Free chapter · Read without an account

PAGE 31

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

A tsaye ta samu abbanta, Ummu na zaune Kan kujera Ameer kuma na kasa kusa da kafarta, da sallama ta shiga kana ganinta kaga marar gsky. "Daga ina kike?". Abbah ya fada cikin tsananin bacin rai.

Da rawar murya ta ce, "Daga d..aga gidansu Meelah". A tsawace Ummu ta ce, "Amma dai ba wannan meelah dana sani ba ko?".

Jikin Maesha ya hau rawa ta kalli Abbah taga ya tsareta da ido. "Tambayarki nake ko?". Ummu ta faɗa cikin tsawa.

"Ummu Allah b....."

"Keeee". Abbah ya daka mata tsawa kafin ya ce, "Karki bari in sa kafar wando daya dake Maesha, wato mu kika maida Yara kanana ko, yaushe aka haifeki da har kike tunanin zaki iya mana wayo, Daga ina kike, idan kika min karya yau sai na miki mugun duka a gidan nan".

Zubewa Maesha tayi a wurin ilahirin jikinta rawa yake ta ce, "Ummu dan Allah ki bawa Abbah haƙuri".

Sake katseta yayi da faɗin, "Haƙuri har kina ma da bakin cewa a bani hakuri". Yayi murmushin takaici ya ce, "Kin bani mamaki Maesha, I'm highly disappointed in you, ban taba tunanin ke zaki fita zakka a cikin yayana ba. Shin lokacin da yaron can Muhammad yazo ban zaunar dake na tambayeki ko kun daidaita ba?".

Cikin kuka ta ɗaga masa kai alamar Eh. "To da uban wa kike haɗuwa a waje? Ko dama kin amince dashi ne dan ki tozarta ni a idon jama'a?". Maesha ta kasa cewa komai sai kuma, Abbah ya ce, "Ina wayarki". Da sauri ta miqa masa.

"To daga yau kar na Kara ganin kafarki a waje, wayar nan kuma kin rabu da ita kenan, sannan zanyi bincike idan har na gano wanda yake binki har makaranta sannan yazo har gida ta fita dake to zan maidawa iyayen Muhammad sadakinsu da dukiyar aure yaso shi wancan ɗin sai yazo da iyayensa da sadaki a daura aure bana buqatar komai sadaki kawai zasu kawo". Yana gama faɗin haka ya wucewarsa ciki, Maesha ta sake fashewa da kuka me cin rai ta rarrafa wurin Ummu saidai kafin tace wani abu Ummu ta rigata da faɗin, "Ni dai Allah ya gani na baku tarbiyya daidai gwargwadon iyawata maesha, kuma ina iya bakin kokarina a kanku, saidai ince Allah ya shiryeki in dai irin rayuwar da kika zaba kenan". Ta fada tana tashi ta bi bayan Abbah.

Zaman yan bori tayi ta fashe da kuka, Ameer ne ya matso kusa da ita yace, "Allah kinyi Sa'a da Abbah bai dake ki ba kinga yanda ya fusata dazu kuwa, sannan wai da wa ma kike haɗuwa a makaranta ne".

"Ameer whl ba kowa bane face Muhammad, kuma Abbah shi yaja hakan da bai kafa wanna dokar ba da saidai yazo gidan acikin mutunci, nima ba hakan nake so ba ba yadda zanyi ne, amma bansan ta ya zasu fahimta ba, bansan aya zai ɗauki abun ba idan yayi bincike ya gano da Muhammad nake haɗuwa maybe ma yace an fasa auran". Ta karashe tana sake fashewa da kuka.

"To yanzun ina kikaje da kika fita dan ance wani ne yazo da mota ya ɗauke ki". Dafe kirji Maesha tayi sai kuma ta tashi da gudu ta wuce ɗakinta tana gunjin kuka, shikenan yanzu in aka gane hotel sukaje ba wanda zai fahimci so ɗaya ne kawai cewa za'ayi kullum ne suke zuwa. Yadda taga rana ranar haka taga dare karshe ma alwala ta dauro ta dinga sallah tana roqon Allah yasa su Abbah su sauko su fahimce ta.

MOHA

Duk a main parlour moha ya samesu da alama isowarsa suke jira, shigowa yayi da sallama abakinsa, ya karasa gaban momma ya durkusa ya tare da dora kansa a cinyarta, idonta ya kawo kwalla ta daura hannunta akansa, da rawar murya tace, "Allah ya albarkaci rayuwarka son, Allah ya kare mana kai gabanka da bayanka, baka san halin da muka shiga bane a rashinka, nasan an ma ba daidai bane amma hukuncin dakayi kokarin dauka ya wuce qa'ida".

Papi yace, "Zo nan son, zo inji duminka, ni a lokacin da nasan dukan nata zaisa ka huce da bazan hanaka ba". Momma ya kalle shi amma batace komai ba. Haka aka shiga maida zance kowa ya tofa albarkacin bakin sa harda su Faez sannan aka gyara zance dai da zummar Kar akara tada ta, sai kusan 1am iyayen sukai masu sallama suka shiga bacci.

Su ma tashi sukayi suka koma part ɗinsu suka kafa wata sabuwar hirar nan Moha ya faɗa musu yadda sukayi da Maesha, sosai Faez yaji dadi dan ya ƙara yadda in Allah ya baka mace ta gari ya gama baka rabin jin daɗin duniya. Tunawa Moha yayi yace zai kirata dan haka ya tashi da sauri ya zaro wayar a caji ya hau kiranta duka yana jin zuwa yanzu ma tayi bacci amma dai zai bar mata missed call in ta tashi ta gani, haka kuwa akayi ya kirata bata daga ba dan haka ya rubuta mata text ya har mata sannan suka cigaba da hira da su Faez.

Washe gari Maesha da matsanancin ciwon kai ta tashi amma hakan bai sa ta fasa taimakawa Ummu da aikin gida ba dan so take ta fara shawo kan Ummu dan tasan ita kadai zata iya tayata yaqi da Abbah, saidai ko gaisuwarta Ummu bata amsa ba ballatana ta ga fuska haka suka gama aikin ta koma ɗaki tayi wanka ta kwanta, a tunaninta za'a aiko Ameer yazo ya kirata yin breakfast sai taji shuru sai ma tashin motar fitar Abbah da taji, kuka ta sake rushewa dashi, cikin haka taji muryar Ummu da meelah a falo, sai gata kuwa ta shigo amma fuskarta da alamun damuwa ta zauna gefen Maesha tana dafa kafadarta tace, "Maesha Meke faruwa?".

Fadawa tayi jikinta ta rushe da kuka ta shiga faɗin, "Na shiga uku Meelah, su Ummu fushi suke dani Abbah yace ba zan kara fita ba da alama makarantar ma ya datse ta sannan ya kwace wayata".

"Ina kikaje jiya? Meysa da kika yi karyar zakizo gidan mu baki kirani kin sanar dani ba, na tsorata a wannan daren kar aje wani abu ne ya faru shiyasa ban ɓoye musu ba".

"Ba karya nayi ba Meelah, gidan ku na fito da niyyar inje sai na hadu dasu aziza a kan layin nan a mota, muke gaisawa har suke cewa basu san anan muke ba ai, an kwantar da saida ba yadda take, shi ne na bisu mukaje dubiyar sam na manta wayana a silent take. Kuma nasan ba komai ya sanya Abbah zargi ba sai dan faɗa masa da akayi akwai wanda nake haɗuwa dashi a makaranta". Ta ɓoyewa Meelah ainihin abinda ya faru jiyan, dan tasan duk wanda zata faɗawa taje hotel da namiji whl ba zai mata tunanin kirki ba, dole ne zargi ya darsu.

"Kina nufin Abbah yasan kuna haduwa da Moha a makaranta?". Gyaɗa mata kai tayi tana shesheqa sannan ta daura da faɗin, "bai san da Moha bane an dai sanar masa ina haɗuwa da wani".

"To yanzu miye abunyi?". Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. Kafin Maesha tace wani abu saiga kiran Moha ya shigo wayar Meelah, ta kalli screen ɗin ta kalli Maesha, "Moha ne".

"Bani shi". Ta faɗa da sauri tana ɗaukan wayar ta kara a kunne, "Hello". Dan shuru Moha yayi kafin ya ce, "Angel, what's wrong? Why are you crying?".

"Qalbi asirin mu ya tonu Abbah ya gano muna haɗuwa a makaranta yanzu haka ya kwace wayata yama ce na daina fita gabaɗaya Bansan ya zanyi ba, gashi sun dau fushi dani sosai". Ta ƙarashe da kuka.

"Ya salam". Moha ya fada yana jin sautin kukan nata har cikin zuciyarsa, sai kuma yace, "Kiyi shuru Mamy zansan yadda zamu billowa abun amma dan Allah ki daina kuka it's hurting me". Dakyar ya rarrasheta tayi shiru sannan sukayi sallama ya kashe yana me ƙara jaddada mata kar tasa damuwa babu abinda zai faru in sha Allah su Abbah zasu sauko.

Ganin yanayinsa yasa Faez tambayarsa Meke faruwa?

Iska ya furzar kana ya masa bayani. Nisawa Faez yayi yace, "To yanzu miye abun yi?".

"Ya zama dole inyi tunanin mafita". Ya faɗa yana miqewa ya shiga zagaye.

Haka kwanaki suka cigaba da ja Moha duk ya shiga damuwa don yanzu ta zama kullum yana kan rokon Meelah taje gidan su Maesha domin ta hadasu, duk kuma lokacin da zasuyi waya sai ta masa kuka hakan ne ke kara dunguma hankalinsa dan haka ya yanke komai zai faru yau zaije gidan ya gana da Abbah.

Maesha kuwa ba ƙaramin tada hankalinta tayi ba duk ta rame ta firgice tun Ummu na share ta har ta dan sauko tana dan sake mata. Kamar yanzu da Maesha ke kwance a daki kamar yadda ta saba Ummu ta shigo ta sameta, a bakin gadon ta zauna tana dubanta ta ce, "Maesha".

"Na'am Ummu". Ta faɗa a hankali.

"Tashi ki zauna muyi magana". Ba musu ta tashi ta zauna, Ummu ta ce, "Karki ɓoye min komai ki faɗamin gsky, waye kike haɗuwa dashi a makaranta?".

Ganin cewa cigaba da ɓoyewar ba zai bata mafita ba yasa ta ce, "Ummu Muhammad ne, kuma saboda ya samu damar dinga zuwa gida ya gabatar da kansa wurin Abbah har ma ya turo da iyayensa amma still sai Abbah yace haɗuwa daya zamuyi saidai mu dinga waya, Ummu ni kai na baso nake ba, ba mutunci bane na dinga haduwa dashi a wajen to amma ya zanyi da Abbah?". Ta ƙarashe hawaye na sauko mata.

Ummu tayi shiru tana tunanin can kuma tace, "A ranar ina kikaje? Waya dauke ki a mota?". Bayani da tawa Meelah Ranar shi ta yiwa Ummu.

"Meysa kika kasa kiran kowa ki sanar masa, idan kuma wani abu ya faru a lokacin fa, wa ya san inda kika tafi? Wa yasan da su wa kika fita? Hakan hatsari ne ga lafiyarki da mutuncin ki, mutane yanzu ba abin yadda bane, komai zai iya faruwa, za'a iya shiga jikin wani naka a saye shi domin a sameka, duk bakiyi tunanin wannan ba kika dauki kafa kika bisu. Wancan ya wuce amma ki kiyaye na gaba Allah kuma ya kare".

"Nagode Ummu, kuma dan ki rokar min Abbah ma ya yafe min".

"Zanyi magana dashi, yanzu yana falo ne tare da mahaifin Jamila".

ABBAH

Abbah amininsa Daddyn Jamila ya nema domin suyi magana kan matsalar Maesha. Bayan sun gaisa Abbah ya koro masa bayani da kuma hukuncin da ya yanke.

Daddyn Jamila ya ɗan girgiza kai yace, "Batun ka katsewa yarinya karatu ma bai taso ba Alhaji Saif, in kayi haƙuri wata biyu ne fa kawai ya rage su fara jarabawa, gashi yanzu har anyi kusan three weeks da komawa amma ita ka hana ta fita, sannan batun ka kira Muhammad ka nuna masa bacin ranka ma abun kunya ne saboda wannan abun in zakayi duba na tsanaki kai ka haddasa shi, saboda ka kafa takunkumin babu zance a gidan Ka har sai ta gama makaranta bayan kuma anyi tambaya anyi komai har an sa ranar, sun bada sadaki shin taya kake tunanin baza su dinga haɗuwa a wani wurin ba? Kayi sa'a ma a makaranta suke haduwa kan idon mutane kuma yaron akwai tarbiya a tare dashi, in ba haka ba in da wani ne gani zaiyi ai wannan wata dama ce a gareshi tunda har yarinya na sonsa kuma bata iya masa musu, bakayi tunanin in wani abu ya nema a wurinta baza ta iya bashi ba? Kuma duk fa abinda zai faru a wuyanka yake. Dan haka ni shawarar da zan baka ma itace karka yadda ka nuna kasan da Muhammad take haɗuwa tunda har kace baka sanarwa ko mahaifiyarta ba dan haka kakira yaro kace masa ya fara zuwa su fahimci juna tunda Abu ya Matso".

Abbah ya sauke nannauyan numfashi sam da kansa a duhu yake bai hango komai ba Saida Daddyn Jamila ya haska masa fitila, duk sai yaji kunya ta kamashi. Daddyn Jamila yace, "Wai koo dan kaga Kayi ana Zainab Ka haye shi ne kake so ka sake kwatawa, kowacce yarinya fa da irin halinta, ko bakaga ita Jamila duk sati biyu sai shi Faezun yazo sun zanta ba, to kaga kuwa har suna haɗuwa a gida ai kaga ita kanta in nemi su haɗu a waje zatayi tunanin wani abu na daban, to wannan shi ne faidar hakan saboda a gujewa aikin dana sani".

Abbah ya nisa yace, "Haka ne, na kuma kuskurena kuma in sha allah Zan gyara, nagode da shawara kwarai da gaske a tsawon shekarun da mukai tare Ka kasance me dorani a hanya idan har kaga zan kauce, nagode kwarai da gaske Allah ya bar zuminci Allah ya bar mu tare cikin aminci".

"Ahh ba wani abun godia Alhaji saif ai an zama daya shekara d shekaru ana tare tun bakin gemu gashi yanzu har ya fara komawa fari". Sukayi dariya gabadaya .


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.