Free chapter · Read without an account
Chapter 26
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 26
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
Tana ƙoƙarin ƙarashe maganarta aka yi kiransa a waya, idanunsa a kanta, yana karantar yanayinta, har wayar ta tsinke, aka sake kira ya ɗauka ganin kira ne daga boss nasa, nan aka basa umurnin komai yake yi ya bari ya taho, ya amsa da to cikin girmamawa, aka katse wayar, cikin sanyin jiki ya kalleta ya ce
"I'm sorry Angel, kiran gaggawa ne, amma nayi miki alkawarin zan saurare ki, ko na taho Tumbin Giwa ko kuma a waya. I hope ba matsala?"
Ta girgiza masa kanta alamun a'a ba matsala, ya miƙe, ya ce
"Na tafi"
"To"
Ta faɗa cikin sauri ya bar wajen, ta sauke numfashi, nan take zuciyarta ta soma bugawa, jikinta yana rawa a hankali, me take shirin aikatawa ne? Me yasa zata sanar da shi? Ya zama dole ne ko bai zama dole ba?.....
Rashin samun amshoshinta yasa ta miƙe, ta dawo bakin titi ta tari mashin ta hau zuwa Tumbin Giwa, ta main gate ta shigo, gidan a cike yake da mutane mata da maza manya da ƙanana. Kowa sha'aninsa yake babu ruwan wani da wani. Tana shigowa bangaren sakiya kuma warin sigari da wiwi ne suka yi mata maraba da zuwa ta tashe hancinta, taƙi jinin warin sigari kwata kwata, kamar ta yi amai ta samu ta wuce.
Tana shigewa ƙaramin ƙofar da ta yi musu iyaka da wajen, taga wani tashin hankalin, kaɗan bucket na ƙarfe ya sameta, saboda yadda aya wulwula aka jeho shi, ta yi gefe tana kallon ikon Allah, maza da mata ne a tsaye a filin gurin wasun su na kwasan dambe, Shamsu Neegah ne ya ɗebo wata asha ya jefawa Sadeebaby tare da cewa
"Haka mu ka yi? Na ce don ubanki haka mu kayi? Na ɗauki makuɗan kuɗaɗe na baki, akan kina ɗakina har sati shi ne zan taddaki da Bala mayen mata, to wallahi ba zata saku ba, ko ki dawo min da kuɗi na ko kuma yau ayi wacce za ayi"
"Na rantse maka Shamsu Neegah zan yi maka rashin mutunci, wasa ma da wasanta banda zagin uwar miji, kana sake cewa don ubana sai naga waya tsaya maka a barikin nan"
Shamsu Neegah ya yi baya cikin ɓacin rai da takaici yana kallon fuskar da tasha bleaching ta koshi har ta soma kodewa ya ce
"Aiko za ki ga abin da nake takama da shi, mara mutunci kawai, me cin amana"
Ta daka tsalle tana cewa
"Yo ashe kai karamin kwaro ne, wa ya faɗa maka bariki na da amana, na bi Bala mayen mata saboda ya fika iya....
Kan ta karasa maganar ta, ya yo kanta ya cire belt na wondonsa ya soma zabga mata, tana ihu tana zaginsa, ba irin ashar da baya fitowa daga bakinta shi kuma bai fasa zabga mata belt ba, yaba riƙe da bakin wondonsa da yake ƙoƙarin suɓulewa saboda rashin belt da ya riƙe masa kugu, abin mamaki wasu suna zaune a wajen harkar gabansu kawai suke yi masu caca suna yi, ƴan Lido da ƴan karta. Zee Dollers ce ta iso ta riƙe belt ɗin ta shiga sakaninsu ta tsaya tana cewa
"Kutmar buro uban nan, ni Zee Dollers yau naga abin mamaki, Sadeebaby kina zaune shirgegen gardi yana jibgarki kamar jaka, yaushe ki ka yi araha har haka?"
Sadeebaby da ta sha na jaki ta mik'e da ƙyar jiki ya yi la'asar ta ce
"Kyale sa don ubansa ai ya daki kuɗin sa, na rantse sai ya yi nadamar dukana da ya yi"
"Kutmar uban nan, aiko wallahi ba ki isa ba, kuɗaɗena suna nan kuma sai kin yi min aikinsu"
"Ai sai mu gani in ana dole"
Waje ya kauraye da hayaniya, me bakin sigari ya fito yana cewa
"Haba mana guys me ye haka? Be wise mana ya muna saka da nishaɗi za ku zo kuna yi mana shouting a ka"
"To sannu Babayo sarakan shan sigari, kada ka shiga harkata don ba zai yi maka daɗi ba"
"Ke shashasha karuwa kawai har kina da wata harka da za a shiga, kada ya yi min daɗi, haka kurum kun hana mu hutawa kuna ta yi mana hayaniya"
Shamsu Neegah ya ce
"Dakata Babayo wannan sakanina da Sadeebaby ne kada ka shiga kamar yanda ta faɗa maka"
"Yo Allah na tuba, kai Shamsu Neegah ai tasha da kai, kai ba kuɗi ba kuma ba harka ba"
"Allah bata sha ba sai ta dawo min da kuɗi na"
Dariya me bakin sigari ya yi ya ce
"Kan ku ake ji"
Ya bar wajen har Bala mayen mata ya shigo, nan fah sabon tashin hankali......
Angel da idanunta suka ciko ƙwalla sabar takaici da bakin cikin abubuwan da suke faruwa a gidansu, wannan wane irin tashin hankali ne? Ta shigo ɗaki ta sauya kaya ta fito ta tadda ana sasanta lamarin, ta yi ficewarta......
*********************************
ALAJA SPECIAL RESTAURANT
ALAJA ganin Bilqees ba ta jin daɗin jikinta hakan yasa bata takureta sai ta yi aiki ba, ita da kanta ta dinga zirga-zirga don ciwon da ta ji ya sanya mata zazzaɓi, ta sha magani ta kwanta. ALAJA ta shigo kitchen ta tadda su Laraba sai faman aiki suke yi, bata ce dasu komai ba, ta fice Jummai ce ta ce
"Laraba yau fa ina cike da son naga na ɓata sakanin Alaja da Bilqees"
"Ai ni ma abin yana raina, kwana biyu nan sai wani ji da ita take, faɗa min me za ki yi mata?"
"Ai abin da muka saba yi mata shi za mu yi, kin san ALAJA bata son abin da zai yi interrupting customers nata, to shi za mu yi wa ƴar gaban goshin ta, ta sille mana ita"
"Hakan ya yi daidai, sai dai shashashar da za ta yi mana aikin ne yanzu ta zama ƴar duniya, ko ya za mu yi"
"Ta isa! yadda muka fara tare haka zamu ƙarashe a tare"
Majada ta shigo kanta yana fuzga, tana ɗan dube dube Jummai ta ce
"Ke Majada zo nan?"
Sai da ta ɗan sha ƙamshi sannan ta iso tana cewa
"Ya aka yi ne manyan Aunties"
"Ke bama son rashin kunya da futsara, mu sa'annin wasan ki ne?"
Cewar Laraba, Jummai ta ce
"Kyale mana, wani sabon iya shege irin na ƙananan ƴan iska take mana"
"Oh ni Majada ina ganin kaina, kun ce bana girmamaku, to yau na girmama ku shi ma ya zama laifi, to ya kuke so nayi?"
Laraba ta zauna da kyau ta ce
"To mara kunya, aiki za ki yi mana"
"Aiki akan waye?"
"Akan ƙawarki mana"
Cewar Jummai, Majada ta ce
"Chabɗi jam, Allah ba zan yi ba, ina da abin yi"
"To ko don ubanki sai kin yi mana, kada ki ga muna binki da lallami"
Cewar Laraba, Majada ta turo baki tare da cewa
"Yau ina da AP a hotel za ku katse min jin daɗi"
Dariya Laraba da Jummai su ka yi, suna tafawa tare da taɓe baki, Jummai ta ce
"Su AP manya, to mu dai aiki ba fashi, dole ki yi mana, kuma ki tabbatar kada a sami matsala"
"To na ji amma dai za a sallame ni"
"Wannan ba matsala bane, kwantar da hankalin ki a gama tukuna"
"To Allah ya kai mu daren"
Ta fice ta basu waje, suna ci gaba da zaginta suna aiki ko a jikinsu, suna sake shawara akan yadda abin zai kasance, so suke yau ALAJA ta hassala da yawa, ko ma ta sallami Bilqees daga aiki a restaurant....
******
Bilqees ta samu ƙarfin jiki, ta tashi ta fito domin ta duba me za ta shiryawa Yallaɓai likita na abincin dare, ta iso kitchen ta soma dube dube duk abin da ya dace ta shirya masa, ta ajiye, har zuwa lokacin da suka shigo, a nutse ta wuce kitchen ta haɗa masa ta fito dasu, kai tsaye ta iso inda yake zaune kamar kullum ta hau shirya masa, tare da cewa
"Sannu da zuwa Yallaɓai likita"
"Sunana Abdulwahab ba Yallaɓai likita ba"
Ta ɗan kallesa duk da hankalinsa yana kan waya, ta ce
"Ai ina yi maka aiki ba zayyu na kira ka da sunanka ba"
Ya ɗan ɗago ya ce
"A'a ban son wannan sunan"
"To"
"Ko kuma ki kira ni da yaron ki"
Ta ɗan waro idanuwa waje har yasa ya ɗan kalleta sai kuma ya kai da kansa, ya ji ta ce
"Ɗana kenan?"
Murmushi ya yi ya ce
"Eh mana"
"A'a Yallaɓai"
"Kin sake faɗi kenan"
Murmushi ta yi, ta ce
"Tuba nake yi"
Ta kammala shirya masa, tana ƙoƙarin barin gurin ya ce
"Mommie nah"
Ta daka tare da cewa
"Na'am"
"Ina Mamanki"
Ta ce
"Tana gida"
"Ok ya yi kyau, yaushe zan ganta?"
Ta ce
"Gidan mu za ka je?"
"Eh mana ko za a yi min rowar gida ne?"
"A'a"
T faɗa a hankali, ya ɗan ɗago tare da cewa
"Za mu yi magana gobe"
"To"
Ta faɗa ta bar wajen, ya sauke numfashi, yana ya yi magana da mahaifiyar...
Dr Faisal ya iso wajensa yana yi masa wasu bayanai sannan ya bar wajen.
********
Laraba da Jummai kam sun shirya tsaf saura su aiwatar da abin da su ka yi niyya, da ƙyar suka samo Majada, ta iso suka bata mai kamar yadda take yi suka ce ta yi, ta tabbatar bayan ta zuba man ta gobe in da Bilqees ta taka, don kada a gane, ta ansa, Bilqees ta shigo kitchen, ta wuce ciki store, Majada ta je da sauri ta zuba man, ta dawo, suna jiran fitowar Bilqees ta taka, sai kawai ga ALAJA ta shigo tana
"Wai ku sabar mugun hali, ba za ku aika min abinci ba, yunwa nake ji"
Suka soma zazzare idanu, suna kallon juna, da Alamu a lokacin da Alaja ke ƙoƙarin shigowa bata ankare da mai ba wanda Majada ta zuba, ta wuce Bilqees ta fito daga cikin store tana kirgawa Alaja abubuwan da za a buƙata washegari don tarɓan customer's, ALAJA ta ce
"Ki koma ki sake dubawa ga biro da takarda sai ki rubuta"
Ta miƙa mata, Bilqees ta shige cikin store Alaja ta fito ta sake taka man cikin rashin sani ta yi dining area, Majada da Laraba da Jummai suka ɗaura hannu aka, cikin ransu suke cewa
"Mun shiga uku, ALAJA ta taka mai"
Cewar Laraba, Jummai ta ce
"Shikenan ta faru ta ƙare, watan tsaida albashina ya kama"
Laraba ta ce
"Ai cewa za ki yi kashin mu ya bushe"
"Wayyo Allah na! Na shiga uku kun jefani cikin bala'i da masifa"
Cewar Majada, lokacin guda suka ruɗe hankalin su ya tashi, suka leƙa suka ga ALAJA ta taka mai da gajeren ƙakafunta waɗan da ta saka musu flat shoes marasa nawi, sanye take da doguwar riga iya ƙasan gwiwarta kaɗan, ta sanya hula me tambarin RESTAURANT nata, sannan ta ɗaura farmala a saman doguwar rigarta na wajen aiki.
Ta doso cikin dining area, Majada ta goge inda ta zuba mai kuma Alaja ta taka cikin sauri take yi don kada a ganta, aiko tsantsi ya kwashi Alaja sai da ta yi sama sannan ta dire ƙasa, mazaunan ta suka ji zafi ta ƙwala ƙara sabar azaba ta ce
"Oh my God! La'ilaha'illallah, wetin be this woo?"
Hakan yasa yawanci hankalinsu ya koma kanta saboda ƙara da ta yi, da kyar taja jiki ta koma da baya, don kada hankalin sauran ma ya dawo kanta, a lokacin Bilqees ta ƙaraso ciki don ta kai mata takarda da biro, ta tadda Alaja riƙe da kugu tana jin jiki, ganin abin da ke faruwa, yasa cikin tsaro da tashin hankali ta ce
"Maaaaaa"
Ta yi sauri ta ƙaraso ta riketa tana yi mata sannu, Alaja tana amsawa da ƙyar, sabar azaba da wajen ke yi mata, ɗakinta Bilqees ta taimaka ta kaita, da ƙyar Alaja ke iya tafiya har suka shigo ɗakin ta zaunar da ita ta ce
"Sannu Maa"
"Yawwa Bilqees, yau dai abin da ya taɓa faruwa dake ya same ni"
"Sannu Maa"
"Ah ohh! Kai naji faɗuwar nan sosai"
"Maaa me kike buƙata?"
"Barni tukuna na dawo daidai, wai wasu shashashashu ne suka zuba ruwa ba su yi mopping ba, na faɗi?"
"I don't know Maa"
"Bani ruwa"
Bilqees ta miƙa mata ruwa ta sha, tana sauke ajiyar zuciya don wahala, Bilqees ta fito dining area ta tadda kowa ya koma normal yana ci gaba da cin abinci, ban da Yallaɓai likita, ban da shayin gargajiya ba abin da yake ci, ta wuce wajen Dr Faisal ta tambaye matarsa ko tana buƙatar wani abin, amma ta ce a'a, ta dawo wajen Yallaɓai likita ta ce
"Yallaɓai sannu da cin abinci"
"Yawwa sannu Mommie nah"
"Kana buƙatan wani abu ne?"
"A'a Alhamdulillah na gode"
"To"
Ta koma in da ALAJA ta faɗi ta duba, taga kamar babu komai, sai kuma taga shatin ƙafar takalmin ALAJA a wajen kamar an zana, ta rage tsawonta ta taɓa da hannu taga mai ne, da mamaki ta sake lakutawa tana sake tantance wa, tabbas mai ne, ta mik'e ta bar wajen, tana mamaki garin yaya ALAJA ta taka mai.....
Customers suka fara watsewa, su Yallaɓai likita suka tafi, ALAJA ta ce kowa ya watse, aka watse ya saura daga ita sai Bilqees ta ce
"Bilqees ɗauko min laptop nawa"
"To Maa"
"Bilqees ta kawo"
ALAJA ta ce
"Buɗe min"
Ta kunna, sannan ta miƙa wa ALAJA shi, ta karɓa ta shiga inda haɗa da CCTV ta yi connecting, a hankali take bi take duba wa, saboda tantama da tayi, akan faɗuwar Bilqees da kuma nata, meye ya jawo haka?"
Majada ta gani tana riƙe da wani roba a hannunta, tana zuba wa a wajen, ta sake dubawa sosai ta tabbatar da lallai abu ta zuba, to menene wannan abin? Ta duba ranakun da Bilqees ta faɗi suma taga Majada ce ta zuba abu, kuma ta goge bayan an taka, Alaja ta furta
"What? Majada!".....
Bilqees ta ce
"Maa menene?"
"Gashi ki gani"
Ta karɓa ta duba, taga abin da yake faruwa, daman duk faɗuwar da take yi shiryayyen abu ne, ALAJA cikin ɓacin rai ta ce su koma gida. Bilqees ta taimaka mata suka fito, masu tsaron wajen suka rufe ko'ina, a farfajiyar restaurant Bilqees ta shigo da me mashin ya ɗauke su ya dawo dasu gida....
********
DR Waahab ya iso Tumbin Giwa cike da tunani, gashi yana kiran number Angel baya shiga, tun da suka rabu da safe yake binta a ransa, yana tunanin me yake damunta? Me ya sameta take cikin damuwa, duk yanayinta ya sauya, jikinta a sanyaye.
Har wannan lokacin tunanin da yake yi kenan, ya sake kiran layin ta, a kashe har wannan lokacin, ya zauna a dakalin dake kofar ship ɗin da last zuwan sa ta ce ya su zauna, a nutse ya tura masa saƙon isowarsa, ya jima a zaune yana ganin giftawan mutane, da abin hawa, ya maida hankalinsa bakin gate na Tumbin Giwa yaga cike yake da mutane, ya jima yana kallon iya shege da ake yi a wajen, ya duba wayar sa yaga har yanzu ba tayi masa reply ba, ya duba time lokaci yaja sosai, yana ƙoƙarin tashi ya ji murya ta
"Uncle"
A hankali ya ɗago, ya kalleta, nan take farin ciki ya mamaye zuciyarsa, wani sanyi yaji cikin ransa, yana kallon idanunta da suke cikin niqabi, ya ɗan sauke numfashi, tare da cewa
"Angel"
A hankali ta ƙaraso kusa dashi, ta ɗan tsaya ya gyara zamansa tare da nuna mata ta zauna a dakalin da yake kusa da nasa, ta zauna cikin sanyin jiki, suna kallon junansu kowanne da abin da yake tunani cikin zuciyarsa......
______________________
Ayi hakuri da typing errors
Ga masu son su yi min gyara ko shawara ƙofa a buɗe take su yi min magana ta number na dake saman page. Ayi hakuri da abubuwan da ake cin karo dasu a cikin labarin, haka labarin ya zo kuma dole ne a faɗi wasu abubuwan, a hakan ma ina ɗan yin alkunya😂 amma ALAJA taɓararta ya fi haka 😃 Tumbin Giwa kuma... To😂
Ina godiya da kuka amshi wannan littafin da hannu bibbiyu, in sha Allahu ina mai tabbatar muku za ku ji daɗin wannan tafiyar amma sai kun yi hakuri domin tafiya ce me tsawo da saƙwanni🥰
Sayyada barrister's palace wannan page naku ne😍
Ayi comments sannan a tayani sharing fisabilillah