Free chapter · Read without an account
Chapter 28
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
SAUTIN ƘARSHE
BY AMANARCOOL
YOTA/021
Under Yota's Amazing Pens
Book 1
Page 28
Bayan tafiyarsu su Sudais ba da jimawa ba sai ga Hajiya Kaka ta dira a gidan, sosai Mammy ta yi farin ciki da ganinta saboda rabonta da gidan an daɗe, ta rasa inda za ta saka ranta saboda jin daɗi zuwanta, bayan ta ci abinci, ta huta. Mammy ta dube ta cikin damuwa ta ce "Hajiya Kaka kin daina sona yanzu, yaushe rabon ki da gidan nan kin fi shekara biyu fa."
Harararta Hajiya Kaka ta yi ta ce "Rufe mini baki, yanzun ma ba saboda ke na zo ba, na zo ne in yi wa yarona ta'aziyar rashin matarsa da ya yi. Duk da ba ki sanar da ni ba ai ita uwar ta ki da ta san darajata ta gaya mini." Ya mutsa fuska ta yi ta ce "Haba Kakus, ni ce ban san darajarki ba? Kar ki manta a hannunki fa na taso, taya za ki ce ban san darajarki ba bayan ke kika riƙe ni har zuwa lokacin da na isa aure?." "Rufe mini baki, ai ni yanzu babu wani daɗin bakin da za ki yi mini, yaushe rabonki da zuwa inda nake? A ƙalla kin kusa shekara ba ki je kin duba ni ba saboda ina zaune a ƙauye, hadda fushin da nake yi da ke a kan rashin shiga cikin yan'uwanki na can da ba kya yi sam bai dame ki ba."
Mammy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Kakus ba haka ba ne, ni narasa ma me zance ki fahimce ni, yanzu dai ki yi haƙuri kin ji Kakata, farin cikin Indo A'isha." Ta ƙarasa maganar tana murmushi.
"Ke ina yayunki yaran kirki?" Hajiya Kaka ta tambayi Zahra dake zaune tana kallonsu tana murmushi
Zahra ta ce "Suna wurin aiki, ai ba su daɗe da fita ba kika zo."
Ta ce "Allah Sarki, ashe kuma raguwa kuka samu? Sannu Zara'u Allah ya ji ƙan ta da rahama ya sa ta huta, ina batun in zo ganin amarya sai kawai wacce yarinyar ta sanar da ni abin da yake faruwa, hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba." Fuskar Zahra ɗauke da damuwa ta amsa mata gaisuwar.
Mammy ta ce "Wai Hajiya ni ba za ki yi mini sannu ba ne?"
"Ba zan yi miki ba, tun da ba ki son zumunci." "A'a ba fa haka ba ne" cewar Mammy tana faɗa fuska.
Hajiya ta ce "To yaya ne? Gaba ɗaya danginki na ƙauye ba ki son zuwa inda suka, sai ki ɗauki shekaru ba ki je ba, balle kuma har ki saka yaranki su je, to ki sani dai duk ƙin ki da garin a can kika tashi, kuma uwar ta ki ma a can ta tashi, auren mahaifinki ne da ta yi shi da yake ɗan birni ne shi ne ya zo da ita nan har ta haife ku a nan." Mammy ta yi dariya ta ce "To wai Kaka duk me ya kawo wannan maganar? Na ce wani abu ne? Ni Allah ne ya ƙaddari zan tashi a can, da ga kai miki ni yaye kika riƙe ni a can, kika hana wa iyayena ni."
"Ai kuma da na riƙe gata na yi miki a can, don na yi miki rainon da ko iyayenki ba za su iya yi miki shi ba" Mammy ta ce "To na ji a bar zancen haka nan, Kaka wai ina labarin ƙawata Hajara ne? Allah Sarki Hajarata, wallahi tana raina har yanzu na kasa mantawa da ita. Duk wata ƙawa da zan yi a duniyar nan bayan Hajara take, ina kewarta sosai da sosai, rabona da ita tun da aka yi mata aure muka je kai ta wannan ƙauyen, me ye ma sunansa? Yawwa Ƙauyen Gwagwa ban sake saka ta a idona ba, sai da ta yi haihuwar fari aka dawo da ita gida, a lokacin ana shirye-shiryen aurena na je na yi mata barka tun da ga ranar ban sake ganinta ba, amma wallahi tana raina fiye da tunaninki Kaka."
Tsare ta da ido Hajiya Kaka ta yi ta ce "Hmmm, A'isha kenan, babu abin da za ki ce mini in yarda, ai Hajara ita ce ke ƙaunarki har yanzu, amma ke kin manta da ita, har gobe idan ta je gida sai ta zo ta gaishe da ni, ta kawo mini alkhairi tare da tambayar kina lafiya? Wani zuwa da ta yi na ce ta bari in ba ta lambarki ta ce a'a ba sai ta karɓa tana dai gaishe ki." Cikin damuwa Mammy ta ce "Allah Sarki Hajara, fushi take yi da ni kenan shi ya sa ta ƙi karɓar lambata, ita a tunaninta na manta da ita kenan? In sha Allah zan samu lokaci in je har in da take aure, domin in nuna mata har yanzu tana nan cikin zuciyata kuma ban manta da ita ba, kawai dai aure ne ya raba mu da kuma nisan da muka yi da juna." Kwaɓe baki Hajiya Kaka ta yi ta ce "Mun ji, saura kuma mu shaida, ai ma yanzu ba a ƙauyen suke da zama ba, ita ma daga baya mijinta ya ɗauke ta suka koma birni."
"Au haba dai? Yanzu kina nufin Hajara sun bar wannan ƙauyen?"
Hajiya Kaka ta ce "Eh, sun bar shi da daɗewa, ai ma mijin nata ya rasu amma har yanzu tana can birnin take da zama ita da yaranta, lokacin daya rasu ma an yi tunanin za ta dawo gida da zama, to da yake kin san idan ka saba da rayuwar birnin nan ba son zama ƙauye kake yi ba."
Mammy ta ce "Allah Sarki! To amma Kaka wane gari ne suka koma da zama?" Cikin ƙosawa ta ce "Ni kamar wani zuwa da ta yi gaishe na tambaye ta ina ne suke da zama ta ce mini Habuja." Zaro ido ta yi ta ce "Wai kina nufin harin nan ne suka dawo da zama?"
"To ni dai Habuja ko Abuja ne haka dai ta ce, don Allah A'isha na gaji da wannan surutun ki bari in huta mana, ke ba ki tausaya wa tsufana, shekaru 85 ai ba wasa ba, don ma Allah ya bamu jiki mai kyau ne."
Mammy ta marairaice fuska ta ce "Don Allah Kaka ko ta sanar dake a wace unguwa suke?"
"To wai ke Shatu ina zan sani? Ni ba ta sanar da ni ba." "To amma Ka.."
"Kin ga bacci nake ji, ki bari sai na tashi kya ci gaba da tambayar ta ki, tun da ƴar jarida kika zama." Daga haka ta tashi a hankali take tafiya har ta shiga ɗakin da aka sauke ta ta kwanta."
Shiru Mammy ta yi tana mamakin yadda aka yi Hajara na cikin garin nan amma ba ta taɓa sani ba, to me ya sa Kaka ba ta sanar da ita ba? Ko dai don ita ba ta tambaye ta Hajaran ba ne ya sa ita ma ta yi mata shiru? Haka dai ta ce gaba da saƙe-saƙe a ranta.
......
Sudais ransa a matuƙar ɓace ya dawo office ɗinsa ya zauna, lumshe idanunsa ya yi yana jin kansa na sara masa kamar zai rabe masa gida biyu. Ya buɗe idanunsa a hankali ya sauke su a kan sakamakon binciken da aka bashi a Asibitin, iskar ya furzar mai zafi, ya jinjina kansa yana ci gaba da nazari a kan wannan al'amarin, wayarsa ce ta fara ringin ko da ya duba Zuhura ce, tsaki ya yi har ya share ta sai kuma wata zuciyar ta umarce shi daya ɗaga ya ji me za ta ce, ɗauka ya yi ba tare da ya yi magana ba ya kara a kunnensa, jin an ɗauka ya sa Zuhura ta ce "Hello Habibi, ya kake? Ya ƙarin haƙuri? Allah ya sa ta huta, ya ba mu haƙurin rashinta." Ya amsa da "Amin" shiru ta yi tana son yi masa hira kuma tana tunanin me za ta ce masa. "Ya kika yi shiru?" Ta ji ya faɗa.
Zuhura ta ce "Babu komai, kawai na kira ka ne in yi maka ya ƙarin haƙuri, sannan kuma in ji muryarka." Sudais ya ce "Ok, to ya kike? Ya gurin aikin naku ina fatan dai babu wata matsala ko?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Habibi gurin aikin nan namu sai a hankali, wasu abubuwa nake gani da na kasa gane kansu, ka san kwana ki na yi maka bayanin game da abin da nake gani, to yanzu abubuwan rashin gaskiya naje gani muraran a gurin manya Drs ɗin nan, ina son in sanar da Abbi amma ina tsoron kar ya ce me ye hujjata na faɗar haka, amma wallahi Habibi ina zargin akwai wani abu da suke aikatawa na rashin gaskiya, ba zan manta wani abu da na ga an yi wa wasu bayin Allah ba kwanaki, abin ya yi matuƙar ba ni mamaki."
Sudais ya gyara zamansa ya ce "Ikon Allah, me kika gani? Zuhura ba na son sharri, wataƙila ma aikinsu suke yi amma kin zo ki na wani zancen." Cikin damuwa ta ce "Wallahi Habibi babu zancen sharri a cikin lamarin nan, da idona na ga komai, abin ya ɗaure mini kai, yarinyar ba ta daɗe da kwanciya a Asibitin ba sai ga shi an dawo da ita rai a hannun Allah."
"Zuhura ki daina irin haka babu kyau, ni ba zan taɓa yarda ba har sai na ga shaidar abin da kika faɗa, idan na ga shaida wataƙila in yarda."
Zuhura ta ce "Ai kuwa sai na tabbatar maka da ba sharri nake yi musu ba, irin wannan abin nake gudu shi ya sa na kasa sanar da Abbi abin da nake zargi." Numfashi ya sauki, kafin ya ce "Kina jina ko Zuhura, don Allah na roƙe ki kar ki sabar da shi wannan zancen, saboda za ki ɗaga masa hankali ne, ba shi ba da kowa ma kar ki yi zancen, ki bar shi iya ni da ke kawai, sannan ko Abbi kar ki taɓa nuna masa kina yin zancen abin da ya shafi Asibitin nan da ni."
Ta ce "To shikenan masoyi in sha Allah ba zan sanar da shi ba, zan bari ne ya gano komai da kansa, amma tabbas sai na tabbatar maka da abin da nake faɗa gaskiya ne." Sudais ya yi shiru yana sauraren ta, sai da ta gama sannan ya yi mata sallama tare da kashe wayarsa.
.....
Tun da suka dawo da ga gurin Malamin nan wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe ta, Inna ta ƙarasa girki ta zo ta tashe domin ta lallaɓa ta samu ta ci ko kaɗan ne, amma ta kasa tashi balle ta kalli in da abincin yake, tana nan kwance aka kira sallar azahar, da ƙyar ta tashi ta yi sallah, tana nan zaune sai ga Jamila ta zo duba ta, duk da cikin ɗari-ɗari ta shigo gidan saboda kunyar da take ji ta Inna, bayan sun gaisa ne da Inna ta kawo mata abincin da ta zubawa Ma'u ba ta ci ba, tana ajiye abincin ta fita ta bar musu ɗakin, Jamila tun da ta zauna take bin Ma'u da kallo ganin yadda gaba ɗaya ta canza, sannan abin da ya fi ba ta mamaki bai wuce yadda ta ga cikinta ya yi tudu kaɗan ba, tun da ƙamshin abincin nan ya daki hancinta ta ji wani irin amai ya taso mata, ai babu shiri ta tashi a guje za ta bar ɗakin, sai dai tana kai bakin ƙofar aman ya zo mata, nan ta fara kwarara shi tun tana iya yunƙuri har ta zo ta kasa motsin kirki. Da sauri Jamila ta ƙaraso inda take tana faɗin "Subhanallah! Sannu Ma'u, jikin ne dai?" Ta yi maganar tana miƙar da ita tsaye, ganin yadda aman ya ɓata mata jiki ya sa ta taimaka mata ta gyara jikinta, ba tare da ƙyamar komai ba Jamila ta gyara gurin, Inna na ganinsu baƙin ciki ya hana ta yin magana, bayan ta gama gyara gurin ne ta koma cikin ɗakin, Ma'u ta dube ta ce "Jamila don Allah ki fitar da wannan abincin ko ganinsa ba na son yi." Kallon abincin ta yi ta kalli Ma'u, ba ta ce ƙala ba ta ɗauke abinci daga kusa da ita, duban ta ta yi da kyau ta ce "Ma'u tashi mu yi magana"
Da ƙyar ta yunƙura ta tashi zaune, cikin damuwa ta ce "Ma'u me yake damunki ne? Don girman Allah ki gaya mini gaskiya kar ki ɓoye mini komai, ki tuna ni da ke babu mai ɓoye wa ɗan'uwansa abin da yake damunsa." Cikin kuka Ma'u ta ce "Jamila ko ban faɗa miki abin da yake damuna ba na san da ga baya za ki sani, Jamila ciki ne da ni!" Ta faɗi maganar tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta.
Kamar mutun mutumi haka Jamila ta dasƙare a gurin tana bin ta da kallo, lokaci ɗaya hawaye suka fara zuba daga saman fuskarta, "Ciki fa kika ce Ma'u? Garin yaya hakan ta faru!"
Cikin takaici ta ce "Ban sani ba Jamila, ina tunanin kin fi kowa sanin halina, kin san ba zan taɓa aikata abin da bai dace ba kamar wannan."
"Na sani Ma'u, amma ya aka yi ciki ya bayyana a jikinki bayan ina da tabbacin ba za ki taɓa aikata zina ba, don Allah ki yi mini bayani kin sa ka ni a ruɗani, ko dai abin da ya faru dake watanni baya mutanen nan sun yi miki wani abu ne?." Jamila ta yi maganar tana tsare ta da ido.
Girgiza kai ta yi ta ce "Babu abin da suka yi mini, ban yadda aka yi cikin nan ya same ni ba, ban sani ba, ni ma haka kawai na gan shi a jikina."
Cikin mamaki Jamila ta ce "To ko dai ana yi ciki haka kawai ba tare da wani abu ya shiga tsakaninka da namiji ba? Ko kuma aljanu ne suka hora miki ciki Ma'u?"
"Ni ma ban sani ba, amma ɗazu mun je gurin wani Malami ya ce ba aljanu ba ne."
Shiru Jamila ta yi ta rasa abin da za ta ce, domin abin ya ɗaure mata kai, duk da ba ka shedun ɗan Adam amma za ta iya rantsuwa akan Ma'u ba za ta taɓa aikata zina ba, wani tunani ne ya faɗo mata a rai, na wani rikici da aka taɓa yi da wata maƙociyarsu lokacin da ta samu ciki, akan ba ta son mijin ta je can wani camis da yake cikin gari sosai ta sayo magani tasha, nan take cikin ya zube, ta tuna har sunan camis ɗin da ta sayo maganin ta ji an faɗa.
Da sauri ta ce "Ma'u kin tuna labarin rikicin da na taɓa baki kwanakin baya da aka yi a maƙotanmu? Na matar da ta sha magani cikinta ya zube?"
Ma'u ta ɗaga mata kai alamar eh
Jami'a ta waiwaya ta duba ko Inna ba za ta ji ta ba ta ce "To ko muma irinsa za mu yi? Ban manta sunan gurin da na ji an ce ta sayo maganin ba, idan kin yadda yau ba sai gobe ba muje can mu sayo maganin, sai ki bari sai kin yi sallar isha'i sai ki sha maganin, kinga tun da dare ne sai cikin ya zube ba tare da kowa ya sani ba, ko da daga baya su Inna sun ji wani abin kika sha ba za su ga laifinki ba." Shiru Ma'u ta yi tana nazarin maganar, Jamila ta ce "Ma'u ba shiru za ki yi ba, ki amince mana, ina son ki rabu da wannan cikin ne, domin idan abin nan ya bayyana ba ke ba ni kaina zan shiga uku ne, saboda an san komai tare muke yinsa da ke." Ba tare da tunanin komai ba Ma'u ta amince da wannan shawarar, canza ka ya ta yi, duban Jamila ta yi ta ce "To ai ba mu da kuɗin da zamu hau abin hawa, da kuma kuɗin sayen maganin."
Jamila ta ce "Kar ki damu, kin ga dubu shida a hannuna da Ammu ta aike ni sai mu yi amfani da su, in ya so idan na koma gida sai in ce mata kuɗin ya ɓata."
"Kina ganin babu matsala Jamila?"
"In sha Allah babu matsalar komai, ai Atika ma da ta sha cikin ya zube"
Inna na zaune taga sun fito a tare, sakin fuska ta yi ta ce "Har kin fito ne Jamila?"
Jamila ta sunkuyar da kai ta ce "Eh Inna na fito"
"To shikenan ki gaishe mini da babar ta ki" ta ce "To Inna za ta ji, ai ma ba ta jin daɗi ne shi ya sa zan koma da wuri"
Inna ta ce "Ayya to ki yi mata sannu"
Ma'u ta ce "Inna ina so zan binta in duba jikin Ammu."
Inna ta ce "Ke da ba kya jin daɗi Ma'u? Ai kamata ya yi ki bari idan kin warke sai ki je ki duba jikin nata." Ma'u ta mairairaice murya tana lallaɓa ta, Inna ganin Jamila tsaye a gurin ya sa ta dole ta haƙura, ta kalli Ma'u dake sanye da ƙaton hijabi har ƙasa, idan ka ganta ba za ka taɓa tunanin akwai ciki a jikinta ba, sai dai ka ɗauka ba ta da lafiya ne saboda fuskarta da ta rame ta ƙara haske. Ta ce "To shikenan kar ki daɗe."
Sallama suka yi mata suka fice daga gidan, sai da suka bar unguwarsu sannan suka tare mai napep
Tafiyar minti talatin suka yi saman abin hawa kafin suka isa cikin gari, Ma'u ta ce "Wannan uwar tafiyar da muka yi sai ka ce ba cikin gari ɗaya ba ne?" Murmushi Jamila ta yi, a daidai bakin camis ɗin da suka gaya masa ya ajiye su, Ma'u ta kalli saman shagon taga sunan camis ɗin ne a rubuce hadda lambar wayar mai gurin. Ƙarasawa suka yi ciki da sallama, ya amsa musu yana bin su da kallo, gashe shi suka yi, ya amsa yana tambayarsu lafiya? Kallon-kallon suka dinga yi, suna tunanin ta ina za su fara yi masa bayanin abin da yake tafe da su, can dai Jamila ta ce "Maganin zubar da ciki za ka ba mu." Zaro idanu ya yi waje yana binsu da kallo, tare da tunanin ko dai wani abin ne aka shirya masa shi ya sa aka turo waɗannan yaran, kafin ya yi magana kira ne ya shigo wayarsa. Ya duba ya ga baƙuwar lamba ce, yana ɗauka ya ji an ce "Idan ka sake ka ba su abin da suka zo nema a shagon, Wallahi summa tallahi sai na lahira ya fika jin daɗi, ka kore su su bar gurin nan." Daga haka aka kashe wayar, bin wayarsa ya yi da kallo yana mamakin waye wannan kuma?
Mun kusa kammala book 1, book 2 na kuɗi ne, ga mai buƙatar ci gaba da bibiyar wannan littafin zai iya tura 1k ɗinsa, 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya.
Amanarcool
***