Free chapter · Read without an account

Beyond the pages!

by Ammi Malami · Sawun Giwa

                 FREE PAGE

Nagode da bibiyar littafina da kukayi har izuwa karshen sa. Consider this a token of my appreciation☺️💕


—-


Na kasa barin wannan a iya tunanina kadai na ce dole ne na rabashi tare daku☺️


—


ABUJA


9:30am


"Wa na kama?"  


Muryar Saleem mai zurfin gaske ta shiga kunnen Juwaira sanda hannayensa dake dauke da danshin ruwan wankan da ya gama yi suka zagayeta. Tana tsaye ne gaban mirrorn dakinta a sannan, ta gama yafa gyalen bakar abayarta kenan wadda ta fito da hasken da fatarta ta kara kyawunta na sake fitowa. 


"Juwaira" 


Ta fada kai tsaye kamar yanda ta saba basa amsa tana kokarin rabasa da jikinta. Saleem ya juyo kansa ya kalleta idanuwansa farare na zagaye fuskarta datayiwa y'ar karamar kwalliya yace 

 

"Juwairar waye?". 


"Juwairan Saleem" 


Ta bashi amsa tana matsa fuskarta baya dan kar ya shafa mata danshin ruwan dake kan tasa fuskar. 


"Amma kasan jirgin ba jiranmu zai tsaya yi ba koh". 


"Wayace" 


Ya bata amsa muryarsa na nutsewa cikin gyalenta da yake kokarin dagawa sama dan ya chusa fuskarsa a cikin ramen wuyanta. Ba shiri ta fara mutsu mutsun fita daga rikonsa.


"Kasan time yana tafiya koh". 


Sanda yayi kokarin juyawa dan ya kalli agogon dake ajiye akan bedside drawer dinsu ne tayi saurin rikosa ta saka tafi hannunta a idanuwansa ta rufe tana dariya dan tasan abinda zai ce idan ya kalli agogon. Sai shima yayi dariyar nan tasa da Juwaira ta san ta keta ce kafin ya cire tafin hannunta data rufe mai fuska dashi yace


"Nayi wani tunani". 


Ya cigaba batareda ya bata damar amsa sa ba "Why not mu tura yaran kawai mu kuma mu tafi Egypt mu d'an huta tunda na dauki leave". 


Juwaira ta fara girgiza kanta tana kokarin turesa. 


"Enough, wannan kasa na biyar kenan da kayi tunani" ta karasa tana dariya. 


Ya janyo hannunta zuwa gadonsu dake a gyara ya matsar da kayan data fiddo mai wanda zai saka yana cewa. 


"I just want some time with you is all, we've been so busy kin daina samun time dina yanxu fa madam". 


"Idan mukaje chan din ai zamu huta, zaka samu time dina har sai ka gaji dani" ta fada mai. 


"Wa? Har abada" sai yayi kasa da muryarsa kad'an yana karawa da


"And we can make another baby kafin mu dawo. What do you say?" ya 

karasa yana kashe mata ido d'aya.  


Ta saka hannayenta biyu ta turasa da iyakar karfinta tana dariyar da ya tayata. Yayi baya kan gadon saboda karfin sata saka wajen turasa kafin ta juya da saurinta ta bar dakin hayaniyar Nurayn wanda yaci sunan Mallam wato Usman sai Mufti wanda shi aka sakawa sunan Abban Saleem wato Muhammad ta shiga kunnenta. Ta girgiza kanta tana sakkowa kasa inda ta iskesu suna hayaniya kaman koh yaushe. Y'ar aikinta data maye gurbin Walida tun lokacinda Walidar tayi aure itace mai kokarin raba fadan da su Nurayn din keyi dan Mufti har ya bata rigarsa da tea dinda yake sha sha dole saida aka chanja mai wata. 


Saleem shima ya shirya ya sakko kasa Mufti ya fada jikinsa yana kukan fadan da sukayi Nurayn Saleem ya fara aikin rarrashi. Suka shiga mota direba ya jasu zuwa gidan Aisha. 



~~


9:30am


Babban daki ne wanda hasken safiyar marar yawa ya cikasa. Kamshi mai dadi na air freshner ne ke tashi a cikinsa Aisha tayi d'an karamin motsi a cikin bargon data rufa kanta dashi har wuya. Cikin baccin da bata gama wartsakewa daga gareshi ba ta mika hannu tana lalubar gadon. Dakin ya dauki sanyi sosai saboda Acn da yake a kunne har a sannan kuma data nemi wannan dumin jikin na Saraki ta rasa sai ta mika hannu kan bedside ta dauki remote din Acn ta kashe sa gabaki d'aya. 


Ta mike kafafuwanta ahankali a cikin gadon tana ware yatsun kafafuwanta daidai sanda babyn cikinta ya mika tasa kafar a cikin cikinta. Y'ar karamar dariya ta kubuce mata kafin ta kai hannu ta shafa cikin ahankali tace 


"Happy awake little one". 


Jikinta yayi mata nauyi sosai shiyasa ta kasa tashi daga kan gadon har zuwa sanda taji motsin bude kofar dakin. Koh bata juya ba tasan su waye suka shigo dan kunnenta har jiyo mata muryarsa tayi sanda yake cewa 


"Shh" 


Taji y'ar karamar dariyar Jannah wadda tasan tana cikin jikinsa a sannan. Zata kuma rantse Jannah ta kai y'an kananan yatsuntsa ta rufe bakinta dasu bayan tayi dariyar. Sai sanda suka karaso gadon tukun ta bude idanuwanta ahankali ta sauke a kansu. Wandon flannel ne a jikinsa kaman koh yaushe sai undershirt dinda ya saka data kamesa. A hannunsa d'aya tray ne dake dauke da abinda kamshinsa ya daki hancinta kai tsaye yana haddasa mata kukan hanjin ciki. A d'ayan hannunsa kuma y'ar autarta ce ya dakko wato Jannah wacca taci sunan Hajiya Firdausi an shiryata cikin wata jar doguwar riga y'ar kanti mai kyaun gaske sai hular da aka saka mata anyi baya da ita aka zubo mata y'ar kalabarta data sha bead ta gaba.


"Mommyy" 


Jannah ta fada cikin y'ar miryarta tana kokarin fita daga rikonsa dan haka sai ya sauke tray din a kan bedside drawer ya kuma sauke jannah a gefen Aisha, yarinyar ta zagaye kananan hannayenta a wuyanta. El Yakoub shima ya sunkuyo kansa ya sumbaci goshinta kamshin da yakeyi na sabulu da kuma turaren da bata taba gajiya da shaka ya shiga hancinta. Dan haka sai ta hada daga shi har Jannah ta zagaye hannayenta a wuyansu. 


"Rise and shine" ya fada mata ahankali bayan ya zauna gefen gadon ya kuma dago daga rungumar da yayi mata. 


"Pancakes?" ta tambaya tana nuna tray din da idanuwanta. 


Ya gyada kansa ahankali "With caramel and eggs". 


Tayi wani murmushin jin dadi dan tun dazu da asuba take kwadayin goated pancakes dinnan nasa da dukda yawon kasashen da sukayi bata taba cin wadda ta kaita dadi ba. 


"Mommy, Habiey and Zayn were doing rough play in the parlor then Daddy now..."  


El Yakoub ya saka hannu biyu ya ciro Jannah daga kirjin Aisha da take kokarin dannewa yace 


"Easy"


Jannah ta saka hannu a bakinta kamar mai laifi tana kallon cikin Aisha ta cikin bargon tace "Sorry baby" ga cikin tunda Saraki ya koya musu yiwa babyn magana tun kafin a haifosa. Aisha tayi y'ar dariya daidai sanda kofar dakin ta bude. Habiey wanda shine d'anta na farko ya kuma ci sunan Habeeb ana kiransa Habiey ya bude kofar dakin amma Zayn ( takwaran mahaifin Aisha mai rasuwa, Muktar ) shine ya rigasa shigowa yayo kan gadon da saurinsa ya kankame Aisha yana ce mata 


"Good morning mommy"


Habiey, wanda shine ya dakko kammanin mahaifinsa sak dan dukda shekarunsa takwas a sannan idan ka kalli girman jikinsa zaka daura masa sha biyu ya karaso bakin gadon yana cewa 


"Daddy su Nurayn sunzo, Uncle Saleem said to hurry it's almost time for the flight". 


Saraki ya gyada kansa yana daga Jannah daga jikinsa yacewa Habiey 


"Say bye to mommy". 


Dukansu suka rungumeta musamman Zayn da ya ringa tambayarta yaushe suma zasu biyosu Qatar dan dama shi mommy's boy ne tun yana babynsa. 


"Sai Baby yazo sannan mommy zatazo" Jannah ta fadawa Zayn. 


"Mommy a hospital za'a cire babyn koh" Zayn ya fada yana shafa cikinta. 


"Yes my love" ta bashi amsa. 


Saraki yayi y'ar dariya cikin nishadin da yake ciki na ganin family dinsa da yake tsananin kauna a tare sun zagaye mahaifiyarsu yace 


"Come on boys". 


"Bye mommy, bye baby" 


Habiey ya fada yana yiwa fuskarta da cikinta kiss. Zayn ma yayi mata bye itada babyn cikinta kafin Jannah ta bisu Aisha tana daga musu hannu. 


"Bari naje na dawo baby" 


Saraki ya fada mata sanda ya sunkuyo ya sumbaceta softly akan lips dinta in the most loving way ya kuma dago ya mata wannan kallon dake shaida soyayyarsa a gareta kafin ya mike tsaye. Aisha tabi bayansa da kallo sanda ya juya da yana bin bayan yaran, ya kamo hannun Jannah da take mika mai alamar ya dauketa sai wannan addu'ar da yayi tun farkon aurensu ta dawo kanta na cewar Allah yasa auren ya zama farkon mafi kyawun bangare na rayuwarsu. Taji wani sanyi ya ratsa ranta saboda sanin da tayi cewa wannan addu'ar ta zama karbabbiya, shaidar hakan kuma yana zagaye da ita ne duk inda ta waiga. 


And this right here is enough. 


Idanuwanta suka sauka akan katon photo frame dinda sukayi itada Saraki da kuma yaransu cikin tsananin farin ciki da soyayyar junansu. Ta yi murmushi ahankali tana shafa cikinta ta furta 


"Alhamdulillah ya Allah" 


—-


              The end💕

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol