Free chapter · Read without an account
Chapter 9
SULTANIM
Na
Mss Samher
Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher
Page9
“Mstwwww ke kika ga wani kyan yabawa anan, yarinya a koɗe uwa bararoji.” Umma tafaɗa tana hararan Maijidda.
Cikin darinyan ƙeta Maijidda tace
“Aa Sa’adatu batun yarinya a koɗe ma bata taso ba, saidai kawai idan baki san gaskiya, danma banda ɗa namiji ai dani kuka turo ma ita.
Murmushi mai sauti Umma tayi jin tasamu mafita a zancen Maijidda.
Tana shiga ɗaki tayi wanka sannan tayi sallan la’asar.
Bata cika san kwanciyan bayan la’asar ba saboda baba ya hana ta, amma gajiyan datayi yasa bata da wani mafita bayan haka.
A hankali abubuwa suka fara dawo mata, tunanin iyayanta da tsananin kewarsu dake damunta, ga rashin sanin ina rayuwanta ta fuskanta kai tsaye,
Da irin wannan tunane tunan bacci yayi gaba da ita.”
Batasan tsawan lokacin data ɗauka tana bacci ba, sai kawai taji ana kiran sunan a hankali.
“Nadrah… Nadrah ki tashi.”
A firgice ta buɗe idonta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar wanda aka tsoratar. Ta ɗago kai taga Talatu tsaye a kanta.
“Kin jima kina bacci, tashi kiyi salla kizo kici abinci.”
Ƙarfe takwas da rabi data gani a agogo yasata goge ido da sauri ta mike tana faɗin
“Ko magrib banyi ba.”
Saida tashiga banɗaki sannan Talatu tafita.
Koda ta idar kitchen naje kamar dai dazu sai da Talatu ta tabbatar taci abinci kafin kowa ya tafi ɗakinsa.
Abuja
Daga bakin parlorn ake sallama, batare daya duba gun ba yace
“Ya salam, malan idan zaka shigo ka shigo duk ka cikamin kunne ko da ƙarfi kakeso na amsa.”
Yana dariya ya ƙaraso cikin parlorn, a kujeran dake kallon na Faruq ya zauna.
“Ya akayi?” Faruq ya tambaya yana hararanshi.
“Kaifa baka da mutunci wallahi. bazan zo wajanka ba saida wani abu.”
“Oho sanin hali ne.”
“Sagir yaji dadin ganinka wajan ɗaurin auransa, atlist kana leƙawa once in a while zaka dinga haɗuwa da mutanan daka ɗaɗe baka gani ba.”
“Nace maka ina ɓukata, shi kuma sai wani dariya yakeyi kamar a kansa aka fara aure” ya ƙare faɗa yana jan guntun tsaki.
Hisham ya kwashe da dariya yana faɗin
“Kenan kar yayi dariya a rana mafi muhimmanci a rayuwarsa, kace kai ranan bikin naka wannan fuskar zaka cigaba da nunawa, nima aure zanzo nayi dan maganan gaskiya nagaji.”
Dagowa Faruq yayi yana kallonasa da kyau kafin a daƙice yace
“Da chan waya hanaka.”
“Nifa tausayinka nakeji mutumina, saboda inayin aure ko bakaso saina kiraka gauro.”
Mikewa yayi tare da saka wayarshi a aljihun wandonsa yana faɗin
“Wallahi ka ishe ni, tashi muje kawai.”
Yana gaba Hisham na binsa a baya da dariya ƙasa ƙasa suka fice.
Motar Hisham suka shiga, Hisham dake zaune a mazaunin driver yace “Ina muka nufa?”
Kafaɗarsa ya ɗage yace
“I have no choice.” Murmushi Hisham yayi ya tada motan suka bar gidan.
Millennium Pack,Abuja.
Wuri ne mai kyau matuƙa, da zarar ka shigo wata iska mai sanyi da ni’ima suke fara maka baraba.
Wannan iskar tana ɗauke da ƙamshin furanni da ciyayi, tana cika zuciya da annashuwa.
Bishiyoyi masu tsayi da faɗadden rassan ganye sun shimfiɗa inuwa a ko’ina, hasken rana yana ratsawa ta cikin ganyayyaki, ya faɗowa ƙasa a hankali.
Akwai sassa daban daban a cikin pack ɗin, gurin shiru babu hayani sai sautin tsuntsaye da kaɗawar iska dake ƙarawa wajan salama.
Millennium pack wuri ne dake sa mutun ya manta da hayaniyar duniya, ya natsu cikin tunani da nishaɗi, zuciya ta samu hutu rai ya samu walwala.
A hankali Faruq kebin wajan da kallo fuskanshi ɗauke da murmushi.
Ƙarkashin wata babbar bishiya suka zauna Faruq yace
“Wani lokaci mutun yana buƙatar wuri irin wannan, Kudos man.”
“I no you will like it mutumina.” Hisham ya faɗa yana murmushi.”
Mutanan dake wajan kowa harkan gabansa yakeyi, mafi yawa samari ne da yammatansu, sai ɗaiɗaikun dalibai da sukazo karatu.”
Sun ɗau lokaci sosai a wajan dan Faruq ƙin tashi yayi har saida sukayi magrib a wajan sannan suka tafi.”
A gate Hisham ya ajiyesa sannan shima ya wuce gida.
Mami na zaune kan darduma da daddare bayan idar da sallan isha’a ta dade tana addu’a sannan ta miƙe, a gefan gadonta ta zauna ta ɗauko wayanta ta kiran kanwarta Halima wato Aunty mama.
