Free chapter · Read without an account
CHAPTER [33
shikaɗai yasan halinda yakeciki,iska yake buƙatan shaƙa,
yadafe kanshi dayaji yaƙara girma tsaban ciwonda yakemai,yana shiga bedroom ɗinnashi idanunshi suka sauka akan trolley ɗin dabaze iya cewa ga lokaci na ƙarshe daye amfani dashiba,kaman yanda ayanzu baze'iya faɗin ko meye acikiba,
jin alaman anshigo besanyashi juyowaba,don ƙamshin tirarenta kaɗai yarigada yabayyanarda kowacece,
Abeey ne shima yashigo,idanunshi yalumshe cikin son danne abinda yake tasomai yafurta,
"I want to be alone pls"...
Abeey yafara magana cikin kuka,
"Sadauki mekake buƙata daga garemu,sokakeyi mudinga baka haƙuri harsekaji ya isheka?ko sokakeyi mudinga binka harse kagaji daganin inuwanmu?
kome kakeso mui maka wallahi zamui maka,abuɗaya muke buƙata daga gareka shine kayafemana,
mun amshi kusa kurenmu,mun san mun ɓatamaka,baseka hukuntamu tawannan fanninba,ubangijin daya halicceka,ya haliccemu,yarigada yahukuntamu,"
Abeey yaƙarke hawaye nazarya akan kumatunshi,
shirune yaratsa ɗakin na tsayin wasu daƙiƙu,suduka sun fiddaran zeyi magana,se suka tsinkayi muryanshi can ƙasan maƙoshi,
"narigada nasabajin gaskiya daga bakinku,bazan iya sauraron wannan sabon abunba,
don Allah kutafi,nasan zanyi kuka natsayin kwanaki 10 kafin inhaƙura amma bazan'iya rayuwa dakuba,
saboda zankasance kullum cikin fargaban ranan dazaku barni,ba'irin wannan rayuwan nakesoba wanda kullum zanzo intabarar soyayyanku"
tunda yafara magana Mommy take girgiza kai hawayenta na tsananta gudu,
"Sadauki don Allah kabarmu mukusanceka da soyayyanmu,kabarmu mununa maka canjin da'aka samu,
wallahi!mungane!mungane kuskuren damuka aikata saboda son zuciyo yinmu,
ashirye muke!ashirye muke mui komai daze nunamaka muna sonka,batun jiyaba,batun yau ko yanzu danake maganaba,balle kai tinanin zamu juyamaka baya yau ko gobe,
tatacciyar soyayyane dake wanzuwa acikin zuciyan ko wasu iyaye,soyayya neda babu algush ko cutarwa balle munafunci ko shiri don cimma wani buri,soyayyane daze kasance ataredamu har bugawan numfashinmu naƙarshe,"
miƙewa yayi daga zaunen dayake,hannunshi ɗaya tallabeda kanshi,bazece beji duk abinda taceba,sedai yahanashi yin tasiri azuciyanshi,sakamakon solving ɗin wani equation dayakeyi acikin kanshi,
seda yakai ƙofan bathroom ɗin,batareda yajuyoba yace,
"seda safenku"
"Sadauki kayafemana"
juyowa yayi agajiye,ya sauke idanunshi acikinnata,
"'akwai abinda nakeso kufahimta aduk nisanta kaina dazanyi daku,
basona kukeyiba,ba ƙaunata kukeji arankuba,ganin laifin kai dakaine yajawo hakan,
wannan shine karo nafarko dawani yakar yamuku zuciya,yasanya kuke ganin komai yafarune saboda sakacinku,
nasani!kunsani! buƙatan mai gayamuku basaka cin kubane yasanya na aikata abinda na aikata kukeyi,toni ayanzu zangayamuku ba-saka-cin-kubane,"
yaƙarke yana musu dalla-dalla,
"S....."
dasauri yatari numfashin Abeey,
"'inbahakabane meyasa seyanzu zaku karɓeni,?shin abaya banso kubane?
banyi baran soyayyan kuba,meyasa kukaƙi karɓata?"
