Free chapter · Read without an account
PAGE 12
MOHA ne zaune a office ɗin sa yana juyi akan kujerarsa wayarsa yake dan bugawa a lips dinsa kafin ya cirota ya shiga wajen rubuta saqon text, number Maesha ya fara lalubowa kafin ya fara rubutu kamar haka I HOPE YOU HAD A GOOD SLEEP ❣️ JUST THINKING OF YOU GETS ME READY FOR MY DAY, GOOD MORNING GORGEOUS, HAVE A GREAT DAY , MORNING KISSES FROM A FAR!! .
Maesha na zaune tana yiwa nabila kitso wayar ta dake hannun Nabil yana game tayi Kara alamar shigowar sako. " Aunty Maesh gashi an turo maki saqo.
Karba tayi ganin new number ne sai kaman baza ta bude ba amma kuma wata zuciyar tace bude, dannawa tayi ta buɗe, saida ta zubawa rubutun ido na tsawon lokaci kafin ta karanta ta ƙara. "To waye wannan ? Ta yiwa kanta tambayar da ba amsa, wata zuciyar tace ko wanna jarababben tsohon daya zo jiya ne, take taji dana sanin yaga takardar datayi ko ba komai data tabbatar shine zatayi blocking haka dai ta hakura ta Ajje wayar ta share ta cigaba da abubuwanta .
MOHA
Kwance yake Yana ta juyi a gado tunanin ta ya hanashi bacci sam, wayarsa ya dauko ya jima yana kallon number kamin ya danna mata Kira saidai har tayi ringing ta katse ba a daga ba shi a ka idarsa baya kiran mutum sau biyu indai yayi na ɗaya to baya karawa amma sai ya samu kansa da Ƙara kiranta a karo na biyu.
Tana kwance amma takasa bacci domin tunanin daya saba hana ta baccin dai shi take yanzu ma watau tunanin moha wanda ita ko sunansa takasa sani kuma yaki ficewa a zuciyarta yayi Mata karfa karfa, har Kiran farko ya katse bata jiba sai a na biyun ne ma ta motsa, number ta zubawa ido tana kallo tabbas number da aka Mata text ce ɗazu, amma koma waye bari taji dai. Ta ƙarashe tana dagawa da sallama shuru yayi Yana lumshe Ido "hello" ta sake fada still beyi magana ba amma sunajin saukar numfashin juna ta cikin wayar.
Cire wayar tayi a kunnenta ta kalla Kana tace waya sani ma ko yan yankan Kai ne, to in ma sune ai ance idan Kayi magana janye jininka zasuyi, kai ni dai nashiga uku. Duk a fili take fada ba tare data san ana ji ba, murmusawa Moha yayi a hankali yace matsoraciya.
Wayar ta sake maidawa kunnenta kana tace in baza ayi magana ba fa I'm hanging up.
"An hanaki kashewa ne dama? Ya fada da muryar sa mai dadin sauraro shuru tayi ya sake cewa uhmmm?
Lokaci guda kwakwalwarta ta hasko mata shi domin muryarsa ko bacci take baza ta bace mata ba amma hakan baisa ta nuna ta nuna ba instead ma sai cewa tayi da wa nake magana please?
Shuru yayi har ta fidda rai taji yace MUHAMMAD SAMEER ADAM JIKAMSHI.
"Gsky Malam maybe wrong number ne.
"Har na fada miki wa nake nema ne da zakiyi saurin cewa wrong number?
Shuru tayi tana tunanin ko ta Kofsa ne. "Malama stop pretending nasan kingane wake magana.
" To ai sai an san mutum ake ganeshi ko, ni kuma ban taba sanin Mai irin sunan nan ba ma. Ta fada tana shan mur kaman moha dinne a gabanta nikuwa nace maesha anaso ana kaiwa kasuwa.
Miqewa yaui zaune daga kwancen da yake yace, "Amma ai zaki iya tuna wanda kika biyo har gida ko?
Dariya tayi kawai kafin tace to ai ni bansan gidanku bane kuma ai badan Kai nazo ba yayata na rako kuma nace Mata Kar muje tabari sai aunty safnan ta koma gidanta tace nai mata shuru.
Da calm voice din sa ya ce, "Ashe de kingane me maganar Kenan.
Sai a lokacin ta tuna baran baramar datayi gsky ni wawiya ce whl gashi duka daya ya bugi cikina, ta faɗa a zuciyarta cike da jin haushi.
Shuru sukayi na dan lokaci shi ya rasa mai zai sake cewa ne tunda har tagane shi ai shi Kenan ita kuma bataso ta nuna zaqewa karya gane daman itama ta zurma akansa.
" Ummm.
"Inaji". Ta fada cikin yanga kamar bataso .
"Miye matakin karatun ki, kin gama secondary? ya fada yana lumshe ido ya jingina kansa da bedrest.
" A'a ban fara ba.
" Fadamin gsky banda girman Kai nasan baifi ace ss 2 kike ba ko.
"Shine nace ma ban fara bama kaji, Ka ganni da girmana kacemin wani SS 2 abinda yafi ss2.
"Masifaffiya kawai . Ya fada Yana murmushi.
"Shekarunki nawa?
"Shekarun mutum ai sirrin sa ne, Miye zakayi da shekaru na.
"Zan haɗa da nawa ne in tashi gini.
"18". Ta faɗa tana tura baki kamar yana ganinta.
Banza ya mata, ita kuma sai jira take yayi magana, can yace " Yaushe ne zaki shiga 19 din.
Da sauri tace, "Nan da two months.
Shuru ya sake yi harta dauka ya sauka daga kan layi ko kuma network ta sake cewa hello?".
"ina jin ki". Ya fada da murya ne tsayawa a rai.
Muting tayi tace mutum sai shegen muskuranci whl zaka sani ne.
Unmuting tayi tana dariya kasa kasa wai karya jita.
"Zagina kikayi ko?". zaro Ido tayi kamar yana gabanta Kana tace "A'a haba dai, ni me ka min da zan zageka
" To mai kike wa dariya
"Bafa dariya nake ba
"Mai karya fa?
" Allah ya yafe masa
"Me kikewa dariya? Ya sake tambaya.
"Wani abu ne fa.
"Hmmmm. Kawai yace yayi shuru.
"Zan kwanta sai da safe. shiru ya mata kamar baiji ba.
"hello!
" Ina jinki
"Nace zan kwanta.
"To kwanta mana Ko kuma sai nazo ne zaki iya baccin? Da sauri ta kashe wayar tana dariya ta janyo pillow ta rungume can kuma ta sake bude text dinsa na safe ta sake karantawa.
"Ga dukkan alamu bani kaɗai na faɗa ba, My goodness". Da sauri ta rufe bakinta tayi Kar ya Zeenah taji domin da dan karfi ta fadi My goodness din.
Kwanciya tayi tana juya wayar cike da farin ciki, muryarsa da yadda yake sauke numfashi ta cikin wayar na neman hanata sukuni.
A bangaren moha ma sai murmushi yake zubawa, ya dade a haka kafin ya fara rubuta mata text kamar haka . "I know I need to get some rest tonight, but I’m not sleepy yet like how I know you are still awake thinking of me, let's catch up in dream, sleep tight baby🌃❤️
Ta dade tana karanta text din kafin tayi addu'a takwanta cike da farin ciki.