Free chapter · Read without an account
Chapter 27
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
SAUTIN ƘARSHE
BY AMANARCOOL
YOTA/021
Under Yota's Amazing Pens
Book 1
Page 27
"Yana ji kin yi shiru? Ko ba ki gane ni ba ne in haska miki fuskata ki gani? Ko da yake ba sai kinga fuskata ba, na zo in sanar miki da ki kular mini da babyna da kyau, kuma ba na son wannan yawan kukan da kike yi. Duk da ba ganinki nake yi ba amma na san kina yinsa, ki dinga cin abinci sosai, kuma ki san irin abin da za ki ci, saboda ina son cikin nan nawa sosai. Ba na son in rasa shi." Daga haka ya miƙe tsaye tare da faɗin "Na bar ki lafiya."
Girgiza kai ta dinga yi tana faɗin "Wai waye kai ne? Ni ban gane ka ba, ka tsaya ka yi mini bayanin ta yadda aka yi wannan cikin ya zo jikina." Ta kai ƙarshen maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Da sauri Inna ta tashi a firgice tana laluben fitlarta ta haske Ma'u da ita tana faɗin "Subhanallah! Ke lafiya dai? Me ya same ki?" Ta yi maganar tana isa bakin gadon da take kwance idanunta a rufe tana rizgar kuka. "Ke Ma'u ki yi mini magana ko ba ki da lafiya ne?" A hankali ta fuɗe idanunta tana bin Inna da kallo, Inna ta sake tambayarta, shiru ta yi tana son ta tantance shin mafarki ta yi ne ko kuma a zahiri ne abin ya faru, amma sam ta kasa tantancewa, kawai sai ta barwa ranta cewar mafarki ne ta yi. Duk da zuciyarza na kokwanto a kan haka. "Wai ba tambayarki nake yi ba Ma'u? Ko in rabu da ke ne in yi kwanciyata?"
Murya a sanyaye ta ce "Na yi mafarki ne"
"To shi ne za ki tashi kina yi wa mutane ihu? Maimakon ki tashi da ambaton sunan Allah a bakinki, tukuna ma waye na ji kina faɗin ya tsaya ya yi miki bayani?" Shiru ta yi ta fara rarraba ido. "Ba magana nake yi miki ba!?" Inna ta daka mata tsawa. "Wani ne ya zo inda nake yana ce mini shi ne uban cikin da yake jikina, wai in kular masa da shi." Ƙwalalo ido waje Inna ta yi, ta ce "Mun shiga uku, kar dai gamo kika yi? Anya Ma'u wannan abin na ki baya rasa nasaba da aljanu kuwa? Domin abin akwai ɗaure kai wallahi." Ita dai Ma'u shiru ta yi ba ta ce komai ba.
Inna ta ce "Ki yi addu'a ki kwanta, idan Allah ya kai mana rai gobe zan yi magana da Gadanga sai mu san abin da ya kamata mu yi, domin kuwa wannan al'amarin kamar akwai mutane ɓoye a cikinsa." Rufe idanunta ta yi, Inna ta koma ta kwanta, sai dai daga ita har Innan babu wanda ya iya komawa bacci, kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa.
Aliyu ma yana waje sai sintiri yake yi. Saboda yana jin kukan Ma'u yayo ɓuzut ya fito, sai dai takaici ya hana shi shiga ɗakin ya ji me take yi wa kuka. Sai da ya ji sun koma kwanciya ne sannan shi ma ya koma ɗakinsa.
....
"Malam don Allah ka yi haƙuri ka daina damuwar nan haka. Duk da na san dole ne ka damu amma ina son ka yi haƙuri, ka bar wa Allah komai, Mustafa dai lokacinsa ya riga ya yi, sai dai mu yi masa addu'a tare da fatan Allah ya ji ƙan sa." Malam ya ɗago da idanunsa da suka canza launi ya dubi Rabi, girgiza kai ya yi ya ce "Rabi ba zan taɓa iya daina damuwa a kan mutuwar Mustafa ba, ba zan iya ba, yaron nan bai ji ba, bai gani ba, rayuwarsa ta salwanta a banza. Kai Allah ya isa, wallahi matuƙar ina numfashi a duniya sai na ɗauki fansa ga duk wani wanda yake da sa hannu a kan mutuwar ɗan'uwana, mutanen banza azzaluman, matsafa kawai. Ni nafi ƙarfin ku wallahi."
Sakin baki Rabi ta yi tana kallonsa, saboda gaba ɗaya ta kasa gane inda maganarsa ta dosa, tunani take yi ko dai ya san waɗanda suka lashe Mustafa ne, da kuma dalilin da ya sa suka lashe shi. "Malam wai me kake nufi da waɗannan kalaman na ka? Na kasa fahimtarsu." Ko kallonta bai yi ba, ya tashi ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan.
....
Washe gari Aliyu ya zo gaishe da Inna, bayan sun gaisa ne. Cikin ɗari-ɗari Ma'u ta gaishe shi, ba ta yi zaton zai amsa ba, amma sai ta ji ya amsa ɗin.
Inna ta dube shi da kyau ta ce "Gadanga magana nake so mu yi da kai ta fahimta, dangane da matsalar nan ta Ma'u, ina zargin kamar akwai aikin mutanen ɓoye a ciki, saboda jiya cikin dare ta tashi tana ihun kuka, da na tambaye me ya same ta? Sai ta ce mini wani ne ya zo ya ce mata shi ne uban cikin da yake jikinta. Shi ya sa nake zargin ko aikin su ne, domin abin akwai mamaki da ruɗani a cikinsa."
Satar kallon Ma'u ya yi, sannan ya kalli Inna ya ce "To yanzu me ya kamata a yi?"
Inna ta ce "Yawwa, so nake mu je da ita gurin Malamin addini, sai ya duba mana ita, idan ma ruƙiyya zai yi mata ko wani abin, ni dai fatana a raba ta da wannan abin da suka saka mata a jiki ko hankalina zai kwanta, wallahi kullum a cikin damuwa nake da tashin hankalin idan jama'a suka san da wannan abin. Tun da har an fara surutu a kan rashin fitar da ba ta yi."
Aliyu ya ce "To shikenan, sai ku shirya zuwa anjima mu je gurin wani malami, idan ma su ne kallo ɗaya zai yi mata ya gane, saboda ya ƙware ta wannan fannin." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "To ya yi, Allah ya shige mana gaba." Ya amsa da "Amin" kafin ya fice daga ɗakin.
.....
Sudais na kwance saman 3seater, idanunsa a rufe, murmushi ya yi kaɗan tare da buɗe idonsa, ya kalli screen ɗin wayarsa ya ga tara saura. Tashi ya yi cikin natsuwa ya shirya ya fito.
Mammy na zaune a danning ita da su Faruk ya ƙaraso gurin, ya gaishe da Mammy yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta amsa cikin jin daɗin ganinsa da ta yi yau yana walwala. Faruk da Zahra suka gaishe shi nan ma ya amsa musu yana murmushi. Mammy ta ce "Ma sha Allah, gaskiya yau na ji daɗin ganinka haka, rabon da in ga kana murmushi tun kafin rasuwar Ilham." Ta yi maganar fuskarta na bayyana damuwa daga ƙarshe. Jan kujera ya yi ya zauna ba tare da ya ce komai ba. Mammy da kanta ta zuba masa abinci, bayan ya kammala ci ne ya kalli Faruk ya ce "Faruku tashi mu je, yau tare da kai za mu tafi."
Faruk ya yi murmushi ya ce "To babban Yaya" tashi suka yi tare da yi wa Mammy sallama. Addu'a ta yi musu sosai, Faruk ya ce "Mammy yau sakwara nake son ci." Ta ce "To shikenan kar ka damu Shalelen Mammy za ki ci har sai ka ture." "Amma fa sai dare sosai zan dawo, saboda daga gurin aiki ina son in je gurin wani partyn abokina da za a y..." Bai ƙarasa maganar ba Sudais ya ce "Ba za ka je ba, ka san ba na son yawon dare ko?" Faruk ya ce "To shikenan babban Yaya na haƙura da tafiyar."
Zahra kuwa kallon Sudais take yi tana mamakin ƙarfin hali irin na sa. Wai ba ya son tafiyar dare. Tari ta yi ta buɗe baki za ta yi magana kenan. Sudais ya wurga mata wani mugun kallo, ai babu shiri ta duƙar da kanta ƙasa tana murmushi. Suna fita Mammy ta dubi Zahra ta ce "Zahrata me kika so faɗa Yayanki ya hana ki?"
Zahra tana dariya ta ce "Mammy rufa mini asiri, ai Yaya yadda kika san aljani haka yake, ina faɗa miki sai ya san na faɗa, gara dai na yi shiru da bakina. Hmmm su Yaya manya, wato baya so a na yawon dare" ta yi maganar tana dariya, Mammy ta share ta ta ce gaba da sabgogenta.
....
Aliyu ya si Inna ta yi zamanta a gida, amma fafur ta ƙi, ta nuna ita ta fi son a yi komai a gabanta, ba yadda ya iya dole ya haƙura suka ta fi tare.
