Free chapter · Read without an account
CHAPTER [43
Miƙewa yay,idanunshi kafe akanta,batareda yasan mezece da itaba.
Idanuntane suka sauka akanshi,tai saurin ɗaukesu daga gareshi kaman wani naman ruwa ko wani abu datai kuskuren gani batareda tai zato ko tsammaniba.
Idanunta kafe suke akan tile's ɗinda ke wurin,laɓɓanta dasuke matuƙar burgeshi suka motsa,muryanta tafito ɗaukeda abinda yafi tsana aduniya.
"Koda ace maza sunƙare,duniyan nan tarage dagani sekai bazan taɓa ƙaunatar kaba,
Idannace natsaneka nagayamaka wata kalmace me daɗi,zahirin abinda nakeji akanka yafi ƙarfin kowace kalma,babu kalman dazatazo kusada abinda nakeji akanka balle tafassarashi.
Don haka kada kacigaba wahaladda kanka akan abinda bazaka taɓa samuba"
Tana gama faɗin haka tajuya tafice daga palon,ko motsi beyiba,balle ye yunƙurin hanata tafiya,don bayamada wannan ƙarfin,
Don kalamanta ba'iya zuciyanshi ta kassaraba hadda jikinshi,sedai beji aranshi zesareba,balle yajanye yadaina ƙaunanta,kaman yanda tace.
Ƙafafuwanshi da sukaimai nauyi yaɗaga yabar gidan jiki amatuƙar saɓule.
*MARDY*
Taƙofan baya tashiga palon taname addu'an Allah yasa babu kuwwa acikin palon.
Aikam Allah ya'amshi addu'anta,don bataga kuwwaba,ɗakinsu tashige wanda yedai dai da ringing ɗin da wayanta takamayi.
Seda tafara saita kanta,kana taɗauki wayanda sallama abakinta.
"Dagaskene wani yanimi izinin taɗidake"
Shine abinda kunnuwanta suka juyomata.
Dasauri tace,
"Hon...
"Dagaskene?"
Yamai maita tambayan cikin matsanancin fushi da ɓacin rai,
Mardy tahaɗiyi wani koren yawu me ɗacin gaske,muryanta narawa tace,
"Eyyy 'am...."
"Dit-dit"
Taji yakatse wayanshi.
Idanuntane suka ciko da ƙwalla masu zafi, tai dialing numbernshi sedai har takatse beɗaukaba,sake kiratayi nanma beɗaukaba.
Idanuntane suka sauka akan wayan Ummah da tabama Asma'u tasanyamata 'a chargy,saboda chargernta yalalace kuma ba akawo mata waniba.
Hannunta har yana rawa wajen ɗaukan wayan,batareda wani ɓata lokaciba tai dialing numbernshi,bugun farko yaɗaga,
Tana buɗe baki daniyyan magana kuka yaƙwacemata,batai yin ƙurin dakatardashiba don beyi shawara da'itaba lokacinda zezo,ayanayin datake ciki ayanzu ba'abinda zatayi tasamu sauƙin abinda takeji samada kukan.
Inda Abba yasan abinda takeji akan Sadauki da ba abinda zesanyashi yaceda ita taje wurinshi,
Seda taimai isanta sannan tazauna akan carpet tana sauke numfashi tareda sheshsheƙan kukanda batasan tsawon lokacinda taɗauka tanayiba,
"Kingama kukan inkashe wayata"
Zaid yafaɗi daga can ɓangaren,
Dasauri taɗauki wayan don taɗauka yakashe wayanshi tun ɗazu.
"Uhm_hmm!!"
Yafaɗi alaman ita yake sauraro.
Mardy tarumtse idanunta,cikin muryan kuka tace,
"kayahakuri,amma wallahi bada izinina yazoba,hasalima bansan dashiba,yanda kaji maganan nan asama haka nima naji,amma don Allah kayahakuri,nasan nayi laifi daban sanar makaba."
Jikinshine yesanyi ƙalau,se yanzu yaga rashin kyautawan da shima ya mata,dan kamata yayi ya kira ya tambayeta cikin natsuwa,
"kiyi haƙuri nima ban kyauta ba,nasa kin zubar da hawaye dan Allah ki yafema wannan mijinnaki da kishi yake neman zautashi."
Mardy tai murmushi me sauti,tana ɗauke kwallan daya ciko idanunta,
"bari in kiraki ta wayanki karmu cinyema Ummah kati."
Goshinta takife a tafin hannunta,ita shaph ta manta wayan ummah ne,balle wani abu waishi kati.
Be jira me zata ce ba ya katse wayan,ko motsawa batayi daga gun ba kiranshi ya shigo wayanta.seda ta fara maidama Ummah wayanta a chargy sannan ta ɗauki kiran tana kwanciya ruph da ciki.
*NO 56 TABARAKALLAH KANO*
*Hajiya Mainah*
zaune take a bakin gadon hannunta dafe da kanta da yake mata ciwo,yalwataccen gashin attach ɗin da akaimata kitso dashi ya hargitse ya rufe fuskanta rijib,numfashi take maidawa a hankali,zuciyanta na mata ciwo maramisaltuwa.
Runtse idanunta tayi da ƙarfi,batareda kuma tinanin komaiba tasa hannu ta ingije yarinyanda ko fuskanta bata saniba balle kuma sunanta.
Hannunta ɗaya dafe da kanta ta miƙe,bata damu da jirin dake neman kayar da ita ba tasa hannu ta buɗe bed side drawer ɗinta ta ciro raper ɗin dubu 300 tawatsamata.
Cikin murya irinna mashaya ma'abota gushewan hankali tai magana,
"na baki mintina 5 kisanya kayanki ki fita daga gidannan"
"Ha......"
"shshhh....."
Hajiya Mainah ta katse matashiyan yarinyan,taɗora da
"mintina 5 nabaki kacal"
taƙarike tana jan ƙafafunta ta shige bathroom.
Shower ta sakar ma kanta,tana tsaye a inda take ta saki towel ɗin dake jikinta,hawayene suka shiga sintiri a fuskarta,suna bin ruwan dake sauka a saman fuskanta suna bin rariya.
Jikinta ta ƙanƙame awuri guda,tana sake fashewa da kuka wanda bayada sauti,saidai wani irin raɗaɗi da baya buƙatan a faɗeshi.
Kuka ne da kullum saitayishi kuma zata cigaba da yinshi na tsawan lokacinda da bata sani ba a rayuwarta.
Bata daina kukan ba sedataji kanta yai mata girma tsaban ciwanda yakemata, idanunta sun mata nauyi dan daƙyar ma take iya buɗe su.
Hannu tasa ta jawo towel ta rufe jikinta tafiya ta shigayi ahankali,bata damu da ta sanyama jikinta wani abu ba,balle ta kauda kwalaben abubuwan da sirinjan alluran da taima jikintaba ta faɗa kan gado ruph da ciki.
Nan take bacci me nauyi yayi awon gaba da ita,kaman a mafarki taji wani abu me ɗumi na fita ta ƙasanta tamkar fitsari.
Idanunta da suka kumbure,sakamakon bacci da kukan da tasha tabuɗe,tun kafin takai hannu ta duba idanunta suka hasko mata yanda farar towel ɗin dake jikinta taɓaci,ga wani irin wari data rasa ko na menene yacikamata hanci.
Da sauri ta miƙe gadon ya ɓaci gaba ɗaya,ya jiƙe sharkaph,saidai tanada tabbacin wannan abin ba fitsari bane sedai wani abun daban.
Sakamakon colour ɗinshi me ruwan ganye ne,ga warinda a yanzu ta gane daga jikinta yake fitowa tareda wannan ruwan.
Ƙwalla ne ya ciko idanunta,kafin ya fara sintiri asaman fuskanta,ta ɗora hannu akai tanajin wani irin tashin hankali na lulluɓeta.
Wayantace ta hau ƙara,kalle kalle ta shiga yi ko zata hangota aikam can ta hangota a yashe akan carpet ɗin da ke gaban gadonta inda ta gama shaye shayenta.
Tana ɗauka taga sunan mijinta ya fito ɓaroɓaro akan screen ɗin take jikinta ya hau kyarma,tana kallon wayan takatse,ba tareda tai wani yunƙuriba,message ya shigo shima ɗaukeda sunan mijinta,daƙyar ta iya saita kanta takaranta saƙon.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 44
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya[,kudai kui min comment,kununamin reaction dinku sannan kui min sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal.
Se anjima......
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
*By Hindatu Auwal.
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOK:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
____________________________________