Free chapter · Read without an account

9

by Nafisa Aliyu Sasaal · FARASHIN ABOTA

*FARASHIN ABOTA*
       *SASAAL*


             9

Sai dai ina ƙarasawa kusa da su yanayin fuskata ta sauya, hawayen da na share tun kafin ƙarasowata, suka ƙara taruwa a cikin idanuna..dalilin matashin da na gani a tsaye tare da su.. 

A  jikina nake jin kamar yana jin kukana kamar zai iya fahimtata duk da kallon ƙyamar da na samu a gareshi jiya..

Sanye yake kayan buga ƙallo shi da Sammani..sai Umar da ke sanye cikin ƙananan kaya.

Sammani na fara gaisarwa idona a ƙasa..

Cikin barkwanci ya amsa, ya na tsokanata da shine jiya na gudu ina jin sa yana kirana ban tsaya ba ko?

Ban ce masa komai ba, har lokacin kaina na ƙasa ban ɗago ba..

A dunƙule na haɗa gaisuwar Umar da ta Saifi..

Umar ne kawai ya amsa yana tambayata ya ya na je gida jiya?

Sam hankalina baya kan tambayarsa balle na ba shi amsa, gaba ɗaya tunanina ya karkata kan dalilin da yasa Saifi baya son amsa gaisuwata..

Ɗagowa na yi na saci kallon inda yake tsaye, sai na ga, ashe ma ya juyawa saitin da nake tsaye baya yana amsa waya..

Ina kallon inda Mairo take naga idonta tsaye ƙyam a kaina..tana yi min wani irin kallo.

Umar bai ji haushi ba, ya ƙara tambayata yaya ya ga yau na sauya gabaki ɗaya?

Mairo na ƙara kallo na ga har lokacin bata daina kallona ba..wannan dalilin yasa na kasa ba shi amsa.

Kamar daga sama na ji ta ce masa;

"Ai dama kai ne baka san halin Hindatu ba, idan banda haka tun ɗazun fa kake yi mata magana tayi banza da kai"

Ina jin tace haka, na ƙura mata ido, a daidai lokacin Saifi ya juyo, yana yiwa Sammani sallamar shi zai wuce fili, idan sun gama sa sameshi acan.

Bayansa na bi da kallo, da tafiyarsa kamar ta cikakken ɗan barni wayayye..

Da alama furucin Mairo a kaina ya shigi Umar sosai..duba da yadda ya haɗe fuskarsa kamar bai taɓa dariya ba.

Sammani kasa haƙuri ya yi, bayan ya tabbatar Saifi ya yi nisa, ya juyo ya na kallon Mairo fuskarsa a haɗe ya ce;

"Wai Mairo mecece matsalarki akan Hindatu da Umar ne eh? Yarinyar nan babu wanda ya san yanayin da ta baro gida, jiya haka kika zaƙe kina figarta kamar ɗiyarki, yanzu kuma ki na ƙoƙarin nuna masa bata da tarbiyya, wannan wace iriyar mummunar ɗabi'a ce haka? Gaskiya idan ki ka cigaba da yin haka, zamu samu gagarumar matsala da ke"

Dafashi Umar ya yi, ya ce;

"A'a Sammani, Mairo ta na gaskiya, ai da ina yi mata magana ina kallonta tana kallon abokinka, da alama tasa amsarwa take so, ba nawa ba..shi kuma naga kamar baya son mutane"

Sammani shiru ya yi, yana hararar Mairo, da alama ya fahimci ko ya yiwa Umar ɗin bayani ba zai fahimta ba.

Ni dai ina tsaye, ina jina kamar ba ni ba, kalaman Mairo nake ta haɗawa waje ɗaya, wanda tayimin akan Umar jiya da kuma wanda tayi yanzu.. 

Tsabar zurfin da nayi cikin lissafi, ban san sanda su Sammani suka tafi suka bar ni, da Mairo a tsaye ba..sai da ta dafo ni.

Hannuna ta kama muka ƙarasa muka zauna akan bencin dake ƙofar gidansu..

Mairairace muryarta ta yi ta ce;

"Hindatu ki yi haƙuri, na faɗawa Umar haka  a kanki ne, domin ya rabu dake, ba domin na ɓata ki ba"

A lokacin kaina sam ya kulle, don haka na ɗaga mata kai ina murmushi..

Itama murmushi tayi ta ce "yauwa ƙawata"

Miƙewa na yi ina karkaɗe rigata na ce mata zan je gida, kar na je Baba ya dawo da wuri, ya min faɗa. gobe zamu haɗu a makaranta.

Hannuna ta riƙo tana ƙurawa fuskata ido..ban yi ƙasa da nawa kan ba, nima  na ƙura mata ido da nawa idanun da damuwa ke kwance a cikinsu..

Kasa magana tayi har na ƙwace hannuna na fara tafiya..

Duk yadda na so  lallashi kaina kasawa na yi na fashe da kuka... A hanya na tsaya na yi wanda ya isheni, har sai da naji sauƙi a cikin zuciyata.. sannan na cigaba da tafiya.

Ko da na isa gida, na yi sa'ar Baba bai dawo ba, sai Inna da samu a tsakar gida, da Jamila a rumfa tana tankaɗen garin dawa..

Duk yadda na so ƙauracewa hira da Inna hakan bai samu ba..

Labaran duniya take ta bani ina murmushin yaƙe haɗe da bata amsa jefi-jefi can na jefo tambayar;

"Shin dagaske Saifi ba shi da uba, kudu mahaifiyarsa ta je aikatau ta dawo da cikinsa"

Baki ta kama kafin ta saki dariya tana cewa;

"Ke kuwa a ina kika samo wannan labarin? Ko ba Saifin gidan Fulanin ba?"

Har ga Allah ban san gidansu ba, amma gudun katsewar labarin na ce mata;

"Eh shi, abokin buga ƙwallon Sammani saurayin Mairo"

Dariya taƙara yi ta ce;

"Ai dama nasan ba zai wuce a bakin ƙawarki ki ka ji ba..batun Saifi ba shi da uba zance ne kawai, kuma uwarsa Zuhura ba tayi aikatau a kudu ba, gwamnati dai ta taɓa samar mata gurbin karatu a ƙasar ƙetare saboda hazaƙarta, kuma dama kowa yasan mahaifinsu ɗan boko ne mazaunin garin Kaduna..ritayarsa a aikine ya dawo da su gidan gandu da zama, a dalilin talaucewarsa da ake ta raɗe-raɗi

Kamar yadda na samu labari saboda nima lokacin aure bai kawo ni nan yankin ba, Zuhura ba ta dawo garin nan daga ƙasar ƙetare ba sai ɗan jaririn ɗanta, shine Saif kamar yadda suke kiransa..

Ga mu mutan gari dai, babu wanda yasan gaskiyar yadda Zuhura ta samo ɗanta Saifi..sai isu-isu danginta, sai kuma ƙananun maganganu da ke yawo a gari"..

Kai na jinjina mata ina murmushi..ban san me tayi niyyar faɗa ba domin tana buɗe baki Baba ya na yin sallama..

Sannu da dawowa nayi masa, ni da Jamila da ke cikin rumfa muka miƙe a tare domin karɓar kayan hannunsa..

Na riga Jamila isa gareshi don haka na haɗa ledojin hannunsa na amsa, da na juyo na bawa Jamila ɗaya na ɗauki ɗaya..

A ɗakin Inna muka ajiye.. Jamila ta dawo rumfa ni kuma na shige ɗakinmu...

Ban fito ba, sai da aka fara kiraye-kirayen sallar magriba.

Bayan na idar a ɗaki na ƙara zamana ni da Jamila muna taɓa hira..

Kamar a mafarki muka ji yaro a waje yana cewa;

"Assalamu alaikum wai ana sallama da Hindatu"

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol