Free chapter · Read without an account

Chapter 5

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??

BOOK 1

Umma Mustapha

Arewapen: Umma mustapha/ @umsar

Wattpad: Umma Mustapha

PAGE 5

Nihla ta ɗaga kanta daga cinyar Hajiya Mama, sannan tana kallonta.

"Yaya Jafar kuma?"

Hajiya Mama ta gyada kai.

"Eh. Kuma ki shirya tun yanzu. Kar ki sa ya zo ya fara wannan hayaniyar tasa."

Nihla ta yi murmushi.

"Nifa shi yasa bana son fita ta hadani da yaya Jafar, saboda idan yazo sai ya rikita kowa wallahi" ban san me ya sa kullum yake cikin sauri ba ."

Hajiya Mama ta kalle tace. 

"Ke dai ki shirya. Jafar ba ya son jira."

Nihla ta miƙe daga kujerar, ta nufi ɗakinta domin ta shirya. Amma kafin ta kai ga shiga cikin dakin, sai suka ji ƙarar horn ɗin mota a harabar gidan.

Nihla ta tsaya cak.

Hajiya Mama ta kalli Baba Jummai.

"kinji Dan halak ko ana maganarsa sai gashi"

Baba Jummai ta tashi tana murmushi.

"Wallahi, kuwa Jafar ne ai tukinsa da ban yake."

Nihla ta ɗan tabe baki.

"Allah ya sa yau bai zo da masifa ba."

Da sauri ta shiga ɗakinta domin ta sauya kayanta. Ba ta fi minti biyu da shiga ɗakin ba, sai ga Jafar ya shigo falon.

Kusa da Hajiya Mama ya zauna, yana cewa:

"Hajiya Mama, tamu Allah ya bar mana ke. Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana."

Murmushi Hajiya Mama ta yi.

"Jafar kenan, sarkin zolaya! Daga ina haka?"

Hannu ya saka cikin gyadar da ke gaban Baba Asabe, ya ɗauki ɗan kaɗan, sannan ya ba Hajiya Mama amsa.

"Wallahi, baban abokina muka raka Airport. Za su tafi Umara."

Baba Jummai da ke gefe ta amsa da:

"Allahu Akbar! Ka ce sun tafi Ƙasa Mai Tsarki? An ƙetare hazo kenan."

Dariya Jafar ya yi.

"Su Baba Jummai, an ji maganar Makka yau. Ba zan lafiya kenan?"

Ita ma dariyar ta yi, sannan ta ba shi amsa.

"Yo, ɗan nan, kowa fa yana son ya je Ƙasa Mai Tsarki domin sauke farali."

Dariya Jafar ya ƙara yi, yana watsa gyadar da ke hannunsa zuwa bakinsa.

"Kar ki damu, Baba Jummai. Ku yi min addu'a na samu wani babban mukami a gwamnati, na zama gwamna ko wani minista. Ai zuwa Makka sai kun gaji da ita."

"Allah ya amsa bakinka," Baba Asabe ta ba shi amsa.

"Ameen," Baba Jummai ta ce.

Jafar ya juya ya kalli Baba Asabe.

"Baba Asabe, a ina kika samo gyadar nan? Wallahi, na ji daɗi sosai. Na jima ban ci gyada mai daɗin wannan ba."

"Makociyata ce take yi."

Dubu biyu ya miƙa mata.

"Gobe. Idan kin tashi zuwa, ki taho min da ita."

Sai ya juya ya mayar da kallonsa kan Hajiya Mama, wadda take fama da waya a hannunta.

" Hajiya Mama, wai ina yarinyar nan take? Ko ba ta san ita nake jira ba? Ni fa, kar ta ɓata min lokaci. Ina da uzurin da zan yi."

Hajiya Mama ta kalle shi.

"Da duk ba ka san da uzurin ba, ka zo ka nemi guri ka zauna kana shegen surutu, sai yanzu kuma za ka damu mutane?"

Miƙewa Jafar ya yi, ya nufi ɗakin da Nihla take.

"Kar ka je ka hargitsa min yarinyar, na faɗa maka," Hajiya Mama ta yi masa kashedi.

Ya ware muryarsa yana ƙwala wa Nihla kira.

"Nihla! Ki fito mu tafi!"

Da sauri Nihla ta fito daga ɗakinta. Ta shirya tsaf cikin doguwar rigar abaya baƙa, wadda ta yi mata kyau sosai. Turarene a hannunta, tana fesawa jikinta, bayan ta gama fesawa ta ajiye kwalbar turaren kusa da Hajiya Mama tana ƙoƙarin rataya jakarta.

Kallon Nihla Jafar ya yi.

"Ba ki yi kyau ba. Gaki baƙa, kin ɗauki baƙar riga kin saka. Gaba ɗaya kun saje da rigar."

Nihla ta kalle shi, ta tura baki irin na shagwaba.

"Kyau na maka shi ya sa ka fadi haka. Kuma na san na fi wannan budurwar taka kyau."

Bai kula ta ba. Ya saka hannu ya ɗauki turaren da Nihla ta ajiye, yana dubawa.

Sai ya kalli Hajiya Mama.

"Wannan turaren fa? Ba shine Wanda nace Miki ki bani ba, Amma kika Hanani."

Ya ci gaba da magana yana nuna rashin jin daɗinsa.

"Yanzu ga shi nan, yar gwal ta ɗauko ta shafa, babu abin da kika ce mata. Amma ni ranar da na shiga ɗakinki na shafa na fito, sai da kika tara min mutane a gidan nan, wai na ɗauki turaren da Yaya Babbah ya kawo miki na shafa. Har da sauya masa wuri kika yi, kika ɓoye shi."

"Amma yanzu ga wannan yar baƙar nan ta ɗauko ta shafa, babu abin da kika ce mata."

Baba Jummai ta yi dariya.

"Kai dai Jafar, an yi babban kwabo! Yanzu kai ka rasa wadda za ka haɗa kanka da ita, sai Nihla?"

Jafar ya cewa: Baba jummai 

"Ba za ka gane ba. Hajiya Mama ta fi son Nihla sama da kowa a gidan nan. Ba ta son laifinta."

Hajiya Mama ta kalle shi.

"Yanzu ai kamata ya yi ka ɗauki mataki kawai."

Dariya Jafar ya yi.

"Wane mutum? Mun haƙura kawai."

Sai ya fesa turaren a jikinsa, sannan shi da Nihla suka fice.

A cikin mota kuwa, Jafar ne yake ta sharara gudu, kamar zai tashi sama. Shi ya sa suka isa wurin yin registration din da wuri.

Sun ɗan samu layi a wurin, don haka Jafar ya ba Nihla mukullin motar.

"Je ki cikin mota ki zauna. Idan layi ya zo kanki, zan zo in kiraki."

Shi kuma ya nemi guri ya zauna yana jiran lokacin da za a zo kansu.

Sai dai sun ɗan samu tsaiko saboda matsalar network, wadda ta dinga kawo musu cikas. Ba su bar wurin ba sai wajen ƙarfe biyu da rabi na rana.

Ba gida suka nufa ba. Sai da suka biya gidansu budurwar Jafar, ya kai Nihla ta yi sallah a can.

"Ki zauna a nan. Zan je in dawo," Jafar ya faɗa mata kafin ya tafi.

Budurwar tasa mai suna Zainab kuwa, sai wani rawar jiki take kamar za ta goya Nihla saboda murna.

A nan dai Nihla ta yi dan ƙaramin wuni, domin Jafar bai dawo ba sai wajen ƙarfe biyar da rabi.

Shima saboda Hajiya Mama ta takura masa da kira, tana ta cewa ya dawo mata da "Yarta", ko kuma ta haɗa shi da Yaya Babbah, don haka ya taho ɗaukar Nihla.

Zainab ta ba Nihla kyautar kayan kwalliya da turare, da kuma dogayen rigunan shan iska guda biyu. Sai kuma kayan snacks ta yi wa Nihla pack ta haɗa mata su.

Daga ganin yadda Zainab take nuna kulawa ga Jafar, ya bayyana cewa tana matuƙar son sa. Abin har mamaki yake ba Nihla idan ta ga yadda Zainab take kashe wa Jafar murya da kulawa.

Har bakin mota ta raka Nihla, tana cewa:

"Ki gaida min Hajiya Mama."

Nihla ta yi mata murmushi tare da yi mata godiya.

Daga nan suka yi sallama suka tafi.

Sai dai a hanya sun biya ta zooroad sun siyi shawarma da gasasshiyar kaza. Ba su isa gida ba sai daf da magariba.

Bayan sun dawo, suka yi parking a harabar gidan. A wajen suka tarar da Baba Idi yana alwala a fanfon da ke harabar gidan.

Da Baba Idi ya hango Nihla, sai ya fara murmushi.

"Uwar masu gida, kun dawo?"

Nihla ta amsa cikin fara'a.

"Eh, mun dawo, Baba Idi."

Sannan ta fara gaishe shi. Ya amsa gaisuwar, yana ci gaba da zolayarta kamar yadda ya saba. Jafar kuwa tuni ya yi gaba ya shige cikin gidan.

Jin an ƙwada kiran sallah a masallacin da ke jikin gidan ya sa Baba Idi ya yi wa Nihla sallama, sannan ya nufi masallaci domin gabatar da sallah.

Baba Idi mai gadin gidansu ne. Ya jima yana yi musu aiki tun mahaifinsu yana raye. Bayan rasuwarsa ma, ya ci gaba da aikinsa har zuwa yanzu.

Baba Idi mutum ne mai fara'a da barkwanci. Ba ya da saurin fushi, kuma zai yi wuya ka ga Wani Abu ya Bata masa rain. Tasu ta zo ɗaya da Nihla da Jafar, domin sukan yi ta hira da zolayar juna.

Cikin gida Nihla ta shiga. Ba ta tarar da kowa ba sai Yaya Aminu, wanda ke zaune yana naɗe hannun rigarsa, alamar ya gama alwala.

"Yaya Aminu, ka dawo?" Nihla ta faɗa, fuskarta ɗauke da murmushi.

"Na dawo," ya ba ta amsa, yana mayar mata da murmushi. Sai ya kalli ledar da ke hannunta.

"Me kika samo ne a cikin ledar?"

Nihla ta yi dariya.

"Budurwar Yaya Jafar ce ta ba ni kyauta."

Kafin Aminu ya sake cewa komai, sai

Yaji ana Shirin tayar da sallah . Sai ya tashi ya nufi masallaci, ya bar Nihla a wajen.

Ita ma ledar ta dora a kan dining, sannan ta nufi ɗakin Hajiya Mama.

Ta tarar da Hajiya Mama tana sallah. Don haka ita ma ta yi alwala, sannan ta tayar da sallarta.

Bayan ta idar da sallah, ta ɗauke abin sallarta ta ajiye shi gefe.

Hajiya Mama ta kalleta.

"Gidan uban wa kuka je kuka zauna? Ba ku dawo ba sai magariba!"

Nihla ta yi saurin amsawa.

"Wallahi, ba laifina ba ne. Laifin Yaya Jafar ne. Shi ne ya kai ni gidan su Zainab, budurwarsa. Ya ce zai je ya dawo, amma bai dawo da wuri ba."

Hajiya Mama ta yi kwafa, sannan ta mike tana cire hijabinta. Ba tare da cewa komai ba, ta fita zuwa falo.

Nihla ma ta bi bayanta.

Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol