Free chapter 路 Read without an account
6
*SHANTYTY馃拑馃挄*
_The Little Sister of Manga_
*_(茦ANWAR MANGA)_*
A charming cinematic Hausa comedy-drama that celebrates family, friendship, mischief, and the unforgettable journey of a spirited young girl whose presence changes everyone's life.
Page 6
Karime ta yi maganar ido a zare tana kuma kasa kunne ai bata ma jira Shantyty ta amsa mata ba, gaba daya suka 蓷unguma zuwa waje, ta saitin shagon Gwage mai provision suka hango mutane tsai-tsaye sun yi cincirindo hakan ya hana su damar hango fuskar matar dake tsaye rungume da yarinya a 茩irjinta.
"Wallahi ba zan yarda ba dole abi min hakkina ni da 'yata, kuma Gwage Allah ya isa ne tsakanina da kai yanzu dama tuntuni abin da kakeyiwa yarinyar nan ke nan babu tausayawa? to kuwa ba zan ta蓳a yarda ba hukuma ce zata rabani da kai, ka cuceni ka cuta 'yata."
Kalaman da matar keyi ke nan cikin sheshsheka da alama taci kuka ta koshi.
"Antynmu me yake faruwa ne, Me ya sama Teemah?"
Karime ta jero ma matar tambayoyin a ru蓷e sai dai da yake ita ma a ru蓷en take sam bata hayyacinta ya sa bata bi ta kan Karime dake jero mata tambayoyi ba.
"Ke dalla ya isa haka da zaki wani zo ki taramin jama'a ai sai ki fa蓷a abin da nayi Wa 'yar taki."
Gwage ya fa蓷a yana daga cikin shagon nasa yana wani ciccin magani.
"Fyade kayi ma 'yata Teemah azzalumi kawai macuci ta turke yarinya 茩arama a shago kana zalinta ba dan Allah ya kawoni ba wata kila kashemin 'ya zakayi..."
Ai da jin kalmar fyade tuni hankalin mutane ya 茩ara dawowa kansu nan fa aka shiga fafatawa tsakaninsu Antyn da Gwage ya nace akan shi bai ta蓳a 'yarta ba bai yi mata komai ba sharri kawai zatayi masa.
"Kaji tsoron Allah Gwage ka kuma tuna da mutuwa da ranar hisabi, gani nayi fa ka riko ta ka fito da ita daga shagonka sa蓳e a kafad'arka ko numfashi bata yi da na 茩ari so nake tambayarka abin da ya faru sai kawai ka miko min ita ka koma shagon gudun kar mutane su farga da kai, ai da ma tun ba yanzu ba na jima da lura yarinyar nan tana cikin wani yanayi a duk lokacin da zan ce tazo na aikota shagonka amma ban taba tunanin lalata mata rayuwa kake ba, ni dai kam ka gama cutar dani."
Ta 茩are maganar tana mai sake fashewa da kuka.
"Malama baki da wata hujja fa da zaki ce ni ne na yi ma 'yarki fyade..."
"Karya kakeyi wallahi kaine nan ai d'azu da na zo shagon nan siyan kati naji kuka amma ka raina min hankali kace ba komai ashe dai biri ya yi kama da mutum Teemah ce a ciki."
Shantyty ce ta katse shi da fa蓷in hakan cikin za茩al-茩alewa.
Wani yawu ya ha蓷iya ganin asirinsa na shirin tonuwa amma duk da hakan bai dandara ba sai cewa ya yi.
"Ke 茦anwar Manga kike ko wa? Aradun Allah ki kiyayeni kika zo siyan kati ko kuwa kar蓳ar bashi?."
Harara ta galla masa tana kama 茩ugu ta ce. "Oho dai ko ma mene ne asirinka ya tonu kai jama'a zaku tsaya kallo ne ba zaku dauki hukunci akan mai yi ma yaran mutane fyade ba? yau an kamashi ya yi ma Teemah, kuka sani ko ba ita ka蓷ai yake lalatawa ba? to bari na fa蓷a muku barin irinsu suna abin da suka ga dama shi ne ke Bama wasu kofa suma suyi domin sunga ba'a 蓷aukar abin da muhimmanci bare a dauki hukunci."
Ai da jin maganar Shantyty tamkar zaburar da mutanen Wurin ta yi musamman ma matasan nan fa suka shiga shagon dama an ce taron yawa yafi taron 茩arfi tuni suka cikumo Gwage Sukayi masa dukan Kawo wuka sai da Sukayi masa lilis sannan yan sanda guda uku suka 茩ari so da kyar ma suka damka shi hannunsu dan da cewa suke sai sun yanke abin nasa suka da abin da zai 茩ara yima wata yarinya fyade.
Shantyty tafi kowa za茩al-茩alewa dan lokacin da suke dukansu fadi take. "ku 茩ara masa bai daku ba kuyi masa lilis yadda gobe ba zai yi sha'awar kallon wata yarinya ba bare tunani mara kyau akanta yazo ransa, ku saki jiki ku jibgi 蓷an banza, ni nan 茦anwar Manga na tsaya muku ba wanda ya isa ya muku komai ai abin da hukuma ta kasayi ne kukeyi."
A lokacin sai ta duba Antyn dake tsaye rungume da 'yarta a kirji. "To zaki tsaya kallon dukan da ake masa ne ko zaki yi gaggawar kaita asibiti?"
Sai a lokacin ma wannan tunanin yazo ma Antyn da sauri kuwa Karime ta tare mata mai napep suka hau zuwa asibiti yayin da Shantyty bata sama sukuni ba sai da taga Gwage ya shiga hannun hukuma.
Ta ta蓳e baki ganin wani mugun kallon da yakeyi mata ta ce. "oho dai aje can a sake cin na jaki ai indai mutum ya ce ba zai nutsu ba kuwa jiki magayi."
Ganin 蓷aya daga cikin Yan sandan yana kokarin datse shagon Gwage 蓷in ne ya sa ta tafi ta sauri tana fa蓷in ya dakata. Ba tsoro ta shiga ciki ta jido biskit da madara har da siga da bonvita sannan ta fito ta duba Gwage dake zaune cikin motar yan sanda ta ce. "Duba ka gani da kyau can asibiti zan kai wurin yarinyar da ka lalata kuma ka ma shirya sai ka biya kudin jinya da komai sannan bashin katin da na ci bazan biya ba domin kuwa biyan bashi ga azzalumi irinka ai zunubi ne mai zaman kansa katin da ka bani ka 蓷auka kawai kayi sadakatul jariya wata kila sanadin hakan Ubangiji ya dubeka ya sa yarinyar da ka cutar zuwa gaba ta yafe maka."
Su dai Yan sanda da yake sun san hali ba wanda ya tanka mata sai ma dariya da ta basu ganin yadda take za茩al-茩alewa babu ko tsoro koda yake ai tana da wanda ya tsaya mata ne dole tayi abin da ta ga dama.
Takaici da ba茩in ciki game da 蓳acin rai basu bari Gwage ya iya dubanta ba ma bare ya bata amsa. Ita ko ta kada kai ta yi gaba kuma kai tsaye Asibitin da su Karime suka tafi ta wuce.
Koda ta je ta samu an shiga da yarinyar ana bata taimakon da ya dace kayan da ta kwasa ta basu daga nan ta dawo gida zuwa lokacin dab ake da kiran la'asar....,