Free chapter 路 Read without an account
FREE PAGE 32/33
馃槀 *ARADU KAMAR AN TOFE LITTAFIN NAN YAWANCIN FANS DIN SA OUT OF 100% , 80% MA SU SUNA AISHA NE馃槀 ABIN DA MAMAKI FA TAKWARORINA NE MASOYA, WANNAM FEJIN SADAUKARWA NE GAREKI NAMESY AYSHA SHU'AIB, TARE DA AYSHATUL-HUMAERA, DA KE MA AISHA馃ぃDA AYSHER馃ぃBAN MA SAN YANDA ZAN BANBANTAKU BA WALLE馃槀KAWAI DA MA DUK WATA MAI SUNA AISHA INA YIN KU IRIN SOSAI DINNAN馃グ馃グ*
**************** ************ ******************
馃槀馃槀 *NA LURA MASOYAN DOMPOL KON BA SA SO TA KOMA KAUYE, DAMAN GWADA KU NAI AI ZAMAN BIRNI YA ZAMA DOLE GA JIDDA, TUNATARWA DAI FREE PAGES NA DAF DA KAREWA DAN HAKA DUK WADDA TA SHIRYA SIYA TA MIN MAGANA*
Baba ya durkusa gaban Iya ya na, "Dan Allah ki yi hakuri ko me aka mi ki daga yau basa a kara ba,in sha Allah, ki ya fe ma na."
Iya ta ce, "To ban da fitsara da iskanci ga ta tsarkin yan tsafta za ta addabarmin diya wai sai tai kitso, ana dole ne? Na ga ita kan ta lokacin da ta aureka a yar gajarta ta ke, ga kai kaman hammatar yan iska, ai ko gwanda jiddan ma ta gajemu tai gashi sak kamar na yan indiya, shine ake bakin ciki ko, hnmm za asha mamaki fa agidannan."
Mama ta karaso" Hajiya Dan Allah ki yafemin na tuba, bazan kara ma ta magana akan komai ba."
Iya ta kada kai tare da fadin, "Yoo ina ma kika ganmu bare ki kara tursasata yin wani abun, na Fada ma Ku fa ba abin da zai hanani barin gidannan Yau."
Daga Mama har Baba ba su San sanda hawaye ya fara zubowa daga idanunsu ba, mussaman Baba da ya San Iyah za ta Iya rabuwa da kowa ma indai akan Jidda ne.
Janyota tai suka cigaba da tafiya ta na hama min masifa, KHALEEL da ya tsaya kallon ikon Allah ne ya yi saurin shan gabansu.
Shima durkusawa Ya yi kamar yadda Baba ya yi, "Hajiya Dan Allah ki yi hakuri, ba za akara takurawa Jidda ba, ai ni na za ta ma kitson kan na ta ya kai shekara ne ba a tsefe ba, da nasan sati biyu ne ma ko magana bazan yi ba."
KHALEEL na magana hanjin cikin Iyahtu na motsawa domin duk a tsorace ta ke gudun kar ya dauko bindiga ya ce zai harbeta cikin sauri ta ke fadin, "Yawwa Dan Albarka daman nasan da ka sani ai bazaka tabamin jikalle ba ko? To Yanzu dai ina bakazo da bindiga ba?"
KHALEEL ya fahimci tsoron bindiga karara afuskar Iyah hakan ya sa shi fadin, "Aa Amman na barta amota ko in dauko mi ki ne?"
Ta na ji ya ce ta na mota ta yi wata irin ajiyar zuciya da ya kai karshen maganar kuwa Wani irin zaro ido Iyah tai tare da fadin, "A'a A'a Dan Allah ka bar ta ni inna ganta ai suma zan, na yarda za mu koma Amman fa kama Mamanku magana in ta kara tabamin 'ya Wallahi sai taga baje kolin iskanci agidannan, in mu ka fita ba ma zamu koma kauyen ba duniya zamu shiga."
KHALEEL ya ce, "Ba ma za ayi hakan ba insha Allah."
Mika hannu ya yi zai karbi daurin kayan, Hajiya Iyah ta ce, "O'o bar ni inshiga da kayana."
Jan Jidda tai su ka koma ciki, ta na shiga ta ga Hajara zaune ban da danna wayarta ba abin da ta ke Iyah ta kalleta tare gyatsine baki, "To fa wannan mai zubin tabaryar daga ina?"
Jidda ta kyakyalle da dariya su ka shige dakin su .
Mama da Baba suna ta yiwa KHALEEL godiya domin sun San in ba dan KHALEEL ba yau ba Wanda ya isa ya hana Jidda da Iyah barin gidannan.
Murmushi kawai KHALEEL ya yi ya na, "Bara na je na kira Hajara mu tafi nasan ta gaji da jirana yanzu."
Suna shiga Mota Hajara ta fara banbamin masifa," in ban da wulakanci ka tafi ka bar ni zaune kamar ka Shanya wake?"
KHALEEL ya ce, "Am So Sorry Madam baki ga case din da ya tashi ba ne, yakamata in tsaya in gyara tunda har da ni aka bata."
Hajara ta ce, "ai shisshiginka ya ja ma, to ma wai wannan yarinyar daga ina? Ga shi ma na ga kaman kuna kama duk da dai ban wani tsaya kallonta ba."
KHALEEL ya ce, "Hmm kanwata Autar Mama."
