Free chapter 路 Read without an account
CHAPTER 10
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Ha蓷uwar rayuka da 茩addara ta tattara wuri guda.*馃敟馃挃}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWAR茒AKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 10.*
**HASEEB**
Har wa yau ya rasa samun cikakken natsuwa tun randa yaci zarafin Jidda a asibitin da amininsa Dr.Ansar ke aiki. Daga baya ya ji a ransa sam be kyauta ba, Bai kamata ya tsoma baki cikin rayuwar wata da bai ma sani ba.
Yana tsaka da aiki, Hadiza ta yi ta damun shi awaya, sai data bashi 2 missed call, a kira na ukun ne ya daga, bayan sun gaisa ta ce"Sorry na dameka alhalin na san kana bakin aiki."
"Ba damuwa ya akayi ? meke tsalle ne?"
"Dama so nake ka duba kan WhatsApp na turo maka hoton yarinyar da take shugaba a gidan Samha. Dakyar na samu hoton ta, ka duba in tayi shikenan sai in ci gaba da shirya komai kafin ku ha蓷u. Don wallahi, yarinyar nan tana bani ciwon kai sosai. Shegen taurin kai gare ta. Idan kuma bata yi ba sai a nemi wata."
Hadiza ta sauke numfashi mai nauyi sannan ta ci gaba "Ka sani ya zama dole ka nemi yarinya a cikin gidan mata, yin hakan shi zai sa Samha ta ji ciwo ganin mijinta na bibiyar yarinyar da ke 茩ar茩ashinta."
Runtse idanunsa ya yi gami da shafa kansa da yake jin yana sara masa sabida tsananin damuwa. Ita Hadiza a lallai sai tasa ya nemi yarinyar da take rayuwa a gidan mata don koyawa Samha hankali.
Sun san cewa Samha ba za ta iya jure ganin mijinta yana bibiyar wata yarinya da take 茩ar茩ashinta ba. Hakan zai matukar 蓷aga mata hankali, kuma muddin tana sonsa, dole ne abin ya girgiza ta sosai.
A nan ne Haseeb yake ganin zai iya samun damar matsa mata lamba ta rushe gidan matan. Sai ya tabbatar da cewa lallai ta shiryu, tare da 蓷aukar alkawarin ba zata sake komawa gidan jiya ba, a sannan zai sallami ita yarinyar da suka 茩ulla soyayyar karya.
"Ok, zan duba amma ba yanzu ba sai na samu natsuwa."
Ya bata amsa sannan ya kashe waya ya maida aljihu, kana ya koma bakin aikinsa.
A 蓳angaren Hadiza kuwa, sai sake kallon hoton yarinyar data tura masa take bayan sun gama waya ita da Haseeb.
Da 茩yar ta samu wannan hoton don na musamman ta kai ziyara gidan mata, amma a waje ta tsaya sai da ta kwashe kusan minti talatin sannan ta ga fitowar Azagwai.
Hadiza ta sha bakar wahala kafin ta samu hoton Jidda a wajenta shima 蓷in wanda suka ta蓳a 蓷aukawa ne tare a tsakar gidan, lokacin da suka shirya bikin cika shekaru shidda da kafuwar Gidan mata.
A hakan ma sai da Azagwai ta yanke fuskarta a hoton sai ya rage fuskan Jidda ka蓷ai sanye da doguwar riga peach color, ta yane kanta da bakin mayafi.
Sosai tayi kyau a hoton, murmushinta ya 茩ara kawata kyakkyawar fuskarta.
Sai dai kafin samun hoton Hadiza ta sha tambayoyi wajen Azagwai kan mai take neman hoton Jidda tayi da shi?
Hadiza ta yi murmushi ta ce"Kar ki wani daga hankalinki abin alheri nake nufinta da shi ba sharri ba. Kuma hoton ai siya zan yi ba wai kyauta za ki ban ba."
Jin zancen kudi yasa Azagwai washe ha茩ora ta ce"Dakyau, yanzu naji batu, hoto kam kin gama samunsa kawai shiga xender mu yi shap shap fita zan yi."
Girgiza kai kawai Hadiza tayi cike da tausayin irin rayuwar da Samha ta jefa ya'yan mutane.
Shap shap ta tura mata hoton, ita kuma ta mata transfer 蓷in dubu ashirin cikin asusun bankin ta.
Da sauri Hadiza tabar kofar gidan gudun kar su jame da wanda ya santa har ayi wani tunani a kanta.
Amma kafin ta tafi sai da ta garga蓷i Azagwai kan kar ta sake wani ya samu labarin ta zo neman hoton Jidda, kai hatta ita kanta Jiddan kar ta kuskura ta fa蓷a mata.
"Hajiya ki sa ranki a inuwa, babu wanda zai ji wannan labarin tunda kin riga kin rufe min baki da shegun."
Ta furta tana dariya, Hadiza bata ce komai ba, ta shige mota tayi tafiyar ta don ta lura yarinyar shakiyiya ce ta gaske, kuma za tayi maitar son ku蓷i.
Taso karban layin wayar Azagwai sabida watarana tana iya kara neman wani taimakonta, amma kwata-kwata ta sha'afa.
Da isarta gida shine ta tura ma Haseeb hoton a lokacin yana bakin aiki.
***
Haseeb ya koma gida a matu茩ar gajiye, jikinsa duk tsami kamar wanda akayi ma shegen duka. Ya sa Samha ta ha蓷a masa ruwan wanka sannan ta fita zuwa kitchen don kawo masa abinci.
Dakyar ya tashi daga saman gado ya tube kaya, ya dora towel a kugu. Matsalarsa da Samha kenan sam bata iya tarairayar miji ba. Kamar yadda zaka ga wasu matan ke yi idan mazajensu sun dawo aiki, su cire masu kaya, su ja su zuwa bandaki, kai hatta wanka ma sai su yi musu kamar jira-jiran goye.
Suna gamawa azo a shafa mai, asa kaya, kai abinci ma abaki za'a ba shi kamar 蓷an yaye. Allah ya sani yana sha'awar irin wannan rayuwar ta ma'aurata masu shimfi蓷a rayuwar turawa a gidajensu amma shi sam ko kadan bai yi dace ba.
Ina ma take da lokacinsa ? Shi 蓷in banza a wajenta. Lokacin da take da shi a rayuwarta kawai shi ne GIDAN MATA.
Duk wani abin da ta san zai kawo ci gaba a wannan gidan shi take sa kai har sai ta ga an ci nasara.
Ga shi ya zama kamar wawa a wajenta, sam baya iya tabuka komai a kan duk wani motsinta. Ko wannan ha蓷i da Hadiza ke so tayi, ita ta kawo masa shawarar ba wai a son ransa bane.
Kuma har yanzu yana kokonto a kan irin aiki mai matukar hadarin da ta gabatar gareshi. Tunani yake zai iya ko ba zai iya ba ?
Sai a yanzu ma ya tuno da hoton data tura masa, da hanzari ya dauki waya, ya kunna data kana ya hau whatsApp.
Sai daya jira sakonni suka gama shigowa duka don rabonsa da hawa online tun safe, sabida ayyuka da suka sha gabansa.
Kai tsaye ya bu蓷e sakon Hadiza gabansa na bugawa da karfin gaske.
Hannu ya kai yana murza idanunsa don sake tabbatar da lallai fuskar yarinyar data addabi kwakwalwarsa da tunaninta a cikin kwanakin nan, ita yake gani a kan allon wayarsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wallahi ita ce....ita ce wallahi"
Ya furta hakan jikinsa na mugun rawa, a yayin da gabansa ya tsananta bugu.
"Wallahi yarinyar nan mai cikin nan ne wacce muka samu sa'insa a asibitin Dr.Ansar."
Jikinsa na rawa ya tura wa Dr.Ansar hoton ta, akasan hoton ya ce" Manchy ka gane wannan yarinyar??"
Ba ya online don haka kai tsaye ya kira shi awaya ya ce"Maza ka duba WhatsApp na tura maka sako,kuma ina bukatar reply cikin gaggawa."
Ya katse wayar, sake komawa kan hoton ya yi tare da zooming 蓷in fuskarta. Tabbas ita 蓷in ce wacce tun daga ranar da suka samu sabani bai sake samun natsuwar kirki ba.
'Yanzu dama ita ce shugabar da yake ji matarsa Samha na yawan magana a kai?'
' Yarinyar da Hadiza ke son ya nema kenan domin maganin Samha?'
Tuni ya ji cikinsa ya hargitse har yake ji lallai yana bukatar ziyartar toilet. Da sauri ya jefar da wayar kan gado ya afka bandaki sai kan toilet seat.
Shigarsa ke da wuya Samha ta shigo 蓷auke da tray 蓷in abinci, dai dai lokacin wayarsa ya shiga vibrating. Dr. Ansar ke kiransa bayan ya gama kallon hoton daya turo masa kan WhatsApp.
Da sauri Samha ta dire tray 蓷in hannunta sannan ta nufi inda wayar yake da kamar zai tsaga 蓷akin da vibration.
Har ya fara zazzage dattin cikinsa, sai kawai ya tuna cewa ai ya manta bai sauka kan WhatsApp 蓷insa kafin ya afka ban蓷aki ba, balle azo kan hoton Jidda da ke kan allon wayarsa.
A kowane lokaci Samha na iya shigowa 蓷akin, kuma abin da zai biyo baya ba zai ta蓳a haifar da 蓷a mai ido ba. Bai gama wannan tunanin ba ya ji motsinta, a hanzarce ya tsaftace jikinsa sannan ya fito bakinsa na ambaton sunan Allah.
"Shi wannan fa akwai nacin tsiya, mutum na tare da iyalinsa ma ba za a barsa ya sarara ba."
Har ta na shirin 蓷agawa domin ta tsage ma Dr. Ansar kasancewar akwai wasa a tsakaninsu sai kawai ta ji an fuzge wayar a hannunta har sai da gabanta ya yi wani irin mummunar fa蓷iwa.
Da sauri ta waiga ta na 茩are masa kallon mamaki, sai uban zufa yake kamar wanda ya ha蓷iyi 蓷an kunama. Duk yabi ya rikice, ya ma rasa abin yi har kiran ya yanke.
Sai da aka sake kira a karo na biyu sannan ya 蓷aga bayan ya fita 蓷akin ya na waigenta gudun kar ta biyo sahunsa. Gaba 蓷aya yanayinsa ya nuna rashin gaskiya a tattare da shi.
A corridor 蓷in 蓷akunansu ya tsaya yana waya da Dr. Ansar cikin kwantar da murya kar Samha ta ji.
Sama-sama suka tattauna sannan a 茩arshe ya ce "Zan sameka a gida nan da mintuna ashirin."
Ya na gama fa蓷in hakan be jira ya sake jin ta cewar Dr. Ansar ba ya katse, bai 蓳ata lokaci ba ya goge hoton Jidda a kan WhatsApp 蓷insa, ya ha蓷a hadda chat 蓷insa da Hadiza ya goge tass, a sannan ya iya sauke ajiyar zuciya mai nauyi hadda wani dafe 茩irjinsa wanda ya yi daidai da fitowar Samha hankalinta a mugun tashe, har sai da ya 蓷an firgita da jin motsinta a kusa da shi don ya bawa 茩ofar 蓷akin baya ne.
Cike da zargi Samha ta ce"Wai me yake faruwa ne na ga duk ka firgice? Wayan ma ka gagara yinsa a gabana har sai da ka fito waje?"
Sai da ya daidaita natsuwarsa sannan ya ce"Dama ciwon Inno mahaifiyar Ansar ne ya tashi tun safe ake ta fama da ita, shiyasa da na ga kiransa hankalina ya yi mugun 蓷agawa. A zatona mummunar labari zan ji daga gare shi, ashe ya kira ya gaya min an sallameta tana gida."
Cikin wani yanayi na tausayi ta ce"Allah sarki Inno ciwon sigar nan dai ya sakata gaba, ubangiji Allah ya bata lafiya."
Haseeb ya amsa da amin, in dai magana ake ta tausayi to babu kamar Samha. kuma bai yi karya ba da gaske dama jikin nata ya motsa amma ba zancen yau bane, akalla zai yi kusan kwana uku shi dai kawai ya yi amfani da ita ne wajen kare kansa.
Bai tsaya cin abinci ba don baya da natsuwar da zai ji da蓷in cinsa, rufaida yogurt kawai ya zuba a kofi ya 蓷an kurba shima 蓷in gudun 蓳acin ranta ne, kar ta ga ta masa 蓷awainiya amma ko ka蓷an be ta蓳a ba duk da ba ita tayi girkin ba.
Haseeb ya tsani cin girkin 'yan aiki, 茩yan茩yami garesa sosai amma haka yake 蓷aure wa yake ci don Samha ta riga ta tsabar masa da wannan rayuwar. Jallabiya mara nauyi ya jawo ya zura sannan ya fice da sauri abin har tsoro ya koma ba Samha ganin yadda yake ta rawar jiki duk da ance masa jikin Innon da sauki. Bata san ma anan ji yake kamar ya zama 蓷an tsuntsu ya tashi sama ba ne.
Sai da ya tsaya ya gabatar da sallar magrib a kan hanya sannan kai tsaye ya nufi gidan Dr. Ansar.
Tuki yake amma gaba 蓷aya kwakwalwarsa a caje take, sai cizan le蓳una da shafar kwantacciyar bakin gashin kansa kawai yake tayi da hannu 蓷aya, 蓷ayan kuma a kan sitiyari ya na sarrafa shi.
Ya shafe mintuna talatin zaune cikin mota ya na jiran fitowar Ansar amma shiru-shiru bai fito ba. Sai a sannan ma tunanin kiran Hadiza ya fa蓷o ransa don shaida mata halin da ake ciki. Sai daya ba ta missed calls har uku, a kira na hu蓷u ne ta daga.
"Dama shi likita gaggawa ne dashi sam bashi da hakuri, wannan kira haka babu sassautawa kar dai ace har yarinyar ta samu 茩arbuwa ne?"
Ta furta hakan cike da tsokana har tana 茩yal茩yala dariyar, ita a ganinta har tarko ya kama ne.
"Ai kuwa ko kusa ba ta samu 茩arbuwa ba. Hadiza akwai matsala babba!"
Da sauri ta dafe 茩irji har ta na 茩o茩arin mi茩ewa tsaye daga kan sallayar da take zaune akai, ta ce" Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Haseeb wani irin matsala kuma? Idan ba ta maka ba ai babu dole a ciki sai a nemi wata gasu nan birjik, har sai ka zaba ka dirje."
"Hadiza ni fa zancen ha蓷uwar mace ba shi ne matsalata ba. Abin da kawai aiki zamu yi na 蓷an gajeran lokaci, to ina ruwana da wani ha蓷uwarta? Kawai so nake in fa蓷a miki idan har yarinyar da kika turo min da hotonta, ita ce kike son 蓷orawa a kan aikin namu to ki shafe batunta don ciki ne gareta."
A karo na biyu ta sake kai wa 茩irjinta bugu, a lokaci 蓷aya ta na salati.
"Ciki fa Haseeb?"
"Yo! To meye abin mamaki? You should expect that from her tunda 'yar 茩walta ce."
Huci mai zafin gaske Hadiza ta fesar kan ta ce"Haka ne! to amma taya kasan tana 蓷auke da juna biyu? Dama ka santa ne?"
Kwashe labarin komai ya yi ya fa蓷a mata na rikicin da ya yi da ita a asibitin Dr. Ansar.
Sam bata so jin hakan ba, da yaya ta samu ta Shawo kan Haseeb ya amince zai nemi yarinya a gidan?Tana jin da蓷i haka ta kusa cimma ruwa sai ga zancen ciki ya bullo.
"To, kin ga dole ta sauka a kan tsarin aikinmu. A canzata da wata don wallahi ba zan bari tsautsayi ya sake ha蓷ani da ita ba. Yarinya ta ga dama ya samu ta 茩ulla min sharri ta ce ni nayi mata ciki."
Ya fa蓷i hakan da iya gaskiyarsa.
Jiki a mace Hadiza ta ce"Wata茩ila zuwa yanzu ai ta zubar da cikin...."
Haseeb ya yi saurin taran numfashinta "Kin san me? Ko ta zubar wallahi still bana bukatar wannan yarinyar, kawai a canzata da wata 蓷in ina ganin zai fi. Kuma duk wacce kika kuma samowa kafin mu fara aiki ya zama dole aje a mata gwaji don tabbatar da cewa bata 蓷auke da juna biyu. Don ba zai yiwu yanzu in kaucewa matsala, daga baya kuma in zo in afka ciki ba, ki huta lafiya."
Kit! Ya katse wayar yana fesar da zazzafar huci daga bakinsa kamar wanda ya ci uban gudu.
Gefensa Ansar ne zaune wanda ya 蓷an jima da shigowa motar, ya kasa kunnuwa yana sauraronsu har suka gama waya. Kasancewar ya san kwanan zance, duba da irin amintar dake tsakaninsu, 蓷aya baya ta蓳a aiwatar da abu ba tare da ya nemi shawarar 蓷an'uwansa ba.
Hannu yasa ya dafe goshinsa da yake jin kamar zai tsage tsabar ciwon kai, a hakan ya 蓷aure ya waiga sashen Ansar ganin shirunsa tayi yawa uffan ya kasa cewa.
"Manchy baka ce komai ba kayi shiru."
Girgiza kai Ansar yayi ya ce"Me kuwa kake son in ce? Ni na gaji da fa蓷a maka gaskiyar da baka son jinsa."
Ya ida magana yana mai kau da kansa gefe wanda hakan zai tabbatar maka da lallai aminin nasa ya 蓳ata masa rai ainun.
Jikin Haseeb ne ya yi bala'in sanyi hakan yasa ya kwantar da murya ya ce"I'm sorry if i hurt you amma don Allah ka yi min uzuri wallahi I'm just confused na rasa ta yadda zan bullowa al'amarin Samha ne."
"Kana ganin bullowa Samha ta wannan hanyar shi ne zai iya gyara komai? To, ka sani zaka sake haddasa matsalar data fi ta da muni ne. Bugu da 茩ari, zaka 蓳atawa kanka da family 蓷inku suna. Idan har na fahimta ita wannan yarinyar da kuka ta蓳a samun sa蓳ani a asibitina ita ce wacce Hadiza ke son 蓷orata kan aikin naku right?"
"Yes!Yes ita ce, kuma ka ga tunanina a kanta ya tabbata gaskiya. Cikin shegen ne take 蓷auke dashi wanda tayi yunkurin zubarwa."
Ansar ya gyara zama ya ce"Wannan tsari na Hadiza sam bai yi ba. Haseeb yanzu sai ka biye mata? Me yasa zaka ba mace damar sarrafa tunaninka? Da zaka kar蓳i shawarata da ni zance ka manta da batun neman duk wata mace mazauniya gidan mata da sunan ha蓷a kai da ita domin maganin Samha. Kar azo garin neman gira a rasa ido, muddin ba jihadi zaka yi na auren ba to kawai mallam ka sallama ka bari Allah ya yi ikonsa akan lamarin Samha."
Ya 蓷auki tsawon lokaci sosai yana fahimtar dashi abubuwan da suka shige masa duhu, sai a yanzu yake ganin wautarsa na biyewa Hadiza da wannan shirmen banzan. Ya yi nadama sosai sannan ya yi hamdala ga ubangiji da ya azurtashi da aboki na gari.
"Ruwa a 蓷an cokali ya ishi mai hankali wanka. Ka je ka natsu kayi tunani a kan zancen da muka tattauna akai, sai da safe my very own Manchy."
Daga haka suka yi sallama Haseeb ya tafi. Amma sai da ya biya ta gidan abincin Yallabai ya karbar wa Samha sa茩o. Abinka da me juna biyu, wai ga蓷a蓷蓷en kifi da arish chips take 茩wadayin ci.
**JIDDA**
Yau ta tashi ne da marmarin cin chicken parmesan wanda yana 蓷aya daga cikin abin da tafi son ci a gidan abincin Yallabai. Da ace yazo ne da shi da kansa zai shiga kichin ya girka mata, kuma gaskiya ita ba zata iya jiran zuwansa ba don ji take muddin bata ci abin da take so ba, ba zata gane ma kanta ba.
Babu shiri ta nemi amintaccen kukunsa Aliyu wanda shi ke jagorantar babban branch 蓷in gidan abincinsa. Kuma tabbas yana 蓷aya daga cikin mutanen da suka san da matsayin da take da shi wajen ubangidansa. Aliyu mutum ne me riko da sirri bai ma fiye surutu ba, shiyasa Yallabi ya aminta dashi 蓷ari bisa 蓷ari wanda hakan yasa ita ma Jiddan sakin jikinta dashi.
Bayan ta kira shi ta bada odan ha蓷a mata lafiyayyen chicken parmesan.
Cike da girmamawa ya amsa mata "An gama ranki ya da蓷e, amma aiko miki dashi za ayi ko dai da kanki zaki zo?"
Dayake tana so a yau ta le茩a gidan mata saboda akwai aikin da za tayi a gidan mata, don wata yazo 茩arshe akwai wa拼anda suke so su biya ku蓷in haraji. Ya zama dole ta je gudun kar ta sake shiga ukunta a wajen uwar 蓷akinta, ganin kamar tana son fara mata wasa da aiki ne.
"No, karka damu zan biyo na karba da kaina dama fita zan yi."
"Ok ma! Ki ban nan da 1hr, idan yayi ready zan sanar dake."
"Ok thanks."
Ta furta sannan ta kashe wayar cike da mamakin yadda ake girmamata da kuma 蓷aukakata saboda ala茩arta da babban mutum kamar Yallabai.
Ko awa 蓷ayan ma be buga ba ya kira yake sanar mata da cewa ya yi ready. A gurguje ta shirya cikin abayarta kalar ruwan hanta da ya yi masifar mata kyau. Ta yane kanta da mayafi sannan ta jawo face mask ta rufe kusan rabin fuskarta da shi.
Tana cikin feshe turare wayarta dake saman dressing mirror ya bada WhatsApp alert sound. Ta kai hannu ta 蓷auki wayar tana dubawa, kusan alokaci 蓷aya Saffy da Azagwai suka turo sa茩o.
"Yaya kin tashi lfy? Dama so nake mu tattauna kan aikinki a gidan mata da kuma aurenki saboda na shiga wani hali na rayuwar da kike yi."
Kai tsaye ta bata amsa "Ki bari idan nasa mana lokacin ha蓷uwa zan sanar dake. Good morning and have a great day ahead, Nagode."
Da sauri takai hankalinta kan chat 蓷in Azagwai.
"Shugaba! Yaushe zaki shigo gari akwai magana fa? amma wallahi sai kin bada wani 蓷an ihsani kafin na fa蓷a ke kin san halina ai."
Gabanta ne taji ya bada rass! don ita fa muddin wani yace yana son magana da ita to kai tsaye take ganin kamar an gano alakarta da Yallabai ne, balle kuma kowa yasan halin Azagwai na gidan mata rediyo me jini kenan. Idan ka bari ta san wani sirri naka to kai kam ka gama yawo.
Ba ta tsaya reply 蓷inta ba, kai tsaye ta kirata a waya, bugu 蓷aya, biyu ta 蓷aga tana" Shugaba! Ya akai ne? In yi pasting aza 蓷in ne?"
Cike da takaicinta ta ce"Don Allah ki gaya min me yake faruwa ne?"
"Wallahi bazan fa蓷a ba ke ma kin sani sai kin biya, kina abu kamar yau kika fara sanina, haba Shugabar mata."
Tsoki Jidda ta ja sannan ta ce a hasale"Ke dai wallahi Azagwai sam baki da tausayi, idan aka baki dama tsaf! zaki iya yi wa gawa bulala."
Sai da aka tsadance ta tura mata 蓷an ihsanin sannan ta fesa mata zance.
"Yauwa! dama ba wani abu bane fa Anty Hadiza ce ta zo shekaranjiya ta biya ku蓷i na tura mata hotonki. Kuma kema kin san ba zan ta蓳a cin amanarki ba dole na fa蓷a miki abin da ke faruwa."
"What?? Wacce Anty Hadizar kike nufi?"
Har sai da Azagwai ta tsorata da tsawar da Jidda ta doka mata, ta蓳e baki tayi ta ce"Yo! Anty Hadizan guda nawa kika sani? To, ta amanar Uwar蓷ak nake nufi....."
A fusace Jidda ta tari numfashinta ta ce,
"Yanzu Azagwai don baki da hankali, ki bada hotona sabida son abin duniya irin naki, ko shakka babu zaki iya aikata komai a kan ku蓷i. Yanzu sabida Allah idan wani muguntar za a min shikenan fa an ci nasara a saukake. Wallahi Shafa'atu baki mori hali ba, kuma bari kiji in fa蓷a miki duk abin da ya same ni mara da蓷i sanadin hoton nan nawa da kika tura ma wata ba tare da sanina ba kin ji na rantse da Allah kuma ki rubuta ki ajje, zan tabbatar da na rabaki da gidan mata sannan in sa ki 茩are rayuwarki a gidan gwale-gwale, stupid girlllll kawai."
Tana gama fa蓷in hakan ta ja dogon tsaki ta yanke wayar zuciyarta na bala'in zafi tamkar wacce aka ba蓷awa barkono a 茩irjinta.
"Me yasa Anty Hadiza za ta min haka? A kan me za ta kar蓳i hotona wajen wacce ba ta iya rike sirrin mutum? Ta yi me dashi?"
Ranta a matukar 蓳ace ta nemeta a waya, A daidai wannan lokacin kuma Hadiza na kan traffic, danger ya tsai da ita, gashi sauri take ta isa wajen aiki da wuri saboda supervisors da za su kawo musu ziyara a yau. A jami'ar Kaduna take aiki wato KASU, non-academic staff ce.
Da 茩yar dai ta samu aka bata hannu ta wuce, wai ahakan kuma so take ta biya Alkaleri's kitchen ta kar蓳i breakfast package don ko kari bata tsaya tayi ba.
Shigowar 茩iran Jidda ba 茩aramin mamaki ya shayar da ita ba, don bata ta蓳a kawo aranta Jiddan za ta nemeta nan kusa ba kan batun da suka ajje. Paka motar gefe tayi domin amsa kiran nata
"Kamar kin san ina shirin nemanki sai kika riga ni."
Hadiza ta furta bayan ta daga wayar.
"Nima 蓷in nemanki nake ruwa a jallo, ki fa蓷a min ina zamu ha蓷u?"
Jidda ta ida magana da 蓷an zafi-zafinta. Ko ka蓷an Hadiza ba tayi mamaki ba don ta san cewa dama ba wani jituwa ne a tsakaninsu ba kuma duk dalilin zancen Haseeb ne da ta bijiro mata da shi, hakan yasa raini me 茩arfin gaske shiga tsakaninsu.
Lokaci da kuma wajen ha蓷uwa suka ajje sannan Jidda ta kashe wayarta.
Sai data daidaita natsuwarta sannan ta fice zuwa gidan abinci, taso kiran Yallabai amma tana tsoro maybe yana tare da uwargidansa, tun asuba da suka yi waya basu sake ba amma dai ya san da cewa za ta ziyarci gidan mata a yau.
**Hadiza da Haseeb suna shirin amfani da Jidda wajen cimma burinsu, alhali ba su san cewa Jidda ta riga ta zama matar Yallabai a 蓳oye ba.馃槼馃挃**
**Shin kuna ganin wannan shirin nasu ne zai tona asirin auren Jidda da Yallabai? 馃憖馃敟**
**Update sai Allah ya kaimu monday in sha Allah...Barka da Juma'a my pipul, Allah ya sadamu da dumbin alherin da ke cikin wannan rana mai albarka, Ameen.馃檹**
Hafnancy.
***.
NAGODE ALL鉂わ笍