Free chapter · Read without an account
CHAPTER [34
batareda yashare hawayen fuskan shiba,haƙuri yashiga bama abinda yesaura azuciyanshi dayemai haƙuri yabarshi yacika alkawarin dayema Mamy,
da dukkan wani abu dayake dashi yaɗaga ƙafanshi suka cigabada takawa har suka iso bakin gate suka hau motan Nawaila, Sameera bata bisuba ta tsaya anan gida.
***
"Dude!mun iso"
idanunshi dake alumshe tun sa'ilinda suka kamo hanya yabuɗe,dawani irin nisantaccen yanayi yake kallon gidan,sedai bece komaiba yabuɗe yafito,
atare suka shiga cikin palon,Abby nazaune shida Sofiyya,
muryan Nawaila kawai sukaji ye sallama,banda Sadauki daya ɗauke kanshi tamkar bagida yashigoba,
Abby dakanshi yamusu jagora zuwa ɗakin Sadauki dayasa aka gyaramai asaman bene,
dama gidan 3 plat ne dayake ɗaukeda babban palo nafarko da saman bene,inda saman benen yake ɗaukeda 2 bedroom kowannensu da bathroom ɗinshi,se madai daicin palo da dining se kitchen,
daga palon farkone zakaje palo na 2,inda shine yake ɗaukeda 3 bedrooms,se ɗayan flate ɗin dake haɗeda palo nabiyu,
gidan yayi matuƙar kyau gamida tsaruwa,da kallo ɗaya zaka shaida gidane na ƴan boko masu jida iya gayu da ado gamida exposure,
apalo Sadauki yadoge suduka bawanda yabitakanshi saboda sanin halinshi dasukayi ahakanma sunyi matuƙar cin sa'a,
@@@
Cikeda natsuwa yazauna ahannun kujeran da Sadauki kekwance,dukda ba bacci yakeyiba idanunshi alumshe suke,
ko sallahn Athuba dasukaje beyarda sunyi ido 4da Abby ba,gashi fitan gaggawa yakamashi,
"Dude!"
yakira sunanshi asanyaye,sanin baze amsashiba yasanyashi cigabada magana cikeda lallashi,
"Sadauki!kowani ahali suna samun matsala da rashin fahimtan juna,hakan bayana nufin yaƙin duniya bane,a'a hakan nanufin ajizanci naɗan adam,
Dude!kowani mutum yana kuskure kuma ubangiji yana yafemasa,
muma mukanyima juna kuskure kuma muyafema juna,hakan baya nanufin wanda ye laifin dawanda ye yafiyan sunada ban banci bane,
don abuɗaya za'asamu aƙarke shine zaman lafiya da natsuwan zuciya,
Don Allah kabasu dama,ka amshesu da kyakkyawan niyya,dayardan ubangijin mu bazakai danasaniba"
Idan kujeran da Sadauki kekai yamotsa to Sadauki yamotsa,
hakanan Nawaila yamiƙe yeficewarshi,
aƙalla yakwashe mintuna 10 yana zaune tukun yabuɗe idanunshi dasukai jajir kaman'an'iza wutan murhu,
bedroom ɗinda Nawaila yakwana yashiga,yanayin dayake ciki behanashi ganin tsaruwan ɗakinba,musamman ma color ɗin furniture's ɗin da suka kasance color ɗinda yake matuƙarso,
Scrolling ɗin idanunshi yashigayi acikin ɗakin kozega trolley ɗinshi,ganin beganshiba yasanyashi shiga ɗakin sauya kaya,
closet yabuɗe kayayyakinshi yagani ajere,wanda yasan aikin Nawaila ne,
yalumshe idanunshi colors ɗin kayan nacikamai kai,ayanda yakejinshi ayanzu dayanda rayuwanshi yasauya baya buƙatan duk waɗannan,
kayayyakin yashiga cirowa yana watsi dasu aduk inda hannunshi yakai,beji shigowan mutum ba,sema gananshi dayaji abayanshi,
"Sadauki mekakeyi haka? wannan kayan meza'ayi dasu?ina kake shirin zuwa"
Yajeromai duka tambayoyin,damuwanshi na fitowa ƙarara,hakan yasa muryanshi yin sanyi naban mamaki,
Shikanshi Sadauki seda sanyin muryan Abby ɗin yataɓashi amma yanda yabashi amsa adake sekarantse beji komaiba,
"fitardasu zanyi,don bana buƙatan kaya masu kaloli da kuma kwalliya,
rayuwata tacanja,komai yatashi daga yanda nasanshi tundaga yarintana har girmana"
"Sadauki!!!"...
"Abby don Allah!kai shiru,basekace komaiba,narigada nasan tun asali baka kuƙatan Sadauki meyawan fara'a da shagwaɓa,
Sadauki mesanya ƙananun kaya da fita tareda abokai maban banta,
zansa asiyomun yadika kala biyu,farida baƙi,aimun ɗinkin tazarce,akoda yaushe fuskata zata kasance aturɓune,babu fara'a balle murmushi,
bazan ƙarama kuwwa shagwaɓa ba balle inbuƙaci lallashi,kuma zandaina yawan surutu daniman kuwwa yaraɓeni,
zandaina!zanbar komai!! shikenan ko? kayi farinciki"
yaƙarke hawaye masu zafi nabin fuskanshi,irin hawayenda ke kawaranya acikin gudan naman dake ƙirjinshi aduk sa'ilinda yatina iyayenshi,
jiki amatuƙar sanyaye yatako zuwa inda yake tsaye,
"waya gayamaka haka!"
yemaganan yana juyo dashi zuwa gareshi,
"kaji kalleni!Abbynka nasanka,Abbynka naƙaunarka aduk yanda kake,
nasan nayi laifi,nayi kuskure,don Allan kayafema wannan Abbynnaka"!
yaƙarke yanasakin kuka mesauti,
zuciyar Sadauki tai wani irin karyewa,sekawai yarungumeshi shima hawaye nabin fuskanshi,
dai daito yakeji awurare maban banta,duk yanda yaso ɓoye soyayyan dayake musu yakasa,zuciyanshi takasa jurewa,kaman yanda Nawaila yafaɗine,
ayanzu bayada fatan dayawuce ubangiji yaɗoraddasu cikin farinciki da ƙaunan juna.
*Budewan ƙwaƙwalwa alokacin bacci*
Gudu takeyi cikin filin wasan,tana dariya cikeda nishaɗi,iskan ruwanda yataso besanyata tsayawaba,
tanajin takun mahaifiyanta datake biyeda ita,sotakeyi setaga ƙarken gudun Nury,hakan yasa batako kallon gabanta,
wata faran motace ƙirar waccan lokacin tanufo dagudun gaske,
Tsayawa tayi chak! kallon motan takeyi zuciyanta nawani irin tsinkewa,tsoro gamida yarintan dake damunta awannan lokacin yasanyata suman tsaye,
"Husnah"!
taji muryan mahaifiyan nata abayanta,
wai wayawa tayi takalleta,se ayanzu taga tazaran dake tsakaninsu,takuma juyowa takalli motan dake gabanta,
tarumtse idanunta zuciyanta natsananta gudu,jitayi wani abu yesama da'ita,kafin tajita timm!alaman faɗuwan wani abu,
"Husnah" "Nury"
muryoyinsu suka fito cikin matsanancin tashin hankali,
duka haka tafarune cikin ƙasada daƙiƙu 5,
jin bataji zafiba,ga ƙamshin mutuminda ' ako'ina taji zata shaidashi,yasanyata buɗe idanunta,
Abbanta tagani,shima ita yake kallo,jikinta gabaɗaya rawa yakeyi,kuka tafashe dashi,
yaƙan ƙameta aƙirjinshi,sautin kukanta behanata jin bugun zuciyan shiba,bayanta yashiga shafawa cikeda lallashi,
"kwantarda hankalinki,Abbanki na atare dake"
"Abba..."
tafaɗi cikin muryan kuka,kaman kiranda taimai shize tabbatar matada Abban natane,
@@@
acikin kunnuwanta tafarajin shesh sheƙan kukanta,tabuɗe idanunta dasuka jiƙe dahawaye akan siliph,
takure jikinta tai tanasake fashewa dakuka,ga jikinta dayake rawa,kokawa takeyi da numfashinta dakeneman ɗaukewa,
agefe guda kuma fafutuka takeyi,cikin kanta take bincikawa kozata samu wani abu agameda rayuwanta nabaya.
Mardy dake kusada itane tafarka,jawota tayi jikinta tana girgizata,ganin yanda takejan numfashi tana fitarwa kaman mekoyan hakan yasanyata tsorata.
"Asma'u"!
tafaɗi daƙarfin gaske,wanda yedai daida ajiyan zuciyan data sauke,
Adamne yafara shigowa,Mubeen na bayanshi,kan gadon yahauro,batareda tinanin komaiba yaɗora kanta acinyanshi,
"ke!ke!!"..
Adam kefaɗi yana shafa fuskanta dayatsunshi,
"Asma'u"..
Mardy takira sunanta cikin tashin hankali,batasanma sunayiba,
"tamuto ko?"
Mardy tafaɗi tana kallon Adam cikin idanuwa,
shiru yayi bece komaiba,don shima zuciyanshi zafi takemasa,
"samo ruwa"
yafadi cikin zuciyanshi yana addu'an ubangiji yasa tinaninshi yazamo gaskiya,
bashi ruwan tayi,yasama ahannunshi yashafamata afuska,san sanyar ajiyan zuciya tasauke lokaci guda tana buɗe idanunta,
wani irin ɓoyayyiyar ajiyan zuciya Adam yasauke,adai adai lokacin su Ummah suka shigo,
Asma'u tayunƙura daniyyan zama Adam yatai makamata,
"Mekefaruwa"
Abba yatambaya yana kallonsu suduka,
"Asma'uce tasuma"
Mardy tafaɗi cikin muryan kuka,
"meyasamu Asma'un"
Ummah ta tambaya tana kamo hannunta,
"Nima bansaniba"
"Ke Asma'u meyasameki"
Abba yatambaya cikeda kulawa,
cikin sanyinta tabashi amsa,
"bakomai kawai inaƙoƙarin tina wani abune"
lallashinta Abba yashigayi tareda yinmata nasiha,seda sukaga tasamu natsuwa sannan suka koma makwancinsu,
Asma'u talumshe idanunta,bazaka taɓa sanin me akenufida ƙuncin rayuwaba sekarasa wasu mutane dakai matuƙar shaƙuwa dasu arayuwa,
Abin bazemaka ciwoba sekanimi sautin muryansu,dariyansu,da hotunansu acikin kanka karasa,
Gashi babu halin sake ganinsu a'ido biyu,bakada daman sake jin muryansu balle dariyansu,
Saboda sunmaka nisa,suntafi wani wuri dabakada halin zuwa balle kagansu,
Dawahala karasa mutum,kazauna dagakai se tinaninshi,
Ta'aziyya gaduk wani maraya dama dukwanda yataɓa ɗan ɗana ɗacin rashi!!!
Tasa hannu tagoge hawayen fuskanta,kewan ahalinta nasake lulluɓeta alokuta nabarkatai,
Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun hadu a chapter 35
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mun comment,kununa mun reaction dinku,sannan kui mun sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se ajima.......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
*®By Hindatu Auwal*
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOKS:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_______________________________________