Free chapter · Read without an account
25
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)
Adabi Writers Association
Book 1
*Page Twenty Five*
*zaku ɗan dinga yi min uzuri idan baku ji ni ba please kasancewar ina da majinyaci*
Duk shiru suka yi kaman ruwa ya ci su, rarraba idanu kawai take tsakaninsu kaman zata iya karance matsalar tsab a fuskokinsu, tana jin yadda gabanta ke dukan tara-tara, bakinta ta ji ya sake fusgo kalaman da bata san sadda suka fita ba
"Dr. Ahmad Don Girman Mahalliccin mu ka faɗa min menene?"
Ta karashe hawaye na ɓalle mata sbd fargabar abin da zata iya ji, Miƙewa yayi ya ƙarbi yaron hannunta gudun kada shi ƙasa, ba tare da ya kalli Mukhtar ba yace
"Am sorry! Zan faɗa miki ne ba saboda komai ba sai saboda mu taru gabaɗaya mu lanƙwasa shi mu gwada sa'ar mu akan wannan cutar, Mukhtar na da leukemia"
Dib haka kunnuwanta suka ɗauke sai wani sautin ƙaraaa me ƙarfi take ji kaman ana haɗa karfe da karfe ana bugawa da tsananin ƙarfi, ganinta ne ya so ɗaukewa jiri ya ɗibe ta ta tafi zata faɗi da hanzari Mukhtar ya riƙe ta, ya buɗe baki zai yi magana kenan suka ji zubewar kwanuka duk basu san Maami ta shigo da tray a hannunta ba, tsallake tray ɗin tayi ta iso gaban Dr Ahmad muryarta yayi sanyi sossai tace
"Wai da gaske kake yi doctor? Da gaske kansar jini Mukhtar ke ɗauke dashi? Meyasa? Garin yaya?"
Numfashi me karfi Alayah ta ja ashe bata suma ba, zuciyarta ne ya so tsayawa da bugu don firgici, tun kan ta ji amsar Dr Ahmad ta fashe da kuka.
"Da gaske ne Maami, Mukhtar na ɗauke da chronic lymphocytic leukemia wato wannan cuta ta kasance wani nau'in cuta ne mai tsanani da ke illata ainihin massarafar jini(blood forming tissues), yanayin shi yana taɓa wannan soft and spongy ƙashi da ake kira bone marrow, wannan ƙashi na bone marrow aikinshi shine samar da cells na jini ya kuma sake shi zuwa duk wani magudanar jini dake a jikin ɗan Adam idan da buƙatar hakan, bone marrow yana ɗauke da abin da ake ƙira White blood cells wato waennan dakarun yaƙi na cikin jiki dake faɗa da infections, da kuma abin da ake kira Red blood cells suna taimakawa wurin shigar oxygen, and na karshen wato platelets shi ana buƙatar shi ne wurin dakatar da kwararar jini, a sadda aka samu shigar leukemia sai ya chanza kwayoyin halittar? (genetic changes).
Abin da ya kamata ku sani game da leukemia:
1. Abin da ke haifar da wannan cuta;
Yawaitar X-ray yayinda mace ke da ciki.
chanzuwar kwayoyin halitta ko kuma introducing chemicals ta ƙarfin tsiya a cikin jini wato chemical exposure.
2. Leukemia ya kasu kashi uku
Acute lymphoblastic leukemia, myelid leukemia sai chronic lymphocytic leukemia wadda shine Mukhtar yake ɗauke dashi a maganar gaskiya ba'a warkewa sai dae ana yin wasu treatments ɗin don samun sauƙin ciwon.
3. Leukemia cells yana ginuwa ne yawanci a liver wato hanta, ko Central nervous system inda zaku samu yawanci me wannan cutar zai yi ta fama da ciwo a ciki ko kuma ƙasan haƙarƙari ta ɓangaren hagu.
4. Ba'a cika gane leukemia da wuri ba, a lokacin da aka gane hakan kuwa zaku samu patient zai yi ta fama da
*yawaitar zufa cikin dare
*kauracewar bacci daga idanu
*Rama marar dalili
*zazzabi da zafin jiki kusan ko da yaushe.
5. Yadda ake gano cutar;
Masana harkar lafiya na iya gane wannan cuta ta hanyar
Lura da alamomin da suka bayyana.
Gwaje-gwaje na jini.
6. Matakan saukaka hauhauwa/rikitarwar cutar sun haɗa da
Bone marrow Transplant (za'a ƙona massarafar jinin ta hanyar anfani da radiology, a sake dashen sabo) sai dae ya kan ragu ne na ɗan wani lokaci ya sake dawowa, sannan yana janyo irritation na skin ko wani lokaci yayi jajazir.
Chemotheraphy: allurai dake taimakawa wurin hana cutar yaduwa da sauri, Dukda wannan ɗin yana da matuƙar ciwo ya kan kuma janyo wata jinyar na daban ko a wurin da ake administerring allurar ko ma yayi causing ciwon gaɓoɓi da sauransu."
Duk idanu kawai suka zubawa likitan dake ta bayani, Maami tace
"Meyasa baka faɗa mana da wuri ba? Ko ba'a tare shi da wuri?"
"Ana yi sossai ma, ai da zarar an ji waenchan alamomi da na zayyoni gaggawar zuwa asibiti shine daidai domin tarbarshi da wuri hakan na taimakawa wurin hana harzuƙa shi, mun san Allah ne me rayarwa kuma mai kashewa amma a likitance tarar shi da wuri na iya ƙara wa'adin kwanakin mutum daga hauhauwar ciwon. Kuma abin da ya sa ban faɗawa familynshi ba Mukhtar be amince ba, ya ƙi sam inda ya bada hujjar cewa a ko yaushe shine silar baƙin ciki da damuwowinku, daga zarar kun sani zaku hana kawunanku walwala da annashuwa wadda ba hakan yake Fatan gani ba zuwa iya lokacin da Allah ya ɗibar mishi duba da Maami kina fama da hawan jini da kuma maman Mukhtar Junior da case ɗinta worse, Dukda hakan da yayi ban barshi ba ni nayi ta matsa mishi yake zuwa akai akai ana duba shi."
Alayah da idanunta har sun soma kumbura sbd kuka tace cikin karyewar murya
"kuna ba da wa'adi? Tsawon wani lokaci kuke tunanin zai iya rayuwa?"
Numfashi Dr Ahmad ya zuƙa kan yace a sanyaye
"Alal haƙiƙa kaso tamanin da biyar 85% cikin ɗari 100% na waenda suke ɗauke da wannan ciwo basu cika haye shekara guda ba, yayinda sauran kason na iya kaiwa shekaru huɗu zuwa shidda"
Hannu Maami ta saka a baki tana ƙoƙarin hana kanta kuka, Miƙewa tayi ta isa wurin Mukhtar da ya rausayar da kanshi ƙasa sai ta rasa me zata mishi tayi scolding nashi ne sbd ɓoye musu da yayi ko ta rungumeshi ta nuna tashin hankalinta?
A hankali ya ɗago ya riƙe hannuwanta idanunshi sun yi mugun rinewa, hannun Alayah ya riƙo ya haɗa da na Maamin
"wannan dalilin ne ya sa na hana faɗa muku, bana so ku tashi hankalinku don Allah, na san Allah ne mai ɗaurawa bawa cuta kuma shi ke yaye masa sai dae wannan ɗin ni na na janyo bisa kuskure ko in ce ganganci"
Hannunshi ya janye ya zare rigan shi yana kallon jikinshi
"dubi abin da na yiwa kaina da sunan ado ashe shine zai halaka ni! Shine zai yi sandina..."
Sai a lokacin kuka ya nemi kubce mai tun sanda ya san yana da cutar.
"Don Allah ku min alfarma Maami, fatee na! Ku yi min alfarmar sauran kwanakin da suka rage min a duniya in yi shi a tsakaninku ba tare da na ga hawayen ɗayanku na zuba ta dalilin tausayina ba, kukan ku shine rauni na! Kar ku karya min zuciya please..."
Abba da tuntuni ya shigo basu san ma ya shigo bane yana dafe da gini gudun faɗuwa yace
"Mukhtar tashi mu tafi... Ahmad mu je asibitin ayi duk abin da ya kamata ya samu sauƙi kuɗi ba matsala bane!"
Kuka yake yi sossai ya sani farin sani kuɗi ba zai taɓa musu maganin komai ba kan wannan cuta ko da ko ina zasu je a duniya, ya sani sai dae ya furta hakan ne kila ko zai samarwa kanshi kwarin gwiwar Mukhtar zai rayu!
Mukhtar ya fara magana Dukda maganan sai ya zama kaman yana ɗan mishi wahala ko yana jiɓancewa yayin maganan
"Abba ba zan yi ba! Ba zan yi komai ba weither Transplant ko Chemotheraphy Abba akwai azaba gwara ku bar ni na mutu cikin salama"
Kukan Maami ne ya fito fili.
"Ka kuwa san duk duniya ba ciwon da ya kai cancer azaba Mukhtar? Gwara dai ayi wani abin don rage raɗaɗin ciwon"
Girgiza kai yayi.
Duk yadda suka yi kokari wurin convincing ɗin shi ya ƙi yace baya so ayi admitting ɗin shi, baya so ya zama abin tausayi a idanun kowa, kila wasu ma Allah ya ƙara zasu mai ba tare da sun duba tuban shi ba, daga karshe da suka fi karfinshi ya yarda zai yi tunani a kai, amma ya san a ranshi bashi da niyyar wannan azabar ko cancer me tsira ce abu guda ne, a raɗe wurin ciwo a ƙone kwayoyin halittar amma bayan lokaci kankani zai sake tsirowa saboda saurin hallitun cancern haka yake a jini ma, ƙone duk wani jini za'a yi a sake Transplant abu ɗaya ne duk ake yi kusan da masu sickler kuma ba shi yake hana cutar dawowa ba gwara ya mutu ba tare da yayi experiencing waennan pains din ba.
Ba Zasu iya faɗin yanayin da suka tsinci kawunansu ba a lokacin har aka kwana biyu ma, gidan ya zama so quite hira da dariya ya musu karanci, Mukhtar din ne da ya samu sauƙi yake kokari kwarai wurin ganin walwalwansu ta dawo sai dae hakan ƙara jefa su cikin jimami da damuwa yake, kaman yau Maami na zaune a parlor sunna Tv ne ke aiki malam Mukhtar yola na rattabo wa'azi sai dae sam hankalinta baya kai, kukan da Mukhtar Junior ya tsanyara ne yasa tayi saurin juyawa ta kalli inda yake zaune a tare da mahaifiyarshi da ta so sake shi ƙasa ba tare da ta sani ba sbd zurfi da tayi a tunani sai dae be samu kaiwa ƙasan ba babanshi ya taro shi.
"Shhhh shssss Me suna! Yi shiru abin ka ur super hero is here baka faɗi ba!"
Idanunshi ya sauƙe cikin na Alayah sai ya sakar mata murmushi, yake tayi ya isa gangan Maami ya zauna tare da jingina kanshi da kafaɗanta
"Maami dubi yaron nan.."
Ta kalleshi kan tace
"Toh ai kullum ina ganinshi menene sabo a wurin?"
Yayi murmushi yace
"akwai fa Maami! Baki ganin yana ƙara wayau kamanninshi da nawa na kara fitowa?"
Tace
"hakane kam babu abin da ya bar maka"
"ko ba komai idan kuka ambaci Mukhtar zai amsa! Idan kuka kalli fuskanshi ni zaku gani a ciki, haƙiƙa nayi matukar godiya ga Allah da be ɗaukeni ba tare da ya ajiye muku replacement ba, da Mukhtar Junior kaɗai zaku ke tunawa dani... Idan ya girma ya mallaki hankalin kanshi na tabbatar daga ke har fatee baza ku barshi ya tashi daga wurin sallah ba tare da ya min adu'a ba, hakan wata ni'ima ce mai girma da ubangijina ya min Alhamdulillah!"
Wani kuka ne ya kufcewa Alayah ta miƙe tayi sama tana sakin kukan me taɓa zuciya, Maami da hawaye ya gangaro mata tace
"ba sai ka tuna mana da cewa zaka tafi ka bar mu ba Mukhtar! Daga mu, kai har likitocin babu wadda ya san wa'adin wani sai Allahn da ya halicce mu, sai Kaga ma ka rayu fiye da abinda likitocin suka hango, ka daina ɗagawa yarinyar nan hankali da wanne kake so taji? Kanta? Kai? Ko kuma mahaifiyarta?"
Lumshe idanu yayi a hankali ya furta
"Don Allah Maami ki yafemin!"
"Sau nawa zan ce na yafe maka duniya da lahira Mukhtar?"
Murmushi ya saki kan ya ajiye mata Mukhtar ya miƙe ya haura wurin Alayah.
A gaban mirror ta zauna tana cigaba da kukanta.
Yana isa gabanta ya duƙa ya ɗauketa chak zuwa bakin gado suka hau a tare, jinginuwa yayi da jikin gadon ya kwantar da ita jikinshi ta baya hannunshi ya sanya duk biyu ya kama nata yana wasa da fingers ɗinta yace
"Fatee na! Ni da nake so na baki wata amana ashe ba zaki iya yi min ba?"
Tace
"Babu abin da zaka bani umarni ban aikata shi ba ya Mukhtar, ba zan taɓa ƙin karbar amanarka ba!"
Ajiyar zuciya ya sauƙe yace
"nauyi nake so in ɗaura miki, zan baki amanar Maami, Little Mukhtar da kuma kanki, ko bayan raina kar ki bari kuyi min kuka! Kar kuyi min kuka please ku yi min Adu'a shi na fi buƙata, Allah ya sani ina son ki! Ina ƙaunar ku ku ukun nan bani da kamar ku a duniya, Fatima you are the one that taught me what it takes to be a good person.
Thank you for loving me even when i wasn't perfect!"
Yana kai nan yana kissing tsakiyar kanta.
Hana kanta kuka tayi kawai ta juyo ta rungumeshi sun dau tsawon lokaci a haka ba tare da waninsu ya motsa ba, knocking da aka yi yasa ya zame ta ya miƙe yaje ya buɗe kofan tabawa ce da lil mukhy, ya karɓeshi ya dawo bakin gadon shi ya taimakawa yaron ya fara shan abincinshi, sai ya matsa baya yana kallonsu adorably! Yana sauƙe numfashi a kai a kai.
Sai dare ya bar ɗakin ko da lokacin bacci yayi sai gasu nan sun biyo shi, kusan hakan ne ta gane kwana biyun bata yarda ta kwana ɗakinta ko be je ba zata zo, a gadon shi suka yi masauki, ko da ta yarda tayi bacci na kankanin lokaci tana farkawa ta ganshi kan sallaya zata yi hanzarin sauƙa itama ta jona shi, idan zazzabi ne ya tasar mishi sossai zata nemi towel da ruwa ta zo tayi ta massaging nashi, sossai take hidimta mishi yana sanya mata albarka, wani lokacin har kuka yake yi, a duk sadda kuma zata ga hawayenshi kaman ya bata kofan nata hawayen ne zata rungume shi suyi kukan a tare.
Sam kula da Mukhtar ya sanya bata yi maganan zuwa asibiti duba Ummi ba Dukda ta san ba barin shiga ake ba, sai yau da ya kasance ma kusan watan ummi guda a Saudiyya ta dubi Mukhtar
"Ya Mukhy ko zaka raka ni?"
Yace
"Ina zamu?"
"Ina so in duba Ummi da jiki ne, kewanta nake sossai"
Ta karashe da lumshe idanunta da kasala da gajiya suka cika shi.
Shiru yayi na seconds kan ya janyo hannunta ya riƙe yace
"Alayah ki natsu ki saurareni ummi bata ƙasar nan, lokacin da kike labour a lokacin ta farka amma bata farka cikin condition me kyau ba..."
Gabaɗaya idanunta suna waje zuciyarta kaman ana kumburawa tayi matukar razana girgiza kai ta fara
"Ki natsu ummi na samun sauƙi Fatee"
"wani irin samun sauƙi ya Mukhtar? Me ya sameta bayan nan? Ta mutu ne ban sani ba?"
"Ummi bata mutu ba, Autan Maami ya fita da ita bayan long process na emergency flight yanzu haka bata ƙasar tana saudi arabia, amma umar ya ce tana samun sauƙi sossai"
Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, yanzu kenan bata da daman ganin umminta ko me ake so a ce?
"zaki ga ummi Alayah, zan fara miki processing Visa"
"ba zan je ba! Ba yanzu ba"
Da sauri ya ɗago ta
"Ummi fa? Meyasa ba yanzu ba?"
"Ya Mukhtar taya zan iya tafiya in barka cikin wannan hali? A'a ba zan je ba, ba yanzu ba ba dai tana samun sauƙi ba? Na barta hannun Allah zai cigaba da kular min da ita"
Ta ƙarasa tana shashekar kuka, da gaske bazata iya ta tafiya ta barshi ba, dare basa bacci zafin zazzaɓin da har wani lokaci fusga yake taya zata iya barinshi haka?
Sun cigaba da jinya a tsaitsaiye har na tsawon sati biyu, zuwa yanzu sossai Mukhtar ya rame wasu abubuwan sai dae Alayah ta mishi hakan yasa Maami ta fi bada karfi kan lil mukhy, haka zai sanya su gaba da kalaman dake kashe musu jiki yana tuna musu tafiya zai yi ya barsu, wani lokacin su haɗu su uku suyi ta zubar da hawaye, tashin hankalin Maami bata samun umar a waya tun sanda suka san da ciwon kullum sai ta gwada da alamun ya tafi aiki me muhimmanci don suna hakan, shi karan kanshi Mukhtar ya kan ce ya gwada Layin sau ba adadi amma baya samu.
Bayan sun gama cin abincin dare yau be iya ya je wurin baba ba, a ɗaki ya ɗan duba karatun kan ya hau gado ya kudundune sbd yadda yake jin zazzabi na sassara kasusuwanshi, ji yake kaman ana tafasa jininshi wani irin karkarwa ya soma a take, kaman an jefo Alayah ta shigo ɗakin ta same shi cikin wannan hali hankali tashe suka yi asibiti.
Likitoci sun jima kanshi kan Dr. Ahmad ya fito yana kallonsu a sanyaye.
"Menene Ahmad?"
Abba ya tambaya shima jikinshi a mace
Dr. Ahmad yace
"Kuyi haƙuri Abba, a matakin da Mukhtar yake dole zamu yi admitting ɗin shi"
"wani mataki? Me hakan ke nufi?"
Maami ta tambaya
Wani Dr ne yace
"ya shiga final stage ɗin shi wato stage 4, dole yana bukatar kulawar malaman asibiti sossai"
Ba zaka iya cewa ga yanayin da suka shiga ba, amma dai iyayenshi sun yi matukar kokarin ƙin zub da kwallah, har aka kai Mukhtar Amenity ward zuwa room nashi Alayah bata daena kuka ba, wani irin tashin hankali ne wannan? Bayan komai ya wuce? Bayan sun gama murnar daidaituwar komai? Meyasa wannan ciwo da bashi da waraka ya shigo?
Sosai tayi kuka, Maami ta so ta koma sbd lil mukhy sai ita ta zauna sam ta ƙi tace Maami su tafi zata kula dashi in ya so a ba lil mukhy madara, basu hanata ba ganin yanayin da take ciki.
Nan ta fara jinyar Mukhtar da kaman jira yake a kwantar dashi jikin ya rikice, kusan komai ya dawo sai an mishi bashi da karfi ko na miskala zarratin, idanunshi sun kara girma yayi wani irin haske, bakinshi kullum a bushe Dukda tana keeping ɗin shi hydrated..
"Sannu fatee na gode!"
Ya faɗa a sadda ta gama goge mai jiki da towel,
Ajiye bowl ɗin tayi ta zauna tare da riƙo hannunshi cikin tausayawa tace
"Sannu ya mukhy, Allah ya baka lafiya"
Idanunshi ya lumshe kawai ta sake cewa
"Menene? da zafi ko ciwon?"
Dry smile yayi yace
"hmmm it boils in and out Fatee! Akwai ciwo sossai"
Hawayenta ne suka gangaro.
"Allah ya sassauta maka ya mukhy"
Ya gyaɗa kai kawai yana me sake lumshe idanu don a yanzu har magananshi ya taɓu shima sun ce yana daga cikin signs na ciwon ya tsananta.
Haƙiƙa Mukhtar na jin jiki, ya kuma nuna jarumta sossai ta yadda duk wadda zai zo duba shi zai sake ya nuna musu yana samun sauƙi alhalin shi kadai ya san abinda yake ji a cikin jininshi.
Yau jikin da sauƙi sossai ya tashi don haka yace su je gida yayi wanka ya huta sai su dawo, Dukda ta so ƙi ya yi convincing ɗinta suka wuto gida, yana rike da hannunta yana tafiya slowly suka shiga room ɗin shi.
"Mu zauna in huta!"
Bakin gado suka je ya zauna, zata miƙe ya riƙe hannunta ya ɗago gajiyayyun idanunsa ya zuba cikin nata a hankali yace
"I need you fatee! Kiyi haƙu...."
Da sauri ta haɗe bakinsu slowly suka isa kwance zuwa gadon cikin yanayin ƙasa da murya tace
"har sai ka bani haƙuri? Kai fa mijina ne! Gani bisa jikinka kayi yadda kake so"
Ta karashe tana shafa kumatunshi, murmushi kwance a kan fuskanshi ya sake manneta slowly yake tafiyar da komai sai dae cikin tsantsar natsuwa da kulawa ba kaman da ba, zata iya rantsuwa bata taɓa sanin cewa haka abin yake ba sai a yau sun bai wa juna duk kulawar da ta dace inda ya ƙarasa da rikidadden zazzaɓi, da kyar suka yi wanka suka koma asibiti.
Jikin ya sake rikice wa, likitoci sun jima sossai kan suka samu yayi bacci a hannunshi ta kwantar da kanta, kuka tayi tayi a wurin cikin jimami da tausayi ta ɗauki tsawon lokaci a haka kan taji yana shafa kanta da ɗayan hannunshi, da sauri ta ɗago suka hada idanu he looks so tired nd pale.
Want the next chapter?
ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol