Free chapter · Read without an account

66

by Halima Zakariyya Haruna · LULLUƁIN BIRI

Washe gari, kamar yadda Baffa ya shirya, haka abin ya kasance.
Tun a yammacin ranar jiya, ya tafi gidan Hakimi tare da Turaki.

Bai je da nufin ayi ta gardama da maimaita magana ba, balle ya je ya tilasta wa ɗan uwansa yin wani abu a kan auren. Abin da ya kai shi gidan shi ne ya fita haƙƙin zumunci. Ya sanar da wanda ya dace abin da ya faru, ya kuma ba su damar jin maganar daga bakinsa kafin ya yanke hukuncin tarewar yarinyar.

Amma tun kafin ma Baffa ya gama bayanin komai, ran Hakimi ya gama ɓaci.
Ya kalle shi da wani irin kallo mai cike da takaici, kamar abin da yake ji bai tsaya kan auren ba ne kawai, yana jin an taɓa masa wani wuri na izza da darajar gidan da suka fito.

Ya zauna yana kallon Turaki na ɗan lokaci, sannan ya janye idanunsa zuwa ga Baffa. Fuskar sa ta nuna ɓacin ran da bai tsaya kan fushinsa ba kawai, fushin da ya taso daga abin da yake ganin an yi wa suna, matsayi da darajar gidansu.

"Dukko! Wannan abin da Turaki ya yi, ya wuce abin da zan iya kallonsa in ce shikenan."

Ya girgiza kai.

"Kawai ya raina mu ne. Ya yi watsi da tarbiyyar da muka yi masa. Ya wulaƙanta darajar zuri'ar mu. Matsayi, nasaba, asali. A ƙarshe ma ya rasa wadda zai aura sai ya je ya ɗauko mana ƴar ƙanan mutane?"

Baffa ya yi shiru. Hakimi ya ci gaba da faɗa sosai.

"Banda Ɗanka mutumin banza ne, ba ya ganin cewa yana da Manya. Ya yanke hukunci shi kaɗai, sannan ya zo mana da rashin hankalin da ya riga ya gama aikatawa saboda bai ganinmu da gashin ido?"

Baffa ya numfasa.

"Idan ka nutsu da kyau zaka fahimce shi..."

Hakimi yaja tsaki yana kauda kallonsa daga kan Baffa. Ya kalli Turaki kai tsaye.

"Ka san kai ɗan wane ne kuwa? Ka kuwa san daga tsatson da ka fito Turaki?"

Turaki ya yi shiru. Har lokacin bai iya jin cewa komai.

"Ka san irin girman mutanen da kake ɗauke da sunansu a bayan na ka? Ka manta da yadda duniya take kallon girmanmu, Martabarmu da darajarmu?"

Ya ɗan yi shiru, sannan ya juya zuwa ga Baffa.

"Dukko mu ƴan manyan gida ne. Duniya ta san mu, ta san tarihin zuriyarmu. Amma Ɗanka ya nemi ya ɓata mana suna da martaba. Allah wadaran naka ya lalace."

Ya sake kallon Turaki. Ya yi wani irin murmushin takaici.

"Duk da ace auren da ka yiwa kanka Ƴar gidan Manyan mutane ka aura. Da abun ya zo mana da sauƙi. Ba mu kaɗai ba, hatta kanka ka wulaƙanta a idon duniya, aurenka kuma ba zai yi albarka ba sam."

Turaki ya ɗan motsa a zaune, amma bai ce komai ba, kalaman sun masa zafi, amma yana jin kamar an danne shi daga yunƙurin yin komai. Hakimi ya ci gaba. Yana nuna Turaki da hannu.

"Wallahi ka gama ma rainamu. Da kana ganin muna da daraja a idonka, da ba zaka yi mana wannan abun kunya da tozarcin ba. A baya da alfahari na ke faɗawa mutane kai Ɗana ne, ɗan ɗan uwana. Amma a yanzu ina jin kunyar ma na ce kai jinina ne."

Baffa ya yi ƙoƙarin saka baki. Hakimi ya dakatar da shi da sauri.

"A'a Dukko. Na ji abin da ya isa na ji. Abin da nake so kai da shi ku sani, shi ne, bamu da sa hannu a lamarin auren nan ta kowacce siffa."

Sai ya kalli Baffa ransa na ƙara ɓaci da jin takaicinsa.

"Abin da ya fi ba ni mamaki da haushi, shi ne kai da kanka ka zo kana neman ba shi kariya. Bayan ka san laifin da ya aikata mai girma ne. Da ace cikin Yarana ne, wallahi tallahi sai na sa an ɗaure min yaro. Domin ban haifi ɗan da zai wulaƙanta ni ya tozarta ni ba. Da mutuncinmu a gari, ace yaje ya yi wa kansa aure babu saninmu? Sannan ya auro ɗiyar wanda bai san kansa ba? Tausayin banza tausayin hofi."

Baffa ya ɗan ɗago kai.

"Ba kariya nake ba shi daga kuskurensa ba. Ina ƙoƙarin ganin an fahimci abin da ya riga ya faru. Sai dai a kiyaye gaba."

Hakimi ya amsa da sauri.

"Shi ya sa na ce maka son Ƴaƴa ya rufe maka ido. Ko da yaushe akan son kare laifin Yaranka kake. Duk lokacin da ɗanka ya yi laifi, sai ka nemi dalilin da zaka ce ai akwai abin da ya sa ya yi. Wani lokacin uba ya kamata ya tsaya ya ce ɗansa ya yi kuskure, ya sa ya gyara, ba ya tsaya ya nemo uzurin kare shi ba. Ban ga wani dalili ko hujja da zata sa mu karɓi wannan matsiyacin auren ba. Babu shi!"

Ya zabga wa Turaki harara, sannan ya ce cikin ɗaga murya.
"Turaki ka ji ni da kyau. Mu ƴan uwan mahaifinka ba za mu taɓa amincewa da wannan auren ba. Ba za mu karɓe ta a matsayin matar da ka kawo cikin wannan zuri'a ba. Saboda haka ka sallameta kawai. Wanna shine umarnina a gareka."

Turaki ya ɗago kansa.

"Amma..."

"Babu amma a nan. Bana son jin wani dogon bayani. Hukuncin da na zartar kenan kafin ma maganar ta je ga Babbanmu"

Turaki ya sake cewa,"Baffa ya amince da auren fa..." 

Ya faɗa ba wai da rashin kunya ba. Abu ɗaya da ya sani tun da har mahaifinsa, da iyayensa mata suka karɓi auren nan. To fa mai saka shi ya rabu da matarsa sai wani ikon Allah. Don ko ita Fullon ta yi kaɗan tasa ya rabu da ita.

"Mahaifinka ya amince da abin da ya fahimta ne. Ni kuma ina magana ne a kan abin da ya shafi ɓangarenmu. Kuma ka riga ka san matsayinmu da irin matsayarmu akan kowanne lamari."

Haka suka yi ta kai ruwa rana. Kowanne yana kare matsayinsa, har zuwa lokacin da maganar ta ƙare ba tare da an samu wata fahimtar juna ba. Rayuka babu daɗi dai aka rabu.
And yanzu abin da ya fi damun Baffa yadda zai tunkari Baɗejo da maganar. Yadda zai je ya fuskance ta da bayanin shi ne yake yawo a cikin kansa.

Domin idan Hakimi ya riga ya tsaya kan wannan matsayar, ya san ɗayan Ɗan uwan nasa ma kan hakan zai tsaya, daga nan kuma bai san irin matakin da mahaifiyarsa za ta ɗauka ba. 
Na farko dai za a sha rigima, na biyu kuma Turaki ya jefa su a matsala.

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe ne a yanzu, motar tana kan titin garin Taraba.
Bello ne ke tuƙi. Turaki yana zaune a kujerar gaba, yayin da Baffa yake a baya tare da amininsa, Alhaji Bello Marafa, da kuma ƙanin Hajiya Ramla, Alhaji Tahir.

Tafiyar ta yi tsawo. Turaki dai tun da aka taho ya yi shiru. Lokaci zuwa lokaci yana kallon hanya ta gilashin motar, wani lokacin kuma ya sunkuyar da kansa yana zurfafa tunani. Yau hira da rigima babu tsakaninsa da Bello. Kowa zuciyarsa a cunkushe take.

Iyayen nasu kuwa sai hira suke yi. Farkon tahowa suna ta maida magana akan auren da kowa ransa ya ɓaci da shi.
Amma yanzu suna ta tattaunawa ne akan batun matsaltsalun nigeria.

Bayan doguwar tafiya, suka isa garin Taraba lafiya. A lokacin da suka isa masallaci, aka yi daidai da sallamar sallar La'asar.
Suka yi alwala, suka shiga masallacin, suka gabatar da sallah tare da wasu tsirarrun mutane da jam'i ya wuce su.

Bayan an idar, Baffa ya tambayi Limamin masallacin. Nan aka sanar da Liman cewa wasu baƙi sun zo suna son ganawa da shi.
Nan Liman ya ce ayi musu iso, Turaki ya ɗan tsaya yana kallonsa a lokacin da suka isa gaban Liman. Wanda ya kai aya a karatun ƙur'anin da yake, ya rufe ƙur'anin yana shafa addu'a.

Liman ya tsaya yana kallon Turaki, kallo irin na mai ƙoƙarin dawo da wani abu a cikin ƙwaƙwalwarsa. Sai kwatsam fuskar ta haska masa kuwa tarr, bai manta ta ba, kuma babban lamarin da ya faru a tsakani ba zai sa ya manta ba.

"Ah! Ah! Ɗan samari kai ne!"

Ya miƙa masa hannu.

"Barka da zuwa dai. Ya wajen iyalin naka?"

Turaki yana murmushi cikin kunya, ya miƙa masa hannu suka yi musabaha.

"Alhamdu Lillah Mallam." 

"To ma sha Allahu. Ashe kai ne ke tafe."

Suka gaisa da sauran mutanen da suka zo tare, sannan liman ya jagorance su zuwa wani wuri na musamman da za su zauna su tattauna. Bayan kowa ya zauna, Alhaji Bello Marafa shi ne ya buɗe maganar. A hankali ya bayyana wa liman dalilin zuwansu gare shi.

Ya fara daga batun auren wanda shine muhimmi. Tukunna ya bayyana masa cewa Baffa ya zo ne domin ya tabbatar da ainihin abin da ya faru daga bakin wanda ya kasance a wurin. Liman ya saurare shi har ya gama. Bai yi saurin magana wajen tarar numfashinsu ba.

Ya kalli Baffa, sannan ya ce,"Alhaji duk abin da wannan Ɗan naka ya faɗa, haka abin ya ke. Gaskiya ya sanar muku, sannan wannan record da ya kunna a yanzu, tabbas anyi haka, duk a gabanmu aka yi, a gaban su Malam Yahya. Sannan nima ɗin zan sanar muku da duk gaskiyar da kuke nema bayan wadda ya sanar muku."

Ya ɗan gyara zamansa, ya furta tasbihi kamar yadda hakan ya zame masa jinin jiki. A kowacce magana ko shiru nasa, to tabbas bakinsa cikin ambaton Allah yake.

"Ba zan yi muku ƙarya a kan irin wannan magana mai girma ba. Aure ba wasa ba ne, kuma ni ba mutum ba ne mai son zuciya. Ina da tsoron Allah, kuma ina sane da nauyin kalmar da zan faɗa a irin wannan al'amari. Kuma ina tsoron ubangiji ya tsayar da ni a ranar shaida."

Baffa ya ɗaga ido yana daɗa sauraron sa. Liman ya kalli Turaki.

"Ni kaina na so ace Manyansa sun shiga lamarin. To amma duba da situation ɗin ni da kaina na yi gaggawar amincewa da ɗaura auren a lokacin. Saboda halin da yarinyar zata iya shiga abun a duba ne, kuma abun a taimaka mata ne."

Ya ɗan yi shiru.

"Na san Hayyo sarai. Na san abin da zai aikata. Don ko maganar Malam Mudi da ya yi a lokacin ƙarya yake yi. Hayyo baƙin maciji ne. Na ga abin da ke gabansa a lokacin. Mutum ne da zai iya karɓar ƙaramin kuɗi a hannun Malam Mudi ya aura masa ƙaramar yarinya ba tare da ya damu da abin da zai biyo baya ba."

Ya numfasa sannan ya ci gaba.

"Hayyo ba mutumin kirki ba ne Alhaji. Auren yarinyar da Ɗanku ya yi ba ƙaramin ceto rayuwarta ya yi ba. Don Allah karku sa ya rabu da ita ta dawo hannun ubanta. Rayuwarta zata lalace wallahi. Auren nan rufin asiri ne da babban gata a gareta ga mutumin kirki dai kamar Ɗanku. Ina masa kyakykyawar shaida a kallon da nake masa."

Baffa ya runtse idanunsa na ɗan lokaci. Shiru ya ɗan ratsa wajen.
Baffa ya sunkuyar da kansa a hankali. A yanzu ya fahimci Ɗansa ya yi gaggawar ɗaukar matakin da ya dace ne. Kuma a karon farko, zuciyar Baffa ta samu cikakkiyar natsuwa a kan auren.

Ba zai taɓa mantawa da kuskuren da Turaki ya yi ba akan auren Sirri. Sai dai a yanzu ya san cewa a ƙarƙashin wannan kuskuren akwai wani dalili mai girma, ƙoƙarin kuɓutar da rayuwar yarinya daga halaka, kuɓutar da yarinya daga hannun mahaifin da zai iya jefa ta cikin wata mummunar rayuwa. Mace abar tausayi ce ƙwarai.

Baffa ya ɗaga kai ya kalli liman.

"Na fahimta Mallam. Allah ya saka maka da alheri. Muna godiya sosai."

Liman ya amsa da Allahumma Amin. Daga nan aka ci gaba da yin wasu tambayoyi, musamman game da waɗanda suka zama shaidu a wajen. Duk abin da suke buƙatar tabbatarwa, liman ya tabbatar musu da shi.

A ƙarshe, Baffa ya samu abin da ya zo nema. Ya tashi da zuciya mai natsuwa. Bayan sun bar wajen, bai ɓata lokaci ba kafin ya kira matansa ya sanar da su abin da suka ji daga bakin liman.

Ya shaida musu komai. Suma ɗin da suka ji cikakken bayani, hankalinsu ya kwanta. Abin da ya kasance musu babban abin fargaba ya zama haske. Maama musamman ta sauke ajiyar zuciya.

"Alhamdu Lillah," ta furta a hankali.

Sai dai duk da irin zagayen da suka yi a garin Taraba, da binciken da suka gudanar, da tambayoyin da suka yi a wurare daban-daban domin gano inda Hayyo ya koma, ba su samu wani sahihin labari ba.

Babu wanda ya iya gaya musu inda yake. Amsa ɗaya ce ya bar unguwar kuma ba a san inda ya koma ba. Maƙotansu ne ma kawai suka ce wataƙila fa ya bar garin gaba ɗaya. 

Daga ƙarshe dole haka suka haƙura. Da yamma suka nufi hotel ɗin da za su kwana, da zummar washe gari su ɗauki hanyar komawa gida.

BAYAN WASU KWANAKI...
Wata jar mota ƙirar Range Rover ta sauka daga kan titin, ta gangara gefe ta yi parking a gaban wani teburin mai sayar da kayan marmari.

Matashin saurayin da ke cikin motar ya zuge glass ɗin motar, ya yi wa mai sayar da pineapple sallama.

"Assalamu alaikum."

Mutumin ya amsa sallamar, ya bar wajen da yake zaune ya ƙaraso kusa da motar.
Zuwansa kenan, Abdulhamid ya miƙa masa hannu suka yi musabaha.

Mai pineapple ɗin ya ce,"Ta nawa za a zuba Yallaɓai?"

Abdulhamid ya amsa,"Sako guda goma. Amma kar a yanka kowacce."

"To to ranka ya daɗe."

Mutumin ya juya ya koma wajen kayan nasa. Ya ɗauki pineapple ya fara zubawa a leda har guda biyar, sannan ya dawo da su.
Abdulhamid ya buɗe booth ɗin motar ya nuna masa inda zai saka.

A zahiri Abdulhamid ba da niyyar siyan pineapple ɗin ya tsaya ba. Sai dai ganin mutumin ya riga ya saka rai da tunanin siyan zai yi, shi ya sa ya siya ɗin kawai.
Bayan ya gama, mutumin ya dawo yana goge hannunsa da durster.

"Yallaɓai an gama sakawa."

Abdulhamid ya juya ya kalli bayan motar. Mahaifinsa yana kwance a kujerar baya kamar mai bacci. Amma Hamid ya san sarai cewa ba bacci yake ba. Ya sake juyowa zuwa ga mai kayan marmarin.

"Bamu apple."

Cikin sauri mutumin ya juya ya koma wajen teburinsa. Bai daɗe ba ya dawo da leda cike da apples. Har yanayin jikinsa ya nuna irin daɗin cinikin da ya yi.

Abdulhamid ya karɓa.

"Nawa ne kuɗin?"

"Ka ba da dubu tara Yallaɓai."

Abdulhamid ya sa hannu cikin aljihunsa ya ciro kuɗi, ya ƙirga dubu goma sha uku ya miƙa masa. Yana shirin rufe glass ɗin motar ne ya tuna, sai ya dakatar da mutumin.

"Yauwa, don Allah tambaya na ke dama."

Abdulhamid ya tambaya yana kallonshi.

"To, Allah ya sa na sani."

"Gidan Alƙali Dukko nake nema."

Mutumin ya yi kamar ya tuna wani abu. Can fuskarsa ta washe da fara'a sosai yana cewa,"Ohh Gidan uban marayu zaka ce."

Abdulhamid ya ɗan tsaya yana kallonsa.

"Uban marayu?"

"Eh fa. Alhajin Allah Uban marayu, gatan kowa kenan."

Sai mutumin ya fara yi masa kwatance, yana nuna masa inda zai bi, da wata alama da zai gane gidan da zarar ya kusa. Abdulhamid dai yana ta sauraronsa sosai.

"Na gode."

"Ba komai Yallaɓai."

Abdulhamid ya ja motar ya bar wajen.
Bayan ɗan tafiya, ya ɗauki apple ɗaya ya juya ya miƙa wa mahaifinsa.

"Abba ka daure ka ci ko ɗaya ne."

Mahaifin nasa bai ce komai ba. Abdulhamid ya sake miƙa apple ɗin kusa da shi.

"Ko rabi ne kawai."

Kamar ba zai karɓa ba, wucewar wasu sakanni Mahaifin nasa ya miƙa hannu da yake karkarwa ya karɓa. Tukunna Abdulhamid ya mayar da hankali kan tuƙinsa. Ba a yi tafiya mai tsawo ba suka iso ƙofar gidan Alƙali Dukko.

A daidai lokacin da suka isa, wata mota ta shigo cikin gidan.
Abdulhamid ya tsaya a gefe, yana kallon yadda ƙaton gidan yake ta gilashin motarsa, gida mai cike da burgewa saboda tsaruwar gininsa.

Bayan motar Maama ta shiga ciki, Abdulhamid ya fito daga motarsa.
Ya ƙarewa gidan kallo na ƴan daƙiƙu, sannan ya ƙarasa bakin gate ya yi knocking. Mai gadi ya buɗe ƙofar ya fito.

"Assalamu alaikum."

"Wa alaikumussalam."

Suka gaisa cikin girmama juna. Anan Abdulhamid ya tambaye shi,"Don Allah ko akwai Hajiya Rabi a nan gidan?"

Fuskar Mai gadin na nuna dogon nazari ya ce.

"A'a wallahi babu Rabi. Wani ya yi maka kwatance da nan ɗin ne?"

Abdulhamid ya gyaɗa kai.

"Eh to. Daga can gidan Sarki aka kwatanta mana nan ɗin. Da acan take aiki, sai aka ce ta dawo nan gidan."

"Ohh…"

Mai gadin ya faɗa don ya fahimta.

"Ah ai nan ɗin main gate ne na gidan. Ɓangaren ma'aikatan gidan tana da nata gate ɗin daban. Da ka zagaya ta baya zaka ga wani gate irin wannan."

"To shikenan na gode sosai."

"Babu komai."

Abdulhamid ya koma motarsa. Ya zagaya zuwa ɗayan gate ɗin, sannan ya fito ya sake gaisawa da mai gadin.

"Don Allah ina neman Mama Rabi."

Mai gadin ya kalle shi.

"A gaskiya ban san wannan sunan ba. Amma bari in kira maka shugabar ma'aikatan, wataƙila ita ta sani."

