Free chapter · Read without an account
Page 04
by Ummu~Fadeela · JUYIN LAMARI
*JUYIN LAMARI*
By
*Ummu Fadeela*
*Page 04*
Gidanmu babba ne wanda zamu iya kiransa da estate. kafin malam Baraya ya rasu ya roki 'ya'yansa su zauna waje daya ko Allah zai sa kansu ya hade waje guda.
Dukkan Baffanni na sun tamfatsa manyan gine gine a cikin gidan kowa da bangarensa, a bangaren su Ya Abdul ma gidan sama ne hawa biyu amma kash.
Har yanzu bangaren babanmu ginin laka ne irin na zamanin baya. Gini ne da idan damuna ta kankama, kullum cikin fargabar zai iya ruftowa a kanmu muke kwana mu hantse. Ga wutar solar da tsabar yawanta har makota ke mora, amma da zarar duhun magariba ta gabato gidan Gadanga dai sai abinda fitilar aci bal-bal ko Obasanjo ya kasa yayi. Domin duk wata hanya da aka san hasken zai kai ga bangarenmu an toshe ta.
Tabbas wannan zumunci akwai Babbar gibi a cikinta.
*****
Duk maganganun da Innani take yi bana jinta, babban burina inje inga halin da uwata da Baba suke ciki. Yanayin da suka fita bai kwanta a raina ba.
Cikin sa'a aka yiwa Baffa Attajiri kiran gaggawa a waya ya fita, Abba da Baffa Mukhtar suka take masa baya.
Wannan ya rage yawaitar mutanen dake falon.
Cikin hanzari na mike har jikina yana rawa na nufi kofa, "Dawo marar kunya bamu gama dake ba"
Na juya na mata kallon tsaf nace, "takaicina da na mahaifina sai yayi ajalinki Innani, tunda baki ganin ni'imar da Allah ya miki. Ni da kike gani sai na zame miki Inuwar qaya.
A guje na fita ganin Yaya Tahir ya taso a fusace zai buge ni.
Sai da na daidaita nutsuwata na shiga bangarenmu.
Umma tana zaune ta baza tagumi, a kallon farko na karanto kololuwar damuwar dake kwance a fuskarta.
"Ummah kar ki damu kan ki a kan abinda Innani take mana. wannan ba sabon abu bane, kuma watarana zata dauki sakamakon ta da hannun hagu. Ai talauci ba hauka bane da ta mayar dake da Baba kwallon da take wasa dashi a kafarta".
"Dubulle kaso casa'in cikin dari na abunda jama'ar gidan nan ke mana, ke ce kike janyosa. Me ya sa ba za ki daina biyewa Abdul ba ko zamu samu salama uhmmm".
Kwantar da kaina nayi a gefen hannunta ina lumshe idanu Nace, "Kiyi mini addu'a Ummatah, soyayyar sa ce ke sarrafa ni har in kasa katabus a gabansa. A duk sadda ya umarce ni da aikata wani abu kuwa, na kan ji tamkar farillah ne a kaina da idan ban aikata ba Allah zai kama ni."
Shafa kaina tayi tace, Allah ga Halima, kai kadai ka san manufar wannan hadin, Allah a sassauta mata"
Sai ta kara da cewa, 'Kullum kina cikin addu'ata Dubulle, amma ki sani tarayyarki da Abdul ba abu ne mai dorewa ba, Ta dan ja numfashi. Tace,
Saboda iyayensa ba za su taba yarda da wannan zumuncin ba. A kan idanunki kin ga yadda ta kaya tsakanin yayarki Ikleema da Tahir, to inaga Abdul da akewa kallon tsoka daya a miya. Bata bari raunin dake zuciyarta ya bayyana ba.
Tana cigaba da shafa kaina tace, Ina miki fatan salama a rayuwa Dubulle, amma bana hango wannan salamar a tare da Abdul.
Duba dari biyu cikin jakata dake sakale a daki kiyi kudin mashin ki dubo mini lafiyar Ikleema. Kwana biyu bata kiramu ko a waya ba.
Kuma ki wuce mata da kurfotin can da na siya mata. Jiki a mace na mike kalamanta suna yawo a kaina na shiga daki.
Kamar yadda Umma ta fada cikin minti goma na fito cikin shiri nace, "Na tafi Umma"
Da a dawo lafiya ta amsa mini na wuce jikina duk ba karfi sakamakon maganganunta gareni.
Daga nesa na hangoshi tsaye yana rike da rails waya kare a kunnensa, da hanzari na janye idanuna lokaci daya gabana ya yanke ya fadi. Na kara saurin tafiyata lura da nayi ya yanke wayar yana kallona.
"Halima"
Na jiyo muryarsa a kusa dani.
"Halima!" Ya ambata a karo na biyu.
"Sunana"
Na amsa cikin murya mai karfi, na dora da.
"Kai yanzu Yaya Abdul baka ji kunya ba. Ba kaji kunyar tunkarata har kana ambaton sunana ba. Eh, wato ga Halima yar iska, an gayyato mutane sun sanyi ni da iyayena a tsakiya suna mana dibar albarka amma ka kasa bude baki kace ai dani Dubulle ke fitar dare, ni take rakawa. To sittin ta qur'ani Yaya ka fita a sabgata."
"Haba Dubulle me haka, ke wayace miki ana fadi in fada da manya? Ai idan babba yana magana shiru ake yi amma kowa a wajan ai ya san tare muke fita mu dawo tare uhmmm."
Shiru nayi ina jin yadda yake matsa yatsun hannuna da ya rike gam yana kallon tsakiyar idanuna da shanyayyun idanunsa.
"Plsss mana Dubun Umma da Abba".
Murmushi ne ya kufce mini ina kallon yadda hannunsa ke rike da nawa nace.
Cika ni to kar a ganmu haka a samu sabon update na tara ahalin Baraya gobe.
Dariya yayi yana sosa kanshi yace, "Dubulle akwai partyn Mus'ab fa anjima ya za'ayi ne.
"Ban zuwa"
Na katse shi tun bai karisa ba.
Ni kaga tafiyata gidan Anty Iklee zan je kada rana tayi.
Ina kokarin fita mota ta shigo hakan yasa na dakata saida suka gama shiga.
Ganin wadda ke motar ya sani daure fuska tamau na cigaba da tafiyata. Al'amin ne da Maryam, manyan yaran Baffa Attajiri. Babu jituwa tsakanina da Maryam bama taba shan inuwa guda har gwara Al'amin wani lokaci.
Ihun da na jiyo ya sani juyowa ala tilas.
Maryam ce tayi tsalle ta rungume Yaya Abdul suna murnar ganin juna.
Da kyar naja kafata na fita nayi sa'a adaidaita ya sauke fasinja a makwaftanmu na shiga ina sauke numfashi a jejjere.
******
Gabadaya mood dina ya sauya, duk na rufe idanuna hoton Maryam nake gani kwance jikin Ya Abdul suna dariya. Da sallama ciki-ciki na shigo gidan. Amaryar Anty Ikleema tana zaune bakin madafa tana jajjagen kayan miya muka gaisa, na shige falon Anty.
"Maraba da Dubulle yanzu nake tunaninku a raina ashe kina tafe."
"Kai Anty kina sha'aninki wai wannan tunkusar kishiyar taki ce ta zama haka, naga duk ta kanjame ta kwaile fuska da bilicin."
"Hoo Dubulle baki abun magana, yo ai tunkusar taji matsa ne tuni ta fitar da mai, ina jin dai laulayi take fama."
Rike baki nayi ina kwalalo idanu waje.
"Kai Anty amma dai mijin nan naku akwai fitina, gaki da tirtsetsen ciki, yau ko gobe ko shekara baki rufa ba ya auro wata har ya kunsa mata rabonta itama.
Ga can uwargidanku Maman Auwal ko wata biyu batayi da haihuwa ba itama Maman hassana mai bin uwargida da danyen goyo a bayanta. Kai wannan masifa har Ina."
Dakuwa Ikleema ta mini.
"Gidanku Dubulle, kuma ke kike ciyar damu hala.
"Gaskiya ce fa Anty sai na fada, yanzu haka idan za a tisa Baban Auwal bai san adadin yaransa ba a gidan nan."
Dariya Ikleema ta fashe da ganin nayi shiru ina baza idanu da dafe kirji.
A hankali na dan zamo daga kujerar Nace, "Barka da hantsi Baban Auwal ashe baka wuce kasuwa ba".
"Yau Halima ce a gidan namu lale maraba, ya kika baro mutanen gidan da Kowa".
"Kowa lafiya suna ma gaishe ki."
"Amma Anty Ikleema halinki bai yi ba, kin san mutumin nan yana dakin ki kika barni na saki baki ina jero zance ke nan." na fada ina mikewa na kara gudun fanka da wangale labule ko iska zai shiga dakin.
Na zauna ina fifita da hannu na tsabar yadda tsami da warin maza ya hana numfashina fita yadda ya kamata tun fitowar mijin Ikleema, nayi tsaki yafi dubu ace mutum yana hulda da mutane ga mata har hudu amma da ya gifta sai an rufe hanci.
To wai su basu san suna tsamin bane, ko matan basa fada musu.
"So kike Sauro su yi watanda damu Dubulle da kika wangale musu kofar? Cewar Anty Ikleema bayan dawowarta daga rakiyar mijinta.
"Kawai ban yadda da amincin iskar dake kadawa a dakin bane, na daga labule iskar Ubangiji ya shigo."
Kada kai tayi ta zauna muka dasa sabon hira, ina bata labarin irin rashin mutuncin da Innani ta mana yau.
"Hmmm wallahi ko Anty, duk ranar da Na samu dama sai mun bar gidan can. Zan ginawa Umma da Baba gida mu bar wancan gidan mai kama dana jaraba".
Da yake Anty Ikleema halin hakurin Umma da Baba ta dauko. Allah shi kyauta kawai ta iya furtawa taja bakinta tayi shiru sai damuwar da ya bayyana a fuskarta. Ta dan gyara zama tace.
"Ni yanzu damuwata bikin yar wajan kawu Lado da za'ayi a can Kura, na san sarai jama'ar gidan duka za'a je.
Anya Dubulle ba gwara mu hada baki mu hana Umma da Baba zuwa ba, yaushe ne ma bikin?"
"Furtawa kika rigani Iklee, amma ai babu fafutukar da ban yi ba na ganin na dakile shirin wannan tafiyar. Fafur Baba yaki, a karshe ma hadisan da ke magana a kan masu yanke zumunci Baba ya fara karanto mini, ala dole naja bakina na tsuke."
"Amma ina tabbatar miki da ni za'a bikin nan. Babu wani mahalukin da zan dagawa kafa a kan lamarin Uwa da UBA na ehee. Ina jin bikin ai bai fi kwana goma ba ya yi saura".
Nan gidan Anty Ikleema na wuni muna hira har magariba ta yi nayi sallah sannan nayi haramar tafiya.
Wayata tayi kara na duba Yaya Abdul ne. Tsaki naja na danne wayar sai da ta mutu ina jin tukukin bakin ciki yana ratsa ni.
Ganin yar'uwata ya sani mancewa da damuwar da na iso da ita na bakin cikin yadda Maryam ta rungumesa dazu, shi kuma ya wage baki yana ta dariya. "Mtssswww"
Na kuma jan tsaki a karo na barkatai.
Anty Ikleema dake mika mini kudin dan sahu ta bini da idanu tana tambayar.
"Lafiya kike Kam?"
A ƙofar gidan naja na tsaya ganin Yaya Abdul cikin shigar gayu yasha kyau sai kamshi yake yi jingine da motarsa yana karkada car keys a hannunsa.
Tasowa yayi yana kallona.
"Plsss Dubulle bana son jin kunya a wannan sabgar, ke kin san idan babu ke bana samun confidence a wajan partyn nan, kina fitar dani kunya gaban gayu. Shi ne nake son kicewa Umma gidan Ikilima zaki kwana, ni kuma inzo in tsara Iklee sai mu wuce kinga babu mai tuhumarki."
Tunda ya fara maganar na ke kallonsa a zahiri, sai da ya kai aya nace.
"Ya Abdul ban zuwa, kaje ka samu Maryam ta fitar da kai a kunyar".
Na juya na fara tafiya ba tare da na kalleshi ba.