Free chapter · Read without an account
Chapter 19
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 19
Sayyada barrister
***
YOTA 13
TEAM FIVE INK LEGENDS
Kwance take a madaidaicin shinfiɗarta, bayan ta kammala shirin kwanciya, wayarta riƙe a hannunta tana game, Mamanta zaune tana shafa mai, bata jima da watsa ruwa ba, ta kalli inda Bilqees ke kwance ta ce
"Da wannan game ɗin ai da kin yi bacci kin hutawa ranki"
"Yanzu zan yi bacci na jira ki fito daga wanka ne"
"Ai ya fi, wannan tashin sassafen naku ai sai an kwanta da wuri"
"Mama ban baki labari ba"
"To Bilqees uwar labarai, yau kuma da wacce aka zo?"
Ta yi dariya sosai ta ce
"Kai Mama to shi kenan na gimtse bakina"
"Ai kuma ba ki isa ba, sai kin bani labarin, ba zayyu ki latsa min zuma a baki ba kuma ki hanani latsa ba"
"To aike Mama cewa fa kike yi na cika surutu"
"To a dai faɗa min"
"Uhm wannan likitan ne ya bani mukullin ɗakinsa na hotel, wai na dinga gyara masa"
"Gyara ɗaki kuma?"
"Eh shi ne na ce ya yi magana da Alaja tukuna"
"To ita me ta ce"
"Da muke tahowa ne ta ce sun yi magana ta amince na dinga yi masa aiki, kuma wai zai biya ni albashi"
"Ikon Allah aiki kan aiki kenan! To amma dai ki kula kuma ki san me kike yi"
"Tam in Allah ya yarda zan kula"
Suna hira Mamanta na bata shawara har suka yi bacci.
Washegari da safe suka bar gida, kai tsaye restaurant suka nufa kamar yadda su ke yi, Bilqees ta shigo side na Server's ta ajiye jakarta ta fito zata wuce kitchen Alaja ta yi kiranta, ta iso tare da cewa
"Gani Maa"
"Ki shirya wa mutumin nan abin karyawa ki kai masa hotel kamar yadda ya ce"
"To Maa"
"Ki tabbatar komai ya yi daidai bana son wasa"
"In sha Allahu Maa"
Bilqees ta wuce kitchen, ta yadda su Jummai da Laraba suna faman aiki ta wuce ta soma shirya wa likita breakfast, duk abin da yake ci in yazo cin abincin safe shi ta haɗa ta jera cikin food carrier ta wuce ɗakinta ta ɗau jakarta ta maƙaleta a baya, ta fito, kai tsaye international hotel ta nufa.
Dr Waahab zaune yake bakin bed yana nunke kayan baccinsa ya kammala sannan ya shige toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin suit baƙi ya yi matuƙar amshi farar fatarsa, ya iso gaban mirror yana ƙoƙarin gyara nicktide nasa ya ji ana nocking, ya dakatar ya iso ya buɗe duk a tunanin sa Dr Faisal ne sai yaga Bilqees ce, ya ɗan bata hanya alamun ta shigo, da sallama ta ƙarso ciki ta ajiye food carrier tare da cewa
"Barka da safiya"
"Mommie nah barka dai"
Ya nuna mata kujera ya ce
"Bismillah zauna"
Ta zauna, ya koma bakin mirror yana ci gaba da shirya wa ya gyara nicktide nasa ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya gyara gashin kansa, a hankali ya kalli inda Bilqees take suka haɗa ido, ya kura mata idanu, ta yi sauri ta sudda kai, ita ma bata san lokacin da ta kura masa idanu ba, kawai tana jin cewa shi mutum ne na musamman, sai kuma mamakin irin tsaftan da yake dashi take yi, sannan ƙamshin turaren sa ya yi mata daɗi musamman irin sanyin ƙamshi da yake dashi, ɗauko food carrier ya yi ya bar ɗakin ya koma palour ya bata damar ta yi aikinta.
A hankali ya sauke numfashi, in dai hasashen da ya yi akan Bilqees gaskiya ne to tabbas ya ceci rayuwarta, ya fahimci ita ɗin ta daban ce a cikin ma'aikatan Alaja, don haka zai taimake ta kada Alaja ta ɓata mata rayuwa bayan wannan shikenan.
A nutse ya yi breakfast, bayan ya kammala ne ya shigo ɗakin, ganin yadda ta gyara masa bed gwanin sha'awa kamar ma bai kwanta akai ba, sai kuma yadda ta gyara masa gaban mirror abin ya matuƙar burge shi, ganin bata ɗakin ya fahimci tana cikin toilet, ya ɗan yi nocking ƙofar toilet ɗin, ta leƙo ya ce
"Zan wuce amma iya abincin dare za a dinga kawo mini, ba lallai ne ki dinga taddani a nan ba, daga gobe zan dinga fitan wuri"
"Ok Yallaɓai"
Ya ɗauki duk wani abin da zai buƙata ya fice. Bilqees ta maida hankalinta sosai ta gyara komai har palour ta gyara ta feshe ko'ina da room freshener sannan ta ɗauko food carrier ta fito sai da ta rufe ƙofar sannan ta taho restaurant.
************************************
Zaune suke yau ma kamar kullum, suna wasa cikin nishaɗi suna jiran isowar kyakkyawar Aunty, ganin yau ta jima bata iso ba yasa suka ci gaba da wasa sun san ba zata manta dasu ba don haka sai sun jirata.
Cikin sauri ta iso wajen, ganin suna nan yasa ta sauke ajiyar zuciya, tana isowa ta ce
"Oyoyo friends"
Aiko suna jin muryarta suka iso gare ta da gudu suka faɗa jikinta, suna murna, da ƙyar ta ɓanɓaro su ta ce su zauna suka zauna bayan sun gaishe ta raba musu Alawa da biscuit, suna murna suna sha.
Bata jima a wajen ba, ta ce suje gida. Bayan sun tafi ne yasa ta zauna shiru tana tunanin abin da ya faru sakaninta da uncle rannan bata ji daɗin hakan ba, sai dai ba zata so ya san komai gare ta ba, bari abin ya fi alkhairi, ta yaya zata ba shi labarin rayuwarta dake cike da ƙalubale, za ta fara yi masa wasan ɓoya har ya hakura da son sanin wacece ita? Ta mik'e ta bar wajen cikin sauri.
A kullum Bilqees ke zuwa hotel ta gyara wa Dr Waahab ɗakinsa sai ta shirya masa abincin dare kamar yadda ya buƙata sannan ta koma restaurant, tun ranar da ta riske shi a ɗakin bata sake sanya shi cikin idanunta ba, sai dai ta iso da safe ta tadda ya cinye abincin ya bar flask ta tattara ta taho da su.
Dr Waahab ya dawo hotel a lokaci dare ya yi, kasancewar ya ce Bilqees ta dinga kawo mashi abinci yasa bai bi yan'uwansa zuwa restaurant ba, ya shigo a gajiye, ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya fito ya sanya jallabiya baƙa, sannan ya zauna cin abinci, ya ci abinci sosai sannan ya ɗan hau online ya yi chatting da yan'uwa da abokan arziki, mutan Nigeria Maiduguri.
Ya dawo kan bed ya kwanta, babu jimawa bacci ya yi awun gaba da shi.
Jar guguwa tattare da yashi da ƙura suka rufe wajen, ba a iya hango komai sai ƙasa dake watsuwa ko'ina. Da ƙyar yake iya ɗaga ƙafarsa yana tafiya yana neman hanya fita ya ji murya kamar daga sama ana kiran suna shi
"Taimako, ka taimake ni, ka ceci rayuwata"
Ba ya iya hango me magana amma kuma jin muryar na mace ce, har zai iso gare ta kuma ya fasa, cen ta sake cewa
"Uncle help me, i need a help"
Jin muryar kamar na kyakkyawar Aunty yasa ya juya a guje ya iso wajen da ƙyar, ganin tabbas ita ce, yasa ya miƙa mata hannun, ta miƙa masa ta taimake ta, suka fito guguwar ta yaye, ya sauke numfashi tare da cewa
"Angel"
Bata ce komai ba, ta soma tafiya da baya², yana binta yana ƙoƙarin yaye mata niqabin ta, amma bai yi nasara ba, ta ɓacewa ganinsa, ya furta da ƙarfi
"Angel.....
Ya farka a bacci da sunanta a bakin shi, duk ya haɗa gumi, yana mamakin mafarki, Angel kuma a mafarkin shi me yake faruwa ne, ko dai tana cikin tashin hankali ne? Ya yi addu'a ya sake komawa bacci....
Gari yana wayewa, yaji duk jikinsa a mace, ya sanar ba zai iya tafiya workshop ba, su tafi. Yana wance tun bayan ya idar da sallar asuba bai koma bacci ba, har Bilqees ta shigo, da mamaki yau likita yana nan bai fita ba, ganin ta shigo ya tashi zaune, ta gaida shi ya amsa tare da yi mata sannu sannan ya fito palour ya bata damar ta yi aikinta.
A nutse ta kammala gyara ɗakin, tana fesa room freshener ya shigo kai tsaye ya tsaya a bakin window ya kurawa wajen kallo ko zai hango Angel amma shiru, yaran ma basu iso ba, ya duba a gogo yaga safiya ce har yanzu, tana kan canza bed sheet ma ya sake ahigowa yaga har yanzu, ta kammala aikinta tana shirin fitowa taga ya sake shigowa yana kallon wajen, ganin yaran sun iso amma Kyakkyawar Aunty bata ƙaraso ba yasa ya kuɗiri niyyar tana isowa zai je...
Bilqees ta yi masa sallama ta tafi, tana mamakin shiru na likita, yau baya son yin magana. Dr Waahab ya sake leƙa window sai yaga Angel ta iso, ya yi sauri ya shirya ya fito, yana ƙoƙarin isowa kuma yaran sun bar wajen, ita ma ta yi bakin titi, kamar zai juya ya koma hotel ɗin wata zuciyar ta ce kabi bayanta.
Da sauri yayi bakin titi ya tari machine ya ce su bi bayan mashin dake gabansu, sun yi tafiya sosai sannan mashin dake ɗauke da angel ya tsaya, ta biya kuɗin sannan ta shige wani katafaren gida, babba ne sosai, motoci da yawa a kofar gidan wasu suna shirin tafiya wasu na isowa kasancewar a bakin titi gidan yake.
Da mamaki yake bin unguwar da kallo, me ya kawo Angel cikin wannan gidan? Gani wani sauri yana zaune gefen titi akan benci yasa Dr Waahab isowa wajensa ya miƙa masa hannu
"Assalamu alaikum"
"Amin wa'alaikassalam"
Cewan saurin, Dr Waahab ya zauna cikin nutsuwa ya ce
"Abokina tambaya ka nake son yi"
"To Allah yasa na sani"
"Don Allah wancan gidan na menene? naga mutane suna shiga suna fita"
"Amma dai kai baƙo ne ko?"
"Eh baƙo ne ni"
"Yawwa alamu sun nuna ai, shi wannan gidan ana yi masa laƙabi da tumbin Giwa, gidan karuwai ne da ƴan dandi, duk wanda ka ganshi a cikin Tumbin Giwa to cikakken ɗan bariki ne kuma riƙakke"
Dr Waahab ya matuƙar kaɗuwa da jin abin da wannan saurayin yake faɗi, cikin tashin hankali ya ce
"Gidan karuwai?"
"Eh mace ce mamallakiyar wajen, ta tara mata fiye da dubu, waɗannan masu mutunci zuwa suke yi su ɗebi ganima su yi gaba"
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunallahu wa ni'imal wakil"
Shine abin da Dr Waahab yake furta wa, nan take idanunsa suka kaɗa su kayi ja, Angel karuwa ce! A gidan karuwai take? Kenan shi yasa taƙi sanar dashi labarin rayuwar ta?"
Da ƙyar ya mik'e, yana jan ƙafafuwan sa, kamar zai tafi kuma ya tsaya to ko shine dalilin da yasa take rufe fuskata? To amma kuma har sadaka take baiwa yara!
To mene haɗinta da wannan gidan? Wannan gidan bashi akai wa tambari da gidan karuwai ba?" Ya ja numfashin daya matse masa ƙirjin da ƙyar, ya sha haɗuwa da abin mamaki da tu'ajjuji sai dai wannan ya naɗe dukkan wasu tashin hankali daya taɓa gani a baya.
Mamakin da yake neman tarwatsa matsa ƙwaƙwalwarsa wacce ta gaza ɗaukan tension ɗinta.
“Ko dai da gaske itama karuwar ce?”
Sai ya yi saurin cewa
"Kai no way"
Ga wani ƙarin mamakin dake neman kashe shi, shine niƙab ɗin fuskarta.
A lokacin daya fahimci inda ta shiga sai ya ji dukkanin haske dake cikin duniyarsa ya dishashe, farin ciki ya gushe, tashin hankali, firgici haɗe da razani suka mamaye duniyarsa baki ɗaya. To wacece ita? sannan menene gaminta da inda ta shiga.
"Biyo ni ka yi?"
Shine furucin da ya fito daga bakinta, cikin tashin hankali yake dubanta cike da mamaki da tambayoyi a bakinsa, kamar ba zai ce komai ba amma ya sauke numfashi tare da daidaita nutsuwarsa ya ce
"Menene haɗin ki da inda ki ka shiga?"
"Nan ɗin muhallina ne, nan ɗin shine rayuwata, bani da inda ya fi nan, kuma ina alfahari da nan ɗin"
"Kina nufin rayuwar.....
Yadda ta watsa masa fararen idanuwanta da suke cikin niƙabin yasa ya kasa ƙarasa maganar da ya yi niyya, ta girgiza kanta sannan ta ce
"Don't judge a book by its cover"
Daga nan ta yi tafiyar ta, ta bar shi cikin ruɗani da tashin hankali......
Rayuwa yake yi shi kaɗai cikin duniyarsa, ba tare da yasan alƙiblansa ba, tafiya yake yi ba tare da yasan inda ya dosa ba, tunani yake yi ba tare da yasan ranar ƙarewar shi ba. Kwatsam haske ya bayyana cikin duniyarsa wanda ya haskake duk wani duhun dake cikin duniyarsa, farin ciki mara misaltuwa ya mamaye rayuwarsa, ji yake babu wanda ya kai shi farin ciki a wannan duniyar. Lokaci guda ta bayyana cikin duniyarsa ji yake ba'a taɓa yin kamarta ba, kuma daga kanta an ƙare, musamman lokacin da ya yi tozali da kyawawan idanuwata waɗanda suke lulluɓe ciki niƙabi
Comment and share fisabilillah