bayada amsan daze bashi matuƙar babuɗemai zuciyanshi zeyi yaga tarin ƙaunanshi daya cikata tareda ɗinbin danasanin abinda ya'aikata agareshiba,sedai bayada ikon yin hakan,
yasake kallon idanun Sadauki,karo nafarko dayaga wani ɗabi'a na Bintu ataredashi bayan fuskanta daya ɗauko,
rikicine zalla acikin ƙwayan nin idanun shi,fushi,taurinkai gamida kafiya suka ƙara kumbura jijiyoyin kanshi dasuke bugawa saboda ciwonda yakemai,se sukai ruɗu ruɗu suka mimmiƙe,
sanin kanshine duk abinda zefaɗa ayanzu bazeyi tasiri akanshiba,matuƙar yaji ɓanci lallashi da roƙo,
shiyasa yabuɗe bakinshi da hukuncin daya yanke tun sa'ilinda aka kammala meeting ɗinnan,
besaniba koyayi dai dai,ko kuma yaso kanshine da abinda yake tsoron nangaba ze iya faruwaba,matuƙar yabarshi yacigaba tafiyar da rayuwanshi ahaka,
abudai ɗayane yatsayu akai da dukkan zuciyanshi shine yana buƙatan ɗanshi akusadashi,
"ga kayan kanan nahaɗamaka acikin trolley ɗinka,kaduba abinda kake buƙata wanda bansamakaba,
nabaka one hour kafito mutafi"
waro idanu sukayi cikeda mamaki,don ita kanta Mommyn tagir giza balle kumashi uban gayyan,
bebi takanshi da halin dayake cikiba,yasakai yafice daga ɗakin,
*Mardy*
zaune suke suduka apalon,gadai idanunsu ƙuri akan tv amma hankalinsu baya wurin,
"Yaya yaushe Ummah zata dawo"
kallon Mubeen ɗin yayi batareda yace komaiba,
sallama sukaji suduka,dagudu su Mubeen suka tashi,yana kallon Mardy tamiƙe itama,shikanshi besan yamiƙeba sedaya ganshi atsaye,
ye murmushin da rabonda ye kalanshi har yamanta,cikin palon taƙariso,se alokacin yaga Abbansu da alamama shiya ɗaukota,
"Mardy yajikin"?
kanta tasunkuyar,zuciyanta nawani irin karyewa,
"I'm sorry Ummah"
tafaɗi muryanta narawa,
'amemakon Ummah ta'amsata secewa tayi,
"kinsha maganinki kuwa"?
kai tagir giza mata,
kallon mubeena tayi,
"jeki ɗaukomun maganinta"
"kunci abinci"?
tasake tambaya,
Adam yace,
"tayaya zamu iya cin abinci!bayan muna kewanki"
"kai yaya bayanzu muka gama cin abinciba"
yanda Mubeen ye maganan da'iya gaskiyanshi yasanyasu darawa,
maganin taɗauko Ummah tabata dakanta,zamewa tayi takwanta akan cinyan Ummah,batajimaba bacci yaɗauketa,dayike akwai maganin bacci acikin magun gunan nata,
hira suka shigayi atsakanin su cikin salon son manta abinda yafaru abaya,
"Ummah!!!!"
Mardy tafaɗi daƙarfi tana miƙewa afirgice,dasauri Ummah tariƙota,
"Ummah kece?mafarki nakeyi?bada gaske bane?!"
tafaɗi cikin wata iriyan raunan niyan murya,hawaye na tsananta gudu akan kuncinta,riƙonda Ummah taimata besanya jikinta yadaina ɓariba,
"Mardy menene"!!!