Zaune suke a gaban Malamin, bayan Inna ta gama yi masa bayanin komai, ya ɗaga kansa ya ƙare wa Ma'u kallo, murmushi ya yi tare da girgiza kai ya ce "Tana tare da mutanen ɓoye a jikinta, sai dai kuma ba masu cutar da ita ba ne, asali ma suna ba ta kare ta ɓangarori da da ma, don haka wannan matsalar ta ta kwata-kwata ba ta da alaƙa da aljanu, ko wani abu makamancin haka. Akwai dai yadda al'amarin yake, ko dai ta haɗu da shu'umin mutum ne, ko kuma dai akwai yadda a ka yi. Amma wannan ba aikin aljanu ba ne."
Tun da ya fara bayani daga Inna har Aliyu babu wanda gabansa bai tsananta bugawa ba, Ma'u kuwa da ma ta san hakan ce za ta faru, saboda a jikinta take jin babu wasu aljanu da suka yi mata haka, kawai dai ta yi musu shiru. Bayan ya gama yi musu bayani ne suka yi masa sallama jiki a sanyaye suka koma gida.
....
Wata pravit hospital ce da a ka tsara ta cikin tsari mai kyau da ɗaukar hankali.
Sudais ne zaune a gaban Dr ya tsare shi da ido yana sauraren ya ji me zai fito daga bakinsa.
Dr ya cire gilas ɗin fuskarsa tare da buɗe file ɗin da ke gabansa ya fara yi masa bayani "Sudais, na kammala binciken da duk ya kama na yi a kan maganin da ka kawo mini, na yi amfani da Toxicology Screening da Chemical Analysis a cikin lab ɗinmu, sakamakon ya tabbatar da abin da likitocin waccan asibitin suka faɗa gaskiya ne. Wannan maganin sunansa na kimiyya shi ne Nephrotoxin-X, ba magani ne da ke cutarwa ba, aikinsa idan a ka sha shi kai tsaye yake tasiri ga ƙodar mutum. Ƙoda na da amfani ne a jikin mutum wajen tsaftace jini. Sai dai wannan maganin yana ɗauke da sinadaran da ke lalata nephrons, wato ƙananan filters ɗin da ke cikin ƙoda, bayan ya fara tasiri a jiki mutum sai ya toshe su. Da zarar ya toshe su jini ba zai taɓa zama tsaftatace ba. Toxin zai fara taruwa a jiki, zuciya, hanta, ƙwaƙwalwa, duka za su fara lalacewa, a ko wane lokaci mutuwa za ta iya zuwar ma mutum saboda kidney failure da multiple organ failure. Alamomin suna fara bayyana ne bayan kwana biyar zuwa sati ɗaya da fara amfani da maganin da yake ɗauke da wannan sinadaran, kamar su gajiya, kumburin ƙafa, tashin zuciya, lokacin ɗaya za a iya jin mutuwar mutum kwatsam. Irin wannan maganin da yake ɗauke da sinadaran nan, ba ya cikin tsarin maganin da ake amfani da shi Sudais, baya cikin jerin magungunan da NAFDAC ko WHO ta amince da su, wannan na cikin nau'in magungunan da wasu asibitoci marasa kishin ƙasa suke amfani da su da sunan taimako ko kuma mai sauƙin farashi, amma a zahiri guba ce. Da zarar an yi amfani da shi sau biyu ko uku ƙoda za ta fara fara samun matsalar da ba za ta dawo daidai ba. Kuma babu wani maganin da zai iya kawar da illarsa da zarar ya fara tasiri a jikin ɗan Adam. Abin da za a iya yi kawai shi ne dialysis. Duk da haka ba ya yi ɗari bisa ɗari." Ya kai ƙarshen maganar yana tura file ɗin gaban Sudais ya ce "Dukkan sakamakon binciken da mu ka yi yana cikin file ɗin ga shi nan. Hoton chemical structure, da rahoton lab. Saboda haka duk wanda yake sayar da wannan maganin bai yi haka cikin kuskure ko rashin sani ba. A na sayar da shi ne da gangan. Duk Asibitin da ya ba wa mutum maganin nan ya san illarsa da kuma abin da zai iya biyo wa baya."
Jinjina kai Sudais ya yi, tare da yi masa godiya sosai, ya tashi zai bar office ɗin Dr ya ce "Amma Sudais a ina ka samu wannan maganin? Kuma wace Asibiti ce a ka fara sanar maka da illarsa?" Sudais ya yi murmushi mai ciwo ya ce "Dr ba a ƙasar nan na same shi ba."
Dr ya ce "Ko da na ji, domin ba za a taɓa sai da irin wannan gurɓataccen magani a nan ba." Sudais ya ce "Haka ne" daga haka ya buɗe ƙofar ya fita, ransa a matuƙar ɓace.
Mun kusa kammala book 1, book 2 na kuɗi ne, ga mai buƙatar ci gaba da bibiyar wannan littafin zai iya tura 1k ɗinsa, 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya.
Amanarcool
***