Free chapter · Read without an account

Chapter 13

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??

BOOK 1

Umma Mustapha

PAGE 13

"Monday tushen aiki, ko bature na tsoranki."

Da safiyar Litinin, wajen ƙarfe tara da arba'in, Nihla ta gama shirinta tsab.

Doguwar rigar atamfa ta saka mai adon ja da baƙi. Ta yi kyakkyawan ɗaurin dankwali wanda 'yan Najeriya suke wa lakabi da Zarah Buhari, sannan ta ɗauko baƙin mayafi da baƙar jaka. Takalmin da ta saka ma baƙi ne.

Ta buɗe aljihun akwatinta, ta zaro kuɗi kusan dubu goma, ta zira su cikin jakarta. Wayarta da power bank ma ta saka.

Ta sake kallon kanta a madubi.

Tsab ta fito, ta yi kyau sosai, kamar ka saceta ka gudu.

Da ta fito, sai ta nufi ƙofar ɗakin Shukura ta tsaya tana bugawa.

Ba daɗewa ba, Shukura ta buɗe ƙofar ta fito.

Ita ma ta shirya cikin doguwar riga ta kanti.

Tun daren jiya Nihla ta roƙi Shukura cewa idan za ta shiga makaranta, ta yi mata magana su tafi tare, domin ita ba ta san hanyar ba.

Shukura ba matsayin karatunsu ɗaya da Nihla take ba. Ita yanzu tana Level 2, yayin da Nihla a yanzu take shiga Level 1.

Tare suka rankaya suka fice daga gidan.

Bayan sun yi ɗan tafiya, suka samu abin hawa da ya kai su bus stop ɗin da ke bakin hostel ɗin Asma'u Sa'id.

Da suka isa wurin, suka tarar da bus ɗin da ke jigilar ɗaukar ɗalibai ta cika. Don haka suka jira wata bus ɗin ta zo.

Shukura ta buɗe jakarta, ta zaro tikiti guda biyu. Ɗaya ta riƙe a hannunta, ɗayan kuma ta miƙa wa Nihla.

Nihla ta karɓa tana kallonsa.

Shukura ta yi mata bayani:

"Dole sai kin bayar da wannan tikitin kafin ki samu damar shiga bus ɗin."

Nihla ta gyada kai.

Sun tsaya, kowa ya hau layi kamar masu jiran sadaka. Layin maza daban, na mata daban.

A haka har wata bus ɗin ta zo. Direba ya fito ya fara karɓar tikiti.

Har aka zo kansu, suka miƙa nasu, sannan suka shiga cikin motar.

Nihla ta ja ta tsaya tana zare ido. Komai baƙo ne a wajenta, musamman da ta ga kamar duk mutanen da ke cikin motar ita suke kallo.

Ta ɗan sunkuyar da kai, sannan ta kalli Shukura.

Shukura da ta lura da yadda Nihla take ji, sai ta ce mata a hankali:

"Nihla, ki shige ciki ki zauna."

Nihla ta bi umarninta.

Ta shiga ciki ta zauna a jikin window.

Shukura kuma ta zauna kusa da ita.

Ba su daɗe da zama ba, sai wani namiji ya zo ya zauna a gefensu.

Direba ya shiga ya zauna, ya ja motar, aka fara tafiya.

Hayaniya ta cika motar. Masu surutu suna surutunsu, wasu kuma suna tsokanar Baba Direba. Shi ma ba laifi, yana wasa da raha, shi ya sa yake da farin jini a wurin ɗalibai.

A haka dai har suka ƙarasa cikin Jami'ar Sule Lamido.

Baba Direba ya yi parking a inda sauran bus ɗin suke parking. Kowa ya fara haramar fita daga motar, su Nihla ma suka biyo ayarin masu fita.

Shukura ta yi wa Nihla ƙoƙari sosai, domin sai da ta raka ta har gaban office ɗin Dr.Nasir.

Ta ce wa Nihla:

"Ki ba ni number ɗinki. Idan mun gama da wuri, ki yi min magana sai mu tafi tare."

Nihla ta yi mata godiya sosai.

Shukura ta juya ta tafi, ita kuma Nihla ta tsaya a bakin office ɗin. Har yanzu ta kasa shiga, kamar a tsorace take da komai.

Hannu ta ɗaga a hankali tana ƙwanƙwasa ƙofar.

Amma shiru, ba a buɗe ba.

Ta sake buga ƙofar, amma har yanzu shiru.

Tana ƙoƙarin fito da wayarta domin ta kira shi, kawai sai ta ga an buɗe ƙofar.

Wata budurwa ce, shekarunta za su zo ɗaya da Nihla, ta buɗe ƙofar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta ce wa Nihla:

"Shigo."

Ta juya tana cewa:

"Yaya Nasir, ko wannan ce baƙuwar taka?"

Dago fuskarsa ya yi daga kan computer ɗin da ke gabansa, yana kallonsu.

Nihla ta gaida shi.

Ya amsa, fuskarsa a sake.

Ya nuna mata kujerar da ke gabansa ya ce:

"Zauna."

Nihla ta zauna.

Fatima, wadda take tsaye, ta buɗe fridge ɗin da ke cikin office ɗin. Ta ɗauko ruwa da lemo ta ajiye wa Nihla a gabanta.

Sannan ta nemi kujerar da ke kusa da Nihla ta zauna.

Dr. Nasir ya nisa, sannan ya fara yi musu nasiha, yana nuna musu muhimmancin abin da ya kawo su. Ya shawarce su da su mayar da hankali sosai a kan karatunsu.

Sannan ya gabatar da Fatima ga Nihla.

"Nihla, ga Fatima nan. Daga yanzu kun zama kawaye, tunda course ɗaya za ku karanta.

"Fatima kanwata ce, ke ma kanwata CE tunda Kanwar abokina ce. Don Allah ku mayar da hankali a kan karatu, kar ku zauna kuna wasa.

"Duk abin da ba ku gane ba, ko abin da zai ba ku wahala, ku zo wurina. Zan yi ƙoƙarin taimaka muku."

Daga haka ya sallamesu.

Fatima ta kasance kanwa ce a wurin Dr. Nasir. da mamansa da mamanta, uwa ɗaya, uba ɗaya suke.

Fatima ta ba Nihla timetable da sauran abubuwan karatu.

Daga nan suka fara shiga lecture ba wasa. Sun mayar da hankalinsu sosai. Ba sa kula kowa, kuma ba sa shiga harkar kowa.

Bayan Shukura, wadda suke ɗan gaisuwar mutunci, Nihla ba ta sake wata kawa ba.

Umsar ✍️ 
***



Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol