Free chapter · Read without an account
25
NAFISATU SASAAL
***
25
"Wacce Hindatun? Banda Fiddausin da Sammani ya kai kuɗin aurenta satin da ya gabata".
A cewar kawun Sammani shi kansa sai da ya tambayi Sammani game da ni, amma ya ce masa mun gama magana.
Inna kasa tsayuwa tayi, sai waje ta nema ta zauna..cikin taushin muryar da ban san ta da shi ba, ta ce;
"Sammani bai yi min adalci ba, da me zan ji da kunyar mutane ko da baƙin cikin da ya ƙunsa mana?"
Baba shiru ya yi, kansa a ƙasa, ya kasa cewa komai..
Ban ji takaici da haushin abinda Sammani ya yi min ba, sai da na zo kwanciya barci, duk yadda na kai ga daurewa sai da kuka ya ƙwace min..
Darasi ɗaya zuwa biyu na fahimta a lokacin..A tsakanin zamanmu da Sammani da kuma Mairo.
Darasin farko shine; mutane suna son ka ne a lokacin da suke buƙatarka..kamar yadda Sammani ya yi min a farkon tafiyarsa..da kuma sanda Mairo ta dawomin lokacin da muka yi faɗa bayan ta ga ta rasa abinci.
Darasi na biyu kuma shine..kowa zai iya barinka a ya yin da ya samu wanda ya fi ka, kamar yadda Mairo ta zaɓi Khalil akan Sammani, shi ma kuma ya zaɓi wata a kaina.
Hawayena na share, gaba ɗaya na ji barcin ya fice min daga ido...yadda na ga rana haka na ga dare..Inna ma ina jiyo sautin kukanta cikin dare..
Har faɗa suka yi da asuba ita da Baba akan yadda ya ƙi amincewa akira Sammani tayi masa wankin babban bargo.
★washe gari da safe, duk so na da koko da wainar rogo kasa ci na yi.
Kafin ƙarfe tarar safiya ta yi, abokanan hirar Inna sun cika gidanmu, wai sun zo yi mata jaje..
Zuwa ƙarfe 12 rana zancen fasa aurena da Sammani ya cika ko ina..ana ta gulmar ya samu ƴar gayu mazauna garin Abuja ƴar asalin nan ƙasar ƙauyenmu..
Kasa fitowa na yi daga ɗaki..
Ina zaune idanuna sun yi jajir saboda kuka da kuma barcin da ban samu ba..Fatima ta yi sallama..
Ina ganinta na fashe da kuka..cikin taushin muryarta ta ke cewa;
"Sai da na gayamiki Hinduu amma kika ƙi ji, da kin ɗauki shawarata da duk ba'a zo nan ba..ki yi haƙuri kin ji"
Ta ƙarasa faɗa tana zama a gefena..
Mu na jiyo yadda su Inna da mutanenta suke ta mayar da zance, har da waɗanda su ke cewa sun san kakanin Fiddausin da Sammani zai aura..
Babu kalar dariyar da mutanen gari ba su yi mana ba..
Sammani bai ƙara kirana waya ba..
Ko saƙo aka turomin gabana yana faɗuwa na ke ɗauko wayar, a raina ina addu'ar Allah Ya sa Sammani ne..sai dai dubawa ina dubawa zan ga ashe kamfanin layi na ne, sai jikina ya yi sanyi.
Na shiga mayucin hali a wannan lokacin, ko aikena ba'a yi, saboda duk inda na gifta sai na samu masu yin gulmata..
Lamura ba su ƙara chaɓemin ba, sai da Khalil ya zo da ɗanƙareriyar mota ya tafi da Mairo, Sammani ya dawo shi kaɗai domin gyara gidansu saboda ranar bikinsa da za'a saka kwana kusa..
Abun mamaki Sammani bai ji kunyata ni da su Baba ba, har cewa yake yi a Majalisa shi ba zai iya auren macen da ba ƴar gayu ba, ya fi mace wayayyiya mai ilimin boko..shiyasa ma ya biyani ƴan kuɗaɗen da nake ikirarin na taimaka masa da su.
Ranar da zancen ya dawo kunnena na yi kuka kamar raina zai fita, alwashin yin ilimi mai zurfi ya ƙara ɗarsu a cikin raina..
Wasu lokutan ina kuka na ke cewa Inna;
"Haƙiƙa Abota da sauƙin kai basu yi min rana ba"
Ta kan yi murmushi ta ce min;
"Abota da sauƙin kai su na da rana Hindatu, ke ce dai ba ki iya sarrafa na ki ba, domin komai ana yinsa ne a gurbin da ya dace shi"
Tunda lamarin ya faru, Aunty bata tako gidanmu ba sai da jarabawata ta fito, ta yi kyau tukunna..
Ba ta lallasheni da kalamai masu taushi ba, sai waɗanda zasu zamurar da ni, na tashi daga Hindatun ƙauye zuwa Hindun Birni..
Ta na nan zaune a gidanmu, har sai da ta jira Baba ya dawo..sai dai duk yadda ta kai ga yiwa Baba bayanin ya bar ni na yi karatu, murje idanunsa ya yi, ya nuna mata bai san zancen ba..
Inna har da kukanta da durƙusawa akan gwiwoyinta biyu tana roƙonsa ya amince..amma ya kafe sai na samu miji na yi aure sannan zai yarjemin na tafi Jami'a, idan mijin ya amince.....
DAWOWAR LABARI
Gwauron numfashi na sauke, ina kallon Toyosi da ta saki baki da hanci tana kallona..
Cikin zumuɗin son sanin abinda ya faru har na zo ƙasar waje, bayan kafiyar Baba akan dole sai na samu miji na yi aure ta ce;
"Hindu, idan na fahimceki, ki na so ki ce min a yanzu haka da aurenki? tun da dai kin ce Baba ya ce dole sai kin samu miji zaki yi karatu a can garin ku ma kenan, balle nan da ba ƙasarki ba..
To wa kika aura kenan????"✍🏻
A nan Free pages ɗinmu ya ƙare...ga mai son cigaba zai tura 700 Nafisat Aliyu Muhammad First bank 3207955182, tura shaidan biya ta ***.
Ranar Labara zamu cigaba da labari da yardar Allah.