Free chapter · Read without an account
4
Motocin masarautar Zarqana sun bar iyakar masarautar tun da sassafe.
Hanyar zuwa Indara tana da nisa, amma kyawun wuraren da suke wucewa ya sa tafiyar ta yi kama da mafarki.
Manyan tsaunuka sun yi layi a nesa.
Koguna suna kyalli ƙarƙashin hasken rana.
A gefen hanya kuma akwai ƙananan garuruwa masu cike da mutane, kasuwanni da gidaje masu ban mamaki.
Amma duk wannan bai hana Azeem tunanin takardar da aka ba shi ba.
Ya sake cire ta daga aljihunsa.
“Azeem ba ɗan wanda yake tsammani ba ne.”
Ya karanta kalmar sau uku.
“Wannan ba zai yiwu ba…”
“Me ba zai yiwu ba?”
Azeem ya ɗago kai da sauri.
Liyana ce.
Ta zauna a gefensa ba tare da ya lura ba.
Ya ninke takardar.
“Babu komai.”
Liyana ta yi murmushi.
“Har yanzu?”
“Har yanzu.”
“Ka san me?”
“Me?”
“Idan ka ci gaba da cewa babu komai, zan fara tunanin cewa ni ce matsalar.”
Azeem ya kalleta.
“Ke?”
“Eh.”
“Ba za ki iya zama matsalata ba.”
Liyana ta yi shiru.
Kalaman sun fito daga bakin Azeem ba tare da ya shirya ba.
Sai ya gane abin da ya faɗa.
Liyana kuwa ta sunkuyar da kai tana ɓoye murmushi.
“Ka maimaita.”
“Me?”
“Abin da ka ce.”
“Na ce… ba za ki iya zama matsalata ba.”
“Na ji.”
Ta ɗago kai.
“Amma ban ji dalili ba.”
Azeem ya yi murmushi.
“Wata rana zan gaya miki.”
“Na riƙe ka da wannan alkawarin.”
Idanunsu suka haɗu.
A wannan lokacin, duniya ta yi kamar ta tsaya.
Amma a bayan motar…
Nadira tana kallonsu ta gilashi.
Hannunta ya matse mayafinta.
“Ba zan bari hakan ya faru ba.”
Saboda nisan tafiya, tawagar ta tsaya a wani babban masaukin sarauta da ke kan iyakar Indara.
An shirya liyafar dare domin baƙin da suka zo daga Zarqana.
Kiɗa mai laushi ya cika lambun.
Fitilu sun haskaka bishiyoyi.
Matan Indara sun sanya kayan ado masu ban sha’awa, yayin da maza suka taru suna gaisawa.
Liyana ta fito sanye da wata riga mai launin shuɗi mai kyau.
Azeem da ke tsaye kusa da ƙofar ya kasa cire idanunsa daga gare ta.
Wani ɗan uwansa ya zo kusa da shi.
“Yarima…”
“Hmm?”
“Idan ka ci gaba da kallonta haka, kowa zai gane.”
Azeem ya ɗan yi murmushi.
“Me za su gane?”
“Abin da kai kanka ba ka yarda ka kira shi da suna ba.”
Azeem ya yi shiru.
Sai ya kalli Liyana.
Soyayya?
Wataƙila.
Amma ya ji tsoro ya kira ta da wannan suna.
Saboda rayuwarsa ta riga ta cika da sirrika.
Bai san ko soyayya za ta zama mafakarsa…
ko kuma wani makamin da za a yi amfani da shi a kansa ba.
A ƘARƘASHIN ITACEN INDARA
Liyana ta fita daga liyafar domin samun iska.
Ta tsaya ƙarƙashin wata babbar bishiya.
Sai ta ji muryar Azeem.
“Kin gudu daga liyafa?”
Ta juya.
“Ba na gudu.”
“Me kika kira wannan?”
“Na zo ne in sami natsuwa.”
Azeem ya matso.
“Me ya dame ki?”
“Ba komai.”
“Kin koya daga wurina kenan.”
Liyana ta yi dariya.
“Wataƙila.”
Sai wani iska mai ƙarfi ya kaɗa.
Mayafin Liyana ya kusa tashi.
Azeem ya riƙe shi kafin ya faɗi.
Hannunsu suka taɓa juna.
Dukansu suka tsaya.
Azeem ya kalli hannunta.
Sai ya kalle ta.
“Liyana…”
“Hmm?”
“Idan na gaya miki cewa ina tsoron wani abu…”
“Zan tambaye ka me kake tsoro.”
“Idan na ce ina tsoron rasa wani…”
Ta yi shiru.
“Wane ne?”
Azeem ya kalleta kai tsaye.
“Ke.”
Liyana ta kasa motsi.
Zuciyarta ta buga.
Amma kafin ta samu damar amsawa—
Sai aka ji ƙarar gilashi ya fashe daga cikin gidan.
Azeem ya juya da sauri.
“Ki tsaya nan.”
Ya ruga cikin gidan.
Liyana ta bi shi.
Da suka isa babban ɗakin liyafar, sai suka ga mutane suna ihu.
A tsakiyar ɗakin…
Sarki Rayyan yana kwance a ƙasa.
Kwalbar abin sha tana gefensa.
Nadira ta durƙusa kusa da shi.
“Mai Martaba!”
Azeem ya ruga wurin mahaifinsa.
“Baba!”
Sarki bai amsa ba.
Azeem ya ɗago kai.
“Ku kira likita!”
Duk mutane suka firgita.
Sai wani mutum daga cikin tawagar ya ce:
“An saka masa guba!”
Shiru ya mamaye ɗakin.
Azeem ya kalli kwalbar.
Sai ya kalli Nadira.
Nadira kuma ta kalli Liyana.
A idanunta akwai wani abu mai ban tsoro.
Ta nuna Liyana da yatsa.
“Ita ce ta kawo abin sha!”
Liyana ta zaro ido.
“Me?”
“Na gan ki kusa da teburin Mai Martaba kafin ya sha.”
“Ba ni na—”
Azeem ya tsaya tsakaninsu.
“Ki yi shiru!”
Nadira ta yi murmushi a ɓoye.
Domin shirin da ta shirya…
ya fara aiki.
Amma ba ta san abu ɗaya ba.
Daga ƙofar ɗakin, wani mutum yana kallon komai.
Mutumin da ya dawo bayan shekaru goma sha biyu.
Ya kalli Nadira.
Sai ya yi murmushi.
“Har yanzu kina yin wannan kuskuren…”
Ya rada.
“Kin manta cewa ni na san duk dabarunki.”