Free chapter · Read without an account
PAGE 29
Yana shiga part dinsu ya wuce ɗaya ɗakin, toilet ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi, sosai yakejin ruwan na shigarsa amma zafin sa yakeji a cikin jikinsa, a gurguje yayi wanka ya dauro alwala ko ya samu saukin radadin daya keji. Da yake akwai wasu kayayyakin nasu ma anan dakin sai kawai ya dauki wasu daga ciki ya sanya ko balle button ɗin rigar bai tsaya yi ba ya fito, ɗakin ya koma ya dauki wallet din sa da wayar sa ya fito da sauri yana me rike numfashi dan baya san ya sake shakar warin turaren da ya kama dakin Shiyasa ko keyn motarsa bai tsaya nema ba kawai ya warci abinda yake a kusa yayo waje, a kan center table yaga keyn motar faez sai kawai ya Zara yayi waje.
A 360 ya zari motar, horn ɗin da yake dannawa ita ta ankarar dasu momma dan a lokacin kokarin tashi suke sukai hameedah hospital domin abin yafi karfin a duba a gida sukaji wanna mahaukaciyar horn dinda moha yake dannawa. Da sauri Papi ya mike yana faɗin, "Meya samu Muhammad ne, Nashed ku bi bayanshi kar wani abu ya same shi".
Faez ne ya ce, "Nash Kuje da Hameedar asibiti ni bari nabi bayansa zan same ku a can". Ya faɗa yana fita da gudu ya nufi part ɗin su ganin ba mukullin sa a inda ya barshi ya sashi nufar ɗakin ba tare da yabi ta kan warin da ya bige shi ba ya hau watsa kayan ɗakin har ya samu key motar Moha din, a guje ya fito ya shiga ya jata da mugun gudu shi ma.
Saidai ko da ya fito ko kurar motarsa bai gani ba kawai dai ya yanke shawarar bin left side dinsa, gudu kawai yake yana shararawa yana danna masa Kira a waya amma baya dagawa, Allah ya temakesa ya hango motar sa a hold up kuma ya tabbatar shi ne a ciki dan haka ko da traffic ɗin ta sake su binsa ya dingayi.
Moha bai tsaya a ko ina ba sai pizza hut ko tsaya wani gyara parking baiyi ba ya fito, a kujerun dake harabar ya zauna ya dafe kansa dake masifar sara masa kamar zai rabe biyu, Faez ne ya ƙaraso wajensa yana haki yace, "Haba moha wai Mai kakeso ne? ka yiwa yarinya jina jina ana kokarin tata kai kuma ka dauko Mota zakaje ka yiwa kanka lahani, wai me yake damunka ne?".
"Faezzzzzzzzz". ya daka masa tsawar da bai taba yi masa irin ta ba, sai kuma ya mike ya cukumu kwalar rigarsa ya shiga jijjiga shi, Faez ya saki baki yana kallon ikon Allah kafin yace, "Ni ma dukan nawa zakayi ne moha? to ko dai maganar su momma din ce ke neman tabbata, anya bawani abu kasha ba kuwa?".
" Get out of my side". Ya faɗa yana sakinsa ya hankada shi baya.
" Ai wurin ba naka bane Kai kadai, dan haka baka da ikon korata".
"Faezzzzzzzzz I said gettttttt outtttttt of my sightttttttt before I do something bad". Ya fada cikin karaji.
Faez bai motsa daga Inda yake ba bai kuma sake cewa komai ba, hannunsa ya dunkula sai kuma ya saki tare da sake matsowa daf dashi ya daura yatsarsa manuniya a kirjin faez din yace, "Kasan me?". sai kuma yayi murmushin da bai kai zuci ba yace, "Karka sake bi na or wallahi kaji na rantse I will do something bad da bazai wa kowa dadi ba". Yana gama fadin haka ya koma mota ya fizgeta da karfi ya bar wajen faez da duk jikinsa yayi sanyi shima ya shiga mota ya juya ya wuce asibiti wajen su momma, lokacin har an shiga da Hameeda ana bata taimakon gaggawa papi na ganinsa yace, "Ina yake faez? ina Muhammad ɗin yake ?".
"Ya tafi, zuciyar sa ta taso sosai bakaga abinda yamin ba kuma ya ja min kashedin Karna kuskura na Kara binsa in ba haka ba he will do something bad, bansan me ya faru da zafi haka ba".
"Innalillahi wa Inna ilaihir raju un". Ya faɗa yana juyowa wajen momma yace, "Ai duk ke kika janyo Aisha me sa zaki mareshi, kinsan yaron nan bai iya zuciya ba sannan bakisan me ya haɗo su ba.
"Amma mana kar idonka ya rufe, ko me Hameedah ta yiwa Moha ai bai kamata ya kamata da irin wannan dukan ba bayan muna cikin gidan idan ya kasheta wani hali kake tunanin zamu shiga.
"Tunaninki kenan, sai cewa kike in ya kasheta in ya kasheta ran nata a hannunsa yake ne da zai iya zareshi a lokacin da yake so? Wannan ai ba daidai bane". Ya fada yana barin wurin wayarsa a hannu yana gwada kiran moha amma wayar a kashe .
Wasa Wasa moha ya kwashe sati guda ba'a san inda yake ba anyi neman duniya babu shi, duk Inda akasan za a sameshi anje baya nan hankalin su papi in yayi dubu ya tashi kullum sai sunyi faɗa da momma yana cewa laifinta ne, wayoyin moha kuwa gabaɗaya basa tafiya. Momma har wata ramar dole tayi, dan tunda take bata taba dukan Moha ba ko da yana karami saidai ta tsawatar masa amma a wannan karan sai gashi ta mare shi da hannunta ba kuma komai ya janyo ba sai gudun ya jefa kansa a matsala.
A bangaren Mahaifin hameedah kuwa yana samun labarin abinda ya faru ya dauki Mama Fatima suka je asibitin da masifa ya shiga dakin yana fadin, "Dole a nemi kashe mana ya mana tunda an gaji da ganin ta ba kaunarta ake ba, ina shi Muhammad ɗin".
Faez da baiji dadin maganganun ba yace, "Baya nan".
"Ai dama ba zai zauna ba mana saboda yayi yunqurin kisan kai ai dole a ɓoye shi, to whl bazan yadda ba sai nabi kadin yata".
Haka ya gama ɗan ƙaramin bala'in sa ba wanda ya sake cewa dashi ci kanka. Kwana biyu da wuni aka sallamo Hameedah taji sauki sosai sai dan abinda ba a rasa ba, direct gidansu aka wuce da ita amma jin cewa ba a ga moha ba sai ta tashi hankalinta.
MAESHA
Ba ƙaramin damuwar rashin samun moha da batayi a waya ta shiga ba, ko abinci kirki bataci kullum tana daki tana aikin gwada wayarsa hadi da tura masa texts dan harta fara tunanin ko wani laifin ta masa a bisa rashin sani.
Ganin abun fa ya miqe yasa ta kira Meelah tace in ba abinda take ta leqo mata da Allah.
Aikuwa ana sallar la'asar sai ga Meelah, bayan sun gaisa Maesha ta shiga faɗa mata damuwar da take cikin ta rashin samun Moha da batayi.
Meelah ta ɗan yi shiru kafin tace, "Ba laifi kika masa ba kawai dai nafi tunanin ko akwai wata matsala ne dan ni ma whl a yanzu kwanakin nan narasa Kan Faez, ba fa ya kira na sai na kira shi, in na kirashin ma baya cikin wata nutsuwa saidai mu gaisa yace min zai kirani daga nan kuma inji shiru na tambaye shi kuma yace ba komai.
Maesha da zuciyarta ta doka ta dafe kirjinta da hannu hadi da lumshe Idanunta sai ga hawaye sharr, "Meela to ko wani abu ne ya faru da Muhammad di na Faez yake boyewa, plzz kiramun shi yanzun".
Itama Meelah sai taji hankalinta ya tashi ta fito da wayar ta hau kiran Faez saidai har ta tsinke ba'a daga ba, saida ta kira kusan sau uku ana hudun ya daga bayan sun gaisa take che masa maesha ce take son zasuyi magana karbar wayar Maesha tayi tana dan saita muryarta tace, "Hello Dr ina wuni.
"Lpy kalau Mamy, ykk? Ygd?".
"Alhamdulillah, dan Allah Moha fa, yau kusan one week kenan ina neman number sa bana samu ko wani abun nai masa ne ban sani ba, dan Allah in Yana kusa ka bani shi".
Faez yayi shuru yana tunani ta sake cewa, "Dr!".
"Naam Mamy".
"Lpy dai?". Ta tambaya zuciyarta na bugawa da karfi.
Nisawa yayi yace.......