Bayan sun gaisa Mami tace
“Akwai maganan da nakeso muyi dake mai muhimmanci, kiyi ƙoƙari kishigo idan kin samu lokaci.”
Auntie Mama tace “zanzo gobe in sha Allah.”
“Tohm Allah ya kaimu”
Da “Amin” ta amsa sannan sukayi sallama.
Da wuri Faruq ya shirya tafiya office da safe saboda yana da meeting da shugaban ma’aikatansu dake Kaduna akan aikin Baffa.
A waya ya sanar da Mami shi yafita amma zai dawo zuwa anjima yayi breakfast.
Da misalin ƙarfe tara na safe suna zaune a cikin ɗakin taron dake company ɗin.
A natse Faruq ya dubi mutumin dake hannun hagunshi yace
“MK Aiki tare daku yana ƙara mana zumma, kamar ko yaushe ina fatan karku bamu kunya.”
Cikin girmamawa MK yace “In sha Allah Sir, bazaka samu wata matsala daga garemu ba.”
“Cikin watanni uku zuwa huɗu mukeso a kammala, Hisham zai ɗinga zuwa yana dubawa lokaci zuwa lokaci, kafin nima nazo.” Ya ƙare faɗa yana miƙa masa document ɗin daya kama.
“In sha Allah Sir.”
“Shikenan idan babu wani abun inaga zan iya tafiya.”
“Muna godiya Sir, Allah ya kara girma.”
Office ɗinsa ya koma yabar Hisham dasu ya ƙarasa sallamansu.
Misalin ƙarfe sha ɗaya daidai Auntie mama ta iso, sunyi kama sosai da Mami saidai Mami ta ɗan fita haske.
Bayan sun gaisa Auntie Mama tace
“Adda kinsa sai tunani nakeyi, ina fatan dai lafiya?.”
Mami tace “Lafiya ƙalau sai Alkairi, kayan lefen yaronki nakeso mu zauna ayi listing, sai muga da wanne zamu fara .”
“Bangane yarona ba, yaushe Faruq ɗin ya samu matar Aure bansani ba.”
“Befa samu ba, mune dai zamu aura masa.”
Auntie mama ta kwashe da dariya tana faɗin “Dama anama namiji auren dole ne.”
“Za’a fara akan Umar.”
Nan Mami ta kwashe komai tafaɗa mata sannan ta ƙara da cewa
“Wallahi Halima tunda naji labarin yarinyan nan kullun sai nayi addua akai kuma batun yana ƙara kwanciya min a rai.”
“Hakane Adda, amma kina ganin babu matsala.”
“Eh in sha Allahu…. Shiyasa na kiraki akan maganan lefen dan ina fatan kada suja lokaci.”
Sauke ajiyar zuciya Auntie mama tayi tana faɗin
“Shikenan wannan ba matsala bane, ƙanwar baban su Hanifa sana’arta kenan, haɗaɗɗun kayan lefe take haɗawa iya kuɗinka dayawan kayanma daga turai dake kawosu.”
“Tazo gidan sauƙi, na bar maki wannan a hannuki.”
“Angama Adda.”
Saida akayi sallan azahar Faruq ya samu sararin tafiya gida.
Ɗan kuntun murmushi
akan fuskansa ya ƙarasa parlorn yana faɗin
“Auntie mama barka da zuwa.”
“Ango kasha ƙamshi.”
Ido suka haɗa da Mami tayi mata alama da sauri ta waske tana cewa “Yawwa Umar, kana lafiya ya office?”
Basar da wanchen maganan shima yayi ta hanyar faɗin “Alhamdulilla.”
Mami ta kira Abu akawo masa breakfast tunda tasan abinda yadawo ci kenan.
Wajan ƙarfe ɗaya da rabi su Zahra suka dawo daga makaranta sunji daɗin ganin Auntie mama sai murna sukeyi Zaina tace
“Auntie mama ya bakizo dasu dasu Hanifa ba?”
“Kin manta suma suna school, amma nace a kawosu nan kawai daga chan.”
“Yes” Zahra da Zaina suka faɗa lokaci ɗaya.
Faruq kam yana gama cin abinci yama Auntie Mama sallama ya fice, gara ya koma office daya zauna yaran nan suna haɗuwa cika gidan da hayani zasuyi.
Ƙarfe biyu dayan mintuna driver ya sauke su Hanifa a haraban gidan, yammata ne biyu bazasu wuce sa’annin su Zahran ba, tun kafin su shigo parlorn suke ihu, kallon da Auntie mama ta musu yasa duk sukayi shiru suna raba idanuwa.
A hankali suka ƙarasa suka gaida Mami ta amsa tana tambayarsu ya school, suka amsa da “Lafiya Alhamdulillah.”
“Ameera ku shiga suna ciki, kuyi wanka kufito kuci abinci.”
Tura ƙofar ɗakin sukayi tare da buɗe hannayansu suna faɗin “Here we are.”
Rungume juna sukayi suna dariya.
Ƙaramin party sukayi yau a gidan Mami, danma Auntie mama bata ɗaukar shirme.
Sai ƙarfe tara sannan suka bar gidan.
Yau saura kwanaki biyar su Abba su dawo, kullun Umma bata yini a gida idan ta fita da safe sai chan yamma take dawowa, Nadrah ta barwa gyaran ɓangaran Abba ita kuma Talatu ta gyara na Mahmud.
Basu san ina take zuwa ba saidai sun lura ta ƙara kyau fatanta na wani sheƙi na musamman.
Ƙarfe sha ɗaya jirginsu ya sauka a Nnamdi Azikiwe Internation Airpot.
Baffa ne yaje Abuja dauko su.……