Free chapter · Read without an account
PAGE 20
RANAR DINNER
Maesha na hango cikin wani purple long sleeve dress me flowers din silver colour ajiki tayi rolling da gyalen kayan kasancewar kayan irin English wears ɗin nan ne, batasa komai a fuskarta ba bayan powder data murza sai kajol da mascara, ta taje cikakkiyar girar nan ta, ta ɗan goga lipgloss Kan lips dinta, takalminta high heel silver colour hakama pose dinta, ta haɗu iya haɗuwa kamar ka sureta ka gudu, Meela ce a gefenta sanye da black fabric dinkin fitted gown ta kafa dauri harda makeup gyalenta a hannu sai fiffika take, Maesha ta kalleta tace, "Ni whl kunya ma nakeji dan sai naga kamar mun zaqe, jibe ki fa kamar kece Hameeda".
Tabe baki Meelah tayi tace, "ke kika sani kuma, ni dai gayyata ta akayi kuma banga inda akace akwai banbancin kwalliya tsakanin wance da wance ba, dan haka sai kiji da tsirfar ki".
Maesha ta girgiza kai kawai tace, "Yanzu kiranta za'ayi ne ko yaya".
" Mu kirata ta mana uwar me bayan ga katin mu a hannu, ai mu shiga kawai mu nemi wajen zama ma haɗu a ciki".
Maesha bata ce komai ba suka fara takawa dan ƙarasawa kofar hall din, jin ƙarar mota a bayansu yasa Maesha faɗin, "Mu bada hanya meelah ga mota nan".
"Allah yasa jirgi ne, ba inda zamu dole su jira mu wuce, kema in kikace zakiyi rawar kai a banza zaki balle da wannan takalmin". Haka suka cigaba da tafiyar su, Moha dashi ke tuka motar harya fara kulewa ganin yana ta musu fitila sunyi banza dashi, sai ma wata tafiya da suke kamar baza su taka ƙasa ba.
Faez ne yace, "Wai wanna kurame ne ne?".
Horn ya danne masu, ba shiri suka juyo tayi dan ganin wani dan masifar ne zai kashe Musu dodon kunne bayan akwai hanyar da zai iya kintatawa ya wuce in ma ba zai iya jira ba.
Faez ne ya fara cewa wannan ai kaman su Maesha ko?.
Murmushi yayi Kana yace ba kama bace ita ce.
"Kai ka gayyaceta kenan?". Faez ya fada yana tsare shi da ido.
"Bani bane, amma kasan yayarta ai kawar safna ce watakil su suka gayyacesu, taka motar yayi yasha gabansu Maesha da har ta saddaqar yatake Mata Yan yatsu ta runtse Ido da sauri Jamila tayi baya.
Kashe motar yayi ya fito, bude idonta tayi jin an kashe motar a gabansu sai akan face dinsa, kifkifta Ido tafara kamar batayi zaton ganinsa ba.
Sassanyar Murmushi ya sakar mata yaja dogon hancinta yace, "Matsoraciya kawai, ga tsoro ga rashin ji".
" Wai dama kai ne".
"Ni dinne dai, bakiyi Tunanin gani na bane".
"Na san zaka zo mana, ina wuni".
"Kina lpy?". Ya tambaya a daidai lokacin da Faez ya zagayo wurinsu, cikin mamaki take kallansa kafin tace, "Doctor kai ne? ina wuni".
Cikin sakin fuska ya amsa da lpy klau mamynmu, ya mutanan gida?".
"Lpy kalau alhamdulillah". Ta faɗa tana kallon Moha sai kuwa ya kashe Mata Ido, saurin dauke kanta tayi kamar bata gani ba tace wa Meela da taja gefe tana latsa waya kamar bata gansu ba. "Meela to muje ko".
"Sai da kika gama shanya ni zakice muje, ashe ma kin sansu shi ne suke ƙoƙarin banke mu". Ta faɗa tana matsowa wurinsu.
"Banda sharri fa Hajiya, a dinga tsoron Allah".
Kai tsaye tace, "In banji tsoron Allah naka zanji bawan Allah, ke kuma muje ".
Yar dariya Faez yayi ya kalli Maesha yace, "ita ce wadda kuka zo ranar ko?".
"Eh ita ce, yar uwa ta ce".
"Amma kuma halin ku daban daban".
"Malam me kake nufi, karka faɗa min ba sugar mana".
"Ahhh namijin goro zan faɗa Miki". Nan fa suka fara Faez na tsokanar Meela ita kuma ta zage sai tsiwa take zubawa dan bilhakki da gaskiya take daukan zancen Faez ɗin sam ta kasa fahimtar tsokanarta yake.
Moha ne ya kalli wrist watch dinda ke a hannunsa Kafin yace, "Muje Mamy". Ya fadawa Maesha a saitin kunnenta, daga masa kai tayi tana juyawa wurin Meela tace, "Mu ƙarasa Meela, kinga ummu tace kar fa mu wuce 10.
Bata ce komai ta shige gaba Faez ya bi bayanta, maesha moha kuma suna daga bayansu, "Mesa baki sanar min zakizo ba".
kallonsa tayi da niyyar bashi amsa amma sai ta shagala da kallon sa dan gani tayi kamar yafi ko yaushe kyau. haɗa yatsunsa biyu yayi ya buga mata saitin fuskarta sukayi kara.
Kunya taji ta rufeta tayi saurin sunkuyar dakai, ganin ta tsargu ya sashi faɗin, "Kinyi kyau sosai Mamy".
"Ai ka fini yin kyau". Ta faɗa ba tare data kalleshi ba. Faez ne ya juyo yana faɗin, "Moha kawo gate pass din ku a hada a basu". Hannu ya mika mata ta mika masa nata ya hada da nasa ya bayar.
Suna shiga arrangement ɗin nasu ya watse don Meela ta dawo baya Kusa da maesha, shi kuma Faez yana gefen Moha, hall din a cike yake tako ina da alama an daɗe da farawa amma dai amarya bata iso ba, yadda ido ya dawo kansu yasa Maesha fara hardewa sai ta rage tafiya don gani take kamar ita kadai ake kallo, zamewa taso yi meela ta damqi hannunta ba tare data kalle ta ba dan ma kar a fahimci faduwa Maesha taso yi.
"Mu zauna ta can Meela".
"A a whl, nutsu kawai mu ƙarasa daga can".
Moha ne yace, "Eh gsky muje daga gaban". Kamar zatayi kuka haka suka ƙarasa last table daga shi sai high table, rabuwa sukayi su Maesha sukayi right side su Moha sukayi left sai ya zama suna opposite da juna .
Meela ce ta zaro iPhone ɗin da Moha ya barwa Maesha daga cikin jakarta ta shiga ɗaukan su hotuna, dan dama itace tasa Maeshan dole ta dauko wayar wai zasu kece raini, sai da suka gama tace, "Ke wai ina kika san wancan me white Geztner ne? Sai naga kamar shine wanda muka taba haɗuwa a hospital din Dr faez ko?".
"Eh kuma shine ne wayar da kike hoto da ita yanzu ba".
Gyara zama tayi tana faɗin, "Bangane ba?". A takaice Maesha ta mata bayanin waye Moha.
Meelah tace, "Yar iska shi ne baki taɓa faɗa min ba, ba ruwana dake whl".
"Bafa abinda kike tunani bane meelah".
"Ummm". Ta faɗa tana tura mata keya, daidai lokacin masu anko suka fara shigowa da alama daga wurin kwalliya aka kwaso su, hameedah da Maryam sun sha kwalliya cikin ankon su ga kitson attachment nan kamar zaiyi magana".
Meela ce ta juyo wurin maesha tace, "ke ni kam kamar Maryam nake gani ko".
"Ita ce mana, ai bai kamata kiyi mamaki ma mu ma aka gayyace mu ballantana su masu abu".
Tabe baki Meelah tayi kawai, wucewa sukazo yi Meela ta kwala kiran Maryam, tare suka juyo ita da hameedah sai kuma wata ta ƙaraso wurinsu tana magana da Hameedar ita kuma Maryam ɗin ta nufo wurinsu Maesha, "Maesha ashe ku ma kunzo.
Meelah tace, "Ba dole muzo ba PA amarya ta kawo mana kati har gida".
Hameedah ce ta karaso wurin ta Mika masu hannu suka gaisa tace, "Maryam ashe kunsan juna?.
"Eh whl course mates dina ne ai.
"Allah sarki ...." Wayarta da ake kira ya katseta hade da barin wurin tana faɗin, "Maryam ki zauna wurin su ina zuwa". Ta karashe tana Wucewa.
