Free chapter · Read without an account
PAGE 24
Meela na kwance tana ta tunanin yadda zata iya fito da maesha da magribar nan sai wata idea ta fado mata da sauri ta dauki wayarta ta dannawa maeshan Kira bugu biyu ta dauka, "Hello Meelah ya akayi ne?".
Cikin murya irin ta marassa lpy masu jin jiki tace, "Kin ganni nan ba yadda nake, raina a hannun mai duka".
Hankali tashe Maesha tace, "Subahanallah meya sameki haka Meelah? Dazun fa mukayi waya lpy".
"Ki bari kawai rashin lpyr lokaci daya kinga har ƙarin ruwa sai da aka min, likitan yace maybe ma sai an hada da jini".
"Innalillahi wa inna ilaihir rajuun kina wani asibitin ne?".
"Ina gida ne ai".
"To bari nayi sallar magriba sai in shigo, Allah ya kara afuwa yasa kaffara".
"Ameeen". Ta amsa kamar gaske sannan ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya tace, "Saura yadda za'ayi ta bini mu fita". Tashi tayi ta shiga wanka kasancewar ita tana fashin sallah, a gurgurje tayi wankan ta fito ta shirya cikin wani lace milk colour Mai touch din custard colour ɗinkin skirt da riga da ya matuqar zama a jikinta dan Meelah tana daga cikin matan nan ne kosassu, ba za dai a Kirata da me kiba ba amma duk kayan da tasan sai ta cika su kuma sun mata kyau. Gyara fuskarta tayi ta sa dan kunne da sarka masu ruwan gold ta kafa dauri me tashin kai ta dauko custard colour mayafi da jaka da takalmi ta ajje bakin gadon sannan ta fita zuwa dakin ummansu ta shiga bata ganta ba tasan bazai wuce tana dakin daddy ba dan haka ta nufi can.
Saida tayi knocking aka bata izinin shiga tukunna ta sa kai suna zaune suna yar hira tace, "Barka da hutawa daddy".
"Yauwa daughter, ina zuwa haka?".
"Amm daddy dama maesha ce ummunsu ta aiketa shi ne tace zata biyomin na rakata.
"To ba damuwa, amma karku dade kinji ko".
"In sha ALLAH, umma sai na dawo". ta fada tana mikewa.
Daddy yace, "Amma da mota zaku fita ko."
"Eh Daddy da motata zamu".
"Okay, Amma da safe Malam hadi yace da ya tada motar m mai ya kare dan haka zan miki transfer yanzu sai ku tsaya ki mata full tank tunda Monday ne zakuyi resuming school ko ?
"Eh daddy".
"To Allah ya kai mu". Ta amsa da ameen tana juyawa ta fice.
Umma ce tace, "Amma daddynsu Kana ganin saken da kakewa Meelah baiyi yawa ba macace fa... "
"Dakata jiddah karki fara da Allah, wani sake ne nawa Jameela kuma? Ni nasan tarbiyyar bana bawa yata kuma na yarda da ita dan haka a duk lokacin da kika san bakinki ba zai fadi alheri ba kiyi shiru".
" In sha Allah". Ta faɗa tana cigaba da lazimin ta.
Meelah tana fita daga dakin ta sauke ajiyar zuciya tana fatan Maesha ta karaso kafin umma ta fito.
A bangaren Maesha kuwa Meelah tana gama waya da meelah ta fita ta sanarwa Ummu abinda ke faruwa cikin damuwa, ummu tace, "Allah sarki Jamila Allah ya bata lpy yasa kaffara, amma irin wannan ai bai kamata a barta a gida ba ko kuma mahaifin nata baya nan ne?".
Maesha tace, "Whl Nima ban sani ba amma da naji halin da take ciki kuma tace min tana gida nayi mamaki".
Ummu ta ɗan yi shuru cikin jimami kafin tace, "To Allah ya kyauta, ni ma ba dan zanje barka ba da munje tare amma Ki mata sannu in sha allah zanshiga in dubata ko zuwa safe ne.
"To shikenan ummu zan fada mata". Ta faɗa tana komawa daki ta shiga ta ɗauro Alwala saboda har an fara kiran Sallah, ko da ta idar da sallar sai ta yi azkar din marece sannan ta tashi ta dauki abayarta black me adon red stones ta daura kan kanana English wears din dake jikinta, ta ɗaura ribbon ta nade gashinta tayi rolling ɗin mayafin ta zira Madam luxe din ta, ta dan goga kwalli ta dauki wayar ta ta fita ta yiwa ummu sallama ta wuce.
Ko da ta shiga bata samu kowa a falon ba dan haka ta wuce dakin Meelan, a zaune ta sameta bakin gado, da mamaki ta bita da kallo kafin ta karasa tana faɗin, "Amma baki kyauta min ba Meelah, kin san yadda kika tayar min da hankali kuwa, ashe jikin ma da sauki, Kai Meelah tsab zaki iyasa jinin mutum ya hau whl".
Tashi tayi tana faɗin, "ke bari kawai, naji jiki ba karya ". Sakin baki Maesha tayi tana kallon kwalliyar da meelan tayi har ta kasa shuru tace, "Wanna kwalliyar fa ko duk acikin rashin lpyr ne?
" Asibiti zani fa Dr yace yana da patients sosai tunda har naji dan dama dama in je kawai ya sake dubani acan din, tunda kinzo ma saiki rakani".
"To ai ni bancewa ummu zani wani waje ba, nan kawai nace Mata zanzo har tana maki ya jiki tace ba dan zataje barka ba da tare ma zamuzo amma zata zo ko da safe ne".
" Allah sarki ummun mu, whl kice mata da sauki kar ta wahalar dakanta basai tazo ba". ta fada tana daukan makullin motar ta dauki jakarta da mayafin ta sa takalmin ta nufi kofa.
Maesha da lamarin meela ya fara daure mata kai ta bita da kallo kawai dan ita bataga alamar wani rashin lpy a tattare da itaba, dan wannan kwalliyar tafi karfin zuwa asibiti, anya kuwa? Amma bari inga gudun ruwan nata.
Katse Mata tunani meelah tayi ta hanyar faɗin, "Muje ko".
Bata ce komai ba ta tashi suka fito, saida suka shiga mota Maesha tace, "Ni kinga kin rikitani ko umma ma ban gaisar ba.
" Umma bata nan idan mu dawo kwa gaisa". Ta faɗa tana tada motar, tayi reverse me gadin ya bude suka fice.
Sai da suka tsaya suka sha mai sannan suka dauki hanya wayar meela tayi Kara dauka tayi dan tayi tunanin Moha ne kuma dama tana son kiran nasa amma sai taga bashi bane new number ne, kamar baza ta daga ba sai kuma ta daga ba tare da tace komai ba. "Barka da dare ranki shi dade". Ta tsinkayo muryar Faez ta cikin wayar, amsawa tayi da, "Ahh doctor ai ban gane number ba.
"To gata nan dai tawa ce, sai ayi saving, kun samu fitowar kuwa?".
"Eh ina hanya na kusa ƙarasowa". Ta faɗa kawai saboda Kar maesha ta zargi wani abu.
"Ke kadai kika taho ne? mamyn fa ?".
"Okay in na karaso ɗin zan kiraka, ba damuwa fa da sauki". Tana fadin haka ta kashe.
Shuru Faez yayi riqe da waya yana tunani yana Juyowa sukayi 4 eyes da Moha da yake kallonsa cikin damuwa yasha wanka cikin kananan Kaya Ash jeans da red t shirt sai long sleeve denim jacket ash da ya daura a sama yayi kyau abinsa.
"Gaskiya akwai matsala". Moha ya fada .
Girgiza masa kai Faez yayi yace, "Babu, saboda a yadda na fahimta suna tare kuma bata so ta sani ne har sai sunzo Shiyasa".
"Allah yasa". Moha ya fada a sanyaye.
PAT∆∆SH
Maesha ce ta kalli meela dan ta fara tsorata tace, "Nan ne asibitin ?
Riqo hannunta tayi tace, "Maesha kinsan dai bazan cutar dake bako, idan har kin yadda dani da kuma amintar mu to ki sauka muje kuma karki tambayeni komai nafi son idonki ya gane Miki".
Cikin dar dar maesha ta bude kofar motar ta fita suka nufi ciki. Kiran faez Meelah tace, "Gamu mun karaso, kuna ina?
"Ku karaso ciki, zaku gan mu".
"Ohk". tace tana sake riko hannun maeshan da gabanta ke ta faduwa dan sai yanzu take dana sanin biyo meelah ba tare da sanin kowa ba.
Text ne ya shigo wayar meela tana dubawa taga yace table ɗin dake gaban ku.
Kallon wurin tayi sai taga ma ai ba kowa da alama duka wajen sukayi reserving, zama sukayi a table ɗin da Faez yace aka fara kawo masu abubuwan tabawa, itadai maesha tayi shiru tana kallon ikon Allah, Hameeda taja mocktails ta hau sha tana dannawa Faez kira yana dagawa tace, "Kuna ina ne, kasan bamu da enough time".
"Turn back". Juyowa tayi sai kuwa idonta ya sauka akan su, thumb ya mata alamar jinjinawa ta masa sannan ta juya saboda hayaniyar da taji, ma'aikatan wuri ne ɗauke da cake Mai hawa uku suna nufo su suna raira wakar happy birthday da bakinsu har suka iso suka dire cake din a gaban maesha, kallon cake din tayi an rubuta HBD Mamieh, da sauri ta kalli Meela sai kuma ta mike, itama meelan mikewa tana kallon yadda take waige waige dan tasan tabbas wanda ya shirya wannan abun yana wurin nan wato moha, dan tunda taga sunan Mamieh ta fahimci shirin sa ne tunda shi ya sa mata sunan.
"Wai me kike nema ne?". Meelah ta tambaya.
Wata waqa ce ta fara tashi me suna, AISHA'S BIRTHDAY "Baby girl, make u don't, I say baby girl today is your day, I say baby girl be feeling joy, Aisha be feeling joy, we will dance a whole day, we will dance a whole day. Aisha u re lucky, Cox now u re one year older I pray to Allah to give u more years aysha aysha aysha baby Aisha.........
Daga bayansu sukaji anabin wakar suna juyowa suka ga moha tsaye rike da wani box Mai kyau anyi wrapping dinsa, Faez ta kalla shi kuma rike yake da wani stick guda biyu Masu dauke da happy birthday juyawa tayi wajen meela saita ganta ta daga balloons biyu daya 1 daya 9 rufe bakinta tayi da hannu sai kuma ta shiga dariya, haɗa baki sukayi wajen cewa happy 365 days in return mamyy.
Tafin hannunta ta sanya a both cheek dinta tana murmushi sai kuma ta miqa hannu ta karbi box ɗin da yake miqo mata ta ajje akan table ɗin tana fadin, "Thank youuuu so much".
Zagayowa sukayi suka zauna su duka da moha da Faez na fuskantar Maesha da meelah.
Ta dubi meelah tace, "Meysa baki sanar dani ba".
"Kin taɓa ganin an fadi surprised".
Sun sake Dan gaggaisawa kafin su tashi yanka cake din Faez da Meela suka Mike suka saita camera, ma'aikatan nan kuwa daga inda suke ma wakar birthday ɗin dake tashi suke bi suna tayasu da tafi harda masu rawa.
Wuqar Maesha ta rike shi ma ya ɗan daura yatsansa a gefe suka yanka, ta ɗauke hannunta shi kuma ya sanya nasa ya yanko ya nufi bakinta dashi, dan kauda Kai tayi cike da kunya, ya ɗan sunkuyo ya mata rada mata a kunne, bude bakin tayi kadan yasa mata itama ta karba ragowar tasa masa, meelah ta ƙaraso ita ma ta sa mata.
Shi kuwa Faez cewa yayi, "To tunda ni duk an tsane ni babu me sa min ku bani waje in ciyar da kai na".
Moha yace, "Tsaya in sama, rufe idonka".
Dan harararsa yayi kafin yace, "Mamy kina kallo in kinga mugunta zai min ki faɗa".
Tana dariya tace, "To".
Rufe idon yayi Moha ya lakuto icing ɗin ya kambala masa a hanci, da sauri ya buɗe ido dariya suka kwashe da ita su duka, ya dauki tissue yana, "Bakomai rayuwa ce".
"Sorry". Moha ya faɗa yana dariya.
Meela tace , "Rabu dasu Dr, zo ni in sa ma".
"Yauwa meelanmu". ya fada Yana zagayowa bangaren meelah ta yanko tasa masa ragowar ya maida bakinta sannan suka koma opposite dasu moha amma a tsaye.
Moha ne ya gyara tsayuwar sa nima mai dauko muku rahoto na qara gyara tawa tsayuwar saboda dauko maku komai yadda yake.
"Maeeshah".
"Na'am". Ta faɗa ba tare data kalle shi ba dan yau wani kwarjini taga yakara Mata.
"Maesha". ya sake kiranta a Karo na biyu.
"Ummm". ta fada cikin sanyin da kusancinsu ya haifar Mata.
"Dago ki kalleni".
A hankali ta dago ta kalle shi amma sai taji baza ta iya jure irin kallon da yake Mata a yanzun dan haka ta fara ƙoƙarin sake maida kan nata kasa, hannunsa yasa ya dago habarta ya saka idonsa cikin nata, bata da zabin da ya wuce ta kalleshin magana ya fara kamar haka "how do I even begin to reveal the secret of my heart, how can I put into words that you became an integral part of me, I couldn't imagine living without you, you have become the very lifeblood that makes my heart beat , there are no words to describe the depth of your meaning to me, but one thing is clear without you I will cease to exist". Yana kaiwa nan ya saki habarta ya saka hannun sa a aljihun jacket din sa ya dauko wata rose flower Mai kyau yasa guiwarsa daya akasa ya mika Mata, " I love you Maeshaah please kema ki amsa min da kina so na, I couldn't bear to hear anything else from u , all I need is ur acceptance, please mamyyyy".