Ya ɗauki waya ya kira. Ba a daɗe ba, sai ga Yami ta fito daga cikin gidan. Zuwanta gaban Abdulhamid da Mai gadi ya yi mata nuni da shi, sai ta tsaya cak.
Idanunta suka yi ƙyam a kan fuskarsa na ƴan daƙiƙu. Kamar tana ƙoƙarin haɗa wani abu da wani don tantancewa.

Ya tsuguna har ƙasa ya gaida ita, ta amsa cike da yabawa hankali da kuma ladabinsa. Sannan ta ce,"Kar dai jikanmu ne kai don na ga kama?."

Abdulhamid ya ɗan yi mamaki, sai da ya kalle ta tukunna ya ce.

"Ehh to, idan wadda nake nema ɗin ita kike nufi, to ni jikanta ne tabbas."

Yami ta ƙara kallonsa sosai. Kamar yadda take kallon fuskarsa, ta kasa ɓoye mamakinta. Domin kamanninsa da Fullo ya yi yawa, tamkar an tsaga kara. Badan badan ba ata rantse Fullo ce ta yi aski tayi shigar maza.

Ta ce a hankali,"Rabi, ba dai farar bafulatana ba ƴar tsamurmura haka?"

Abdulhamid ya ɗan yi murmushi tare da cewa,"Ita ce in sha Allahu."

Fuskar Yami ta haska da murmushi gami da farin ciki.

"Allah sarki! Ai da yake ma ta kwana biyu da tashi daga nan ɗin. Amma bari sai mu je yanzu na raka ka gidan da suka koma. Da ke ba anan unguwar ba ne."

Hamid ya gyaɗa kai.

"To shikenan. Allah yasa ban takura ki ba."

Yami ta koma cikin gida domin ta shirya. Bayan ɗan lokaci ta dawo, suka shiga motar. Da farko ta nufin shiga kujerar baya, amma Hamid ya ce,"A'a Yami ki zo ta gaba."

"Ah ah da ka barni a bayan dai."

Haka dai ta dawo ta zauna a kujerar gaba. Ba ta ma lura da wanda yake zaune a bayan motar ba. Hankalinta yana kan Hamid da farin cikin da take haskowa a fuskar Ƙawarta. Don tana yawan mata zancensa.
Haka suka kama hanya. Sun yi tafiya mai nisa kafin su isa inda gidan su Fullo yake.

A daidai lokacin da motarsu ta shigo farkon layin, Ita kuma Fullo ta fito daga layin. Sanye take da uniform, fuskar ta rufe da niƙab, zata tafi Islamiyya.

Motar ta wuce ta gabanta ba tare da ta gane wanda yake ciki ba. Ba da daɗewa ba suka isa gidan. Ƙofar gate ɗin a buɗe take, don haka Yami bata tsaya knocking ba. Ta nufi cikin gidan da hanzari tana cewa,"Bari na sanar musu."

A parlo ta sami Kaka ita kaɗai, tana kallon talabijin. Suka gaisa a tsaye. Yami ta kama hannunta.

"Taso ƙawata, taso! Taso!"

Kaka ta bi ta da wani kallo.

"Lafiya dai ƙawata?"

"Lafiya lau ƙawata. Ke dai fito da sauri ki ga abin mamaki. Abin farin ciki kuma."

"Ni kam me yake faruwa Ƙawata? Ki sanar min mana kafin na je ga gani."

"Ke dai ki zo kawai. Ai bana ɗorar ba sai kin fara gani da idonki. Amma dai sapiras ne inji turawa."

Cikin azama Kaka ta miƙe daga kan kujerar. Ta ɗauki hijabin Ummi da ke ajiye a kan kujerar ta saka, sannan ta bi bayan Yami da sauri. Hankalinta bai kwanta ba sam. Don har wata irin faɗuwar gaba take ji.

Don yadda Yami take cikin hanzari ya nuna mata cewa akwai wani babban al'amari da ya faru. Suna fitowa bakin gate, Kaka ta ɗago kai, karaf idanunta suka sauka akan kyakykyawan matashin da Yami ke nuna mata.

Sai ta tsaya cak. Hannunta ya tafi kan ƙirjinta ta dafe shi da ƙarfi. Abdulhamid yana jingine a jikin motar. Ta kalle shi. Ta sake kallonsa. Kamar idanunta sun ƙi yarda da abin da suke gani. 

Kafin ta furta,"Wa idanuna suke gane min? Ƙawata wasa zaki yi da hankalina ne?"

Wani irin farin ciki ya mamaye Abdulhamid. Ya baro jikin motar da yake jingine, ya nufi Kaka.

"Daada."

Ya faɗi sunan yana ƙarasawa ya rungume ta. Kaka ta ɗan ture shi daga jikinta tana hawaye da dariya a lokaci guda.

"Abdulhamid! Kai ne ka zama mutum haka? Tukunna ma da gaske kai ɗin ne ko kuwa kamanni ne?"

Ta kama fuskarsa da hannuwanta.

"Dama zamu ƙara ganawa a rayuwar nan Hamid?"

Ta share hawaye. Abdulhamid ya sauke numfashi.

