Free chapter · Read without an account
PAGE 21
Suna fitowa Meelah tace, "Ke wai me ya sameki lokaci guda kika yi wani sukuku ko baki jin daɗi ne ?"
"Bakomai fa mee.... Shan gabansu da yayi ya katse ta, "Mamy ina ta kiran wayarki bakiyi picking ba shine zaki tafi ba sallama, haka akeyi?".
Meela ce tace kinga ni barin jiraki a mota". Ta fada tana barin wurin, Maesha bata ce komai ba ta shiga ƙoƙarin keɓewa ta wuce, sake shan gabanta yayi yana faɗin, "Mamy magana fa nake kina kokarin wucewa, wai meke faruwa ne".
"Me kake so in ce ne Moha, dan allah ka bani hanya in wuce". ta fada da rawa muryar. Wata zuciyar tace miye naki na tada hankali dama ai be taɓa cewa yana sonki ba ballantana azo maganar aure....
Katse mata tunanin yayi ta hanyar faɗin, "Yanzun fa muka shiga lpy, wani abun ne ya faru? fadamin mana kinyi shuru?". ya Tambaya adan rikice, step daya taja baya idonta cikin nasa suna kallon juna kusan second 60 kafin ta sauke kanta tana maida kukan dake neman kubce mata tayi Murmushin ƙarfin hali tace, "Ashe dai duk yadda muke akwai abinda ake ɓoye min, yanzu da saidai inji a gari, za ai min aunty bansani ba, maybe ma da ko bikin bazan sani ba".
kallonta yake kamar wani sakarai dan ya kasa fahimtar maganarta ta, "Ban fahimce ki ba, bikin wa za'a yi baki sani ba?".
Harɗe hannuwanta tayi a kirji tana ƙoƙarin tausar kanta ba tare data kalle shi ba tace, "Auranka da auntyn mu Hameedah mana, ashe abu ya kankama haka, ko da yake ni bani da matsayin da za'a iya faɗamin ai, bakomai Nagode". tana gama fadin haka ta wuce shi ta nufi wajen motarsu da sauri har tana hardewa, tana shiga Meela ta tada motar suka fice.
Sai da suka hau titi meelah tace, "Wai me yake ce miki?". Jin shuru yasa ta juyo sai kuwa tayi arba da hawaye shimfide akan fuskarta. "Subahanallahi Maesha, dan ALLAH miye damuwarki, ki faɗamin karki boyemin bazan juri ganin kina zubar da hawayen nan ba".
Wani kukan taji ya taho Mata tace, "Meela ya zaimin haka meysa saida ya koyamin sonsa zai yaudareniiiii".
Takarasa da kukan. "Shi waye wai? Moha din?". Ta jero mata tambayoyin itama.
Bata iya amsa mata ba ta cigaba da kukanta har suka ƙarasa Meela tayi parking a ƙofar gate din su Maesha. Share hawayenta tayi ta shiga ƙoƙarin buɗe kofar, meelah ta kira sunanta, "Maesha!".
Juyowa tayi amma ba tace komai ba. "To kinga, kiyi shuru karkiyi kuka da safe zanzo kinji". Girgiza Mata Kai tayi sannan ta fice ta buga gate ɗin, ba bata lokaci me gadin ya buɗe mata yana mata sannu da zuwa ta shige ba tare data saurare shi ba.
A bude ta samu kofar parlourn basu Kai ga kullewa ba duk suna zaune kamar yadda suka saba, da sallama ta shiga suka amsa mata.
Ummu tace, "Sai yanzu kuke dawowa Maesha, kinga time kuwa wajen 10:38pm fa".
"Ummu kiyi hakuri whl muna ta sauri ma.
"Kya ce haka ai.
Abba yace, " Mamana me ya samu idonki yayi ja haka".
Murmushin yaqe tayi tace, "Wani abu ne ya fadamin a Ido, ummu zan shiga in kwanta saida safen ku Abbah". tana faɗin haka ta wuce daki.
Ummun ta kalli abbah amma kafin tayi magana Ameer yace, "Ummu kamar akwai abinda yake damun Maesha fa".
Shuru tayi bata che masa komai ba ganin haka yasa ya tashi yai musu saida safe ya wuce ɗakinsa.
Maesha na shiga daki ta rage kayan jikinta ta fada toilet, agurgurje tayi wanka ta ɗauro alwala ta fito, doguwar rigar bacci ta zira ta sanya hijabi ta tada sallah, sallar isha i ta rama sannan tayi shafa'i da wutiri kamar yadda ta saba kafin ta shafa sannan ta tashi ta hau gado tai addu'a ya rufe idanunta amma bacci yace baisan zance ba, tunane tunane ta shigayi take hawaye ya shiga mata zarya, itace har biyu na dare bata samu bacci ba.
MOHA
Tunda maesha ta gama magana ta wuce yake in shock maganganun ta yake maimaitawa amma kansa ya kasa ɗauka ballatana ya sanya kowanne a ma'auni, komawa cikin hall ɗin yayi faez ne yace, "Ka gansu?".
Shuru yayi kamar baiji ba, "Ya dai inata ma Magana kayi shiru, me ya faru ne?". Faez ya sake tambaya ganin yadda yanayinsa ya sauya daga yadda ya fita.
"Bakomai". Ya fada yana dauke kai gefe guda ya shiga saka da warwara, zuwa 11 ya miqe yace, "Faez, kaga tashi mu wuce kawai".
"Baza mu ƙara ko da 30 minutes ba?". Girgiza masa kai yayi alamar a'a, haka Faez ya miqe dan yasan tunda yace a'a to fa ba zai zauna din ba.
Haka suka fita suka tafi gida, ko da suka shiga Moha ya kasa zaune ya kasa tsaye safa da marwa kawai yake, shi kuwa faez zama yayi yana kallonsa ganin abun bana karewa bane ya sashi tashi ya shige daki yayi wanka, saidai har ya fito moha yana safa da marwa a Inda ya barshi. "Malam ni wai gamo kayi ne?". Faez ya tambaya a tsorace dan abin Moha ya fara bashi tsoro.
Moha da wani tunani ya shiga kansa yasa ya juyo rai a bace zaiyi Magana sai yaji horn ɗin mota, fasa maganar yayi ya nufi jikin window ya yaye labulen, ganin motar su momma ce yasa ya komo yana faɗin, "In ma gamon nayi idonka zai gane ma yanzu". ya fada still Yana tsaye.
"Hmmmmm". Faez ya faɗa yana barin falon.
12:40am daidai aka sakeyin horn wata motar ta shigo, a lokacin kuma faez ya dawo falon da mug ɗin coffee a hannunsa, sake leqawa Moha yayi kamar yadda yayi dazu, da sauri ya juyo ya zari wayar sa dake Kan table ya dannawa wata number da ko suna babu kira, ring uku aka dauka, "Karaso part ɗin mu yanzu". Shi ne abinda ya faɗa kawai ya kashe wayar yana cizar lips ɗinsa da karfi kamar zai rabashi biyu.
Ajje mug ɗin Faez yayi ya buga tagumi Yana kallon ikon Allah dan shi whl yanzu lamarin ya fara bashi tsoro. Hameeda ce ta turo ƙofar ta shigo gwagwaronta a hannu ba ko sallama sai cewa da tayi, "Gani na amsa kiranka ya Moh".
Kujera ya nuna Mata da hannu ba tare da ya kalleta ba, ganin Hameedah ce wadda Moha ya kira ga kuma yanayin da Moha din yake ciki yasa Faez silalewa tun kafin ma Hameedar ta lura dashi a parlourn ta samu bakin faɗin ai gaban idonsa akayi kaza, can kuryar dinning ya koma ya labe ya zuba masu Ido.
Moha ne ya dora kafarsa daya akan center Table ɗin Kafin yace, "Me kika fada mata?
"Wacece ya moh?". Ta tambaya tsakaninta da Allah.
"Maeeshah". ya fadi sunan kamar bayaso.
"Maesha kuma? To me zan fada mata ni da bama tare muka zauna ba".
Kallon ta yayi amma baice komai ba, "Ka santa ne dama ya Moh ?".
Cikin tsawar da saida hantar cikinta ta Kada ya sake faɗin, "Karki kawo min shashancin banza da wofi mana, whl whl whl kikamin karya Hameedah saina take kanki a falon nan sai dai duk abinda zai faru ya faru". Ya faɗa da iyakar bakin gaskiyar sa.
Kuka ta fara a tsorace ganin yanayinsa ta shiga faɗin, "Whl na rantsema da Allah ya Moh ban yi maganar Ka da itaba, kamar yadda na fada ma ne tunda muka gaisa da ita saida zata tafi ta kirawoni mukayi sallama, whl Allah bance mata komai akanka ba bansan ma ta sanka ba".
Murmushin kin ma rainawa kanki hankali yayi lokaci guda kuma ya sake birkicewa yace, "Karya kike whl". Ya faɗa da tsawar data sa Faez ya sake kulewa a lungu, Hameeda kuwa bata san lokacin data sauko kasa ba ta rike kafarsa ɗaya, "Dan girman allah Kayi hakuri whl ni banyi maganar ka ba saidai na tuna a lokacin da nazo tambayarka power bank ɗin nan ya Faez yace babu na koma wurinsu sai ƙawata Maryam take tsokana da sunan ka". Ta faɗa tana takure jikinta waje guda.
"Okayyy har tsokanar ki ma ake da sunana, Munafuka algunguma uban Mai kikace keda shegiyar ƙawar taki? wato ma gulmata kike zuwa kina yi keda Munafukan kawayenki ko?".
"Allah ba komai tace ba itama tayi maganar ne cikin wasa take cewa ke da ya Moh ɗin naki ne, irin dai haka".
"Owoooo , to na fahimta watau zuwa kike kina cewa kawayenki ni saurayinki ne ko?". Shuru tayi tana cigaba da hawayen takaicin daya gumeta jin wai duk wannan akan wata macen ne yau Moha ke mata wannan wulakancin.
"Dan ubanki magana nake, shegiya me zubin Munafukai".
" Kayi haƙuri hakan baza ta sake faruwa ba".
"Allah yasa ma ta faru ki ga yadda zanyi dake, banza karya marar zuciya get out of my side".
ya ƙarasa a tsawace, batasan lokacin data ganta a bakin kofar ba kamar wadda iska ta dauko.
Ajiyar zuciya ya shiga sauke wa kafin karshe ya yiwa kansa masauki kan kujera, ya dafe kansa dake sara masa saboda ihun da yayi, ya dau wasu mintuna a haka kafin ya bude Idanunsa ya sauke su akan Faez dake leqen kofa dan ganin ko Hameedah ta wuce. Moha ne ya mike zai shige ciki Faez ya juyo suka hada ido, tsaki yaja kawai ya shigewarsa ya barshi.