Free chapter · Read without an account
11
*SASAAL*
***
11
"Idan kin koma gida, ki faɗawa Baba bakya son Umar a mayar masa da wayarsa, ke kin fi son kiyi aurenki ki zauna a ƙauye kusa da su, hankalinki sai ya fi kwanciya"..
Kafin ta kammala furta kalmanta tuni fushi ya lulluɓe zuciyata har ma da ganina..jikina har tsuma yake yi..
Hijjabinta na saki, na ƙanƙance idanuna ina kallon tsakiyar idanunta na ce;
"Yaushe zaki fahimci ba na ce miki a'a akan dukka muradanki da suka saɓawa nawa muradan domin mu dawwamar da amintar da ke tsakaninmu ne?
Ba zan bawa zuciyata damar tunani ba akan kalamanki Mairo..domin na fahimci kin fi son kullum ki ganni cikin tsumma.
Yau da ke ce kika samu miji mai wadata a birni mai daraja irin Kano da na fi kowa farin ciki..amma ke na lura har hana idonki barci kike yi.. saboda na samu miji ɗan birni.
Indai akan batun barin soyayyata da Umar ne, ki je na haƙura da ƙawancemu"
Ina gama faɗa, na fice na bar mata ajin.
Ni kaɗai na yi break.
Ko da aka dawo aji, ban ji nauyin zama a kusa da ita ba.
Babu wanda yayiwa wani magana a tsakaninmu har aka tashi..
Ana kaɗa ƙararrawa na ɗauki jakata na fita..
Ban tsaya jiransu Jamila ba, tun da dama can ba mu saba komawa gida tare da su ba nayi tafiyata..
Ina tafe ina tunanin halin Mairo, da alama Sammani jiya bayan sun bar wajena ya biya gidansu..tun da nasan labarin bai bazu a gari ba, balle na ce a bakin jama'a ta ji.
Wani sashen na zuciyata na rayamin abinda nayi mata shine daidai ne.
Wani sashen kuma na bani rashin gaskiya akan maiyasa bazan nutsu na auna kalamanta ba, wataƙila na tsinci wata gaskiyar a ciki..
Har na isa gida ban daina saƙe-saƙe ba.
Da sallama na shiga, lokacin Inna tana zaune a rumfa tana gyaran chitta..
Amsawa ta yi, tana cewa;
"Ai daman nasan sai ke, domin su Jamila, su da gidan nan sai sun gama gallafirunsu tukunna"
Dariya nayi, na ƙaraso cikin rumfar ina yi mata sannu da gida.
Bayan ta amsa, ban tsaya ta jani da hira ba, na wuce ɗakinmu..
Kayan makarantar jikina na sauya zuwa na gida..na ninke na makarantar na adana sannan na fito..
Inna tana hangowa fitowata, tace na shiga ɗakinta na ɗauko wayata na kunna..
Wani irin daɗine ya ziyarceni..ƙafafuna suna rawa na shiga ɗakinta..
A gefen gadonta na hango wayar, kamar wacce zata ɗauki fasasshen ƙwai haka na kai hannu na ɗauki wayar a hankali.
Karambani kunnata na fara yi, cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya kawo..
Haƙorana na washe ina kallon cikin wayar..
Tuna Inna tana waje kar ta ga daɗewata yasa na fito da sauri..
A ɗan nesa da ita na zauna, ina kallon wayar.
Ta kira sunana kenan zata yimin magana wayar ta fara ringing..da gudu na miƙe nayi ɗaki.
Ina jiyo dariyarta.
Ina shiga ɗaki na zauna a bakin katifarmu..ina kallon fuskar wayar, ja da kore na gani.
Na saka hannuna akan koren amma yaƙi ɗaguwa har wayar ta katse..ko sakan ɗaya ba'ayi ba aka ƙara kira.
Akan ja na ɗora hannuna, shima dai har wayar ta gama ringing bai ɗagu ba..
Tsoro da kunya ne suka kamani..gashi babu Sammani akusa balle ya koya min..
Inna ma ba iyawa tayi ba, domin ko Baba mai tocila ce a hannunsa.
Ina nan zaune cikin tunanin aka ƙara kira..
Kan koren na ɗora hannuna, sai nayi hikimar jansa gefe.
Ai kuwa sai ga muryar Umar nan yana sallama..kamar yana kusa dani haka na saka tafukan hannayena na rufe fuskata.
Sai da ya ƙarayin sallama a karo na biyu sannan na amsa..
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce;
"Gaskiya Hindu kin sani cikin fargaba, tun jiya nake jkiranki amma shiru wayar a kashe..
Anyway Ina fatan kina lafiya?"
Gaishe shi na fara yi, ya amsa yana tambayata yaya su Baba na ce masa lafiya ƙalau..
Cigaba ya yi da tambaya makaranta da ƙawata Mairo..dukka na amsa masa da lafiya ƙalau.
Fara ja na yayi da hirar yaya nake jinsa a raina..shiru nayi ina dariya.
Bai matsamin ba, ya ce na huta, tunda na ce masa yanzu na dawo daga makaranta anjima zai kirani..don haka na shirya amsa tambayoyinsa.
Sannan Idan an kawo wuta na saka wayar a caji..
Ban yi ƙasa a gwiwa ba, na gayamasa bamu da kalar chajar wayar a gidanmu.
Ɗan dariya ya yi, ya fara ba ni haƙurin mantawa yayi da chajar bai sako ba.
Amma zai kira Sammani a waya yasa ya kawomin anjima, ya kuma koyamin yadda zan yi amfani da wayar. Kafin ya siyomin sabuwa dal a kwali idan zai ƙara dawowa.
Da zamu yi sallama sai da ya ce min yana so na turanci..
Ko da ya katse kasa tashi na yi, sai murmushi da nake ta yi, ina shafa gefen fuskata saboda daɗi..
Kamar mara gaskiya haka na taso na fito tsakar gida..
A daidai lokacin su Jamila suka yi sallama.
Duk da haka Inna bata ƙyaleni ba, sai da ta tsokaneni da na zo na bata labarin hirar da muka yi da Umar.
Surutunsu Jamila ne ya ɗauke mata hankali, har na ci abinci na yi wanka na koma ɗaki ba ta bi ta kaina ba.
Tunawa da maganar Sammani zai zo kawo min chaja, ya sa bayan na idar da sallah na fito na sanar da ita..sannan na ƙara komawa ciki.
Ko cikakken minti biyar ban yi ba, barci ya ɗaukeni.
Ban farka ba, sai da Inna ta tasheni lokacin anfara kiraye-kirayen sallar la'asar.
Daƙyar na miƙe saboda yanda jikina ya mutu, na fito tsakar gida na kama ruwa nayi alola..na koma ɗaki.
Ko da na idar kwanciya na yi, ina jiran zuwan Sammani, saboda na san ba zai zo da daddare ba..
Har na fara wani sabon barcin daga kan sallayar da nake kishinkiɗe, Inna ta ɗago labulen ɗakin tana cemin na fito Sammani ya na ƙofar gida..
Bata gayamin wacce Sammani ya aiko ba, sai da na fita na ganshi da Mairo a tsaye, ta ci ado cikin atamfar ledar da dangin mahaifiyarta ba sa rabo da ɗinka mata su.
Sammani kawai na gaisar na juya mata baya kamar ban ganta ba.
Murmushi Sammani ya yi ya ce;
"Da alama Mairo tayi miki halin na ta kenan"
Kawar da zancensa na yi, ta hanyar tambayarsa ya mutan gida.
Amsawa ya yi ya ɗora da faɗin;
"Ke Mairo me kika yiwa Hindatu na ga ta ƙi yi miki magana, nasan da wahala idan laifinta ne"
Kamar jira take yi sai ta fashe da kuka tana cewa;
"Domin Allah saboda na bawa Hindatu shawara kar ta kula Umar tayi aure ta zauna a kusa da iyayenta sai ta fi samun gata, shine zata ce ina yi mata hassada..har da gayamin maganganu marasa daɗi..
Yanzu ni ga bani ba, ai kai zan aura, kuma wallahi ko wani ya zo daga birni ba zan iya auransa ba, ya je yayi ta ganamin azaba"
Ta ƙarasa faɗa tana rushewa da kuka.
Wani malalacin murmushi mai cike da ma'anoni sammani ya yi ya ce;
"Mairo kenan! Ni dai abinda zan gayamiki shine ki kiyayi wannan zuciyarta taki, ki koyi sarrafata..ban da abinki Shi Allah ina ruwanSa, wataƙila duk wannan abun da kikewa Hindatu ba rabon Umar ba ce, rabon wani hamshaƙin Attajirin ce, da zai fitar da ita daga ƙasarmu baki ɗaya ba ma iya Kano da kika ce ɓatawa kanki lokaci akai ba..
Duk don na gwada hankalinki yasa tun a dare jiya na yi miki bayanin komai, a yanzu ma, saboda ina so nasan haƙiƙanin abinda kika aikata mata a Makaranta yasa na taho da ke..
hmm Maryam(mairo)! Ki ji tsoron Allah, ki sani abotarku da Hindatu ba shi da farashi, samun irinsa zai yi wahala a gare ki.
Idan kin ɗauki shawarata kanki, idan ma baki ɗauka ba kan ki"
Ya na gama faɗa ta taho ta rumgumeni tana ba ni haƙurin..sharrin zuciya ne, kuma ita bata furta kalamanta don tana da wata muguwar manufa a kaina ba
Nima a take zuciyata ta karya na kamo fuskarta ina share mata hawayenta..
A nan dai Sammani ya shiryamu..na karɓi chajar muka shigo gida tare da ita domin ganin wayar da Umar ya ba ni..
Ban san zuciyar Mairo ba, amma a zahiri dai ta nuna farin cikinta matuƙa, har da cemin ita ma Sammani ya ce zai siyamata irinta mu yi anko..
Bata jima ba, na rakota ƙofar gida, saboda Sammani da zai koya min wasu abubuwan da ban iya ba, a cikin wayar.
Cikin hikima Sammani ya nunamin abubuwa a cikin mituna da ba su wuce goma ba, kuma nayi sa'a babu abinda ban fahimta ba.
Ban koma ciki ba, sai da na ga tafiyarsu, ina ɗagawa Mairo hannu, itama tana ɗagomin har suka sha kwana.
Daga zuwansu Mairo da tafiyarsu, ƙwarai na lura da sauyin fuskar Inna, sai dai bata ce min komai ba.
Da dare ya yi, bayan munyi sallar Isha'i Umar ya kirani..
Mun fi hour ɗaya muna waya, tun ina noƙewa har na saki jiki, na gayamasa yadda nake ji a kansa..
Sai ƙarfe goma saura muka yi sallama, ya ce na kwanta saboda zuwa makaranta gobe...
★washe gari, bayan mun gama shiryawa, da yake lokaci bai ƙure ba, sai da na biyawa Mairo..
A tare muka jero ina bata labarin yadda Umar yake gayamin kalamai masu daɗi..
Sam ban lura da yadda take jeromin tambayoyi ba, sai na gama bata amsa tukunna sai na ji dama ban faɗa ba..
Kamar wasa daga wannan rana Mairo ta ƙara jana a jiki, da zarar mun zauna ba ta da hirar da ya wuce na Umar, tana tambayata ina bata amsa.
Ranar da ya kama ranar asabar, da sassafe ƙanin Mahaifiyata da saƙon bata da lafiya..rai a hannun Allah...
Baba bai nuna alamar fushi rashin nemana da bata yi ba, ya cewa ƙanin mahaifiyarta tawa, In sha Allahu anjima zai shiryani na zo na dubata.
Bayan tafiyarsa, ina jiyo muryar Baba da Inna suna rigama ƙasa-ƙasa kan ta yarda mu tafi tare da Jamila, ita kuma ta ce sam bata san zancen ba, ba zata tura ɗiyarta inda hankalinta ba zai kwanta ba..
Duk yadda Baba ya yi da Inna haka ta murje idanunta ta nuna bata san zancen ba, har da ce masa ai yana da ƴaƴan ƴan uwa, yaje ya tambayesu..
Da gangan ta faɗi haka, saboda ta san yadda dangin Baba suka tsani mahaifiyata a dalilin watsin da tayi da ni..
Ina jin alamar fitowar Baba nayi maza na kulle idanuna a tunani ɗakinmu zai shigo, sai da na ji alamar takunsa ya yi hanyar waje, sannan na buɗe idanuna na tashi na zauna..
Ashe da Baba ya fita, gidansu Mairo ya nufa ya roƙi alfarma a wajen mahaifinta kan zata rakani ƙauyensu Mahaifiyata kwana ɗaya kawai zamu yi, mu dawo washe gari..
Sai da ya dawo gida ya shigo ɗakinmu yake ba ni labari, sannan ya ɗora da nayi maza na shirya, kar dare ya yi mana.
Duk da dai Yankin na su ba shi da nisa da namu, kuma gidansu sananne gidane domin ƙanin kakana shine Sarkin noman Yankin..
Baba ya na barin ɗakinmu na tashi na shirya a gurguje, cikin sabuwar atamfata ta sallah, na ɗauki jakar makaranta ta, na zuba kaya kala ɗaya, sannan na saka wayata a gefen kayan.
Tsakar gida na fito rataye da jakata.
A rumfa na hangosu a zaune, Baba yana cin soyayyiyar gyaɗa, Inna kuma tana tankaɗen gari tuwo..
Ƙasarawa na yi, na tsugunna ina yiwa Inna sallama, ba yabo ba fallasa ta amsa ta na cemin na yiwa mai jiki sannu.
Baba hannu ya zura a aljihun wandonsa ya fito da kuɗi ya miƙamin, yana cewa na kawo wayata ya sakamin lambarsa, idan mun kai can na kira shi.
Jakar bayana na zamo na ciro wayar na miƙa masa ya sakamin lambarsa, ya miƙomin na yi saving..
Har na tashi na bar gida, ina jiyo shi, yana yi min addu'ar tsari kala-kala..
Cike da zumuɗi na nufi gidansu Mairo..
Abinda ya bani mamaki kuma ya tsinkarmin da zuciya shine yadda na ga Mairo take nuna wani irin zumuɗin da sam ban san ta da shi ba..kamar ba dubiya zamu je ba.
Kasa haƙuri na yi muryata a sanyaye na ce;
"Wai Mairo zuwa ƙauyensu Innar tawa dubiya kike yiwa wannan zumuɗin?"
Idanunta ta juya ta ce;
"A'a Hindatu kawai dai ina farin cikine Umar zai kiraki da daddare a gabana, na ji irin kalaman da kike bani labarin yana gayamiki..
Ina fatan dai kin sako wayar a jaka?"...✍🏻