"Ki yi haƙuri Kaka. Na yi kuskure a yafe min don Allah. Kuma ubangiji ne bai nufa zan zo gareki ba. Amma wallahi kina raina a kowacce rana ke da Ƴar uwata, da kuma duniyata(Ummi). Kullu yaumin da ku zuciyata ke motsawa."

Kaka ta share hawayen farin ciki. Kuma a lokacin ne idanunta suka koma kan motar.

"Amma to ya aka yi ka zo nan Hamid?"

Ta ƙara kallon motar.

"Kar dai wani abu ne ya faru mara daɗi? Kuma ita wannan babbar motar mai numfashi ta wa ye?"

Abdulhamid ya yi murmushi.

"Kaka ai ban manta da kina aiki a gidan Sarki ba. Na faɗa miki, tsawon shekarun nan Allah ne kawai bai nufa ba sai yanzu."

Kaka ta ɗan taɓe baki.

"Don dai ka ga bana tare da abin da yake da muhimmanci a wurinka ne, shi ya sa ka kasa nemana, lokacin da mahaifiyarka ke wurina ai kana zuwa akai akai."

Abdulhamid ya yi shiru. Ya ga Kaka na ta kallonsa, amma idanunta suna ta komawa kan motar, da alama dai tana son jin amsar tambayar da ta masa.

Sai ya ce,"Mota ta ce. Ba zai yiwu mu shiga daga cikin gidan ba ne?"

Kaka ta kalle shi.

"Zai yiwu mana Abdulhamid. Ai shiga cikin gida ma dole. Gidanku fa ka zo. Taho mu je."

Ta juya za ta fara tafiya Hamid ya dakatar da ita.

"Kaka…"

Ta juyo tana kallonsa.

"Mota ba za ta shiga ciki ba ne?"

Kaka ta kalli gate ɗin.

"To sai dai ka duba. Tun tarewarmu a gidan dai ta wannan ƙaramar ƙofar muke shiga. Mu ba mota garemu ba."

Abdulhamid ya ƙarasa ya duba. Ya ga gate ɗin ba mai zugewa ba ne, don haka ya dawo.

"To Kaka bari na fito da shi."

Kaka ta tsaya.

"Wa fa?"

Ya yi ɗan jimm damuwa na bayyana ƙarara a fuskarsa sannan ya ce,"Tare da Abba muke, ba zai iya tafiya ba sai na taimaka masa".  

Kaka ta ɗan tsaya cike da mamaki da al'ajabi. Hayyo ne zai biyo shi su zo nan ko kuwa wani Abban yake nufi?

Idanun Kaka a waje da son jin ƙarin bayani ta ce,"Kana nufin Babanka Hayyo wai?".  
  
Ya ɗaga mata kai,"Ehh Kaka".  
  
Da maɗaukakin mamaki ta ce,"To me ya sami ƙafar tasa da ba zai iya takawa ba, ko wani mulkakken ya zama da yafi ƙarfin taka ƙasa? Bayan cikin ƙasar dai za a cusa shi."
  
Abdulhamid ya sauke numfashi mai nauyi.

"Babu wani mulki face jarabawar Ubangiji."

Kaka ta taɓe baki.

"Alhaki dai yake bibiyarsa ko. Ba wata jarabawa."

Abdulhamid bai ce komai ba. Ya koma motar. Ya buɗe booth ya fito da wheelchair. Sai ya buɗe ƙofar baya, ya shiga ya taimaka wa Hayyo ya fito. A hankali ya ɗorasa a kan wheelchair.
Kaka kuwa tun da ta ɗago ido ta gan shi, ta yi masa kallo ɗaya. Tsoro ya ratsa jikinta. Wani irin tsoro da ba ta shirya ji ba akansa. Amma kafin tsoron ya gama mamaye ta, tausayi ya biyo bayansa. Domin idanunta sun gane mata abin da bata taɓa tsammanin gani tare da shi ba a wannan duniyar, yo ai ita ce take sai an dangana ga lahira.

Hayyo ya rame. Ya rame ƙwarai. Fuskarsa ta canja, ya zama siriri, banda fatar da ta lulluɓe ƙashinsa, zaka rantse da ubangijin samma da ƙassai skeleton ne. Ƙarfinsa ya gushe gaba ɗaya. Mutumin da a da yake tafiya da girman izza, wanda ƙarfinsa da kaurin jikinsa suke sa mutane su ji tsoronsa, amma yanzu ya zama kamar wata halittar dabba mai suna kangaru.

Ga girman shekaru ya bayyana a jikinsa sosai, girman shekarun da ya wuce nasa. Ya hayyu ya qayyum, hannunsa fa kamar a shanye take gani ko?

Gaba ɗaya ta kasa haɗa wannan mutumin da wanda take da hotonsa a zuciyarta.
Abdulhamid ya turo shi suka ƙaraso inda Kaka ke tsaye cike da tsoron duniya, hoton abubuwan da suka faru a baya suna ta haska mata a ido tarr.  
Ita dai banda Abdulhamid ya faɗa mata ya ce Abbansa, da sai ta rantse ta ce ƙarya ne ba shi bane, don gaba ɗaya ya fita daga kamanninsa tsabar wahala, kamar ba wannan ƙaƙƙarfan namijin da ke zage dukkan ƙarfinsa ya zane mata Ƴarta ba.

Ta girgiza kai tana ƙara jin tsoro na al'amarin sakayyar wanda aka zalunta daga ubangiji, a hankali ta ce da shi,"Hayyo kai ne haka?".   
  
Hayyo da ke kan wheelchair ya ɗago wuyansa da ƙyar. Idan idanunta daidai suke gane mata, hawaye fal idanuwansa na tarin nadama.
Wuyansa ya laƙwashe, kansa yana buƙatar taimako kafin ya iya ɗagawa.

Ya kalli Kaka. Ya buɗe bakinsa.

"Nannnnaaammm… Daddddda…"

Muryarsa ta fito cikin ƙinƙinar da sai wanda ya saurara da kyau zai iya gane kalmar.
Kuma cikin murya sak ta masu koyon magana, muryar a shaƙe kamar ta mage.
Kaka ta tsaya tana kallon sarautar Allah. Ba ta iya cewa komai ba jikinta dai ya yi mugun sanyi. Da yake tana da saurin rauni da tausayi.

Sai kawai idanunta suka cika da hawaye. Ta ɗaga hannunta zuwa bakinta, kafin ta fashe da kuka mai ƙarfi.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un…"

Ta sake maimaitawa cikin kuka.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un…"

Hamid ya tsaya yana kallonta, shi ma zuciyarsa ta cika da wani yanayi da ba zai iya fassarawa. Ya yi murmushi mai ciwo a ƙasan ransa. Wai a hakan ma fa Abban na su ya fara jin sauƙi akan watannin baya.
Kaka dai ta kasa ɗauke idanunta daga kan Hayyo cike da tsantsar tsoro.

A gabanta ba Hayyo ɗin da ta sani kawai take gani ba. Tana ganin rayuwar da ta wuce ne. Tana ganin zaluncin da ya yi wa matansa da Ƴaƴansa. 

Ta ƙara kallonsa, hawaye na bin kumatunta.

"Hayyo na kasa yarda kai ne ka koma haka. Haka rayuwa ta mayar da kai Hayyo? Duniya abun tsoro. Ka aikata mai kyau sai ka ga da kyau, akasin hakan zaka girbi abin da ka shuka."

Cikin murya mai matuƙar rauni ta yi maganar, tana kallon fuskarsa da ta sauya halitta gaba ɗaya. Magana ta tsakani da Allah tsoro ma yake bata. 

Tunawa take da irin golden voice ɗinsa. A da, Hayyo yana daga cikin mazajen da Allah ya yi wa baiwar halitta. Kyau, daɗin murya, cikar zati da haiba… duk Allah ya ba shi. Ƙarya ne Hayyo ya yi magana kana wajen ka ce baka ji daɗin muryarsa ba. Amon muryarsa ma ɗaya ne daga cikin abubuwan da suke jan hankalin mata zuwa gare shi, balle uwa uba kyau kamar balarabe.

Amma yanzu muryar da take ji ba ita ce waccan muryar ba. Hawaye ya cika idanun Hayyo. Ya yi ƙoƙarin ɗaga kansa, bakinsa yana rawa sosai ya ce.

"Dadddd… dddddaaa Allllahhhh… kiiii yaaafeeee miiiimmmm… dddda Allllahhhh… kiiii neeemmmooo minnn… Haliiimaaaatttt…"

Kalmar ta fito a wahalce. Sai da aka ɗauki kusan cikakken minti guda da ƴan daƙiƙu kafin ya iya furta abin da a zahiri za a faɗa cikin sakanni biyu.
Bakinsa yana rawa, haƙoransa suna daddatsewa a kan harshensa, kalmomin kuma suna fitowa a kakkarye.

Abdulhamid ya ɗauki handkerchief ya fara goge masa yawun da ke malalawa daga bakinsa. Yawun ya riga ya ɓata gaban babbar rigarsa, kamar an sheƙa masa ruwa. Ƙafafunsa suka shiga rawa a kan wheelchair.

Ya kamo hannun Abdulhamid da ƙarfi gwargwadon ƙarfin da yake da shi.

"Zaazzzannnn… saukkkkkaaaa… innnneeee miiii… yaaaaaffiyyarrr… Dddddaaaada…"

Abdulhamid ya kalle shi, sannan ya kalli Kaka.

"Yana so ya sauko. Yana so ya nemi yafiyarki."

Kaka ta share hawaye, amma wasu suka sake gangarowa.

"Hayyo ba sai ka sauko ba."

Ta kalle shi na ɗan lokaci.
"Yi zamanka tukunna. Ai dama yanzu tun a duniya Allah ke sakayya. Na jima ina faɗa maka talala ake maka."

Yami ma kuka take. Domin da wuya mutum ya ga irin halin da Hayyo yake ciki ya kasa zubar da hawaye. Saboda yanayin da yake ciki yana tunasar da mutum wani abu mai girma, wato tsoron Allah da sakamakon zalunci.

Kaka ta ɗago kanta ta kalli gidan.

"Mu shiga ko."

Ta juya ta yi gaba. Abdulhamid ya bi bayanta yana tura wheelchair ɗin Hayyo, Yami kuma ta biyo su. Suna nufar entrance ɗin parlon gidan, sai Ummi ta fito.

"Lafiya Dada? Na fito ban ganki a parlon ba. Yanzu kuma na ganki a haka… me ya faru?"

Kaka ta buɗe baki, amma kalmomin sun ƙi fitowa. Har yanzu tana cikin girgizar abin da ta gani. Kafin ta iya yi wa Ummi wani bayani, Ummi ta ji hannayen mutum sun kama ƙafafunta. Sai ɗigar hawaye ke sauka a kan ƙafarta.

Ta sauke idonta. Hamid ne.
Ya zube a gabanta yana riƙe da ƙafafunta. Ba fuskarsa ta kalla ba. Saman kansa kawai ta kalla, tana hango wannan ramin da ya shata a tsakiyar kansa, inda gashi ya daina fitowa gaba ɗaya, wanda sanadin hakan dalilin wani jahilin duka da Hayyo ya yi masa ne, lokacin yana ɗan shekara bakwai.

Sai ta ji zuciyarta ta buga. Akwai wani abu da Allah ya dasa tsakanin ɗa da uwa, wani irin tasiri da ba sai an ga fuska ba kafin zuciyar uwa ta gane ɗanta.
Ta ji wani abu ya tsarga mata. Idanunta suka kulle.

"Abdulhamid…"

Ta kira sunansa da amon sautin da ya tafi ya taɓa har zuciyar Hayyo.   
Ummi ta sake cewa,"Me kake nema a ƙafafuna Abdulhamid? Laifin me ka yi min?"

Sai ta ɗan motsa ƙafafunta.

"Tashi tsaye na ganka ɗana."

Abdulhamid ya miƙe. Hawaye na zubo masa. Ummi ta rungume shi da ƙarfi. Shi ma ya rungumeta yana jin ashe kewarta da yake ji a lokacin da bata tare da su ba komai ba ne. A yanzu da yake jin ɗumin jikinta na tsarga masa ne yake jin asalin kewarta na ratsa ɓargo da jinin jikinsa.

Duk su biyun kuka suke yi. Ummi ana jiyo sautin nata kukan da yake fita a hankali, while Abdulhamid kuma hawaye ne kawai ke zuba mai tarin yawa da tsananin zafi a saman kuncinsa. Wucewar daƙiƙa uku Abdulhamid ya zare jikinsa daga nata yana bin mahaifiyar tasa da kallo, wadda yaga ta ƙara kyau da girma kamar ba ita ba. Alamar ta samu lafiya da kwanciyar hankali ba kamar lokacin da take gidan mahaifinsu ba. Rayuwar da tarihinta ba zai taɓa gogewa ba a rayuwarsa, har kullum idonsa na haska masa fefen bidiyon yadda mahaifinsa ke zage ƙarfinsa ya yiwa Umminsu duka, tana ihu tana roƙonsa amma ba zai ƙyaleta ba sai ta gama galabaita.

Shekarun da suka rabu ba su rage mata komai ba. A ganinsa ma, kamar ta ƙara zama wata sabuwar mace ne, wanda ba don uwa ba ce, zai iya cewa mai kama da Umminsa ce ba ita ɗin ba ce.
Ummi ta share hawayenta.

"Ya aka yi ka zo nan Abdul Hamid?"

Ta sake tambaya.

"Wa ya faɗa maka inda muke?"

Abdul Hamid ya buɗe baki zai amsa.
Sai dai kafin ya furta komai, idonta ya sauka kan wheelchair ɗin da ke bayan sa. Wadda ke karkarwa tana neman faɗuwa.

A kallo ɗaya. Duk irin lalacewar da halittarsa ta yi, ba zai yiwu ta kasa gane shi ba. Hayyo!

Ai kuwa ba bu shiri ta yi saurin ɗauke ƙwayar idonta daga kan mutumin da take jin ta tsane shi tsana mafi muni. Ta koma kallon wani wuri daban.

Abdul Hamid ya buɗe baki zai yi magana. Ummi ta ɗaga masa hannu cikin fusata.

"Kul."

Ta kulle idanunta tana huci. Na tsawon daƙiƙa guda ta tsaya a haka. Sannan ta buɗe su. Ƙwayar idonta ta yi jawur. Damuwar da ta kwashe shekaru tana ɗauke da ita, wadda ta yi ƙoƙarin binne ta a can ƙuryar zuciyarta, ta taso gaba ɗaya ta mamaye fuskarta.

Ta kalli Abdul hamid.

"Tunanina duk sanda zan ganka, zan kasance cikin farin ciki ne."

Muryarta ta fara rawa. Sai ta ƙara ɗaga muryarta da ke shaida tsantsar ɓacin rai.

"Me yasa ka zo min da wannan abin cikin gida?"

Abdul Hamid ya yi shiru.

"Ina tambayarka me yasa?"

Ta sake maimaitawa. Sai ta nuna masa ƙofa da hannu.

"To idan baka sani ba, ka sani yanzu."

Ta ja numfashin da take jin kamar yana barazanar ɗaukewa.

"Bana so. Kuma bana ƙaunar sake haɗa ido da azzalumin mahaifinka har in bar duniya."

Hawaye suka sake cika mata ido, amma wannan karon ba ta share su ba.
"Dan haka, tun ina shaida cewa kai ɗana ne ka fitar da shi daga gidan nan. In kuma ba haka ka koma inda ka fito kaima na yafe ka, Halimatu kaɗai ta ishe ni."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol