Free chapter · Read without an account
DA JININSA NAKE RAYUWA
*DA JININSA NAKE RAYUWA*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
FUTURE WRITERS ASSOCITION (FUWA)
To iyalan Fam (JUMSS)
Gaisuwa.
Fatima Musa
Fatima Isa Manu
Nana Khadi
Meenat ‘yan doma
Nussy bee
Amanar cool
Mutanen alheri, Allah Ya biyaku da gidan aljanna, Allah Ya ƙara basira da ilimi mai amfani.
TSOKACI…
Ƙaddara wata saƙa ce mai sarƙaƙƙiya, wadda wani lokacin take haɗa maƙwabtan da ke nesa da juna ta hanyar da babu wani tunani na ɗan adam da zai iya fahimta.
Soyayya a ɗabi'ance abu ce mai sauƙi da ke shiga zuciyar ɗan adam ba tare da shawara ko izini ba.
Amma a lokacin da ta tsiro a tsakanin bangon addini, al'ada, da kuma ƙiyayyar da al'umma ke haɓakawa, tana zama tamkar ciyawar da ta fito a tsakiyar wuta, kowane gefe zafi yake fuskanta.
Sadaukarwa ita ce ainihin ma'aunin ƙauna.
Idan rayuwa ta kawo mutum matakin da mutuncinsa, jininsa, ko makomar rayuwarsa ke zama farashin da zai biya don ceto wani, a nan ake gane tsantsar ƙauna mai amsa sunanta. Amma menene yakan faru idan wannan jininsa na sadaukarwa ya zama sanadin da zai sa mai karɓa ya ɗaura rayuwarsa a kanta, alhalin duniya gaba ɗaya tana shirin rushe wannan ginin?
Auren manufa kuwa ba komai ba ne face makaranta ta wucin gadi, inda zuciyoyi biyu masu ra'ayoyi mabanbanta ke haɗuwa a ƙarƙashin rufin asiri ɗaya, guda tana kukan abin da ta rasa, guda kuma tana gudanar da lissafin kasuwanci da mutuncin iyali.
A cikin wannan littafi na DA JININSA NAKE RAYUWA, za mu gani ko shin jinin da ya ceto rayuwa zai iya doke katangar addini da al'ada, ko kuma auren manufa ne zai zama sabuwar ƙaddarar da za ta sake tsara makomar zuciyar da ke cikin mawuyacin halin zaɓi.
SHIMFIƊA…
Jihar Kano, Najeriya.
Jihar Kano tana ɗaya daga cikin tsofaffin jihohi a Najeriya, wadda aka ƙirƙira a ranar 27 ga watan Mayu, 1967 a ƙarƙashin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon. Jihar ta samo asali ne daga tsohon lardin Kano mai daɗadden tarihi tun kafin zuwan Turawa.
Kano matattara ce ta al'ummomi da ɗabi'u daban-daban. Babbar al'umma ce wadda addinin Musulunci da al’ada me ƙarfi ke shimfiɗe a zaman takewarta. Mutanen Kano suna da matuƙar riƙo da dokokin addini, kiyaye mutuncin iyali, da kare kimar al'ada a kowane fanni na rayuwa.
Sutura, aure, mu'amala, da zamantakewar iyali duka suna ɗaure ne a ƙarƙashin waɗannan ginshiƙai guda biyu.
A tsakiyar wannan birni mai ɗumbin tarihi, aminci da haɗin kai suna kan gaba, amma kuma akwai layukan da al'umma ba ta taɓa ƙetare su, bambancin addini da sharuɗɗan al'ada. A irin wannan muhalli, soyayya tsakanin tsarin addinai biyu mabanbanta ba abu ne kawai da ake kallo a matsayin saɓawa al'ada ba abu ne da zai iya rura wutar fitina, karya dokokin iyali, da kuma sanya ɗaiɗaikun mutane shiga mawuyacin halin zaɓi tsakanin zuciyoyinsu da al'ummarsu.
Duk da haka, kasuwanci ne ke zagayawa a jinin jikin kowane ɗan jihar Kano. Birnin matattara ce ta manyan masana'antu da 'yan kasuwa masu tasiri, inda dukiya da iko ke zama abubuwan da ke sauya ƙaddarar rayuwar mutane da dama. A cikin irin wannan al'umma ta izzah da amintaccen tsari, auren manufa tsakanin iyalai guda biyu yakan zama Hanyar Bullewa don kare mutunci, kasuwanci, da martabar iyali daga abin kunya.
A lokaci guda kuma, Kano matattarar fasaha ce da nuna bajinta; mutanen garin suna da sani a kan harkokin siyasa da na yau da kullum, kuma akwai mu'amala mai ƙarfi ta maƙwabtaka, inda murna ko baƙin cikin mutum ɗaya ya zama na kowa a unguwa ko ƙauye.
Kano tana can Arewa maso Yammacin Najeriya. A taswirar ƙasar, ita ce jiha mafi girman tasiri ta fuskar fuskantar kasuwanci da siyasa a Arewa. Yanayin garin yana da zafi sosai a lokacin rani musamman tsakanin watannin Maris zuwa Mayu, sannan akwai hunturu mai ratsa jiki tsakanin watannin Nuwamba zuwa Janairu.
Shafi na ɗaya
(01)
Sharaɗa NNDC, gida mai lamba 144C.
"Ke wai wace irin banzar yarinya ce da ba ta san ciwon kanta ba, Husna?!"
Muryar Mama ta karaɗe gidan tamkar ƙarar tsawar da ke barazanar tsaga benen gidan.
Husna ta riga ta yi nisa a cikin kukan da take yi, gwiwoyinta a haɗe da ƙirjinta yayin da take zaune a kan lallausan kafet ɗin ɗakin. Babu abin da Husna ke ji sai wani irin raɗaɗi mai zafi da ke daskarewa a cikin zuciyarta.
"A ce gida kamar wannan, gidan da ake taƙama da addini da tarbiyya, gidan malamai gaba da baya, amma ki dage sai kin ɗauko abin kunya kin yafa mana! Wai ke Husna kece zaki buɗe baki ki ce mana kina son wanda ba musulmi ba? Arne? Mutumin da ko yankan farce ba za mu haɗa da shi ba a addinance da al'adance?"
Mama ta faɗa tana ci gaba da masifa tana kai komo a tsakiyar ɗakin, fuskarta ta yi jajir saboda ɓacin rai. Duk wata kalma da take furtawa tana sauka ne a jikin Husna kamar ana zuba mata ruwan ɗanyen dalma.
A hankali Husna ta ɗaga kanta wanda ya yi mata wani irin nauyi, hawaye na wanke mata fuska, ta ce.
"Mama, ba za ku gane ba ne..." muryarta ta fito a kausashe kamar ba ita ke gunjin kuka ba. "Ba zan iya rayuwa babu shi ba. Idan na bar shi, tamkar na ci amanar rayuwata ne! Mama, jininsa ne fa yake gudu a cikin jijiyoyina. Da jininsa nake rayuwa!"
Kafin Husna ta rufe bakinta, ta ji saukar wani zazzafan mari a kuncinta wanda ya sa ta ga wasu taurari na wani ƙanƙanin lokaci. Wannan shi ne marin farko da Mama ta taɓa yi mata a duk tsawon rayuwarta, domin Husna ta kasance yarinya mafi soyuwa a zuciyar kowa da ke gidan, yarinyar da ake so ake kuma alfahari da ita, tun daga kan Abba, Mama, yayyenta maza har da ƙaninta ma Ashir.
"Rufe mini baki, shashasha mara tunani!"
Mama ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai tana nuna ta da yatsa.
"Wannan jinin da kake iƙirari ba shi ya halicce ki ba! Allah ne Ya ƙaddara jininsa zai shiga jikinki ya zama silar rayuwarki, kuma bai ci ki ce zaki sayar da addininki da mutuncin zuri'arki saboda shi ba! Ke yarinya ce mai taurin kai. Mahaifinki ya riga ya gama yanke hukunci, kuma babu abin da zai canza. Don haka ki goge wannan haukan daga ƙwaƙwalwarki, domin kuwa ko raba ki da rayuwar za a yi, ba za ki taɓa auren wanda ba musulmi ba!”
Kalaman Mama suka kusa dakatar da numfashin Husna, a hankali ta kwantar da kanta a kan kafet ɗin ɗakin ta sake rushewa da wani irin matsanancin kuka. Akwai ciwo mai tsanani idan mutanen da suka fi kowa ƙaunarka a duniya su ne suke ƙoƙarin raba ka da jinin da ke bugawa a zuciyarka. Amma ita dai ta san har yanzu ba azo wani dalili da zai hanata bawa zuciyarta abin da take so, na menene ma wai za a ce ba za ta auri wanda take so ba, ita a yanzu kukan nan da take yi ma ba na duk faɗa da nisihar da Abba ya yi mata bane kafin ya fita, kawai cewa da ya yi ba za ta auri wanda zuciyarta ke muradi ba shi ya sanya ta kuka, dan ita ko kaɗan bata son jin wannan kalmar, mutuwa kaɗai ce zata raba ta da abin da take so.
Sama sama ta ji ana sallama a tsakar gidan, tana ƙoƙarin ɗaga kai ta ga wace ke sallamar ta ga Hajiya Bilki ta shigo, aminiyar Mama a duniya, tun yarinta har zuwa girma, alaƙar su ba ta kasance iya ta ƙawance ba alaƙa ce ta ‘yan uwantaka, da Mama da Hajiya Bilki Cousin suke, abin da ya ƙarawa amintarsu ƙarfi kenan.
Da mamaki Hajiya Bilki take kallon Husna da ke kwance tana numfashi sama sama, ta kalli Mama da ke ƙoƙarin zama a kan kujera ta ce.
“Aminiya me yake damun Husna haka, na ji tana fitar da numfashi da ƙyar?”
Kallon Husna Mama ta yi, tana jin wani sabon ɓacin ran na ta so mata, gani take kamar ma soyayyar da suka nuna ma Husna ita ce ta jawo musu duka wannan abun da suke fama da shi, tun tana yarinya Husna tana da taurin kai da tsiwa, ga tsinnaniyar kafiya a kan abin da take so, sabida irin soyayyar da suke mata idon su ya rufe ba su isa su tanƙwarata ba, gashi yanzu anzo matsayin da take neman zamar musu fitina.
“Aminiya sokwanci da rashin lissafi irin nata, har yanzu tana nan a kan bakanta na auren wanda take so, wanda ba musulmi na, bai da haɗi da addini ubangji, ga kafiya kamar kafura.”
“Hasbunallahu wani’imal wakil, Husna me yake damun rayuwarki haka? Me kike shirin ja mana, ba zaki daina wannan taurin kan naki ba wanda ba zai haifar miki da komai ba sai wahala, wallahi baki isa ki zamar mana zakka ba cikin zuri’a, ba ki isa na faɗa miki.”
Kallon Hajiya Bilki Husna ta yi, duk soyayyar da ke tsakaninta da Hajiya Bilki sai ta ji ta disashe, a take wata tsana ta mamaye gurbin soyayyar ta ji kamar ta tashi ta yi tsallen albarka ta kama wuyan Hajiya Bilki ta yi ta cizo, a take wata zuciya ta yinƙuro mata ta miƙe tsaye ta yi cikin ɗakin, kafin ta shiga ta ce.
“Ni dai wallahi babu wanda zai hanani auren wanda nake so, naga kuma ai duk waɗanda kuke so kuka aura.”
“Husna, ungo wannan.”
Hajiya Bilki ta faɗa, Mama kam miƙewa ta yi tana jin gwanda ta je ta matse Husna ta mutu duk su huta da wannan ibtila’in da take shirin jefa su, da sauri Hajiya Bilki ta riƙo tana tana faɗin.
“A’a Aminiya karki kuskura ki biyewa zuciya ta kai ki akaita abin da zaki yi dana sani, duka babu abin da yake yi sai wahalal da bawa, ke a wahale ita a wahale, addu’a da nasiha ne kawai zasu yi mata.”
“Ai ni Aminiya gwanda na maƙureta ta mutu kowa ya huta, wai yau Husna ce take buɗe baki tana faɗin irin wannan maganar, Husna dai? Yarinyar da na so fiye da kowa cikin ‘ya’yana, yarinyar da ta samu gata daga ko ina, ba ga Alhaji ba, ba ga ni bare sauran ‘yan uwanta, amma Husna ke ƙoƙarin tozarta mu.”
Jawo hannun Mama ta yi ta zauna a kan kujera, sannan ta ce.
“Na sani kina jin zafi a cikin zuciyarki, amma dan Allah ki yi haƙuri, wai kin manta halin da muka shiga a baya? Kin manta faman da muka yi, to dan Allah wannan ma kar ya dameki, zai wuce in sha Allah.”
Sauki ajiyar zuciya Mama ta yi, sai dai kuma wannan da bambamci sosai tsakaninsa da na baya, shi Namiji ne, Husna kuma macece, sannan duk faman da suka yi bai hana abin faruwa ba, ita ina zata sa kanta idan Husna ta auri wanda ba musulmi ba?
Hajiya Bilki ba ta bar gidan ba sai da ta tabbatar ta taushi zuciyar Mama, duk itama zuciyarta a raunane take da abin da Husna ke shirin janyo musu, wanda har ya mantar da ita tata matsalal da ta kawo ta, sai da tazo tafiya sannan ta ce.
“Aminiya kin san Halima ta dawo gida, wallahi ta ajiye auren wai ta zaɓi kula da dukiyar mahaifinta a kan auren, ina zan sa raina da wannan abun? Yara kowa a kangare.”
“Auzubillahi Aminiya ki dakata dan Allah.”
Mama ta faɗa, sannan ta ci gaba da cewa.
“Shaye shaye suke? Zaki haɗa Ashraf da ta yayansa Faruq ɗan Hajiya Babba? Ko zaki haɗa Leemah ɗin da sauran ‘yan uwanta mata na gidan? Ga Nusaiba yanzu tana zaune gidan mijinta, ai ko a haka yakamata mu ci gaba godewa Allah, sannan mu roƙe shi ya ci gaba da tsare mana su tare da shiriya, ita kuma Leemah ina ga ai laifin Alhaji ne, a kan wane dalili yarinya tana gidan aure ya ce zai ba ta ragamar kula da kamfani?”
“Kema kya faɗa dai Aminya, ni wallahi bana son su a kan harkar kasuwancin nan, Ashraf da yake namiji ya je ya yi dai, amma matan ya barsu dan Allah. Hajiya Kubrah babu abin da ba zata iya ba a kan yaranta su kula da kamfanunuwan mahaifinsu, ni wallahi nawa na yafe tun da kowacce tana cikin rufin asiri, kuma a yanzu kamfanin da Ashraf yake ginawa ya fara samun ci gaba, a yanzu haka wasu kuɗaɗe kawai yake so Alhaji ya bashi ko aro ko kyauta ya ƙara shikenan ko da shi kaɗai suka dogara ya isa.”
“Aminya mu dage da addu’a, in Allah Ya yarda komai zai daidaita, kuma nasan Alhaji zai bada kuɗin nan.”
“Allah Ya sa, amma kinsan girman kan ɗan naki, ba zai iya tambayarshi kuɗi ba.”
“Zan yi magana da shi, ai idan ana nema sauke kai ake.”
“To ki dai faɗa masa.”
Hajiya Bilki ta faɗa, daga nan kuma ta fara haramar tafiya. Husna, tun da ta shiga ɗaki ta kwanta a kan gado kukan ma gaba ɗaya ya ƙauracewa idonta, daman ita ba ma gwanar yin kuka ba ce komai da ƙarfinta da taurin rai take yin sa, ko a makarantar kwana ma ba ta saduda da komai ba cikin hallayarta, dan ita kanta ta fahimci taurin kai da kafiya a jinin jikinta yake, yanda ta yi imanin cewa da Jininsa take rayuwa, to haka ta yi imani babu wani wahala da zai sa ta rabu da shi, tun tana jin maganarsu Mama sama sama har bacci ya ɗauke ta.
Sai gab da magriba ta tashi, shima surutun Ashir ne ya tashe ta tun da ya dawo daga makaranta yake ta tsalle a cikin ɗakin, wai sai ta tashi ta yi mai ƙarin karatu, tana buɗe idonta ta ce da shi.
“Ashir dan Allah ɗan ɗauko min wayar Mama ba ta sani ba.”
Buɗar bakin Ashir sai cewa ya yi.
“La yahillu maalu imri’in musulmin illa bi tibi nafsi minhu, ba hallata ka ɗauki dukiyar wani musulmi ba sai da yardarsa.”
Tsaki Husna ta ja, daman shi Ashir ba a abun arziƙi da shi, jiya ma daga yaga tana yi wa Yaya Abdul gunguni ya ce wai mai zagin iyayensa ba zai shiga aljanna ba, da ta ce mai ai Yaya Abdul ta yi wa sai ya ce Babbanwa magajin uba ne.
Yanda Ashir yake ji kamar shi kaɗai ya fara karatun addini, baiƙi ya zauna yana so ya ƙure Abba ba, haka zai ta janyowa yayansa hadisai suna fassarawa, ko ya aka sami kuskure wajen fassarar sai ya ce na su ba daidai ba ne.
“Ki zo ki yi min.”
Ya faɗa yana janyo hannunta, a fusace ta sake ɗagowa ta ce da shi.
“Idan baka fita ba sai na tsinka ma mari, na ce ba zan yi ba ko, ana dole ne?”
Sake jan hannunta ya yi, ta sa hannu ta tsinka mai mari ya fita aguje yana kuka, daidai lokacin kuma Yaya Walida ya shigo, Yaya Walid wuta ne yafi kowa faɗa cikin gidan, daman shine ma ya taɓa dukan Husna, shima bai fi sau biyu ba, dan ana biyun ma sai da suka yi faɗan gaske shi da Alhaji daga ranar kuma bai sake dukanta ba sai dai faɗa.
Ashir ne ya nufe shi yana kuka, Yaya Walid ya ce.
“Me ya faru waye ya dake ka?”
Cikin Kuka ya ce.
“Yaya Husna ce, dan na ce ta yi min ƙarin karatu shine ta mare ni.”
“Dan Allah Walid shiga ka ɓallamin yarinyar nan, yau idan na faɗa maka abin da ta yi min zaka iya zubar da hawaye wallahi, zagina ne kawai ya rage.”
Mama ta faɗa, dan tun ɗazu ranta zafi yake mata, idan ta tuna abin da Husna ta yi mata.
“Husna dai Mama? Dan Allah karki ce haka? Na ɗauka abin da Abba ya faɗa mata ɗazu ta ɗauka?”
“Bata ɗauka ba, ba ta kuma da niyar ɗauka ma, dan har cewa ta yi da ni da Aminiya wai ai muma waɗanda muke so muka aura.”
Ba ƙaramin mamaki Yaya Walid ya yi ba da jin abin da Mama ta faɗa, wai Husna ce ta buɗe baki ta yi wannan maganar, Husna dai sanyin idanun kowa a cikin gidan nan, me ta gani a tare da shi wannan wanda ba musulmin ba, wace irin soyayya take gani a tare da shi wadda ba ta gani a wajen ‘yan uwanta, ya tabbatar babu soyayyar da zai nuna mata wadda ba ta samu ba a gida, Husna da idan bata da lafiya kowa jinyar tsaye yake yi, babu wanda ke iya bacci kowa yana zagaye da ita, akwai lokacin da suka kaita asibiti a ƙafa suka ɗauketa a baya, da ƙyar ake karɓarta daga wajen ɗaya kowa so yake shi kaɗai zai kaita ko ance ya gaji sai ya ce a’a, a lokacin Abba baya nan su kuma mashin ɗaya ne da su kuma an kai shi juye, kawai suka saɓeta a baya sabida a ransa napep, sun nuna ma Husna soyayya kuma har yanzu suna kan nuna mata, kuma dukkansu sun yi imani da cewar soyyyar da suke mata ko rabinta iyayensu ba ta kai ba.
Me ya sa Husna za ta yi haka, a kan namiji wanda ba addinin su ɗaya ba, ina Husna ta kai iliminta, su kam gaba ɗaya wannan makaranatar kwanan bata ƙare su da komai ba, duk da abin da Husna ta nuna ta wani ɓarin hallace ni, amma kuma ta shiga hurumin addini, shi tausayinma Abba yake wallahi, ya za ayi ya iya buɗe baki ya ce wanda ba musulmi zai bawa ‘yarsa. A fili ya furta.
“Astagfirullah.”
Alhaji ne ya shigo gidan shima bakinsa ɗauke da sallama, ganin Ashir na kuka, ga Yaya Walid ya nausa duniyar tunani, haka Mama fuskarta a jagule ciki ciki ma ta amsa sallamar.
“Mama wani abu ya faru, ko Husna ce ba lafiya?”
Ashir ne ya ce.
“Dukana ta yi, kuma ta yi wa Mama rashin kunya har ta ce wai ai taga ita da Mimi waɗanda suke so suka aura.”
Daman haka Ashir yake, akwai saurin hadda da ya ji magana zai haddace ta tas, kamar a gabansa aka yi shi ya sa Mama bata magana a gabansa, ba ta bare ‘yan uwansa ma su yi a gabansa. Ƙirjin Alhaji ne ya bada wani rassss, wai Husna ce ta yi haka, a fusace ya ce.
“Tana ina?”
“Ɗakin ta.”
Ashir ɗin ya faɗa, Husna ta na ji Alhaji ya ce tana ina ta miƙe, tasan ƙarfine da shi kamar shari’a, a kan ta ya yi faɗa da Yaya Walid da yake yayansa kuma Yaya Walid ɗin aka zane, ko a waje ma da haka ake faɗa da shi a kan kowa na gidan, itama idan suna faɗansu na sakwanni haka yake jibgarta sai ya gama yazo yana bata haƙuri, sabida ita ɗin ce idan ta so rigimarta duk haƙurinka sai ka biye mata. Miƙewa ta yi ta sauka daga kan gadon ta tsaya a bakin ƙofa cikin shirin ko ta kwana, idan takama ma su yi doki doka da shi, tun da duk sun rufe ido sun ce son zuciyarsu suke so, itama zata rufe ido ta yi yaƙi da kowa a kan son na ta zuciyar.
Ya kuka ji salon wannan labarin? Ina fatan zaku bini sannu a hankali na feɗe muku biri har wutsiya.
Legendspen
***