FreeArewaPen original
MATAR POLICE
- 1views
- 43chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
NobleWriter
Sample · FREE PAGE 1/2
**************** ************ ******************Wata yarinya na Hango yar kimanin shekara Tara ta na ta kokarin danewa bishiyar mangoro.Wa su yara sa'anninta da ke kasan ta ne daya daga cikin su ke fadin, "Ke Jidda ki yi sauri fa kar Mallam Mudi ya zo , ya ganmu."Tsayawa ta yi da hayewa bishiyar ta joyo ta kalleta, ta galla ma ta harara kan ta ce, "Yoo ya zo ma na, ai bishiya ta kowace ba wai Dan ya ganta cikin gonarshi ba, ke Wallahi ma inna so sai na fito cikin dare na sassare bishiyar nan."Tsaki ta yi ta Dane saman bishiyar abinta, mangoro ta fara tsinkowa ta na mika mu su banda masifa ba abin da ta ke yi, wallahi in kuka barmin mangoro daya ya fada kasa na ga kwarzane ko dayane hum hun yara za su yi kuka Yasin."Ta na cikin masifar nan sai ga Mallam Mudi ya nufosu ya na yar wakarshi.Jidda ce ta fara lura da zuwan shi hakan ya Sa ta saurin fadin, "Lantana, Indo, Ku kai min mangorona wajen IYA ga Mallam Mudi nan."Ai kuwa gudu su ka fara me naci ban ba ka ba, Mallam Mudi kuwa daga idon da zai yi Sai ga Jidda rashe-rashe a kan bishiyar shi.Dirka tai da gudu garin binta ya fadi juyowa ta yi ta ma Sa gwalo ta ce, "Hhhh indai ni mutum zai bi ai Sai dai ya karye." Ta na dariya ta cigaba da gudunta har ta shige gida.Ta na shiga , "IYATAAAA ina ki ke? Ina su Lantana da Indo kar dai ba su kawomin mangorona ba."IYA ta fito ta na, "Oh Ni Kulu banga kowa ba agidannan tin da ki ka fita."Kama kugu Jidda tai ta ce, "Kambu.... To Wallahi yau da masifa akarkarar nan da alama sun manta halinane ko, na fi su iya shege, ni da wahala su da ci tab-di-jan yau sun taro bala'i."Fita kawai ta yi fuuu kamar wani jirgi ai ko ta na bin bayan layi Sai ga Su Shatu da Lantana, kallon su tsaya yi ta na girgiza kugu , "Ai na aza kunci gadone in malafar gidanku aradu."Indo ta ce, "Aa fa mun bi ta nan ne sabode kar Malam Mudi ya kama mu."Tsaki ta yi ta ce, "Naji to kuzo mu koma gida."A girme ba su girmeta ba, ajiki kam Lantana da Indo sunyi biyun Jidda Amman hakan ba ya sa Jidda jin tsoron tabasu ko yi ma su masifa inta kamama har mari ta ke ma su ,gashi bala'in tsoronta su ke, kamar mala'ikarsu.Suna shiga gida IYA ta ce, "To 'Ya'yan albarka mangoro a ka samo kenan."Harara Jidda ta galla ma ta, ta ce, "Yasin gwandama ki kama chakon bakin nan na ki Dan ba sha zakiyi ba."IYA ta bude baki za ta yi magana kenan Sai gashi an bankado kofar galan-galan kamar za ta fice, Mallam Mudi ne tsaye ya na huci, ya ce, "Wallahi Sai kun ba ni mangorona da kuka Sa ta."Jidda ta kalli shi ta ce, "Jan... Cha.... Suwaye bara yin da zasu ma Satan ma to? IYA Wallahi ki ma Sa magana ya fitan ma na agida."IYA ta daura hannun aka ta na fadin, "Oh ni kuluwa jikar Adam ni ban San me yar jikata ta tare ma Ku ba a garin nan kowa ya tsaneta daga Wannan ya ce ta yi kaza sai kaza...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.