Sowa ma'aikatan wurin suka sa, su kuwa su Faez shi da meela sai murmushi suke suna video, Faez kan ma Instagram ya shiga ya kunna live.
Maesha da komai ya mata tsaye ta dubi Moha dake durƙushe a gabanta, she couldn't believe wai moha ne agabanta a durkushe yana barar soyayarta, ita da take fatan ko a waya ya furta mata sai gashi a bainar jama'a yake furta mata kalmar so, lalle in kaga ka kwankwasa kofa ka sake taqi buɗewa to maybe Allah ya shirya buɗe ma wadda tafi ta ne, ta tuna yadda ta kwana jiya da tunanin Moha yaudararta yake.
Katse mata tunanin yayi ta hanyar faɗin, "Pleaseeeee Mamy". kallon sa tayi ta kalli rose flowers sai kawai itama ta durkusa gabansa ta rike flowern ta sama shi kuma hannunsa na riqe da ita ta kasan, kana ta fara faɗin, "How do I begin to tell you that you own maesha's heart completely, you have left no room for anyone else, from the moment you entered my life I realised that my past was shrouded in darkness, but you brought radiant light to my universe, Muhammad my heart beat solely for you only you Muhammad, I love you, I love you more than you could ever imagine". Tana kaiwa nan suka miqe a tare tafi ne ya karadai wajen gabaɗaya, har da masu kallon live ɗin cikin kuwa harda Hameedah da zuciyarta ta kusan bugawa, abinda ya faru kuwa Maryam ce ta buɗe Instagram sai taga Faez na live ta shiga dan ganin me akey, sosai ta buɗe take kallo, tabbas ba gizo bane wanna Moha ɗin hameedah ne kuma wanna Maesha ce kam buuuu ta kwantsama wata uwar ashar tana sauka ta kira hameedah direct call.
"Hello friendy".
Cikin takaici tace, "Ke dalla shashasha hau IG kiga live ɗin abinda ke faruwa yanzu".
"Me akayi ne har kike kirana da sha sha sha". Ta faɗa a qule.
" idan kika hau kika gani zaki tabbatar. Live ɗin Faez abokin Moha zaki shiga". Tana faɗin haka ta kashe wayar.
Bude datar tayi ta shiga daidai lokacin da suka miqe a tare aka kawo musu wani cake ɗin madaidaici red and white an rubata, Mr and Mrs Moha to be da hoton heart biyu a jiki, ƙasa kuma an rubuta Aymuh, Maesha ta ɗauki wukar da aka yiwa style da wani kyalle ja ta daura akan cake din moha ma ya sake dora yatsansa kamar dazu, yankowa ya sakeyi zai bata a baki har ta buɗe bakin sai ya fasa ya maida bakinsa, bata fuska tayi yayi yar dariya sannan ya yanko wani yasa masa ya goga masa cream din akan hancinta, itama lakuta tayi ta goga masa a goshi.
Sakin wayar hameeda tayi ta dora hannun ta aka ta saki wani ihun kuka, "Wayyo allah na na shiga uku na mutu na lalace, whl karya kike maesha baki isa kizo yau yau ki kwacemin muradina da fata na ba, sai na ga karshenki whl whl whl ko zanyi yawo tsirara baza ki zamu Moha ba, moha nawa ne ni kaɗai". Ta faɗa kamar wadda bata cikin hayyacinta, ranar kwana tayi tana kuka.
Sai 10pm suka bar wurin motar su Maesha a gaba tasu Faez a baya sai da suka rakasu har kan layin su sannan suka juya suka dauki hanyar gida.
Zuciyar kowannensu fess suka koma gida dan Meela ma faez baiyi kasa a guiwa ba ya zayyane mata sirrin zuciyarsa ita ma kuma batayi kwaron baki wurin amince masa ba.
Maesha kam tama manta da cewa dubiya taje kuma ummu bata san basa gidan su meelan ba, tana shiga da farin cikin ta fasa kan ummu tana faɗin, "Wash ummu nagaji.
"Da yanzu nake shirin kiranki inji ko kwana zakiyi, naga har na dawo baki dawo ba".
"Sai gani a tafe kuma".
"Ya jikin nata?".
sai a lokacin ta tuna dubiya fa taje, "Jiki da sauki ummu tana gaisheki kuma tace basai ma kinje ba.
" to haka akeso Allah ya kara sauki.
" ummu ina su abbah da ameer
" Abban ki yau da wuri ya shiga bacci ameer kuma Yana daki kinsan inajin on 1st zasuyi jamb maybe Yana karatu ne, ni ma ke kadai na zauna jira.
"To shikenan Ummu barin shiga daga ciki sai da safe".