Free chapter · Read without an account
PAGE 28
Hameedah da taji a ranta wannan aikin tabbas zasuyi nasara tace, "Ina so a raba su, a juyo da hankalinsa kaina, in kuma hakan baza ta faru ba to kowa ya rasa".
Bokanya ta daga kai tana wasu maganganun can sukaji an jefo wasu abubuwa, ɗaya kwalba ce me dauke da wani baqin turare daya kuma a wani abu ne a dunqule. Dauka tayi ta miqawa Hameedah tana faɗin, "Wanna dunkulallen hayaki zakiyi, saikin tabbatar shi kadai ne a daki saiki turara masa shi, muddun ya shaqa to zai mance da wata yarinya sai ke kawai zai dinga gani, saidai baza kiyi aikin ba sai nanda kwana arba'in domin akwai aikin da zamuyi akan su kafin nan, wanna kuma sai kina period in kika tabbatar yana bacci sai ki shafa kije wurin kansa ki kira sunan sa sau uku in dai ya amsa shikenan aikin ki ya gama".
Cikin jindadi ta karɓa ta sa a jaka sannan ta fidda kuɗi masu yawa ta ajje suka tashi zasu fita har sunsa Kai ta daka Matsu tsawa tana faɗin, "Ba a fita ta gaba dan haka ku fita da baya, ku fita da baya".
Tsawar ta tsorata hameedah har ta furta auzubillahi minash shaidanir Rajim".
Wani irin ihu ne ya karadai ilahirin bukkar take kofar ta rufe ihun ya cigaba da tashi duk kunnesu suka toshe da hannuwansu sunajin yadda ake wani wul wul wul dasu can sukaji kamar an watsosu waje har Hameedah na gangarawa ta kurje a hannu da ƙafa ai tana buɗe idanunta ta ganta a waje, bata bi ta kan ciwon ba ta tashi ta lalumi Jakarta ta ara ana kare. Maryam na ihun ta tsayata amma inaaa bata ma san tana yi ba gashi takasa gudu sosai saboda yadda rigar ta matse ta, ganin in fa tayi wasa Hameedah zata mata nisa yasa ta tattare rigar ta cire takalman ta fita a guje sai gashi har ta wuce Hameedah, kamar masu racing haka suka fito bakin titi.
Mota suka faɗa Hameedah taja suka bar wurin. A kofar gidan su Maryam ta ajjeta tare da faɗin zasuyi magana a waya.
Bata koma gidansu ba ta wuce gidansu moha duk da kuwa yadda iyayenta suka matsa Mata Kan ta Komo gida ta dodare kunnuwanta dan so take ta fara aiwatar da maganin farko tukunna, sunyi fadan har sun gaji karshema dai na picking call dinsu tayi, adam kuwa cewa yayi shi fa ba ruwan sa Hameedah ba yarinya bace kuma auren zuminci ba dole bane.
Haka hameedah ta zauna dakon jiran zuwan period dinta, a ranar da yazo kuwa sai murna take, kasancewar weekend ne kowa yana gida dan yamma na yi ma gidan nasu ya fara cika da masu kai kawo harda ma amarya amra da tazo gaishe da momma, ita kuwa hameeda wanka ta dauka sannan ta dauki turarenta ta ƙulle bakin dankwali ta fita amma saidai kash cikin rashin saa tana fita ta ganshi a parlour dan haka tayita dakon ko zai shiga ya huta amma ina har dare yayi suka koma bangarensu bata samu wannan damar ba.
Tun daga wannan ranar ta shiga targetting ɗin sa saidai Allah bai bata Sa'a ta gama saddakarwa yau ko ba shi kadai bane zata aiwatar kawai dan a gobe take sa ran samun tsarki, fitowa tayi zata shiga kitchen taji momma na faɗin, "Ina shi moha din yake?".
Labewa tayi dan taji mai Faez da nashed ɗin zasuce sai kuwa taji faez yace yana can yana bacci wai yau yasha aiki ya gaji.
Tsalle ta daka cikin farin ciki ta koma daki aguje ta dauki turaren ta sanya a aljihun rigarta ta fito. " Hameeda ina zuwa haka ?
" Umm momma dama zanje garden ne".
"To amma da kin dauki ko dankwali ne yawon kai a haka ba dadi".
"Zan gyara in sha Allah, yanzun abu zan dauko In dawo". Tana faɗin haka ta fice da sauri dan ma Kar momma ta sake tsayar da ita.
A parloursu ta tsaya ta mirza turaren sosai dukda warin sa saida ya kusa sata amai amma haka ta daure nufi dakin, tana shiga ta hangoshi karshen gado ya qudundune acikin blanket. A daidai kansa ta tsaya ta fara Kiransa kamar yadda bokanya ta faɗa mata, ai kuwa tana kiran na karshe ya bude Ido ba tare daya amsa ba domin shi a mafarki ya ganta tana Kiransa amma da ya bude Ido sai ya ganta a tsaye a kansa, " la ilaha illallah, auzubillahi minar shaydani Rajim, alhamdulilahil lazi ahyana ba ada ma amatana wa ilahin nushur". ya fada still idan sa akanta.
Wani kamewa tayi ta zuba masa Ido dan tayi tunanin a baccin ne zai amsa mata kiran yana tashi kuma aiki ya kankama.
Ganin yadda yake kallon ta kamar ya samu hoto yasa ta shiga washe baki tare da zama bakin gadon tana wani kwankwasa tace, "Darling, mai kakeso in kawoma?". Ta fada tana kokarin riqo hannayensa wani adungure da baisan lokacin da yayi shi ba sai jinsa yayi a toilet, amai ya shiga kwararawa kamar zai fitar da yayan cikinsa, da sauri ta tashi ta bishi toilet ɗin tana faɗin, "Sannu Darling, dama baka da lpy ne?".
kuskure bakin sa yayi sannan ya dago ba zato ba tsammani taga wata wuta fit ta shafe ganinta, taga taga tayi batasan lokacin data wuntsilo waje ba daga cikin toilet ɗin, cikin zafin zuciyar da bai taba jin irin saba ya fito ya sawa kofar dakin key sannan ya cire ya sanya a aljihunsa, belt ya ɗauko hameeda da har lokacin bata gama dawowa cikin hayyacinta ba taji duka na shigarta ta ko ina, ihu tafara tana neman taimako amma ina dukanta kawai yake da iya karfin sa yana kara mata da hauri .
Nashed daya manta wani abunsa a dakin yacewa faez bari ya je ya dauko abu a daki yana dawowa. Momma tace ka tashi moha ma bakyau baccin bayan la'asar ɗin nan. Da toh ya amsa yana ficewa.
Tun daga parlour ya fara jiyo ihun Hameedah da sauri ya karasa amma sai yaji ƙofar a datse bubbugawa ya shiga yi yana faɗin, "Moha open the door, Miye hakan kakeyi, ka buɗe mana". Da karfi yake fada yana bubbuga kofar amma ba alamar Moha yama jishi ballatana ya bude kofar, dukanta kawai yake kamar ya samu wani gardin.
Nashed ya tsorata sosai yace, "Dan girman Allah moh Ka bude kofar nan, idan kanayiwa annabi Muhammad SAW ka bude". Shuru yaji kamar anyi ruwa an dauke sai sautin kukan hameedah, bude kofar yaji anayi ai bai bari ya ƙarasa ba ya hankada shi ya shiga saidai mai wani irin warin da ya doki hancinsa ya sashi toshe hancin yayi baya amma baibar wajen kofar ba, Hameedah ganin yau moha rayuwarta yake nema yasa ta Mike tana tangadi ta mangaje Nashed tayi waje. Kamar wanda aka tunzura moha yabi bayanta rike da belt din a hannunsa, Nashed na kokarin rikoshi ya fisge da karfi yabi bayanta sai kuwa shi ma ya rufa musu baya.
Shigowar papi Kenan faez yana gaisheshi saiga hameedah ta fado parlourn, gabansu ta fadi tana nuna masu kofa tana wani irin gunjin kuka, moha ne ya shigo fuskar nan babu annuri kamar namijin zaki, huci kawai yake, yana karasowa baiyi wata wata ba ya cigaba da zabga Mata belt din faez ne ya tashi da sauri ya rikeshi amma ina kamar ana tunzira shi.
Papi da momma sai magana suke masa hankali tashe amma sam baya jinsu duk kokarin faez da nashed nasan gannin sun riqe moha sun gagara kamar wani kuntacce haka ya koma, dauke shi da mari momma tayi saidai kafin ta sauke hannun ta ya maidashi Kan hameedah.
Wata irin tsawa papi ya daka masa, " Kai Muhammad, Kana da hankali kuwa ana ma magana Kana kara birkicewa, kisan kai kake so kayi ne?".
Dagowa yayi hannunsa dafe da Inda momma ta mareshi baya baya ya fara Saida yazo tsakiyar falon sannan ya tsaya yana binsu da Ido, idonsa yayi ja muryarsa har rawa take yace, "momma akan wanna shegiyar kika mareni
" To ko zaka rama ne Muhammad, innalillahi wa inna ilaihir rajuun ni wai me ya same ka ne ko ka fara shaye shaye ne, me ma ya haɗa ku da zaka kamata da irin wannan dukan?".
Murmushi yayi yace, " Wanna momma? Wannan dai? ". Ya fada Yana nuna Hameedah dake yashe awajen sai kawai ya kada kansa yayi waje, hameedah kuwa tayi flat a wajen. Papi da ya rasa meke masa dadi ya zauna jakwaf ya dafe Kai, momma ce tace, "Faez duba yar mutane karta mutu mu shiga wani hali". Ta faɗa da tsantsar tashin hankali.