"Ummah shine!shine yaƙara zuwa,haryanzu beha ƙuraba"
taƙarke maganan cikin gunjin kuka,kuka take da dukkan ƙarfinta,kuka takeyi tanajin wani irin ciwo aƙirjinta,ga tsoron Sadauki dayagama bin kowani lungu da saƙo najikinta,
jikin sune yesanyi suduka,ɗakin yewani irin shiru naban mamaki,se sautin kukan mardy dayake tashi,
cikeda lallashi Ummah take bubbuga bayanta,har kukan yatsagaita tashiga sakin ajiyan zuciya ajejjere,
miƙewa Adam yayi yaƙariso inda take,hannunta yakamo duka biyun asanda yake durƙusawa agabanta,
suduka kallonshi sukeyi,
"buɗe idanunki kikalleni"
jajayen idanunta tasauke acikin nashi idanun dasuke ƙunsheda wani abu daya shallake tinaninta,
"Mardy Sadauki bayanan,kuma Sadauki bazezo nanba,amma zekasance anan!zaki ganshi anan!zamui magananshi anan!kinsan meyasa?
saboda yanacikin zuciyanki,tsoronshi nacikin kowani gaɓa dake jikinki,saboda imagination ɗinki akanshi yake akullum akoda yaushe,
Mardy komai zedawo dai daine idan kika rabuda Sadauki,sekin fara cireshi da tsoronshi acikin zuciyanki sannan zaki rayuwan farinciki,natsuwanki dakomai naki zedawo gareki"
kai tashiga girgizawa hawaye nazuban mata,
"bazan iyaba,wallahi bazan iyaba,nikaɗai nasan halinda nake ciki,kona faɗa bazaka ganeba"
Idanunshi yalumshe hawaye masu ɗumi nabin fuskanshi,bayada juriya sam!akan maku santanshi,zuciyanshi bata iya ɗauka,tanada rauni tawannan fannin,
"Yaya don Allah kadaina kuka"
Mardy tafaɗi hawayenta naƙara ƙarfi wajen kwaranya,
"zandaina kukane kaɗai asanda kika daina kuka,shin kinmantane damuwan ɗayanmu nanufin damuwanmu muduka!"
kai tajinjina,acikin idanunshi take ganin yanda ze iya bata rayuwanshi don kawai ita tarayu,dagaske yakeyi rayuwanshi bakomai bane akan makusan tanshi,
"Yaya ku kasance akoda yaushe kunamun addu'a,insha Allah komai zeyi dai dai,muma zamuci gabada farinciki kaman daa"
*SADAUKI*
Nawaila da sameera dake palo sunajin duk abinda kefaruwa,koda one hour ɗin yacika Sadauki befitoba sesuka miƙe suka shiga,don sunsan ataurinkai irin nashi bazeyi abinda akace maiba,
"'inkagama kafito kai ake jira"
Sameera tafaɗa tana kasheshi da manyan idanuwanta kalannashi,
"ba'inda zani"
ye maganan ataƙaice,
"kodan Mamy"
Nawaila yafaɗi yana kamo kafaɗanshi,
kai yakauda yaname cewa,
"bakai zakagayamun abinda mamy zataso dawanda bazatasoba"
Sameera ce tazagaya taɗayan ɓarayin daya maida kanshi,
"Sadauki karasa komai da Mamy tataphi tabarka dashi,don Allah karkarasa wannan alƙawarin dakaimata shima"
Idanunshi yarumtse batareda yace dasu komaiba,hannunshi Sameera takama,bataso ye tinani,bataso yatina abubbuwan dasuka wuce,lurada hakan da Nawaila yayi yasanyashi yin magana cikeda lallashi,
"every body makes mistakes in life. but doesn't mean they have to pay for them for the rest of their lives. some times good people make bad choices,it doesn't mean they are bad.it means they are humans."
Sadauki ye shiru yanajin yanda sabbi da tsoffin ciwukan dake ƙirjinshi suke buɗewa dawani irin ciwo me zafi,
suduka sun fahimci halinda yake ciki,sedai ayanzu baƙatan dazasuimai samada sutayashi cika burin Mamy,
miƙardashi sukayi,ahankali suka fara janshi,se alokacin yabuɗe idanun shi,muryanshi akarye yafito,zuciyan shi namai ƙuna,
"banason ganinsu,banason magana dasu,banason duk wani abu daze sanya naji inada alaƙa dasu,
kugayaamun tayaya zan rayu dasu a'inuwa ɗaya"?
shiru sukayi suduka don basada amsan dazasu bashi,
Masu karatu kuya hakuri semun hadu a chapter 34
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku,sannan kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima.......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_____________________________________