Tsaki Hajara ta yi, "Ka ji da shi dai in ma Matar ka ce."
Dagowa KHALEEL ya yi ya kalleta, "Haba Hajara mai zan yi da kanwata kuma? Kanwar ma Jidda, Allah ya sawake Wallahi kin chuceni ma, ko da wata ce awaje banjin zan Iya kara mi ki kishiya bare wannan yar shilar me nasama ya ci bare ya ba na kasa."
Dariya Hajara ta yi, "Yoo waya sani Abu aduhu Ai sa an laluba akan San na kwarai,hhhhhh ni ko ma zan so ace an baka wannan yar shilar ko na huta."
KHALEEL ya ba ta rai, "Stop it, Sweety ba na son irin wannan wasan kin fi kowa sani tam."
Duk kasancewar KHALEEL ya san wasa Hajara ta ke Amman ran shi ya matukar baci tun da ta dangan ta shi da Jidda kuma ma amatsayin ma ta, tsanar Jidda ne karara ya shiga ran shi, jima ya ke kwata-kwata ba ya son kara ganinta domin ya tsani yarinyar maganar ta ma inda hali bai son akara a inda ya ke.
1wk ltr
Jidda zaune afalo ban da tsalle-tsalle ba abin da ta ke yi, Hamza ne ya shigo da Sallamarsa da gudu ta je ta rungumesa , "Oyo yo Yayana."
Mamaki Hamza ya yi ganin Jidda agidan na su.
"Ah Jidda yaushe Ku ka zo?"cewar Hamza.
Jidda ta ce, " Tab ai mun jima tun kwanaki fa har ma Baba ya sani makaranta, Yawwa Yaya Hamza ka dawo Dan Allah za ka goyani?
Hamza ya rikye baki, "Kin gan ki Yanzu ai kin zama katuwa inna goyaki Mama za ta yi Fada, kin ga ma fa yunwa na ke ji, ya na ji gidan shiru, ina Anty Mariya da Mama?"
Jidda ta ce, "Anty Mariya ta je rabon ankon bikinta kuma ta ki tafiya da ni, Mama da Kaka kuma kowa ya na dakinsa."
Hamza ya ce, "Owk shikenan Yanzu dai bara na Je nai wanka na yi alwala, inna yi sallah ma gaisa."
Hamza na shiga daki Uncle ne ya shigo da sallamarshi, ko kallonsa Jidda ba ta yi ba, domin ta tsani mutum nan haka kawai batare da tasan dalili ba.
Ya ce, "Jidda ina Mariya."
Murguda ma shi baki ta yi, "Ta tafi anguwa nima ban sani ba ma."
Kallonta ya yi kawai ya cizan bakin sa ya wuce daki.
Kwanan KHALEEL wajen bakwai bai leka ko gidan Su Mama ba, sai da ta kirashi awaya ta ji lafiya kan ya yanke shawarar zuwa, Amman azuciyarsa ba abin da ya ke Addu'a illa Allah ya sa kar ya hadu da Jidda domin Dan ita ya kauracewa gidan ko kadan ba ya son ganinta ga yanayinta ya ki ficewa daga idanunsa ko ya yarufe ita kawai ya ke hange.
Ita kuwa Hajara ta sami abin yi, ta na ganin sa zata fara angon Jidda ikon Allah, ma su kitso duk bayan wata guda.
Kamar kullum dai yau ma shigarshi ya yi cikin Kanikinsa na yan sanda, ya yi matukar kyau ban da tashin kamshi ba abin da ya ke.
Hajara ta kalle shi tare da fadin, "Ango agaida Amarya Dan nasan wannan wankan sai Jidda ikon Allah."
Ko kallonta bai yi ba sai tsaki da ya jefar ma ta ya fice.
Driving ya ke ahankali kamar Wanda bai son Zuwa in da za shi bare ma amsar hakane ba son zuwa ya ke ba.
A haka har ya isa dai-dai get din gidan hamdala ya yi azuciyarsa da Allah bai sa ya fara karo da Jidda ba, bude ma sa mai gadi ya yi sannan ya je ya yi parking awajen da aka tadana domin yi.
Fitowar da zai yi ko ba wadda ya fara tozali da ita illa Jidda, tsaye ta yi daga daga da kwakwar manja daga bakinta har hannunta.
Kallonshi ta yi ta na washe baki, ya yi kokari domin kawar da kan shi, a zuciyar sa kuwa ya na fadin, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Wucewa ta zo yi gaban shi ta, taka mi shi kafa, zafin zuciya nan ta ke ya wasketa da mari, ita ko Jidda kyankyame shi ta yi, ta shafe shi da manjan da ke hannunta duk uniform din ya baci.
Bai Ankara ba kawai sai ga ni ya yi ta zura aguje ta na mai gwalo kallon jikinsa ya yi kan ya lura da abin da ta mai, shima bin ta ya yi aguje tamkar yaran da ke wasan kasa.
Urs Xayyeesherth [11/27, 10:25 AM] Xayyeesherthul-humaerath馃グ: 掳掳掳掳掳掳 _*MATAR POLICE*_ 掳掳掳掳掳掳
27November 2020
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*馃
__________________________________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._ __________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_ 1- _BABU RUWAN SO_ 2- _KUCHAKAR KISHIYA_ 3- _WASA DA SO_ 4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_ 5- _JAMEEL (Nafseen)_ 6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER *** SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_