Free chapter · Read without an account

21

by Nafisa Aliyu Sasaal · FARASHIN ABOTA

*NAFISATU_SASAAL*
      ***


21

Kalmar "karki wahalarmin da kankin" da ya furta, tuni ya wargaza min lissafi, na ji kamata ya yi na tura masa dubu uku ya ci abincin kwana biyu.

Da ya ji nace zan tura masa dubu uku, ya yi manejin kwana biyu da shi, sai ya ƙara marairaice muryarsa ya na cewa;

"Na gode rabin raina, Allah Ya barmu tare, gaskiya na yi kuɗi dole ki ji daɗi"

Tsabar daɗi ban san sanda na saki dariya ba..

Kaf tunani ba ya bani cewar mutane suna iya furta kalmar da ba shi ne a cikin zuciyarsu ba..

A hasashena tunanin kowa da zuciyar kowa kamar nawa yake..domin ni idan ina son abu ba na iya ɓoyewa, haka idan na tsaneshi ko ina jin tsoronsa ko ba na ji..duk ba na iya ɓoyewa..shiyasa tunanina ya bar kan batun Fatima, na saki jiki na ƙarbi soyayyar Sammani da hannu bibbiyu.

Haka muka yi sallama, yana ta lallaɓani da kalamansa masu daɗin gaske.

Hijabina na saka, na je maɓoyar kuɗina na ɗauki dubu huɗu, na fito tsakar gida.

 Lokacin Inna tana cikin rumfa tana ƴan aikace-aikacenta jefi-jefi tayi magana ita kaɗai, domin ita sam ba ta yarda da zama shiru ba a rayuwarta..

Ƙaryar zan je siyo awara na yi mata..

Ina fita na fara zuba sauri kamar zan tashi sama..

Ina kan hanya Sammani ya turamin da lambar asusunsa.

Cikin ƙanƙanin lokaci na isa bakin kasuwa, hijabina na janyo na rufe rabin fuskata..na nufi shagon me tura kuɗi.

Ina jin ya ce ya tura, na matsa gefe, na dannawa Sammani kira, bugu ɗaya ya ɗauka.

Tun kafin nayi magana  ya fara zubomin wasu irin godiya, har sai da na dakatar da shi ina dariyar jin daɗi..

Daga wannan rana soyayyarmu da Sammani ya zama abun burgewa, kullum da safe sai ya turomin saƙo, na kula masa da kaina, kuma nayi wanka na ci abinci.

A cikin sati ɗaya muka yi wani irin shaƙuwa..ba na iya wuni ban ji muryarsa ba..

Sau biyu ina zuwa gidansu Fatima a cikin satin, kuma kullum idan na je sai ta jamin kunne na kula, kar na saki jiki da Sammani..

Kalamanta a matsayin na Mairo nake kallansu, domin nasan da kunya Sammani ya dawo daga baya ya ce baya so na...

A cikin sati na biyu da tafiyar Sammani na tura masa katin waya ya fi a ƙirga..

Bini-bini sai ya sako hirar ba shi da kati ko ba shi da abinci, ba ya roƙona kai tsaye, sai dai cikin alaye..Ni kuma jikina yana rawa nake tura masa..yana sakamin albarka.

A wani yammaci wanda ya yi daidai da wata ɗaya da tafiyar Sammani..ya kirani a waya, yake shaidamin Saifi ya dawo, yanzu yawan wayarmu zai ragu, saboda ya ce zai kai shi makarantar koyan na'ura mai ƙwaƙwalwa, domin ya sama masa aiki mai tsoka a ƙaton shagon siyar da kayayyakin amfani, sannan zai cigaba da samun horo a harkar ƙwallon ƙafa..

Ba ƙaramin farin ciki na ji ba, har na fara hasashen wahala ta kusa yanke mana, na yi aure nima na tara kuɗi su Inna su ji daɗi..

Idan ban yi ƙarya ba sai na ce daga wannan wayar Sammani sai da ya yi sati bai kirani ba, sai dai ni na saka kati na kirashi.

Muna cikin haka jarabawarmu ta fito..na Fatima ya yi kyau, nawa kuma sam bai yi kyau.

Nasha kuka har sai da na daina gani da kyau..ba irin lallashin da Inna da Fatima ba su yi ba, amma na kasa yakice abinda a cikin raina..

Ban samu sauƙi ba, sai da Fatima ta kirani a waya ta haɗani da mahaifiyar Saifi, ta kwantar min da hankalin na yi haƙuri, shekara mai zuwa zata biyamin na je Dutse na zana inda zan fito da sakamako mai kyau..

Da na gayawa Inna da Baba, Baba cewa ya yi gobe Inna ta shirya muje tare mu yi musu godiya..

★haka kuwa akayi, washe gari, tare da Inna da muka je, sai da muka yi kusan hour biyu a gidan, su na jan Inna da hira.

Bayan mun dawo gida, batun damuwa akan faɗuwar jarabawata ya kau a raina..sai kuma tunanin Sammani da daɗaɗan kalamansa..

Rashin samun nasarar Jam ɗin Fatima, yasa itama dole aka dakata da nema mata gurbin karatu, sai ya zamana kusan kullum idan bata gidanmu ina gidansu..

A cikin kwanakin da suka biyo baya, idan na kira Sammani baya ɗauka, sai washe gari  zai kirani ya na bani haƙurin aikine ya riƙeshi, abubuwa sun yi masa yawa..shima yana gama bayaninsa zai min sallama ya ce yana zuwa, daganan ba zai ƙara kirana ba, sai idan ni na kirashi..

A hankali abun ya fara damuna, har hakan ya fara shafar walwalata..

Kamar wasa, watanni biyar suka shuɗe muna haka da Sammani yau da daɗi gobe babu..da yake kuma ina neman na kaina ban taɓa cewa ya bani kuɗi ba.. shima kuma bai taɓa yimin kyautar kati ba.

Ban taɓa kallon hakan a matsayin gazawa ba, sai wataƙila shima ba shi da shine.

Fatima ce ta fara lura da sauyina, ko da ta tambayeni ce mata nayi babu komai..duk da haka bata fasa yimin faɗan kar na lalata farin cikina saboda mutumin da ban san rayuwar da yake yi a can ba..

A haka muka cigaba da tafiya, kullum Sammani ya na bani uzurirrikan da nake saka ran akwai ranar wucewar su..

Domin a zahiri shi bai ce min baya so na ba, kuma bai daina tunamin ni tasa ba ce, sai dai a zahirin gaskiyar na da ƙi ƙarɓa shine; Sammani bai shirya ajiye a matsayin da yake ikirari na Uwar ƴaƴansa ba.

********************************************
Cikin ikon Allah shekara ta zagayo, Ƙanin Mahaifiyar Saifi, Mahaifi ga Fatima ya biya mana jarabawar Jam ni da ita..

A wannan karon Baba da kansa ya yi tattaki har gidan shi da Inna suka yi musu godiya..anan suka ƙara nusantar da shi, muhimmancin yin ilimin ga ƴa mace.


A na saura kwana ɗaya jarabawa Mahaifin Fatima da kansa, ya kai mu dutse muka kwana.. washe gari ya kai mu wajen zanawa.

Haƙiƙa nasha wahala, na kuma ji kunya, domin daƙyar da ƙwarin gwiwar son cika muradina na iya sarrafa na'urar zana jarabawar da aka nunamin..

Sai da muka fito nake bawa Fatima labari..ai kuwa garin dariya har da faɗuwarta.

Ko da muka dawo ƙauye na kira Sammani na gayamasa ba ƙaramin farin cikinsa ya nuna ba, har da cemin;

"Yanzu ya ƙara samun nutsuwar mallakata a matsayin abokiyar rayuwarsa"

Ranar har sakin jiki ya yi muka sha hira.

Cikin ikon Allah da jarabawar Jam ta fito, Fatima ce tayi nasara ni ban yi ba, ai kuwa nasha kuka, saboda kulle kaina na yi a ɗaki nayi ta kukan wataƙila ba ni da rabon yin boko ne, shiyasa ba na yin narasa a jarabawa.

Kamar dai waccen shekarar haka Fatima da ƴan uwanta suka ƙarfafeni akan In sha Allahu Idan na zana Wa'ec da Neco wannan karon zan yi nasara.

Washe garin ranar, muna zaune a waje ni da Inna, Jamilu ya shigo da labarin ga ƙatuwar mota can ta sauke Mairo..ciki ne ma da ita.

Inna fuska tayi kamar ba ta ji shi ba, nima ban ɗago daga abinda nake yi ba, dole haka ya haƙura ya fita..

Kamar jiran fitarsa Inna take yi, ta fara masifar Allah Ya sa ta ga ƙafar Mairo a gidan nan, wallahi sai ta yi mata rashin arziƙi..

Ai kuwa kamar Inna ta sani, ko minti talatin ba ta yi da rufe baki ba, yaro ya yi sallama..wai Mairo ta ce, a kira mata Hindatu..

Kafin ya ɗora da bayani na gaba, Inna ta ɗebi ruwan mai tsanin sanyi da ya kwana a waje, Kasancewar lokacin sanyi ya fara shigowa ta watsa.

Banƙarewa yaron ya yi ya saka ihu ya fita a guje.

Dariyar mugunta ta kwashe da shi..ta ce;

"Ɗan banza gobe ka kuma"

Nima kasa daurewa na yi, na saki ƴar dariya ina cewa;

"Inna to ai ba shi da laifi, aiko shi fa akayi"

Ɗan dariya tayi ta ce;

"Na fi so, ya je ya gayamata na watsa masa ruwa, wataƙila zuciya ta ciyota ta biyo bayansa, tunda ta auri mai kuɗi, anan zata san ba ni da kirki"

Dariya kawai na yi, ban ce komai ba.

Tun Inna tana jiran zuwa Mairo, har ta gama aikinta shiru..dole haka ta haƙura ta shige ɗaki domin hutawa...

A daren ranar ma haka na  zauna jiran kiran Sammani amma shiru, har barci mai nauyi ya ɗaukeni..

★washe gari a bakin Jamila na ke jin labarin wai ance Mairo haihuwa ta zo yi gida..wai har gyaramata ɗakinta akayi.

Mamakine ne ya kamani sai dai ban ce komai ba.

A ganina anya ba matsala Mairo ta samu da Khalil ba kuwa, banda haka wa take da shi a ƙauye da zata baro birni wai ta zo haihuwa?

Ina nan zaune shiru Fatima ta shigo da murmushi kwance a saman fuskarta..

Dole nima na saki tawa fuskar ina tambayarta yau da alama tana cikin farin ciki.

Fararen idanunta ta juya ta ce;

"Albishirinki?"

Ɓata fuska na yi, na ce;

 "Don Allah ki gayamin, ba na son wulaƙanci" na ƙarasa faɗa ina dariya..

Dariya ta ɗan yi tace;

"Jibi Yaya Saif da Sammani za su zo hutu, kin ga wataƙila yana dawowa a saka ranar aurenku, tun da shima yanzu ya kama ƙasa"

Dariyar jin daɗi na saki, ina rufe fuskata😅..✍🏻

Yaya kuke kallon haɗuwar, Sammani, Hindatu, Mairo da Saifi a ƙauye ɗaya?

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol