Free chapter · Read without an account
6
*FARASHIN ABOTA*
*SASAAL*
6
Wani irin kallon ta yi min, ta yi gaba ta jan tsaki..
Da sauri na bi bayanta ina cewa;
"Me nayi miki da zafi haka Mairo?"
Ba ta waiwayo ba, kuma ba ta cemin komai ba, ta cigaba da tafiyarta..
Sammani kai tsaye filin bugo wasa ƙwallonsu ya nufa da Umar..
Wajen dogayen reshen bishiyar da aka mayar abun zama, Sammani da Umar su ka ƙarasa suka zauna..
Mu na ganin haka muma muka ƙarasa wanda yake fuskantarsu mu ka zauna..
Hira Umar ya fara jan mu da shi ta hanyar tambayarmu yanayin zamantakewar ƙauyen cikin raha, sai dai kafin na ba shi, Mairo take saurin amshewa, sai ya zamana hirar ta koma a tsakanin su uku da Sammani..
Ba a iya saman fuska ba, har a cikin zuciyata ban ji komai na rashin daɗi ba..sai ma kallonsu da nake ta yi da murmushi kwance a saman fuskata..
Muna nan zaune na hango wani matashi daga can nesa ya na nufo inda mu ke zaune, ƙuri nayi masa da ido, ina jiran ya ƙaraso, domin gani nake yi kamar na sanshi..
Shigarsa sak irin ta Sammani, sai dai shi tashi kalar jesin jaa ce turarriya..ya zuba dukka hannayensa a cikin aljihun wandonsa..
Ya na ƙara kusantomu, siffarsa da kammaninsa na ƙara bayyana a gareni..
Dogo ne, mai tsakaicin kauri, fatarsa ba ta cika duhu ba, kuma bata cika haske ba..daga inda nake zaune ba na tantance komai na halittar fuskarsa sai dogon karan hancinsa...
Ƙasa na yi da kaina, amma gaba ɗaya hankalina ya bar kan hirarsu Sammani ya koma kan jiran ƙarasowar matashin.
Ban motsa ba, har sai da na ji muryarsa ya yi sallama..
Ɗagowa nayi ina kallonsa..ban san yadda zan misalta kyansa da na gani a idona ba, kuma ban taɓa ganin ko mai kama da shi a Yankinmu ba, sai dai wani irin kallo zallar ƙyama da ya yi min ne, yasa na yi saurin yin ƙasa da kaina..
A karon farko a rayuwata da na ji na muzanta, saboda samun kallon ƙasƙanci daga wani..
Hannu ya bawa Sammani.. Sammani ya cafe hannun yana yi masa kirari da sunaye kala-kala ba tare da ya amma ambaci asalin sunan ba.
Bayan sun gama gaisawa Sammani ya kalli Umar yana yi masa bayanin irin yadda matashin ya ƙware a iya buga ƙwallon ƙafa...
Ina kallonsu ta ƙasan ido, tun da matashin ya miƙa musu hannu suka gaisa ya mayar da shi cikin aljihun wandonsa kamar yadda suke tun kafin ya ƙaraso..bai ƙara ce musu komai ba.
Mairo ciki salo ta gaishe shi, ya amsa, a taƙaice..anan ma Umar bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya gabatar masa da Mairo a matsayin wacce zai aura..
Gudun kar a ga rashin tarbiyyata yasa na ce masa;
"Ina wuni"
Yi ya yi kamar bai ji ni ba..hakan ya sa na ƙarajin wani irin kunya ya lulluɓeni na ƙurawa ƙafafuwana dake sanye cikin silifas ido...
Ina jin san da yake yiwa su Umar sallama..ba tare da ya gayamusu abinda ya kawo shi.. har ya bar wajen.
Kasa jurewa nayi, na bi dogayen sawayensa da kallo ta gefen ido, har sai da ya ɓacewa ganina..
Umar da alama tausayina ne ya kamashi...cikin sanyin murya ya ce;
"Sammani, ina son ƙanwar nan taka, babu ruwanta da hayaniya, ina son macen da bata da rawar kai..
Gaskiya kafin na koma Kano jibi, ya kamata ka sasantamu"
Sammani dariyar jindaɗi ya bushe da shi..
Ni kaina sai na ji damuwar zuciyata ta gushe... Ba wai dan na ɗauki zancen nasa da muhimmanci ba, sai dan karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa; "anayi da kai ya fi ba'ayi da kai"..
Mairo zurbur ta yi ta miƙe tana kamo hannuna tana cewa;
"Mu zamu koma gida, kar Inna ta yiwa Hindatu faɗa"
Umar murmushi ya yi ya miƙe shima, ya na kallon Sammani ya ce;
"Bai kamata mu bar su, su bi wannan hanyar su kaɗai ba, ya kamata mu rakasu gida ko?"
Sammani cikin al'ajabin Mairo da ya kasa ɓoyuwa a saman fuskarsa ya ce;
"Hakan zai fi gaskiya"
Kafin Sammani ya kai ga tashi har Mairo ta ja hannuna mun yi gaba..
Takaicinta ne ya kamani, sai na ji kamar na ce mata a'a amma tsoron samun matsala a abotarmu, da gudun ɓacin ranta yasa na kasa faɗa, ta cigaba da figata kamar ƴar cikinta...✍🏻