Kujerar kusa da meelah taja ta zauna tana faɗin , "Ashe kunsan juna da Hameeda?".
Meela tace, "Whl kuwa ai yayarta friend ɗin yayar mu ce". Nan aka shiga hira tsakanin Meelah da Maryam amma duk amsar duniya Meelah sai ta jefawa Maryam magana a fakaice ita kuwa ta saki baki sai nuna isa take .
Ita dai maesha duk ta takura saboda motsin duniya zatayi sai taji idon Moha a kanta, haka har amarya da ango suka iso, hameedah tazo jan Maryam tace, "Kash gashi bakuyi anko ba da sai muje tare, za'a shigo da amarya ne".
Meelah tace, "kuma kinga da munyi ankon nan da mun karawa gari hayaniya ba".
Maida kallon ta tayi kan Maesha tace, "Bari muje". Tana faɗin haka suka wuce, Meelah ta bisu da hararar gefen ido tare da faɗin, "Shegiya Maryam an samu shiga sai wani rawar Kai ake".
Girgiza kai kawai maesha tayi tace, "To yanzu kuma mai ta miki, bakya ganin Matsayin da take dashi wurin masu bikin".
Tsuka taja ta dauke kai, ita kuma ta maida hankalinta kan wayarta.
Shi kuwa Moha idonsa akan Maesha sai ɗaukanta hotuna yake ba tare da saninta ba, Faez da shima yana lure da Meelah tunda suka zauna ya ɗan karkato wurin Moha yace, "Malam Ni fa inaga nayi kamu".
Kallonsa yayi yace, "Me ka kama?"
"Wannan meelah ɗin mana yar uwar mamynka, kaga tunda duk gida ne ka gabatar dani kawai".
"Kauɗi kauɗi kenan, ina jin yadda kuke karawa ai tun daga waje dama irinta ne daidai kai ai".
"Naji dai, ni dai yanzu a san ya za'ayi dani".
"Za'a duba lamarinka". Ya faɗa hankalinsa akan wayarsa yana rubutawa Maesha text.
Amarya da ango sun shigo anfara gabatar da event anci an sha an girgije, ita dai Maesha tsakura kawai tayi dan bata saba cin abinci sosai cikin mutane ba, ita kuwa Meelah ta haɗa da nata taci ta koshi abinta Maesha nata mata magana tace kanki akeji.
Faez kuwa sai dariya yake Moha ya kalle shi yace, "Kai lpy dai?".
"Man, i love this girl whl, tana burgeni".
"Hmmm". Ya faɗa yana maida hankalinsa kan amarya da ango dake rawa.
Haka ce takasance wajen moha shima tsakura kawai yay, 10 nayi Maesha ta cewa meela, "Tashi mu wuce kinga dare ya fara.
" To ai saiki tsaya hameedan tazo Ki mata sallama kar tace abinci mukazo ci".
"Abincin ma bakici bane". Maesha ta faɗa tana harararta hadi da dannawa Hameedah kira, saidai har ta katse bata daga ba, sake Kira tayi sai a nan ta daga saboda hayaniya da kida dakyar ta iya jinta. "Ohk ina zuwa". Hameeda ta faɗa. Safna ce tace, "keda waye?".
"Maesha fa, wai tafiya zasuyi.
"Au tazo ashe, tana ina ne, ni ai ban ma ganta ba.
" Suna can ta gaba ne.
" Ohk kikawo ta mu gaisa mana kafin su wuce, ga su Momma ma sai ta gaishe su.
"okay". ta fada tana wucewa ganin wayarta na ƙoƙarin mutuwa yasa ta fara tsayawa side ɗin su Moha ko zata samu power bank tasan bazai rasa. Duk da ma dai tunda yamata rashin mutuncin nan ta daga masa kafa. A gaban table din su ta tsaya Faez yace, "Su Hameedah kirjin biki, anan nan ana ta kai kawo dai.
"Whl kuwa kaidai bari ana ta hidima, ya moha power bank zaka aramin plz nasan baza ka rasa ba". Bai dago ba balle tasa ran zai amsa Mata Faez ne yace, "Banji fa yau mun fito da power Bank din nan.
Duk da taji Hushaima basar da ita da Moha yayi sai ta saki murmushi tace, "Bari nema wurin su ya Adam to". Ta faɗa tana nufar wurin su Maesha, Maryam dake zaune kusa da su Meelah tace, "Ke da ya Moh din naki ne kenan, naga sai murmusawa ake".
Wani makirin murnushin ta sake saki, "Ke dai bari ya Moh ko rigima.
"Ai wanna ya moh din naki sai ke gwara ma ayi auran kuje can ku karata abunku kowa ya huta".
Maesha tana jinsu sai taji wani abu ya tokareta a kirji har saida ta runtse Ido dan jin maganar Maryam din tayi kamar ta zuba mata narkakkiyar dalma a zuciya amma saita fisge kamar basu take saurara ba har saida hameedan tace, "Maesha tafiya zakuyi da wuri haka?".
Lura da yanayin data shiga yasa Meela faɗin, "Whl Ummu ce tace karmu wuce 10.
" Allah sarki to muje Ku gaisa da aunty safna kafin Ku wuce.
Da Okay ta amsa sannan suka miqe Meelah ta yiwa Maryam dan daga can zasu wuce. "To maesha sai mun haɗu a school ". Maesha tayi Murmushin yaqe tace, "In sha Allah".
Faez ne yace, "Ba dai tafiya zasuyi ba.
"Su wa? Moha ya tambaya dan yayi zurfi cikin kallon wani pic din daya dauki maesha ne.
"Su mamy mana". Dan tun ranar da yaji moha nacewa mamy shima yakama saboda ya gane dalilin sunan momma ne saisa shi ma ya saye.
Sai a lokacin ya dago yaga basa nan, "ina suke ?".
"sunyi can tare da hameeda, kuma inajin tafiya zasuyi, ni damuwata ma ban karbi number meelan ba".
Kiran wayarta moha ya fara amma bata picking kusan three missed calls sai ya dauka ko saboda taro ne batajin karar wayar, mikewa yayi Faez yace, " Ina zuwa kuma?
" I'm coming". ya fada Yana kokarin barin table din.
"To tsaya mu tafi tare.
" No yi zaman ka
" Kai dalla ni ba kai zan bi ba number zan je amsa.
"Wai yane? ka bari zan baka number mana idan mun koma gida".
Komawa Faez yayi ya zauna dan a tunaninsa ko Maesha zai tambaya ta turo masa number sai ya bashi, shi kuma ya fice yana kalle kalle, saidai sama da ƙasa bai hango ko mai kama dasu ba, jim yayi yana tunani in dai tashinsu Kenan Faez ya tabashi to bai kai ace sun tafi ba hakan yasa ya jingina jikin motarsa yana facing hall din still Yana sake kiran number maesha.
A bangaren Maesha kuwa tanajin vibrating din wayar kuma taga shine amma taki dauka har suka isa wurin safna suka gaisa sukayi mata Allah ya sanya alheri nan tace suzo su gaishe da momma, kamar Maesha zatace mata lokacin da aka basu har ya gota sai kuma tayi shuru, suka bita a baya zuwa table ɗin su momma, suna zaune ita da uwar amarya da mama fatima sai iyayen su faez mata, "Momma ga su Maesha zasu tafi".
Risinawa su Maesha sukayi suka gaishe dasu momma, cike da faraa momma take tambayar Maesha mutanan gida, ta amsa da "Kowa lpy kalau Momma".
"Tafiya zakuyi da wuri haka?
Kanta a kasa tace, "Eh whl, dake a gida ance kar muyi dare ne.
" Eh kuma gsky ne to Allah ya muku Albarka, da abun hawa kuka zo ne?".
"Eh".
"Ohh, to ba damuwa mun gode kunji, ku gaida iyayen naku".
"Zasuji in sha ALLAH". Suka faɗa suna barin wurin.
Uwar amarya ce tace, "Ayshah wannan yaran fa?".
Mama fatima ta amsa da, "kannen kawar Safna ne ai".
"Amma dai daga gani ba namu bane". Dariyar manyan mata sukayi kafin tace, "Eh nasu ne can gabas ta tsakiya, yan Oman ne ai".
"Yauwa nifa in ce daga ganin ta gaban ba tamu bace, Masha ALLAH gata da nutsuwa kuma, ai ba dan kar a gwale mu ba da na tambayawa Sadeeq".
"Ahhh to me zai hana in dai da gaske kuke sai ku motso kawai". Da haka suka cigaba da hirar su Maesha.