Free chapter · Read without an account

PAGE 30

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

Nisawa yayi yace, "Mamy matsala aka samu whl, mu kan mu rabon mu dashi kusan satin kenan...... Nan ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar masa.

"Innalillahi wa Inna ilaihir raju un". Shi ne abinda ta hau maimaitawa cikin kuka.

"Kiyi haƙuri ki tayamu da addu'a Mamy, Allah ya huce zuciyar sa ya dawo ko ya bude wayar". Ya ƙarasa shi ma kamar zaiyi kuka da sauri ta mikawa Meelah wayar tana rushewa da wani sabon kukan. Ko da meela ta karba wayar ta duba har ya kashe shi ma.

Ajiyar zuciya ta sauke ta dafa Maesha da faɗin, "kinga kiyi shuru muyi tunanin abunyi, dan ni fa inajin akwai wani abu akasa haka kawai bazai biyota da irin wanna dukan ba kinsan hameedah tana sonsa, tabbas labarin baikon Ku ne ya tunzira ta tai masa abinda yasa shi daukan zafi haka". Ita kuwa maesha bama gane abinda Meelah ke faɗa take ba daƙyar ta lallasheta tayi shuru sai kawai ta mata sallama dan karta sake dawo mata da maganar ta shiga damuwa.

Ranar ma Maesha wunin daki tayi dan har wani zazzaɓi ta fara ji, saida tayi sallar magrip ta dauko wayarta ta fara trying number moha kamar kullum cikin Sa'a kuwa ta shiga, hannun ta har rawa yake saidai harya tsinke bai daga ba Kira ta sake still bai daga ba tana kokarin sake Kira akaro na uku kiransa ya shigo da sauri ta ɗaga, "H-ee-hello qalbi Kana jina, dan Allah karka kashe". Ta fada da raunin murya kamar mai shirin fashewa da kuka.

Shuru yayi yana sauraronta, "Haba mana qalbi meysa kake son kashe angel ɗin ka da kanka ne, kasan yadda zuciyata ta azabtu da rashin ka kuwa, ko tunanin halin da zan shiga ma bakayi ba saboda ka daina so na ko, ni miye laifina, me nayi?". Ta karashe cikin kuka, still baiyi magana ba kuma tanajin saukar numfashin sa mean bai tsinke wayar ba dorawa tayi da fadin, "Dan Allah duk inda kake kazo gida yanzu, ina son ganinka pleaseeee Qalbi, in dai har yanzu kana so na dan Allah ka......" Bai bari ta ƙarasa ba ya kashe wayarsa.

Wani irin kuka me ciwo ta sake rushewa dashi tana me kwanciya kan pray mat ɗin har aka Kira sallah Isha'i, tsananin ciwon da kanta yake yi yasa a zaune tayi sallar tana idarwa taji karar wayarta daga jin ringing din ta san shi ne dan haka ta janyo ta da sauri amsa, "Ki fito ina waje". Shi ne abinda ya fada ya datse Kiran.

Sai a lokacin ta tuna da abinda tayi, ya zatayi da Abbah? Zuciyarta ta wani irin bugawa, tsam tayi daga inda take zaune can kuma ta miqe da sauri ta zira takalminta ta ɗauki niqab ta boye a hijabinta ta fita, kitchen ta leqa ya sanarwa ummu zata leqa gidansu meela ta karbi wani littafi ta dawo, Ummu ta mata gargadin kar tayi dare sosai ta amsa mata da to sannan ta fita.

Ba kowa akan layin sai wani me container daga can gefe, ta hannun damarta taga ana mata fitila dan haka ta ciro niqab dinta ta daura sannan ta nufi motar, tana zuwa ya bude mata ta shiga saidai kafin tayi wani tunanin ya figi motar a guje, gabanta ya fadi amma ta dake ta dubeshi ya rame sosai ya zama wani iri kamar ba Moha data sani ba, cikin muryar lallashi ta ce, "Haba qalbi meysa zakayi haka? Faez ya faɗa min komai, Menene abinda yayi zafi da har zakabar gida na tsawon wannan lokacin, baka san ba a gyara barna da barna ba? ka san halinda su momma zasu shiga kuwa? Meysa baka tsaya ka masu bayanin abinda ya haɗa ku ba ko dan ka wanke kanka a wurin kowa". Kallonta yayi kawai amma baice mata uffan ba yaci gaba da tukinsa cikin ganganci, hotel din da ya tare na kwana bakwai nan ya koma. "Me zamuyi anan?". Ta faɗa da yar rawar murya me cike da tsoro .

Bai ce mata komai ba yayi parking ya buɗe motar ya fita, ganin ba sarki sai Allah kuma zai iya mata nisa ta rasa inda yake yasa ta sauke niqab ɗin tana addu'a ta sauka tabi bayansa, lokacin har ya shige ya karbi key a reception yana tsaye gaban elevator da alama ita yake jura tana karasowa ya danna ya shiga bin bayansa tayi tana sake tambayarsa mai zasuyi a nan, amma ko kallonta baiyi ba sai ma lumshe idonsa da yayi ya jingina da bangon elevator din.

Zuba masa ido tayi kawai har elevator ya buɗe alamar sun iso, ficewa yayi tabi bayansa har zuwa ɗakin da yake zaune ya sa key ya buɗe ya shige tabi bayansa bakinta ɗauke da addu'a, a wani madaidaicin falo suka tsinci kansu Moha ya karasa Kan 3 seater ya kwanta ya rufe idanunsa. Rufe kofar Maesha tayi ta karaso ta zauna a side stool ta ce, "Albi ka yiwa Allah ka fadamin abinda ya haɗaka da hameeda in dai har ina da mahimmanci awajen ka kamar yadda na rufe idona daga tsoron kowanne irin hukunci za'a min na biyoka hotel inda ban taɓa zuwa.

Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya tashi zaune yana fuskantarta yace, "Mamy, mey sa ba wanda zai fahimceni, mey sa ni ba wanda zai tambayi me aka mun, kowa sai ya fara ganin laifina.

"Kayi hakuri rudani ne yasa basu tsaya tambayarka ba amma ai da baka baro gida ba dole zasu nemi jin ba'a si, miye amfanin tahowa nan din da kayi ka zauna, soyayyar da ake ma ce fa ta sa sukayi haka ko Kana tunanin idan Ka kashe Hameedah ko ka illata ta sosai kai ma za a barkane? Kai kadai fa garesu haba mana kayi musu uzuri".

Kallonta kawai yake kamar wata hoto amma da alama maganganunta suna tasiri a kansa. Ajiyar zuciya ta sauke ganin ta fara shawo kansa tace, "Yanzu duk ba wanna ba faɗamin damuwar, me ya hadaku?".

Numfasawa yayi ya zayyane Mata duk abinda yafaru tun daga ganinta da yayi a bacci cikin wata iriyar siffa me ban tsoro har zuwa farkawar da yayi da zumudin san ganinta a zahiri amma yana arba da ita sai yaji kamar an watsa masa barkono a zuciyarsa, da warin turaren da ya shaqa da yadda suka kwashe da ita bai boye Mata komai ba har Marin da momma ta masa yana Kai aya ya koma ya kwanta ya rufe idonsa.

Ajiyar zuciya maesha ta sauke tana Nazarin maganganun nasa tare da dunqule su wuri guri ta sa a ma'auni, tabbas akwai lauje cikin naɗi amma zato zunubi baza ta yanke hukunci ba tunda bata da tabbas dan haka tace, "Tunda ka tare anan ka karanta Alqur'ani ko da a wayar ka ne?".

Shuru yayi hakan yasa tasan amsar a a ce dan haka taci gaba, "Al qur'ani magani ne na duk wata cuta Qalbi, kana da dumuwar da ta kasa barinka to karanta Al qur'ani, baka da lpy karanta Al qur'ani, wata bukata ce dakai shi ma karanta Al qur'ani, babu wani abinda Alqur'ani bai kunsa ba. Da ace tun lokacin da zuciyarka take tafasa alwala kayi ka karanta shi da yanzu zuciyar Ka tayi sanyi tun a lokacin ka koma gida".

Baice mata komai ba, parlourn ne ya dau shuru na wasu dakikai Maesha sai raba idanu take dan har ga Allah hankalinta bai kwanta da zaman wajen ba dan tunda suka shigo ta rasa nutsuwar ta, karatu ta fara a cikin suratul yasin da kira'ar ta mai dadin sauraro da saukar da nutsuwa a zuciyar mai sauraro.

Sake nutsuwa Moha yayi dan sai yaji kamar ana zare masa wani zare da ya ɗaure shi ajikinsa, kafin wani lokaci duk wani cinkushewar da zuciyarsa tayi ya nemeshi ya rasa wani sanyi yaji yana ratsa shi, ya buɗe idanunsa ya saukar akanta, tashi tayi ba tare data tsaya da karatun ba ta buɗe fridge din dake parlourn ta ɗauko masa ruwa mai sanyi ta miqa masa, tashi yayi ya karba ya bude ya kafa kai ya shanye duka sannan ya ajje robar yana sauke ajiyar zuciya.

Dagowa tayi taga ya tsatsareta da idk sai taji ta takura ta tashi daga inda take zaune ta koma kujerar dake opposite dashi, wayarsa ce ta fara neman agaji amma ko motsawa baiyi ba wani kiran ne ya sake shigowa ganin bashida niyyar dauka yasa Maesha dago kanta suka hada Ido, murmushi ya mata ita kuma ta masa alama da ya dauka.

Jawo wayar yayi ya daga yana me sawa a handsfree momma ce take Kira, sallama yayi Momma ta amsa hankali tashe ta ɗora da faɗin, "Idan kana yiwa Allah da manzonsa Muhammad ka dawo gida, haba son ashe zaka iya fushi damu har na tsawon one week sannan ka kashe wayoyinka, kasan halin da muke ciki kuwa, to ga mahaifinka nan jininsa ya hau sosai yana kwance ba lpy, dan Allah ka taimaka ka dawo gida, duk duniya Kai muke kallo muji dadi ka yi haƙuri in mun ma laifi ka yafe mana".

Shuru yayi yana sauraronta idanunsa akan Maesha data sauke niqab dinta tana ƙoƙarin mikewa bayan ta kai aya. Lumshe Idanunsa yayi a sanyaye yace, "Zan dawo momma.

"Kamin alqawarin zaka dawo yanzu."

"Na miki alqawari Momma".

"To shikenan My son Ina jira, Allah ya kawoka lpy kashe ya tsare mana kai a duk inda kake".

Da Ameen ya amsa sannan ya kashe wayar ya mike ya fara tafiya da niyyar shigewa ɗakin Maesha ce tace ummm gida fa?".

Juyowa yayi ya sakar mata wani kallo, cikin sigar wasa yace, "Anan zamu kwana gobe a daura mana aure". Waro idanunta tayi shi kuma yayi shigewarsa.

Abubuwansa masu mahimmanci ya tattaro ya fito, inda ya barta anan ya sameta tayi tsuru tsuru, "Muje to Matsoraciya". Ya fada yana mufar kofa tabi bayansa tana sauke ajiyar zuciya.

Sai 10:43pm yayi parking a dan nesa da gidansu.

"Innalillahi wa inna ilaihir rajuun". Ta fada tana duba wayarta data ga missed calls rututu, na Meelah, Ameer, ummu sai na Abbah. "Shikenan na shiga uku na mutu na lalace". Ta faɗa kamar zata yi kuka.

"Menene ?". Ya tambaya yana kallonta cikin kulawa.

"Karya na yiwa Ummu nace gidan su Meelah zan shiga yanzu haka sun kirata tace banje ba gashi nan har da missed calls ɗin Abbah, yau tawa ta kare".

Shuru yayi yana tunani sai kuma yace, "Ba abinda zai faru in sha Allah, karki damu ba abinda zai faru kije kawai". Ya faɗa da nufin ya ƙarfafa mata guiwa.

Girgiza masa Kai kawai tayi ita tsoron shiga gidan ma take, "Duk abinda zai faru ki sanya a ranki bake kadai bace, we are in this together kinji ko?". Gyada masa kai tayi tana buɗe ƙofar zata fita yace, " Thank you so much angel, indeed nayi zaben mata ta gari kuma nasan our future children will be proud of having a mother like you".

Murmushin yaqe ta masa tana rufe ƙofar shi kuma yace, " I will call u idan naje gida in sha Allah".

"Okay ka gaida su momma". Ta faɗa tana cire niqab din fuskarta ta cusa a hijabi sannan ta nufi gidan cike da fargabar abinda zata tarar.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.