa yafema kainaba balleshi,abuge yake lokacinda ya'aikata haka agareni,bayacikin hayyacinshi"
Sheik Imran yakalleta dakyau,kana yakalli Sadauki dakanshi ke duƙe yace,
"wannan hukuncin baze sauyaba saboda maganan ki,saboda kuduka kunada laifi,shi shaye shaye,ke kuma shiganda bedaceba,dukanku addininku yahanaku aikata waɗannan abubbuwan.
shaye shaye mummunan abune daze fitardakai dagacikin hayyacinka,yasanyaka aikata abubbuwa marasa kyau da muni,mutumin daye shaye shaye ba'abinda baze'iya aikatawaba,ciki harda kisankai,basena zurfafaba kunga illan shaye shaye awurin Sadauki,
alokacinda besha komaiba kallonki kawai yadingayi yanabin sahunki,duk dahaka bewuce iyakanshiba,amma dabaya cikin hayyacinshi ya'aikata abinda yazomai araine kawai,haka kowani me shaye shaye yake,yana aikata duk wani abu dayazomai arai kuma batareda wani tinaniba,
se mutum yadawo hayyacinshi seyashiga cikin dana sani mara 'adadi,shaye shaye tanada illoli dayawa ciki harda taɓa lafiya.
kekuma sanya tufafin dabe daceba,mace wace halittace dakeda banbanci meyawan gaske dana miji,shiyasa "John Gray" ye littafin men are from mars,women are from Venus in love,'
a'inda yabayyana tamkar jinsi biyun sunzone daga duniyoyi maban banta,don haka yanda mace keson asota daban da yanda namiji keson asoshi.
"chap man"yayi bayani sosai alittafin "love language",soyayyar itakanta tana shigan namijine ta ido wato (eyes), shiyasa ko alqur'ani akace kurufe tsiraicinku,da al'auranku,dayawan lokaci inzaki lura zakitama namiji magana amma baya fahimta sakamakon hankalinshi nakanki,keyake gani,yaren jikinki yake ganewa,
shiyasa namiji keda kalan type and choice na macenda yakeso aranshi, dazaran akabama namiji macenda bata cikin choices and type ɗinshi sekaga duk abinta zataimai bazata taɓa burgeshiba,
bcs of irin haka mlm bahaushe ye wata karin magana na matan kushe bata daraja,kamar yanda suka bayyana"alfred,bruner,stuart,"'acikin littafansu "understanding human nature,the proper study of man kind and study of thinking,"
'itakam mace dazaran kabita yanda addinin musulunci dakuma yanda halittansu yake,kaman yanda masana suka bayyana soyayyar kanta na shigan sune ta feelings,pores and ears,sedai ƙarfin soyayyan mace yafi shiga ta kunni,
dayawan lokaci zakaga mace tazo wucewane kawai taji na miji na magana setaji tana sonshi,saboda kalamanshi da'iya sarrafa harshenshi,mace naso azugata,ayabeta,akwanzar tata dasauransu,
Allah dakanshi yemana umarnin mu'amalantarsu da kyauta tawa,kuma don raunin dasuke dashi annabi(s) yatabbatar manada mafi khairin mutane shine mafi khairin ga iyalansa,yafaɗamana cewa mukyauta tamusu wurin mu'amalantarsu don an haliccesune daga rib,insuka karkace garin miƙardasu seka ɓallasu don haka akyautata"
jikinsune duka ye sanyi,musamman mahmud,ƙarshen maganan sheik Imran jiyayi kaman dashi yakeyi.
sadauki yalumshe idanunshi yanajin wani rahama na ratsashi,se'ayanzu yakejin komai na warwarewa nadaga cikin abinda yacunkushe ƙwaƙwal wanshi,
se ayanzu yaji numfashinshi nakaiwa inda yakamata,amma tundaga yammacin jiya daya dawo hayyacinshi yaji kaman antaremai numfashi,
sakayau yaji zuciyanshi babu duk wannan nauyin da kumburin,dagashi se ubangijinshine yasan halinda yashiga.
lawyern shi yaduƙo sukai magana tukun yamiƙe yadurƙusa agabansu,kanshi aƙasa,baki yabuɗe daniyyan yin magana,kuka meƙarfi yatahomai,kukane dayake explaining abinda yake ƙasan ranshi,jikinshi har yana ɓari,cikin kukan kalaman suka kuɓuto daga can ƙasan zuciyanshi
"don Allah kuyi ha..ƙu....ri"
yaƙarke yanasakin gunjin kuka,gabaɗayansu seda tausayin shi yakamasu,
"bakomai Allah shiyafemu gaba ɗaya"
Baba lecturer da mahmud suka haɗa baki wajen faɗi.
jajayen idanunshi yasauke akan kumburarriyan fuskan mardy,soyikeyi yaroƙeta,yabata haƙuri,kozata gane bahalinshi bane,amma taƙi yarda suhaɗa ido,yabuɗe baki yakai sau biyar amma bakalman data fito.
miƙewa tayi don tagajida kallon dayake mata,inyana kallonta jitakeyi duk wani natsuwa nata yakau,besan yariƙo hijjab ɗinta ba sedayaga tawatsamai kallo mecikeda tsana,
ɗan confidence ɗinda yasamu ayanzu ne yaji yana zaganyewa tareda tsananta agareshi,
"don Allah..."
yajawo kalman daƙyar ƙwalla na ciko gurbin idanuwanshi,soyikeyi takalli cikin idanunshi koyayane imbata gazgata kalaman shiba zataga matsayan komai acikinsu.
dasauri takauda kanta hawaye masu zaphi namata layi akan fuskanta,
"kainesa dani"
kukane mara sauti yaci ƙarfinta,zafin,raɗaɗin,yafi kwatancen duk mai kwatance,ba kalman dazata iya zuwa wurin balle tai bayanin yanayin,macenda irin haka yasametane kaɗai zata fahimta,
Sadauki yalumshe idanunshi,jijiyoyin kanshi na kumbura da tashin hankali mara adadi,jin kalamanta yakeyi kaman wasu abubbuwa masu kaifi dasuke yanka jijiyoyi da tsoka najikinshi,
hawaye suka taranmai,yana kallonta tawuce,iyayenta suka kammala magana da lawyernshi batareda yafahimci ko kalma ɗayaba,
shima miƙewa yayi asaiɓance,kewan Mamy ne yatasomai lokaci guda,kewanta yakeji har cikin ƙasusuwan jikinshi,rarrashi yake buƙata awannan lokacin sedai bayida wanda ze lallasheshi,yarasa wannan arayuwanshi,Mamy ce kuma tatafi shikenan,
tafiya yakeyi da ƙafafuwanshi cikin fitan hayyaci,gabaɗaya bayida natsuwan dazeyi tinanin wani abu bayan damuwan shi,balle ye tinanin wani abu waishi abun hawa,
da ciwo mara misaltuwa hawayenshi ke kwaranya,hannunshi kawai yake sawa yana gogewa saboda dishi dishi yake ganin hanya.
*Mommy*
tunda kalamanda suka fito daga bakin saleem suka shiga cikin kunnuwanta komai yakwance mata,feelings ɗinda taketa dannewa tsawon shekaru 22ne suka samu nasaran danneta,
tanaso taganshi ko sau ɗayane,takalleshi zuciyanta cikeda soyayya kaman kowace uwa,meyasa mutuwa zatai mata haka?
shin batasan tana buƙatan ganin fuskan ɗanta cikeda farinciki abayan duk wani alwashi nataba,
tasarai!tasaran zeyi rayuwa metsayi shiyasa takeyin komai yanda ranta yakeso,shiyasa taƙi karɓanshi amatsayin ɗa!harse mahaifinshi yakarɓeshi,datasan mutuwa zatai mata haka data rungumeshi,
batasan zuciyanta taci galaba akantaba sedata ganta atsakiyan ɗakin Sadauki dake ɓangaren mamy,
tasauke jajayen idanunta dasukai jajir kaman garwashin wuta akan photon shi,tasa hannu tana shafa fuskanshi dayake ɗaukeda murmushi kaman kakira sunanshi ya'amsa,
se'alokacin hawaye masu zaphi suka wankematafuska,batadamudatasharesuba,motsi taji alaman anshigo,tajuya jiƙaƙƙun idanunta suka sauka akan gudan jininta dayake azabure,jikinshi ye futu-futu sekace wanda ye burwaya aƙasa,
"Sadauki"
tafurta cikeda kokonto,tamkar kiran sunannashine zetabbatar mata da shiɗenne atsaye ba gizo yakemataba,
kallonta shima yakeyi cikin irin yanayin datake kallonshi,atare suka kai hannu suka taɓa fuskan juna,ye saurin janye hannunshi yana sheƙewa da dariya idanunshi na fitadda ruwan ƙwalla,
Momy tai sakato tana kallonshi cikeda al'ajabi,cikin dariyan dayakeyi kuka yaci ƙarfinshi,Momy takai hannu zata riƙeshi ye saurin jadabaya,
"base kinzoba awannan lokacin,kijira zuwa wani lokacin,n..."
saukan hannunta ajikinshi yasa sauran kalaman suɓucemai,kaman saukan wuta haka yaji hannunta ajikinshi,ye saurin ture hannunta yana jada baya,
nandanan yashiga haɗa gumi yana tsiyaya kaman wanda yahaɗiyi kunama,ganin tana yunƙurin sake kai hannunta jikinshi yasanyashi dakamata tsawa,
"bakya ganine?kuka nakeyi ina cikin ƙuna megautsi,kalan wanda nayi yasanyaki farin ciki lokacinda Mamy ta rasu..."
harshenshi ne yasarƙe,yajin gina kanshi da garu yaname cigabada zubadda ƙwalla,
kokaɗan bataji haushin shiba sema tausayin shi dayakamata,takai hannu yature,tasake kai hannu yature,kaman ƙaramin yaro,
tun yana ture hannunta har yahaƙura tarungumeshi ajikinta,suduka kuka sukeyi sosai,sanyi sanyi yakeji acikin ƙirjinshi,betaɓa sanin yanda kulawan mahaifiya yakeba seyau,
abinda yadaɗe yana haɗiyewane tsawon shekaru yatasomai tun daga ƙasan zuciyanshi yasaukan mai 'a maƙoshi,kalaman Mamy suka cikamai kunni hakan yasanyashi zare jikinshi ahankali yashige bathroom,
bedamuda ruwan sanyine kona zafibane yakama wanka abinshi,yana kammalawa yafito,jikinshi yamace gabaɗaya,har cikin ƙasusuwan jikinshi yakejin gajiyan dayayi,yasauke numfashi ganin bata ɗakin,
hayaniyan dayakeji 'a palon behanashi shiryawa yanda yakesoba,yana juyowa idanunshi suka sami muhalli acikin idanun Abeey,
kallo ɗaya zakaimai kashaida yana cikin mutanenda basa cikin kwanciyan hankali,idanunshi sunyi kicin-kicin alaman besamu bacciba,ga kumburin dasukayi alaman yaci kuka har yazarce misali,
kallon kallo suka shigayi atsakaninsu,kallone meƙunsheda ma'anoni dadama,sallaman Mommy yasanyasu kallonta,Abeey yabuɗe baki yaname sauke idanunshi ƙasa,
"ka...kazo"
kogezau Sadauki beyiba se kallonshi dayakefaman yi,ganin beda niyyan motsawa balle yanuna alaman yaji yasanyashi jan hannunshi suka fito palon,
ganin iyalan gidan yayi azaune suduka,bamusu yazauna batareda yace komaiba,Sheik Usman yabuɗe taroda addu'a,Sheik Imran yagabatar da abinda yatarasu,
Sadauki dai babaka se kunni,kokawa yakeyi da'abinda yakeji agameda su suduka,ihu yakeso yemusu yafitarda abinda ke cikinshi,shiyasa yakama muraja'an karatun alqur'ani akanshi don inya maida hankali akansu to za'asamu matsala,
"Sadauki"
Saleem yakira sunanshi da ƙarfin gaske,ye firgigit yaname matse idanunshi sekace wanda akatasa daga bacci,Sheik Imran yamai maita tambayan agareshi,
"Sadauki kayafemana?kashirya karɓanmu amatsayin danginka"?
karo nafarko da harshenshi yemai nauyi abakin shi,yadafe kanshi dayake barazanan rabewa gida biyu,sabon zazzaɓi na saukan mai,kalaman Mamy ne suka shiga yawo akanshi,
"Sadauki burina ɗayane aduniya shine inga rananda iyayenka da ƴan uwanka zasu tashi daga zaman son zuciyan dasukeyi,
rananda zasu amshi kusa kurensu,sedai bansaniba ko ubangiji yemun wannan tsawon ran amma inada tabbaci akanka,inada cikakken yaƙini akan duk wani magana dazata fito daga bakinka,
kaimun alƙwari zaka amshi ƴan uwanka,zaka koma hannun iyayenka aduk sanda suka buƙaci hakan"
ze'iya rantsuwa akan yanajin sautin muryanta acikin kunnuwanshi,yanda kasan yanzu take gayamai,kaman wancan lokacin jin jina kanshi kawai yayi,soyakeyi yabar wurin kozemanta da nan yafaru,
bejira abashi umarnin tafiyaba yamiƙe yafice daga palon,
kaitsaye get yanufa batareda yanimi abun hawaba yadinga tafiya akan diga diganshi,ayanayin dayike baya buƙatan komai samada kaɗaici,shiyasa yanufi inda bawanda zeyi tsammanin nan yaje,
Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun haɗu a chapter 24
Dafatan labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba ɗayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment sannan kui mana sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
HIKAYA WRITERS ASSOCIATION
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
________________________________________