Free chapter · Read without an account
First crack
A Daren tayiwa rayyan screenshot din email din ,inda ya kirata suka fara tsara tafiya abuja kuma ya tabbatar mata dashi zaayi tafiyar da kyar ta iya bacci ranar Sabida murna
Tsabar doki tana idar da sallar asubah ta nufi dakin mama Bayan an mata iso ta gaishe da iyayen nata cikin ladabi wayar ta bude tare da
nuna musu saƙon nasarar da ta samu na tafiya shirin Residency a Abuja nan da kwana huɗu.
Masha Allah auta am very proud of you cewar abba yana kallon ta cike da alfahari ,
“Allah yasa albarka Mimi mama ta fada tare da Ninke sallaya ,sai dai babu maganar tafiya ke ɗaya har Abuja. Dole Mubeen ya raka ki, ya jira har ki gama ku dawo tare
Nuwayrah ta gyaɗa kanta cikin gamsuwa da biyayya, “To Mama, nagode. Rayyan ma yace tare zamu ,Allah ya kaimu mama tace tana kwanciya gefen gado ,haka nuwayrah ta yini cikin walwala Kallo daya zaka mata Kaga Farincikin da take ciki ,sanda ta fadawa jawad kuwa ji tayi Kamar ma yafi fita murna sai adduar samun nasara yake mata ,Yauwa pookie Anjima da laasar su baffa zasu zo kawo kudin auren mu inshallah ,and also next week zamu tafi umrah dasu Anty Hajara ,ah lalle love Wannan satin dai namu ne abubuwan alkairi left right and centre Allah ya kaimu lafiya .
A yammacin ranar, Nuwayrah ta shiga shirin tafiya gidansu ƙawarta Salima Gambo, Yau Henna Party na yayar Salima. Ta ci kwalliya cikin laffaya wadda ta amshi surar jikinta, glass dinta na Makale a fuskarta ,har ta manta rabon ta da zuwa biki ,dangin mama duk suna Bauchi ,dangin abba kuwa suna Zaria shiyasa takan dade bataje biki ba ,Tana Chan Wajan henna party iyayen jawad suna gidansu Ana sa rana .
Suna tsakiyar hirar , wayar Nuwayrah ta fara ruri. Ganin sunan Jawad ❤️ ya sa ta sakar murmushi
“Pookie!” Muryar Jawad ta fito cike da farin ciki. “An sa ranar auren mu pookie nanda wata hudu inshallah zaki zama Mrs jawad Komai ya tafi daidai.
Nuwayrah ta ji wani sanyayyen farin ciki ya ziyarci zuciyarta. “Alhamdulillah, Love ,am so happy can’t wait to be called Mrs jawad
Salima Gambo da ke tsaye a gefenta tana sauraren komai, kawai ta fincike wayar daga hannun Nuwayrah cikin wasa . Ta saka a kunnenta tare da ɗaga murya
“Jawad Ango ,nice na fara maka congratulations,kuma ka Kira a daidai yanzu aka gama yiwa amaryar ka henna hannu da kafa and she looks so beautiful dan haka ka tura kudin lalle
Daga ɗayan ɓangaren, Jawad ya yi wani 'dan jim na 'yan daƙiƙu—kamar yadda ya saba idan wani al'amari na kuɗi ya gitta masa ba tare da ya yi kasafi a kai ba. Muna godiya salima ,yanzu nan zan tura mata kuɗin henna din ba damuwa
Salima ta maida wa Nuwayrah wayar tana mata gwalo cikin dariya
,Haba salima menene haka Kamar wata karamar yarinya ?yanzu ay sai ki saka yayi zaton nice nace ki tambayeshi gaskia bana so kar ki Kara min haka ,a sanyaye salima ta dafa kafadar nuwayrah ,am sorry Mimi ban zaci ranki zai bace ba hakan be zai Kara faruwa ba inshallah.suka koma aka cigaba henna party .
Kafin magrib ta fara shirin komawa gida Sabida bata driving din dare duk da gilashin ganin hanya da daddare na mutukar bata wahala ,
Tana shiga gidan, ta Sami gidan cikin wani irin shiru mai nauyi. Mama ta samu ranta ɓace—sai mita take ita kaɗai Akan yadda kudin sukayi kadan a Wannan zamanin da ake ciki iya sadaki ma kawai 150k minimum .wannan ay harkar tsiya ne cewar mama tana hararar nuwayrah Kamar ita ta kawo kudin sum sum ta gaishe da maman ta wuce daki dan a yadda taga ran mama ya bace yanzu zata dawo kanta
kamar yadda Sadiq ya saba, ya shigo ɗakin Nuwayrah yin hirarsu ta dare . Nuwayrah tana zaune a kan keken dinki tana aikin project ɗinta na makaranta, yayin da Sadiq yake zaune a gefen gado yana duba hotunan Henna party da ta ɗauka a cikin wayarta.
Suna cikin haka, sai ga notification na shigar kuɗi (credit alert notification) ya bayyana ta samun wayar.
Idanun Sadiq suka faɗa kan adadin kuɗin da ke rubuce a jiki: N3,000. Ya bude idonsa cikin tsananin mamaki yayin da yake karanta bayanin da ke jiki:
Transaction Narrative: Kudin Henna
From: JAWAD SULEIMAN
“WTF? Sadiq ya furta da ƙarfi cikin al'ajabi, ya mike daga kan gadon.
Nuwayrah ta tsayar da ɗinkinta ta juyo tana kallonsa. “Lafiya Yaya? Mei ya faru?
3k Jawad ya tura miki matsayin kuɗin Henna, Mimi?! Wani irin marowaci ne shi?” Sadiq ya tambaya yana ware idanunsa cike da takaici.
Nuwayrah ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ta juyo ta ci gaba da dinkin ta . “Kai Yaya... I thought wani abun ne daban ya ba ka tsoro. Abin da yake da shi ne ya bayar ay
Shut up, Mimi Sadiq ya daka mata tsawa cikin ɓacin rai. “A karon farko yau na yarda da maganar Mama! N100k fa kadai ya bayar matsayin kuɗin gaisuwa, da sa rana ,sadaki kuma N100,000—are you this cheap? Kuma mutumin nan ya fi ƙarfin waɗannan kuɗaɗen nesa ba kusa ba. Why is he being so stingy to you? yaushe rabon danaje dauren aure naji sadaki 100k a 2026 din nan ?
Nuwayrah ta tsaya da dinkin , ta zuba ido tana kallon Yaya Sadiq yayin da zuciyarta ke harbawa
“Yaya, please don’t make a big deal out of nothing! Shi ba marowaci ba ne kamar yadda kuke tunani... Ku ne kawai kuke ganin haka, Nuwayrah ta faɗa cikin rawar murya tana ƙoƙarin kare jawad .
Sadiq ya nade hannayensa a ƙirjin sa, ya kafe ta da idanunsa cike da mamaki . “Me ya taɓa ba ki tunda kuka haɗu? Ya taɓa sa miki credit a waya? Ko ya taɓa siya miki wani abu anything? Faɗa min mana, ina jinki
Shiru Nuwayrah ta yi. Ta sunkuyar da kanta ƙasa tana cizon leɓenta , tabbas ta sani sarai a maganar gaskiya—babu wani Abu ɗaya na kyauta da ya taɓa shiga tsakaninta da Jawad tun haɗuwarsu.
“Look, Mimi,” Sadiq ya furta cikin sanyin murya, “Ihsaani yana da daɗi a soyayya . Idan har tun kafin ku yi aure yana miki irin wannan rowar, me kike tunanin zai faru bayan Kunyi aure ? Irin su Jawad ne masu barin matansu da duk wani nauyi da responsibility na gida. ki sake tunani mimi ,idan sabida aikin gidan yayi miki yawa ne zan kawo mai aiki duk abinda mama zata sai dai tayi.kar dan kinga qawayen kina ta aure kice kema dole sai kinyi yanzu ,duka duka shekarar ki 24 fa mimi .
Nuwayrah ta ɗaga kanta da sauri, Yaya, me kake nufi? Na rabu da Jawad saboda kawai ba shi da sakin hannu sosai? I am a hardworking woman! Zan iya ɗaukar nauyin kaina .tunda na gama secondary nake dinki ni ba cima zaune bace dan haka ba ruwana da wata rowarsa
Mimi... are you this desperate?
Yes, I am Nuwayrah ta amsa da ƙarfi, hawayen takaici na zuba a Idonta . “Maza nawa ne suka zo da niyyar aurena suka gudu? Jawad ne kaɗai ya tsaya ! Ba shi da wani aibu illa wannan so-called rowar da kuke magana a kai kuma zan iya canza shi You can call me desperate, I don't care! It's my love life, not yours ba ruwanka da rayuwata yaya sadiq .jawad na zaba kuma shi zan aura period.
Wani murmushi mai ciwo Sadiq yayi Ya ɗaga hannayensa biyu alamar saduda.
“Thank you da kika tunatar da ni cewa love life ɗinki ne ba nawa ba..Allah ya tabbatar muku da alheri , ya juya, tare da buga ƙofar ɗakin da ƙarfi .
kuka Nuwayrah ta fashe dashi a tsakiyar dakin .